[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A
CHAPTER 19Lambar wayar dake jiki Umar ya danna a wayarsa, ya latsa kira yayi take kuwa ta fara k’ara, Har ta tsinke ba’a d’aga ba hakan yasa ya sake kira,
Saida ya kira sau uku sannan aka d’auka,
“Hello-salamun alaikum” Umar ya furya a hankali bayan ya saka wayara hands free. Daga can d’aya b’angaren aka amsa da
“Wa‘alaikumussalam, sunana Sarki Manu, how may I help you?”, “Alhamdulillah, Sulaiman Usman Saraki, is that your real name?“, “of course thats my real name” ya bashi amsa.
“Sunana Barr. Umar Mohd Bashir, cikakken lawyer mai zaman kanshi, idan ba zaka damu ba akwai wata magana da nake so muyi da kai
Dafe gaba Sarki Manu yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya, “Wace irin magana ce?” Ya tambayeshi.
” so idan babu damuwa mu had’u dakai face-to-face muyi maganar”. Shiru yayi kafin yace
“Babu damuwa ina zamu had’u d’in?”, “Ina kake ganin yafl? Wurinka ko kuma zakazo gidana?”,
“Ka bani address d’inka ni zanzo ko zuwa anjima ne insha Allahu”, “Nagode kuwa abokina, yanzu zan texting maka address d’in” yayi hanging up na wayar. ‘ Sosai Ummimah taji dad’i, tasan Sarki Manu yanada sauk‘in hali sosai, ba za‘a sha wahala wurin shawo kanshi ba.
Bayan sallar isha’i kuwa Sarki Manu yazo k’ofar gidan, kiran Umar ya latsa tare da shaida masa gashi nan k’ofar gidanshi, Cike da jindad’i Umarya fita ya sameshi tsaye ya paka mashin d’inshi,
Gabanshi yaje yace “Har ka iso kenam abokina?”,
“Wallahi kuwa na iso, ashema gidan babu wahalar ganewa, tambaya d’aya kawai nayi”, “Ehh ai dayake unguwartamu sabuwa ce babu mutane sosai, gida baya wahalar ganewa”, “Ehh na gani kam”, “Bismillah shiga daga ciki” Umar ya fad’a tare da k’ok’arknjan mashin d’in dan ya shigar dashi cikin gida. Koda suka shiga gida kai tsaye parlor‘n bak’i Umar ya zarce dashi,
Awaya ya kira Sultana yace da ita ‘a kawowa bak’o drink’ da kanta ta zira hijabinta ta had’a exotic da cups guda biyu ta d’ora a tray ta kai ma Sarki Manu, Bayan sun gaisa ta fita tana nazarin a halin da suka tab’a samunshi, yanzu kam da alama duk ya tuba da wannan halayen ya daina su, saboda yanda ya zama a full gentle man.
“Kasha lemo abokina” Umarya fad’a bayan ya zuba masa a cup shima ya zuba a d’ayan cup d‘in ya sha. Gyatsa yayi tare da hamdala ga Allah yace “Ina saurarenka Barr. Tun lokacin da mukayi wayar nan hankalima bai kwanta ba, na
matsu inji neman da kake min, dan nasan koma wace irin magana ceto mai muhimmanci ne, saisa na zab’i mu had’u a gidanka dan mu tattaunata”.
Ajiye cup d’in hannunshi yayi bayan ya goge bakinshi da tissue yace “Ehh tabbas matsala ce kuma mai girma, abunda ya faru shine; …… ‘ ‘ ya kwashe komai tun daga farko har k’arshe ya fad’a masa.
Saurin tashi tsaye Sarki Manu yayi ido bud’e yana mamaki sosai, “Malam da gaske kake wannan maganar k0 da wasa kake?“, Shima Umar mik’ewartsaye yayi ya dafa kafad’ar Sarki Manu yace “Ka kwantar da hankalinka muyi magana sosai, am very serious about the issue, yanzu haka yarinyar tana nan cikin gidana as I told you”. 
Zama yayi har yanzu mamaki yake, Saboda shi sam bayyi zaton Ummimah na raye ba, a yanayin halin da suka barta ciki babu wanda zai tab’a tunanin tanada rai, “in har da gaskene ina son ganin yarinyar, idan itace zan iya ganeta dukda kallon duhu na mata”, 
“Karka damu yanzu kuwa zaka ganta” ya sake latsa kiran Sultana yace mata ‘suzo ita da Ummimah yanzu’. Babu b‘ata lokaci kuwa sai gasu sun shigo, Kallonta da yayi shi ya tabbatar masa da itace, Saboda ya rik’e kamanninta, nan ya hau tuno lokacin da takema abokananshi magiya akan su k’yaleta amma suka k’i, Wani irin kuka ya kufce masa wanda ya rasa gane kona menene, 
“Allah yaji k’anku abokaina” ya furta cikin kuka. 
“Abokanka? Su waye suka rasu?” Umar ya tambayeshi. “A duk cikin wanda suka mata fyad’e yanzu haka mutum d’aya kawai ke raye, kuma shima d’in yana can rai hannun Allah, tun lokacin da suka mata abun a duk cikinsu babu wanda ya sake samun farin ciki, Kullum cikin tashin hankali suke wanda suka rasa dalilin faruwar hakan, 
Kwatsam sati d’ayan nan daya wuce labari ya riskemu wai sunyi shaye shaye suka shiga mota shine motar ta kife dasu, mutum d’aya kawai ya rayu amma shima tamkar mataccen yake, 
Magana kawai yake iyayi amma baya ko iya tafiya, komai saidai a masa daga kwance, 
Sannan kuma a accident d’in yaji masa ciwo a mazakuntarsa wanda babushi babu aure har abada, silar wannan abun daya samesu na d’aukarwa kaina alwashin babuni babu shaye shayen kayan maye har abada, na duk’ufarma istighfari ko Allah zai yafe min laifukana a baya” ya sake fashewa da wani kukan. 
“Allah yaji k’an wanda suka mutu, shi kuma maras lafiyan Allah ya bashi lafiya, karka damu ai Allahi Gafurur-Raheemu ne, zai iya yafe maka kura kuranka”, “To nagode sosai” ya fad’a bayan ya share hawayenshi. 
“To Sarki Manu zaka iya zuwa kotu ka maimaita duk bayanan da kayi yanzu?”, 
“Me zai hana kuwa? Idan zaka yarda ma tunda yanzu dare yayi gobe muyi sammako mu tafi Jalingo, muje gidansu YB zan masa bayani, kuma nasan shima a shirye yake da zuwa kotu domin ya bada bayanin komai yanda ya faru, tunda dama tuni gang d’inmu muka rabu da AK tunda ya mana iskanci, nasan zai bada bayanin duk abunda ya sani may be ma a samu bayanin da koni ban sanshi ba”. 
Murmushi Umar yayi yace “Aikuwa da naji dad’i sosai wallahi,Allah ya kaimu goben zan biyo in d’aukeka sai mu tafi”, “Bama saika biyo ba, ni da kaina zanzo sai mu wuce, zanyi k‘ok’arin zuwa da sassafe yanda zamu gama komai cikin lokaci mujuyo goben”, “To babu damuwa saraki Allah ya kaimu goben sai kazo”. 
Mik’ewa sukayi tsaye, bayan ya kalli Ummimah ya k’ara tausaya mata sosai yace 
“Karki damu komai ya kusa zuwa k’arshe insha Allahu, lallaima Gentle wato banda wulak’antaki da tasa akayi ashe harda kisa abun ya kai? Kuma suzo su fiki baki saboda su masu kud’i ne ko? Allah ya fisu tasu tazo k’arshe da izinin Allah”. 
Share hawayenta tayi tace “Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi”, “Ameen” ya fad’a tare da ficewa daga d’akin Umar ya mara masa baya. 
Abunda ya kasance kenan kuwa washe gari, da sassafe yazo suka tafi Jalingo, Wuraren k‘arfe goman safe suka isa, Kai tsaye gidansu YB Sarki ya kaisu, A k’oiar gida Umar ya tsaya shi kuma Sarki Manu ya shiga har cikin gidan, Ya samu hankalin ‘yan gidan a tashe sanadiyyar ciwon YB daya motsa sai sabbatu yake yana fad’in mugayen halayen da suka aikata kafin wannan al‘amarin ya faru, Cike da tausayi ya zauna kusa dashi yana fad’in Sannu abokina, ka daina kuka insha Allahu zaka samu lafiya”, “Ya za’ayi in samu lafiya bayan aika aikarda nayi kafin cutarta sameni? Taya kake tunanin zan samu sauk’i Sarki Manu? Na tabbatar da matuk’ar ban nemi yafiya ga wad’anda na cuta ba to Allah ba zai tab’a k‘yaleni ba, insha wahala anan kuma inje lahira ma babu kyau” ya fashe da kuka sosai yana matsar kanshu dake mishi barazanar fashewa. “ “Dan Allah ka daina fad’in haka, wata magana ce ke tafe dani…” ya masa bayanin komai tun daga farko har k’arshe. 
Zanje! Wallahi zanje in bada shaida, zan fad’a masu cewa mune muka mata fyad’e, zan tonawa Gentle asiri ince itace ta sakamu” ya fara k’ok’arin mirginawa amma ya kasa, Mahaifinshi dake gefe yana sauraren komai yace “Ka shigo da Barr. D’in nan ciki”. Tashi kuwa yayi babu jimawa sal’ gasu sun shigo tare, Gaishesu Umar yayi ya masu ya mai jiki shima ya tausayawa rayuwar da YB yake ciki, Neman k’arin bayani mahaifin YB yayi, Umar bai b’oye masa komai ba kuwa, “Babu damuwa zamuzo tare insha Allahu, komai yazo k’arshe tunda dai ya amsa laifinsa yayi d’in, zai bada shaidar duk abunda ya sani”. Da farin ciki su Umar suka bar gidan, yanzu kam insha Allahu komai yazo k’arshe kenan, yanzu abunda ya rage masu kawai su san inda Safiyya take, wannan d‘inma sun san indai tana raye to zata bayyana da izinin Allah. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]