[Advertisements⬇️]

TSANGAYAR MATI CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANGAYAR MATI
CHAPTER 11

Abulle tayi k’asa k’asa da murya. “Makarin shine a jika wandon kwarto a shanye.”
Nene ta zabura tayi zaman ‘yan bori wanda yayi daidai da sullusowar tusa mai kara. Abule ta toshe hancinta, a hankali Nene ta numfasa har da lumshe idanu don ba karamin sassauci ta samu a cikinta ba.
”Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar… Af! Faduwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo bana manta ashe muna dasu a kurkusa ba? Ga Basharin Shafa?”
Abule wacce itama shaff ta mance da batun Jikan Lamidon ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin zuciyarta wasai, babban abinda ya sanyamata damuwa da lamarin ba komai bane sai na tsoron kada ya kasance Nene bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari su zageta. Ta daki cinyarta tana mai washe rinannun hakoranta.
“Kai Allah mungode maka. ai ni dinma kaf tunanina bai je nan ba. Kojiya da daddare ya haurawa Kulu Gurguwa.” Suka saki shewa don Nene har ta hango warakarta a saukake.
“Kai Allah Ya karowa Bashari ilimin kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. Ashe kwarto ma da ranarsa. (Kunji jahilcil)‘
Dariya suka kara kwashewa da ita.
Ayammacin ranar Shafa na durkushe a gaban murhu tana kokarin iza wuta ta tsinkayi sallamar Nene da Abule. Da mamaki ta dubesu kafin ta mike. Abule taci burki anan tana karewa gidan Shafar kallo domin rabonsu da shiga gidan har sun mance. Daga can gefen garu ta hangi jerin manyan duwatsu wanda ta taimakonsa ne Shafa ke karewa cikin gidansu kallo. Tabe baki tayi gami da bin sahun Nene da harta shige rumfar Shafar ba tare da k0 neman izni ba.
Shafa za tayi magana Abule ta hanata ta hanyar riko hannunta tanamata alamar tayi shiru gami da yi mata nuni da gidansu, nan take ta fahimci basu kaunar Fadime da Inna
su san da zuwansu. Ta gyara zaman daure kirjinta suka shige ciki. Nene ta washe baki. “Shafa Shafa, Shafar Bashari, uwargida ran gida! Kin tare gaba kin tare baya, turmin tsakar gida sha Iugude!“ ‘Wannan haka yake.” Fad’lllin Abule tana gyada kai kamar kadangaruwa.
Shafa ta yamutsa fuska tana kallonsu dai-d’ai.
Halan dai Nene acan asibitin har allurar mahaukata suka manta suka yi maki?” Nene ta hau daure fuska za ta kwabomata mai zafi ganin haka yasa Abule saurin tarewa. 
“Kai Shafa, dadina dake zolaya. Nene ai taki ce, banda abinki ai makwafci ance yafi dan uwa, a baya ma rashin fahimta ne.” 
Dariya Shafa tayi gami da tafa hannuwa. Nene da Abule suka dubi juna, dakyar dai suka shawo kanta ta yarda zata sauraresu. 
Nene ce ta soma magana bayan ta gyara zaman nafkin dinta. 
“Ki taimakeni Shafa ki bani aron wandon Bashari.” 
Shafa ta fiddo idanu gami da dafe kirji. 
“Yau naga ta kaina Nene me zakiyi da wandon Basharina? Anya Nene ba ki samu matsalar kwakwalwa ba? Au to na fahimta, wato dai duk matattarar kwararar gudawar da aka sanyamaki bai isheki ba sai kin hada da wandon Basharina? To minene amfanin na Mati?“ Nene ta share zufa tana zirziza kai. Abule ta cafke zancan. 
“Kinga Shafa duk ba haka bane, wannan maganar da zamu yi sirri ce, don Allah ki rufamana asiri.” 
Shafa ta dan zubamasu idanu na ‘yan dakiku kafin ta gyada kai don ba zata bari gulmarnan ta wuce ta ba.’lnajin ku.‘ 
Abule ta zayyanemata duk abinda ya faru da kuma makarin asirin. 
Shafa ta saki shewa har da tafa hannuwa. Yau abin namu ne 0h ni  
Saida ta basu wuya Nene harda matsar kwalla sannan ta amince da sharadin Nenen ta kyautarmata da tunkiyarta da take kiwo. Ba musu Nene ta aminta daganan ta mike ta fita zuwa dakin kwanansu ta hau lalube. Jimawa kadan sai gata rike da wani tsohon wandon Bashari da ya gada gun Lamid’o ta mikamata. 
“Gashinan, kuma kada ya kai gobe a wajenki, ko ta katanga ki jehomin.” 
Nene ta hau godiya kafin kuma cikin lallami ta ce. 
“Ki taimakamin Shafa. ki bani sabon dinki mana.‘ “Cab! Ai idan kinga Bashari yayi sabon dinki to mutuwa akayi a danginsa don haka ban bayarwa, idan ba kwa so ku kara gaba.” Ta karashe tana girgiza k’afa gami da jefamusu tafin hannunta. 
“A’a me yayi zafi? Muje Abule hakan ma ya wadatar” ” To karki manta dai ki jefon ta katanga.” Da komawarsu kuwa Abule ta tarkata lallen ta watsar Masai, shi zaman duniya dama rabo ne, idan baka da shi kuwa zaka zo ne a banza ka koma a wofi. Tuna hakan yasa ta nutsuwa tana fita daga batun Fadi. To haka ma ga Nene sai wayar gari akai aka ganta sumul tamkar mai bugun lska. Itama ta mai da rayuwarta shiru ta hanyar aro nutsuwar dole. Daga bisa ni ta kulla Amintaka da Shafa bama ta zaman gidan balle ta zubda hali. Bayan watanni, ranar wata laraba wanda ya yi daidai da kwanan Inna guda a birni taje hado kayan haihuwar fadi. Fadumen ta tashi da nakuda. Gidan daga Abule sai Nene dake shirin fita. 
Ta gyara zaman yafenta tana mai sauke kabar shiga dakinta. Ta juyo gami da duban Abule, za tayi magana kenan sukaji nishi da salatin Fadime. Cikin hanzari suka dubi juna. “kinji abinda naji?” Abule ta yatsina fuska” naji mana kila abinne yazo.“ “Toya za,ai k0 mu dubo yar magaji… ” Abule tayi saurin rufe mata baki. “Ke gafara, kinmanta yanda ta musanya miki magani? To yaune ranar ramuwa ce dan haka maza kwabe gyalen nan ki dauka sude muyi yanzu dan karma makota su jiyo bayan awa guda ma lekata.” Da sauri Nene ta aje gyalen ta juye hatsinta a turmi suka hau dukansa ba kajin karan komi sai tunkwaltunkwal. 
Fadime cikin azaba haka ta rarrafo bakin kofarta tana kiransu amman suka yi biriss da ita. Har sai da suka barjin muryarta tukun suka zubda tabaren suna masu nufarta. Ganin ruwa gefenta yasa Nene zare ido ‘Ke abu ai fayat ta fashe.‘ 
Abule ta karasa itama tana leke-lek’e, a karshe suka kinkimi Fadime suka maidata ciki. Haka suka karbi haihuwar santalelan danta suka yanke cibi. Nene dake rike da jaririn wanda bai bar komai na Mati ba, katon kan Fadime yayo. Ta yiwa Abule ido kafin ta fice zuwa d’akinta rike da jaririn wanda ta cusawa yatsanta a bakinsa gudun kada sautin kukansa ya ankarar da gulmammun makwaftansu. 
Abule ta dubi Fadime wacce ba karamin karuwa ta samu ba wajen haihuwa sai mutkususu take da alamar dal akwai abinda ke damunta. A hankah ta sulale tabi bayan Nene. Idanu ta ware a tsorace ganin Nene na kokarin sanyajaririn cikin kwali. 
“Nene Bakya tsoron asirinmu ya tonu?” Nene ta harareta. “Kinsan iyakar tsawon lokacin da na dauka ina ajiyar kwalinnan? Ai bazan bari damarnan ta kufcemin ba, yau dan kwal ubannan sai kwanan daji.” 
Kafin Abule tace wani abu suka tsinkayi sallamar Mati. 
A razane suka dubi juna har Nene batasan sadda ta cire yatsanta daga bakin jinjirin ba ai kuwa ya canyara kuka. “Lafiya Fadi? Kin haihu ne?‘ 
Mati dake jefowa Fadinsa tambayoyi ya tsaya gami da saurin bin inda ya jiyo kukan jaririn. 
Duk kokarinsu na kada ya fahimci shirunsu saida ya gane. Nan ya hau salallami, wani wawan tsalle daya doka sai gashinan gaban Nene, ya kwasheta da mari kafin ya fiddo jaririn daga kwali. 
“Ka gantanan, yasin ba hannuna ciki! Yanzu na shigo daga makwafta ina..” Fadin Abule yayinda Mati ya katseta da sauri. 
“Dalla can rufemin baki kema bakar munafuka ce! Wato kun yi shirin kashemin mata da da k0?” Sautin karar Fadime ya kidimashi, a guje ya fice zuwa d’akinta. 
Kan kace me Shafa da Delu sun shigo domin tun kukan jaririn na farko sun tsinkaya saidai basu k’ara ji ba sai yanzun da Mati ke balbalin fada. Lekowarsu suka san abinda ke faruwa suka bazamo cikin gidan. 
Su ya bari a wajen Fadime yayinda ya fice nemo abin hawa don mika Fadime asibiti. 
Delu na gyara jaririn tana zubamusu habaici Shafa na tayata. Su kam kowacce na dakinta sun kunshe gaba daya a tsorace suke da abinda zai biyo baya. 
“Shegen, ashe dagamin kafa kawai yake.” Fadin Nene a k’asa-k’asa tana shafa kuncinta. 
Mati na dawowa aka wuce kai Fadime ga likita bayan ya kora Nene da Abule gidajensu da (saki) d’ai-d’ai. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]