[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 20 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A


CHAPTER 20
‘KOTU’

Kotu ta cika mak’il dan zan iya cewa duk zaman da sukeyi babu wanda al’ummah suka halarta sosai kamarshi,
Saboda sosai Alhaji Abu Abu ya gayyato mutane dan ya tabbatar dasu zasuyi nasarah, tunda dai yasan su Barr. Umar basuda wata shaida saisa suka canja salon shari’ar, kuma ma canjin salon da sukayi bai amfana masu komai ba saboda gashi sunyi takarda wacce taci uwar original one d’in.
Mai gabatar da k’ara ne ya tashi ya gabatar sannan alk’ali yace “Kotu najiran Barr. Sultana domin taci gaba daga inda ta tsaya”.
Tasowa tayi bayan ta gyara daidaituwar rigarta ta iso inda Ummimah da Gentle suke, “Kotu na son ganin Dr. Khalid idan yana kusa, ya fito da takardar asibitinshi kamaryanda yayima kotu alk‘awarin zai kawota yau”. Tasowa yayi cike da confidence, takardar ya mik‘ama Sultana ta duba sosai, saida gabanta ya fad‘i saboda babu wanda zai ganta yace bata kirki bace,
Ganin reaction d’in fuskarta yasa Barr. Sa’eed sakin murmushin mugunta sannan ya kalli Barr. Umar daya tsurawa Sultana ido dan shima ya fahimci yanayinta. Mik’a takardar tayi har ta isa ga alk’ali, Bayan ya dudduba sosai yayi rubutu sannan ya miyar da ita ga Sultana, “A bisa duba da kotu tayi ga wannan takardar, kotu ta gamsu da cewa asibiti dai ta Dr. Khalid ce shi kad’ai, dan haka batun wannan maganarta kau”. ‘
Dukda gabansu ya fadi amma basuji komai ba dan sun san duk wannan ba wani abu bane saboda babbar hujjar da garesu ta isa tasa a yanke hukunci yanzu yanzu.
Wata takarda Sultana ta sake zarowa tace “Wannan takarda ce wadda ta nunar da cewa anyiwa Aishatu Abubakar fyad’e har sanadiyyar haka ta kamu da cutar hawan jini, Sannan kuma gashi nan k’asa signing d’inka ne farko sai na Dr. Rafiq a k’asa, Kenan kaima kasan fyad’e ne aka mata tunda har kayi signing?”.
Gabanshi ne ya hau dukan uku uku ya hau rarraba ido, “Ni wannan signing d’in ba nawa bane, akwai dai yanda akayi amma ni bansan da wannan maganar ba, abunda na sani d’aya ne kawai ta zubar da ciki ne, wannan takardar kawai nasan nayi signing amma fa ni ban ma tab’a ganin wannan d’in ba”. Murmushi Sultana tayi tare da d’aga d’ayar takardar asibitin da yace itace tashi, “Dr. Khalid ka duba da kyau ka gani mana, waye zaiga wannan signing d’in kuma har ya banbantasu? Ko makaho ya laluba yasan iri d’aya ne kuma mutum d’aya yayisu, kadai canja magana”.
Objection my lord! Barr. Sultana tana k’ok’arin forcing d’in Dr. Khalid akan ya amsa abunda bashi yayi ba, ya fad’a mata cewa wannan sugning d’in ba nashi bane amma kuma ita tayi insisting akan nashi ne bayan kuma batada wata hujjar data tabbatar fa hakan” Barr. Sa’eed ya fad’a jin ana neman k’ure Dr. Khalid. “Barr. Sultana a kiyaye” alk’alin ya fad’a tare da miyar da kallonshi ga Sultana. “Iyakar tambayar da zan masa kenan ya mai shari’ah” ta furta hade da komawa
mazauninta ta zauna. “Ko akwai mai magana a cikin sauran lawyers d’in” alk’ali ya tambaya.
Tasowa Umar yayi ya gyara zama hularsa yace “Sulaiman Usman Saraki, Yusuf Bilal Mohd, kotu zata so ganinsu idan suna kusa”.
Daga k’ofar shigowa sarki Manu ya shigo, a bayanshi kuma gado ne irin wanda ake d‘ora marasa lafiya d’in nan, YB ne kwance cikin gadon duk yabi ya lalace kamar bashi ba.
Ido bud’e Gentle ke kallonsu, Ko a mafarki bata taba tunanin wannan rana ba, Shikenan yau tasu ta k’are, asirinta zai tonu kenan, Gabanta sai dukan uku uku yake ta kasa rufe bakinta, Tunani take waima ya akayi hakan ta kasance?, D’an marin kanta take wai idan ma barci akeyi ta farka. A k’asa aka ajiye gadon kusa da Ummimah, Gentle kuwa tasha mamakin halin da taga YB ciki, K’yafta masa ido kawai take tare da d’an murmushin yak’e wanda da k’yar take fiddoshi. Gyaran murya Umar yayi yace Sarki Manu kotu zata sojin cikakken sunanka, garin daka tashi, sannan kuma menene alak’arka da Salmah Gentle?”. Tuni Gentle ciki ya d’uri ruwa, zawayi takeji amma babu halin tace zatayi, Sai raba ido take tana kallon mahaifinta sannan kuma tajuya ta kalli lawyernta. “Sunana Sulaiman Usman Saraki, zan iya cewa na d‘an tab’a rashinji a baya kam Allah ya shiryeni yanzu, alak’ata da ita kuwa ita budurwar wani abokinmu ne Abdul K’adir amma duk da AK muke kiransa”. “Ko zaka iya yima kotu bayanin yanayin tarayyar Gentle da saurayin nata AK?”, “ehh zan iya mana, yana sonta tana sonshi sosai, harma son da take masa yafi wanda yake mata yawa, hakan yasa ya rainata sosai saboda yaji tana yawan fad’in ba zata iya rayuwa idan babushi ba,
Babu abunda zai nema a wurinta ya rasa, zina kuwa sun miyar da ita tamkar abincinsu, sun zama kamar miji da mata, abun nasu har a cikin makaranta yinshi suke kuma kusan kowa ya san da hakan, Wata rana….” ya basu labarin abunda ya faru ranar da akayima Ummimah fyad’e.
Salati duka mutanen dake cikin kotun suka d’auka, Alhaji Abu Abu kuwa sai cire hula yayi, dukda sanyin da akeyi amma shi zufa yakeyi tsabar
kunya da yaji, gashi d‘an siyasa sananne kuma a gaban jama’a wannan abun yana neman ya kasance. “K’arya kakeyi wallahi ni banma sanka be? A gidan uwarwa ka sanni? Kaji min mutum da sharri, k0 tab’a ganinka banyi ba amma kake fad’in haka,ya mai shari’ah karka yarda dashi wallahi k’arya yake”. Daka mata tsawa alk’ali yayi hade da buga teburinshi, “Karki manta nan kotu ce ba wurin shirme ba, ki nemi izinin magana idan kina son kiyi ba wai ki sakota haka ba”.
Shiru tayi gabanta sai fad’uwa yake, Ji take tamkar k’afarta ba zata iya d’aukar gangarjikinta ba. Ga YB umar ya koma yace “Me zaka iya fad’i game da maganganun da Sarki Manu yayi?” Cikin muryar ciwo YB yace “Babu k’ari ko kad’an a bayananshi, Ina d’aya daga cikin wanda sukama Aishatu fyad’e kuma Gentle ce ta sakamu,
Duk sauran wanda mukayi abun tare babu wanda ya sake samun kwanciyar hankali tun daga ranar da muka mata fyad’en,
Kwatsam kwanakin baya munyi shaye shayenmu muka had‘u da tsautsayin accident, baki d’aya mutanen motar suka rasu nine kawai Allah ya kub’utar dani,
Tun daga wannan lokacin nake rok’on Allah ya had’ani da koda kad’an ne daga mutanen dana zalunta in nemi yafiyarsu,
Kuma case d’in Aishatu yana d‘aya daga cikin abubuwan da nayi wanda suke yawan fad’o min a rai, Tun daga wannan lokacin nake fatan Allah ya gwada min ranar da zan had’u da ita dan neman gafararta amma Allah bayyi ba sai yanzu,
Ko tantama babu Gentle itace ta saka muka mata fyad‘e, Bayan nan kuma akwai abubuwa da dama wanda ta saka aka mata,
Itace ta tura ‘yan daba suka sace k’annen Aishatu ‘yan biyu, Tasa an kashe d’aya daga cikinsu aka kai gawarta kan layinsu aka yar, Itace ta had’a baki da manyan makaranta aka kori Aishatu akan laifin wai ta zubar da cikin shege harda fad’in wai ba wannan ne na farko ba, 
Itace tasa aka kona gidansu Aishatu wanda da bakinta ta bamu labari saboda ni nayi zaton ma bata raye, dan yanda muka mata fyad’e mu kusan takwas sau’inta ma duk bamu da wani k’arfi sosai a lokacin saboda yanda muka bugu, 
Ban tab’a zaton ma tana raye ba saida ita Gentle d‘in ta bamu wannan labaran, 
Ina rok’on wannan kotu mai adalci datayi gaggawar yanke mana hukunci tare da k’watarwa Aishatu hakk’inta” ya k’arisa maganar cikin rawar murya hade da fashewa da kuka. ’ 
Duk mutanen kotun babu wanda bayyi mamaki ba, Hamdala kawai ke tashi a ciki banda bangaren iyayen Gentle da har yanzu suke ganin k’age ne aka mata. “Yanzu haka d’aya daga cikin k’annen Aishatu tana wurin Gentle a b’oye, banda azaba babu abunda ake mata” YB ya fad’a a hankali. 
Har Sarki Manu saida yayi mamaki sosai, saboda shi duk baima san da wannan mugayen abubuwan da Gentle tasa akama Ummimah ba. 
Kuka Gentle ta fasa da k’arfin gaske wanda duk fad’in kotun babu wanda baiji ba, “Na shiga uku ni Salmah, na cuci kaina, kaico na ni Salmah, dama hausawa sunce ‘kwana dubu na b’arawo, rana d’aya ta  mai kaya’ yau gashi asirina ya ‘tonu abunda ban tab’a zato ba, nasan tawa ta k’are saboda banida wata hujjar da zan kare kaina” a boye tayi maganar amma bata san a bayyane tayita ba, Baki d’aya kallo ya koma gareta saboda da k’arfi ne tayi maganar kowa yaji. 


Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]