TSANGAYAR MATI CHAPTER 9

TSANGAYAR MATI 

CHAPTER 9“Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu, haba ai ko karamin yaro yasan ruwa ba a sheka mai Zobo a zuba Sugar shi kenan ya zama lemo, batun lalle kuma kin manta Inna da shegen san fadanci kamar matar Bawan Sarki?Ai kawai kururuta mata kai zakiyi harta sake ta baki kafar ki kunsa. ” Nene tayi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta gintse fuska ganin Fadime ta Fito zuwa makewayi. “Shegiya kai da wata fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah Abule yadda naki jinin Matar nan banki a cemin karta fito raye daga makewayin nan ba , bani zoban ki gani duka gidan zan hada idan yaso in bata gani sai najuye maganin” Ta fada tana wartar ledar zobon da Abule ta riga ta siyo. “A’A hankali dai Nene dan kadan yace a zuba saboda karfinsa.” Ta balla mata harara “Wallahi duka zanjuye idan za a sha giya asha ta dubu Abule!” Ta fada tana mai ficewa daga d’akin. Kai tsaye madafi tayi ta dauko kwanon sha tajuye zobon, ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta juya. Nan da nan ta kasafta na kowa, na Inna ta fara dauka dauka za ta kai mata, da shigarta kuwa ta tarar da ita tana gyangyadi dan haka ta aje tajuya za ta fita. ” Na shige su ni Uwar Biyu, Nene me nake gani haka?” tajuyo da sauri tana kallonta kafin kuma ta saki murmushi. “Zobo ne muka samu tsaraba daga Abule, shi ne na hadamana lemo da shi na san ai kin sanshi a birni.” Inna ta balla mata harara tana turo kallabi goshi.” Toke ina kika taba ganin anyi zobo ba a tace tikar ba? Wannan zobo zamu sha k0 roman zobo? ldan baku iya abu ba ku dinga tambayata mana, ni nan da kuke ganni na bayan zobo durinkis (DRINKS)har mangwar durinkis (MANGO DRINKS) Na iya, dan haka bansan jahilci dauki ki tace shi sai ki kawon. Sum-sum Nene ta fice jin Inna ta koma yaren ‘yan samajannati. Sake gyarawa tayi, tukun ta dauki na Fadime ta kai mata daki, komawarta daki keda wuya Mati ya sawo kai Gidan. Kai tsaye dakin Fadi yayi yana doka sallama, fasa kai dan karamin kwanon shan dakin tayi ta aje tana amsa masa da murmushi kuma ta mike tana kokarin zare masa zungureriyar hular dake kansa. Ya shaki kamshinta da yake so na Karkar dan haka ya washe baki “ALLAH Amarya son ki nake kamar na mutu” Tayi murmushi tana rangwada kwalelen kanta “A’A Maigidana mai ya kawo mutuwa kuma, muna tare ai.” “Hmm! Ba zaki gane ba ne, idan kina kusa da ni ji nake kamar numfashi… KYYYATTT…FYYTTATAT… Ya dakata yana mai kakalo kaki, kafin kuma ya dunkulo majinar yana mai furzo ta waje da bata dire ko’ina ba sai cikin kwananshan Fadime dake cike da zobo. lta da shi suka zubawa kwanon ido kafin kuma ta kwabe fuska. “Haba Maigida nasha ce maka ka dainamin tofe-tofe a bangon daki ko kasa, wannan ko a kan titi ne ba abin so bane. Yanzu kalli yadda ka haramtamin abinda tunda na gani yawuna ke tsinkewa. ” Ki hakuri na mantane, yanzu bari na karbo miki kasona saiki sha.” ya fada yana mai daukan kwanon ya fice. Bisa randa ya tadda wani kwanon rufe da Fai-Fai Dan haka ya aje wancan ya dau wannan ya tafi. Nene da ta shiga makewayi rage ciki tana fitowa tayo inda ta ajje zobanta, ganinsa bude ya sata doka ashar “Ko wane shegen ya budemin oho, to idanma diba akai ansha wuta bal-bal tunda nawa ne. Ta fada tana hararar dakin Inna, kafin kuma ta daga kwanon ta kwankwade tas! Har kakin Mati. Minti biyar dasha cikinta ya yi wani irin juyi,jin kamar ruwa da wani wari na binta ya sata lekawa abin data gani na binta ratata ya sata doka ihu tana dafe mazaunanta “Wayyo ni Mati! Yoyon Kashi ya kamani. 


Hmmm

About Ismail

Check Also

TSANGAYAR MATI CHAPTER 5

TSANGAYAR MATI  CHAPTER 5 Inna ta d’aga hanci sama taja iska, sai kuma ta furzar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *