[Advertisements⬇️]

TSANGAYAR MATI CHAPTER 12 TEND QARSHE - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANGAYAR MATI

CHAPTER 12 THEND QARSHE
BAYAN WATA GO MA

Rayuwa ta mika a gidansu Mati, abubuwa da yawa sun faru ciki harda dawowarsu Nene bayan sunyi Bikon Mati sau kusan goma. Wanda Nene sai da ta koma yini a gona gun Mati tsaban son ta koma dakinta. A rana sai tai wanka sau hudu ko biyar. Goge hakora kuwa masu sai da gawayin kauyen sai da suka shaidata, haka ma masu Gishiri. Saboda tsabar tsafta sai da ta koma yawo da tsumma tana gage kafarta idan tai kura. Wannan fa duk shawarar kawarta shafa ce. To haka ma ga Abule itama sosai ta nutsu dan har dan abin kwalama take kaima Mati gona. Musamman ma Kundun Kaza da ta san yana so. Karshe dai ya mai dasu. A daren Inna ta tarasu da tata nasiharta nunamusu laifinta ne tare da neman gafararsu.
“Haba Inna, ta ina kika zama mai laifi? Mu keda laifi mu yakamata mu nemi gafara.” Fad‘in Nene kenan tana mai k’arashewa da sheshshek‘ar kuka
Fuskar Inna cike da damuwa ta girgiza kai bayan ta k’aremusu kallo gaba daya har Matin tana mai shafa kanjikanta Atiku dake saman cinyarta, ya sha billensa a goshi an rambad’amasa kwalli yayinda fuskar ke ta kyallin mai. Ta cigaba da magana.
“Um um Nene, bari fad’in haka, maganar nan haka take. Abule da bakinta ta sanarmin musabbin wannan rashin jituwar a sadda take zuwa yawon biko, nayi kuskuren ware wani kaso na dukiyata da zummar bawa jikan Matina na farko, kai kuma Mati bai kyautu ace kai da kake Maigida ba kana nuna halin k’aranta, Abule ta sanarmin da irin yanda ka sanyata k’aryar ciki wanda tun daga ranar zaman lafiya ya k’ara k’aranci a gidanka. To yanzu wannan sai ya zama izna gareka, matuk’ar kana son had’in kan iyalanka kada ka k’ara wannan gangancin. Nima a karshe ina neman gafarar…”
Da sauri duk suka tari numfashinta kowa na kara neman gafararta, Nene dake tashin k’amshin turaren matan arewa ta rungumo kafadar Abule dayan kuma ta rungumo Fad’ime wacce farinciki ya cikatta don har zuciyarta bata son fad’ace-fad‘ace, washe bakinta ta yi wanda yasha durji da gawayi tace. “Yanzu mun zama tsintsiya madaurinmu d’aya. Daga gareni Nenen Mati babu abinda zai k’ara fitowa daga wurina.” Farinciki ya cikasu babu ma ya Mati wanda haraiken kiss ya yi musu ta iska bayan ya fakaici idon Inna, suka tuntsire da dariya kuwa.
Cikin iko na Ubangiji kuwa tun daga ranar babu hayaniyar da ta k’ara tada hankula a GIDAN MATI, Nene a matsayinta na babba taja girmanta da sauran mutuncinta da ya rage, hakanan Fad’ime tana binsu sau da k‘afa, saida ya zamana rainon Tanimu ya koma ga Nene, kai kace itace ta haifeshi. Fad’ime me kawaici kuwa ta d’auke kanta daga Atiku, muddin ba nono zai sha ba to fa babu abinda ke had’asu sai kwanciyar bacci. Bangaren Mati shima kuma daidai gwargwado yana kokarin yin adalci tsakankaninsu. Wannan ya kwantarwa Inna hankali.

SAUYIN RAyUWA

Gida ne wanda ya sha filasta madaidaici, tsakar gidan an shafeshi da sumunti. Dakuna ne jeras har hud’u sai falo babba guda daya wanda daidai ‘alakan k’auye ya tsaru.
Nene ce ta fito daga d’akin dakejikin na maigidannasu tare da Atiku da kanwarsa Sa’a, ta cakare cikin atamfa mai kalar ruwan masara, tana kokarin rufe k’ofar d’akinnata bayan ta saki hannun Atiku ta ce.
“Wai mutanennan kuna so dai dare ya yi mana ba mu bar gidan bikinnan ba k0? Abule! Kanwata!”
Kusan a tare suka amsa gami da fitowa daga d’akunansu sanye cikin atamfa irinnata.
Abule rik’e da d’iyarta da Allah ya bata wacce ko wata shida bata cika ba a duniya yayinda Fad’ime ke goyon yaronta na uku Sallau don Nene kam Allah bai bata ba.
Nene ta washe baki.
“lnye, cakarewa. To ai ni har kun fini kyau.” Suka dara. “Wane mu?”
Fad’in Abule da ke saita zaninta. Suka rufe ko’ina suka jera gidan Delu wacce ke aurar da yanmatanta uku.
Kowa a gidan bikin ya yaba da shigarsu, Shafa ita kanta ta yi kyau tamkar ba ita ba, cikin hukuncin Allah mijinta Bashari ya shiryu ya daina kwartanci, hakanan Delu itama mijinta ya daina dukanta tun watarana da diyarsu Bushira wacce duk cikin yaran yafl kaunarta saboda nutsuwarta ta gwada d’aga hannu da zummar ramawa uwarsu, wannan abu ya
dagamasa hankali ainun karshe dai ya saduda bayan limamin garin ya shiga lamarin ya mishi nasiha. ’

Karshe. Mu hadu a wani sabon Littafi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]