TSANGAYAR MATI CHAPTER 10

TSANGAYAR MATI

CHAPTER 10
lhun Nene yajanyo Hankalin mutan gidan, gaba daya suka fito har da Abule wacce ta gwaggwase a daka tana kwaba lallen. Kan kace me tuni Delu ta gyara zamanta jikin garu tana leke, itama Shafa ba’a barta a baya ba wajen ganewa idonta. Mati a rude ya nufeta. “Nene, lafi…” Kii! Yaja burki sakamakon wari da karar sakin tusa daya bugi kunnuwa da hancinsa. Inna ta sanya salati.
“Me zan gani haka Nene? Wane irin shashanci ne haka ki wuce Makewayi mana” Nene dake ta kokarin danne mazaunanta da hannu ta daddage taja numfashi sama tana mai hadejikinta dan ta tsayar da gudawar, ganin kamar an kara kunnu ta yasa ta sakin wani wawan ihun “Wallahi bata tsayawa, na shiga uku ruwanjikina zai kare. Kai Mati! Kai mati zan mutu, zata zuken jini” Ai sai ta zabura ta danna a guje zuwa karshen gidan abu na yoyo. Mati yayi sauri ya bita ganin ta zube gun,
“Nene, nene,jin shiru yasa shi toshe hanci yana jijjagata, sai kuma ya dago a tsorace yana duban Inna.
“Kamar fa bata numfashi Inna” “kai kauce nan, wane irin bata numfashi matsa ni kaga na bata fastu aidi (First Aid)shashasha ko dabarun lafiya baka iya ba dake kanka ya cika da kashinjakai.” “Um Inna yanzu dai bata ba’a ake ba ki duba ta kiga ni Aradun Allah Inna bata motsi”
Inna ta dan watsa masa harara, sai kuma ta hau karewa Nene dake yashe kallo, ganin har yanzu Abun na tuttulowa daga jikinta yasa ta kallob Mati “Tunda dai kai ne Mijinta matso kusa daidai bakinta ka lalubo harshenta ka gantsara mata cizo, shine zai sa ta farfadowa, ya waiga ga Abule dake matsar kwalla, ya dora idonsa kan su Delu dake bisa katanga, ai sai ya hau girgiza kai yana mai sharce gumi “Bazan iya ba! Kwarankwatsa dubu Inna wannan zalunci ne, yazan ciji marar lafiya. Kuma sannan wannan ai Yahudanci ne.” ai sai inna ta zabga salati tana mai fashewa da kuka Mati yace mata Azzaluma, kafin kuma ta share hawayen tana mai watsa masa dakuwa “To ka tsayajahilci Nenen ta mutu, numfashin mutum na daukewa da minti goma idan bai samu taimakon gaggawa ba yake mutuwa”
Jin haka ya sa Mati yin wurin Nene da sauri yana lalumar bakinta. Da dai ya zakulo harshen ai sai ya gatsashi da karfi. Baya yayi yana ganin Nene tayi wani irin cilla kafa. Tana fadi a hankali ” Na mutu Mati” cikin magagi. Abule ta kara sautin kukanta “Inna dan Allah mu kai ta gun kula da lafiyan da kika kai Fadime kwanaki” Mati ya kalle ta, sai kuma yayi waje da sauri. Ba dadewa sai ga shi da mai Baro. Abule ta taya shi kama Nene aka dora ta bisansa. Suka dunguma Asibitin kauye.
Bayan dube-duben da likitan yayi sakamako ya fita. Nene dai banda Maleria ba abinda ke damunta. Likita duk tambayoyin da yayi sun tabbata ba abinda taci na bata ciki tunda dai abincinsu guda ne. Dan haka ya daura mata karin ruwa ya rubutawa Mati 0.R.S da Napkin na manya aje a siyo mata. Ta kuma dinga daura napkin din duk bayan sati biyu. Karshe ya sallemusu da cewarsuje Birni a duba ta da kyau shi kam iya nasa kenan. Da komawarsu gida Abule tayi wuf! Ta fada dakin Nene tana sakayo kaba. Kallonta take cike da tausayi ganin harta tsotse rana guda.
“Ni Nene anya ba maganin fadi kika sha ba? Na ganta sumul fa” Nene dakeji da yoyon kashinta ta mike a hankali jiki na rawa” Shi ne wlh a randa na tadda shi a bude nasha,ashe dana shiga bandaki musanyamin tayi bakar muguwa wayyo ni. Menene makarin ki taimake ni Abule” Abule ta dafe kirji ido warwaje “Lalle dara taci gida Nene! Makarin da wuya Nene, ba zamu iya ba, saita kuma rushewa da kuka.‘
Nene tayi ruf da ciki tana numfarfashi. “Ki fadamin Abule, ko menene shi zan iya.”
Jin haka Abule ta fyace majina ta soma magana.

Hmm

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *