[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A


CHAPTER 16Washe gari.

Tunda sassafe Haydar ya tashi daga barci, ido ya bud’e bayan ya lalaubi Safiyya bai jita ba, Daga can gefe ya hangi Hafsa tanata sharar bacci abunda cikin kwanciyar hankali.
Zaune ya tashijikinshi zafi rau yana fad’in “Aunt Shifiyya” amma shiru baijita ba dan a tunaninshi k0 tana toilet ne, Sauka yayi daga kan gadon ya fara knocking toilet amma har yanzu baiji alamarta ba.
Kuka ya fasa da k’arfl tare da barin d’akin ya doshi kitchen ko tana can amma Ina,a
b’uruntun Sultana ta jiyo tana had’a break fast saboda sammako zasuyi a kotu.
K’arar kukanshi data jiyo yasa tayi saurin fitowa ta tareshi dan dama a tsarinta bata barin yaro ya shiga kitchen saboda tana amfani da gas da electric, “Haydar wats your problem?” Ta tambayeshi bayan ta rungumeshi. “Momy banga Aunty shafiyya ba tunda na tashi” ya fad’a cikin kuka.
“Kajika Haydar da wata magana, yo ina zataje kuwa? May be ko ta shiga toilet ne yasa baka ganta ba, kayi shiru ka daina kukan nan ba nisa tayi ba” Sultana ta fad’a cikin sigar rarrashi tana rarrasar d’anta Haydar.
Da haka har ta samu yayi shiru ta kwantar dashi parlor kan three seater wani baccin ya
d’aukeshi, Murmushi tayi tare da nufar komawa kitchen saiga Ummimah ta fito,
“Ina kwana Aunty?” Ta fad’a bayan ta duk’a har k’asa.
“Lafiya k’alau Ummimah, ya jiki ya warware ko?”,
“Alhamdulillah ya warware sosai Aunty, yaune zamu fara zama ko?”,
“Ehh yau ne kuma yanzu ma bada dad’ewa ba, ance k’arfe takwas ta mana can, saisa na tashi na fara had’a break fast dan karmu makara”,
“0k Allah ya taimaka ya bamu nasarah Aunty, baki ba zai iya gode maku ba saboda duk wata hanya da zamubi domin gode maku kun wuceta, addu’ah kawai itace ta dace daku, Allah ya saka maku da alkhairi ya rabaku daga sharrin shaid’an daku da zuriyarku”,
“Ameen Ummimah, muci gaba dai da addu’ah insha Allahu zamu dace”.
Murmushi tayi sannan tace “Muje in tayaki aikin Aunty”.
Tare suka shiga kitchen d’in sukaci gaba da aiki sunayi suna fira,
Jin har yanzu Safiyya bata fito ba kuma abunda ba halinta bane yasa Sultana bin sawunta,
A hanyar fita kitchen Zarah da Rabiatu ma suka biyosu,
Bayan sun gaisa Zarah tace
“Munzo mu tayaki aikin ne Aunty”.
Murmushi fal a fuskarta tace
“Ai dama kunyi zamanku wallahi har mun kusa k’arisawa, nasan ‘yan mata da son barcin safe”,
“Babu komai Aunty aima mun tashi tun d‘azu har mun shirya” Rabiatu ta fad’a tare da shigewa kitchen d’in Zarah tabi bayanta.
D’akin Safiyya ta shiga da nufin taga ta shirya Hafsa amma da mamaki sai taga sabanin haka,
Hafsa kwance haryanzu bata tashi ba sannan kuma babu Safiyya, 
Mamaki tai sosai sannan tace 
“Safiyya” amma shiru babu amsa, 
Bakin toilet d‘in ta nufa tace 
“Wai lafiyanki kuwa Safiyya?” Nan ma dai shiru. Bankada k’ofar tayi taga wayam babu kowa a ciki, Dawo da kallonta tayi a gado saima yanzu ta kula da jini dake kwance bisa zanin gadon, Hankali tashe ta matsa inda jinin yake ta tabbatar da jinin gaske ne. 
A rikice ta fita daga d’akin ta nufl d’akin Umar duk hankalinta ya tashi, “Uncle Umar banga Safiyya ba, saijini kwance a bisa gadonta” ta fad’a a hargitse. 
Fita tayi yabi bayanta shima hankalin nashi ya tashi, 
Ganinjinin da yayi yasa yaci burki yana k‘wala mata kira, 
“Safiyya! Safiyyall” Amma babu ita, “Ya salam” ya fad’a a bayyane, “Meya kawojini a bisa gadonta? To ina ta shiga?” Ya tambayi kansa, Ganin baida amsar tambayar yasa yace 
“To ai ba zamu tsaya anan ba, wata k’ila ko ta zagaya bayan gida ne”. 
Fita yayi Sultana tabi bayanshi duk da bata zaton Safiyya na baya, saboda inhartana can to meya hanata shirya Hafsa School? 
A daidai k’ofar da zata fitar dasu daga parlor sukaci karo da Haladu mai gadi, 
“Sannu yallab’ai“ ya fad’a yana kallon Umar amma shi Umar neman hanyar fita kawai yake. 
“Yallabai akwai matsala fa” Haladu ya sake fad‘i yana kallon Umar. ‘ “Kabar wannan matsalar har sai mun gano inda ‘yar mutane take sannan ka fad’eta” Umar ya bashi amsa cike da tashin hankali. 
“Yallab’ai wata k’ila wannan matsalar tanada nasaba da batar Safiyya” Haladu ya fad’a bayan ya kawar da kanshi daga idon Umar yana kallon Sultana. 
Cikin fargaba Sultana tace “Muna saurarenka Haladu”. 
“Yallab’ai dama yau da tsakar dare…” ya kwashe duk abunda ya faru ya fad’a masu. 
‘Babu k0 tantama sun tafi da Safiyya, kuma sunyi tunanin Sultana ce yasa suka tafi da ita’ Umar ya fad’a a ranshi. 
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Allahumma ajirna fi musibati,
 wakhlifna khairun minha’ Sultana ta furta bayan ta duk’e k’asa ta saki wani kuka mai k’ara wanda yake cike da tausayi. 
K’arar kukanta ce ta fito dasu Ummimah, Parlor’n suka iso a bakin k’ofa sukaga Sultana ta had’e kai da guiwa tanata rizgar kuka, Cike da tausayi suka k’arisa inda take, Tambayarta abunda ya faru suka hau yi, bata b’oye masu komai ba tun daga farko har k’arshe saida ta fad’a masu. 
“Allah sarki nasan duk mune muka ja mata, Allah dai yasa karsu mata komai, duk abunda zasuyi ya tsaya a kanmu muda mukayi laifin ba wai yarinyar da batajiba bata gani ba” Mama ce tayi wannan maganar a daidai lokacin data iso d‘akin saboda taji duk maganganun da sukeyi. 
“Ki daina fad’in wannan maganar mama, insha Allahu idanma dan karmu shiga kotu yau ne yasa sukayi wannan aika aikarto sunyi a banza, saboda da izinin Allah badajimawar nan ba zamu tafi, duk abunda zasuyi saidai suyi, nasan dai Allah ba zaima bawa abunda ba k’addararsa bace, duk abunda ya samu bawa to tabbasa dama can k’adddararsa ce, dan haka kuje ku fara shiri ba gudu baja da baya, kudai kawai ku sakata a addu’ah, bansan ya zanyi ba idan suka kashe Safiyya, mun shak’u sosai ta shak’u da yarana, 
Harma tafi sanin damuwarsu fiye dani saboda ta fini zama dasu, 
Idan sun kasheki Allah yaji k’anki Safiyya, Allah yayi miki sakayya, 
A iya zamana dake baki tab’a k’untata min ba, Kullum burinki shine kiga kin faranta min, 
Yanda kike son yarana kuwa ko ke kika haifesu sai haka, 
Idan kuma kina raye sun b’oyeki ne Allah ya bayyanaki, Allah ya kub’utar dake daga hannunsu, Allah ya dawo dake garemu” Sultana ta k’ara fashewa da kuka. 
Sosai Umar ke rarrashinta amma ina, ko saurararsa batayi, 
A yanda ta shak’u da Safiyya ko ‘yar uwarta ta jini sai haka, 
Bare kuma dama ita ta rasa iyayenta tunda yarintarta, 
Ta rasa d’an uwanta Hassan d’inta ta hanyar lalata rayuwarsa da akayi, Daga mijinta sai Safiyya ne da ‘ya’yanta kawai take gani taji dad’i, 
To yau kuma gashi an rabata da Safiyya, bata san inda aka kai mata ita ba, Ita yanzu batama san me zata fad’awa iyayen Safiyya ba. 
Da k’yarta iya tashi ta shirya cikin jar atamfa da manyan flower bak‘ak’e, d’inkin doguwar riga ne wadda ta saukar mata har k’asa. 
A daidai fitowarta Su Ummimah suka fito, Dukkaninsu babu mai walwala saboda b‘atar Safiyya. 
Umar ya kalleta cike da tausayi yace “Motar ba zata d’aukemu ba, Ki tafi da taki sai su shiga ciki suma, Hafsa kuma dama ta makara makaranta dole saidai ta bimu, Haydar ma babu mai rainonshi dole tare zamu tafi”. 
Kai kawai Sultana ta d‘aga masa har yanzu bata cikin natsuwa. 
Tare suka fito suka shisshiga mota, Haladu ya bud’e masu gate kenan wata matrix ta tsaya a k’ofar gidan, Alama akayiwa Umar dake gaba ya tsaya, Babu musu kuwa ya kashe motar tare da fita ya doshi inda waccan matrix d’in take. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]