[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 35 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE


CHAPTER 35Tukin awa guda ce takai Miemah gida, afusace taflto cikin gaggawa tanemi taimakon securities na gida suka kai Zayyad d’akin Zaid inda batareda bata lokaciba aka ‘kira Likita yazo ya goggoge wajen ciwon ya d’aura mai drip sannan ya rubutamusu magunguna.
Hatsarin yazo masa dasauki sabida babu karaya ko d’aya ajikinsa, kansa ne dai ya buge sosai amma Insha Allah komei zaiyi dedei. Cewar likitan ‘kikwantar da hankalinki. Miemah tana share hawayen dasuka tarunmata a ido tace‘ Na’gode doctor nidei ayanzu banida wata buri face naga Zaid ya farfado ka’min mahaifinsa da Ma’inah sudawo su sameshi cikin wannan halin, na’san zusufl kowa damuwa.
Allah yasa, Likitan yafad’a cikin sany’in murya inda yahafa jakarsa yanamata sallama ‘sai anjuma akula dashi sosai anjuma kad’an zan dawo muga ko akwai wani improvement daza’a samu.
Ahaka hirarsu ta kasance tareda Miemah sannan ya sallameta yataf’l, Miemah ta’koma d’aki tazauna tasashi agaba sai kuka take tana fata yabud’e idanuwansu before Mutanen gida sudawo.
Dreba yanajansu cikin Mota kirar Lemozine 2019, motan ta daukesu duka Aunty Nasiba,
Umma Aisha da Aunty Rahila suna zaune akujeran baya sai kuma mommy dake zaune
tareda y’arta, sosai ta manneta ajiki tamkarjinjira tarike Mainah tana shafamata fuska.
Anisa koh sune a tsakiya tareda kannenta babu mai cewa wani Sannu idanuwarsu duk Yana kan wayoyinsu. Daddy, Mahaifin Zaid (Baba) Tareda shi Zaid d’in duk agaba suke zaune,
Zaid kam sai sacen kallon Ma’inah yaketayi ta window, burinsa ayanzu kawai shine yaga ya mallaketa, takoma Mrs Zald Muhammad Zablr.
Bayan tukin awa guda dreba yaja mota ya gangaro cikin ma’keken mansion d’insu, ahankali yakejansu har saida suka karaso ciki ya saukesu Mamy abangarensu sannan yaje Gangarensu Mommy, Umma Aisha tareda Daddy da y’arsu Ma’inah. Zaid ne na karshe a bakin kofa yasaukeshi, yanama ma’aikatansa dake gida suka taru akansa sunata mamaki, kowannensu yashiga duniyar tunani da rud’ani. Zaid yarasa gane dalilin hakan har saida ya daka musu tsawa ”What the hell are you guys doing here? Ko fuskan tawace ta chanza muku..?
Alhaji gaskiya akwai matsala. Sergeant Sani yafad’a babu fargaba yace’ kenan wannan na nufin, wani ne yakeson yai wasa da hankulan mu gaba d’aya. Zaid yai shiru yanabinsu da kallo, kowa da abinda yake Fad’i shiko bai gane abinda suke nufiba gaba d’aya…
Miemah tana zaune agefen Zayyad tana hawaye ganin haryanzu shiruu babu motsi tattare dashi, sai adduoi take tofa masa amma babu chanji. “Ya Allah kabashi lafiya.Abinda take
fad’i aranta tun tuni kenan. ‘karar wayarta ne yakatsemata wannan tunanin. Ganin momy
ce ke kiranta yasa tai saurin share hawayenta tas! Sannan tayi receiving’ Hello Mommy.
“Sweetheart ina kikaje? mundawo gida bamu samekiba. Rasa abun fad’a tai, tashiga tunani “Taya zanfara fad’a musu cewa Zaid yayi mumunar hatsari rai ahannun Allah kuma nice sillan, lnaaa wallahi bazan iyaba. Shiruuu da Mommy taji y’artata tai yasa hankalinta ya’kara tashi ‘Miemah lafiya, don Allah kicemun kinanan kalau babu abinda ya tsameki.
Har yanzu Miemah batayi maganaba. Kukan Mommy taji awayan “Miemah kifad’amin inda kike yanzu zamuzo tareda Daddy mud’aukeki mudawo dake gida, Sweetheart speak to me please shiru ba magani bace. Miemah ta’kasa fad’in komai har saida taji muryan Ma’inah cikin damuwa take magana cewa” Twinny meye ya tsameki? Kodei Maisha ce tasaceki?
Anan ne Miemah tafashe da kuka tafara ambaton sunan “Zaid’ bata tsaya sun ‘kara wani kalmaba ta katse wayan tacigaba da kuka. 
Sake wayan Ma’inah tai yafad’i kasa, inda ta tsaya shiruu tamkar gunki, sanda tai tsayuwar akalla minti biyar sannan tafara zubda kwalla tanacewa’ Mommy meye yasameshi, Mommy Zaid, Mommy Zaid, Zaid, Daddy meye ya sameshi? 
“Ki kwantar da hankalinki Mamana he will be fine. Daddy yashare mata hawaye sannan yajuye Gangaren Mommy yanacewa’ ki kula da ita yanzu zanje gidan Zaid. Mikewa Mommy tai wuf!!! tarike hannayen y’arta “ai tare zamu tafi, Y’ata Miemah tana bukatana kusa da ita awannan lokacin. 
Sanda sukayi Sallama da Umma Aisha, Sannan suka nufi garrage ba tare da bata  lokaciba Daddy yaja mota tamkar zata tashi sama. Ahaka yacigaba da tuki har saida ya’kai ZMZ Mansion. Babu sassauci ya juya fuu! Aka bud’e Masa gate suka ‘karaso ciki. Sunfuto aguje, ana musu magana babu wanda suka saurara har saida suka kai falon Zaid. 
Bayan yayi sallama da Ba’ki, dawowarsa palour saiga surukansa duka biyu. Ma’inah tayo wajensa aguje tarungumeshi kai tseye tana kuka Ya rasa meke faruwa. Share mata hawaye yafarayi cikin rud’ani, yana rarrashinta “kiyi shiru kinji, waye ya tabaminke fad’amin, yanzu zanje in koya masa hankali. Ina Miemah? Mommy da Daddy suka had’a ba’ki alokaci d’aya suna tambayansa. Miemah Kuma? Zaid ya’kara maida musu da tambayan, ‘Ai ni tun d’azun na rabu da Miemah, inako Zan ganta cikin wannan daren. “
“Har yanzu Miemah na tsaye akansa, duk sahon awowinda tai ad’akin addua take tofa masa Kuma ko kad’an babu chanji a tattaredashi sai yanzu yatsunsa suka fara motsi ahankali ahankali. Miemah ta mike fuskarta sake Shar! Farin ciki ya mamayeta. Ganin yafara samun sauki, wannan lokacin ne yakamata ta sanar da mutan gida abindake faruwa. Aguje Miemah tafito tanata zumudi, ahaka ta gangaro kasa har zuwa falonsa tana shigowa idanuwarta akan Zaid suka fara fad’owa “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun, Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ a tsorace tafara ambaton sunayen Allah tana mamaki. Ba shiri ta zube kasa idanuwarta ta zaro sosai takebinsa da kallo, ba’kinta ko sun kasa rufuwa tsabar mamakin kallon Zaid da tai. “Kenan Zayyad newanda yai hatsari? Mafarkina yazama gaskiya Zayyad ne wallahi ba Zaid bane. Haka tafara zuba maganganu ita kad’ei tamkar zarerriya. 
Mommy ce tai saurin zuwa wajen y’arta, ta rungumeta “Sweetheart meye yasameki? Kuma meye yakawoki nan? Aguje Ma’inah tayo wajen Y’ar uwarnata cikin hawaye taketambayan Zaid ‘Meye yatsameta? Teddy please tell me you are fine. Har yanzu Miemah ta‘kasa furta wani kalma. Saida Daddy yazo yariketa alokacin jikinta na karkaruwa sosai. Zaid shima mamakin ganinta agidansa yayi sunata tambayansa shima shiru yai bashida amsa. 
Awannan lokacin ne suka amsa sallamar Baba dasu Aunty Nasiba, Aunty Rahila hardasu Anisa da kannenta alokaci d’aya, sun tahone tareda rundunan y’an Sanda Kai tseye suka karaso cikin falon. Mikewa sukayi dukkansu inda zuciyarsu ta’kara tsinkewa Raz!!! sosai suka rasa meke faruwa agidan. Miemah ta manne kanta tsakanin Mommy da Daddy, Ma’inah koh abayan Zaid ta labe tana lekowa. Zaid ya’kasa furta komai tsayawa yai jugumm! Yanabinsu da kallo tamkar gunki, ya rike Hannayen Ma’inah dika biyu to make sure she is save. “Yana d‘akin ‘Dana kuje kufitar dashi. Baba yafad‘a a tsawace. Babu mutsu y’an Sandan suka tashi Fuuu! Suna haurawa. Zaid neya dakatar dasu. “Stop! Meke faruwa anan gidan ne What is happening? shima yafad’a kusan a tsawacen. 
” Zaid, you can’t believe me, Zayyad yananan anan gidan Kuma yanzu haka yana cikin d’akinka. Baba yafad’a cikin karkaruwar murya. Aunty Nasiba uwar bakice ta tabe baki tana mamaki Dan Gaye ya dawo? Zaid Koh d’aga kai yai sukayi Ido hudu da Miemah sannan yace aje afitardashi yanzun nan ….. Bai karasa furucinsaba Miemah ta katseshi bubu tsoro tace”Babu wanda zai taba Zayyad cikin wannan halin koma menene zakuyi masa sai kujira har sai ya warke tukunna. 
Kallo d’aya Zaid yaima Yan Sandan suka wuce kai tseye sukabi umarninsa, suna zuwa d’akin suka babballe drip da ledan jininda aka makala masa sannan kamar yedda aka umarcesu haka suka dagoshi sama suka sauko dashi falo. 
Tabe baki Zaid yai yazuba masa Ido Zayyad tashi kabar nan gidan before! lose my temper. “You are just pretending my friend leave this house. Baba ya dakamasa tsawa. He is not pretending. Miemah tabuga ihu ‘Da kaina na bugeshi a mota kuma yanzu haka Zayyad ba’ya cikin hayacinsa ku tausaya masa dan Allah. Bai dace wani ya tausayamasa ba, Zayyad bashida hankali, bashida imani kuma bashida tausayi, yanzu zakusan wanene Zayyad. Yayi shiruu nad’an wasu mintuna sannan yafara basu labari. 

“Flashback“ 

Y’an biyu ne, tare aka haifesu da Zaid wannan yasa sukeda mugun kamanni Wanda ba kowane yakan iya banbancesu ba. Sun taso cikin sananin soyayya da gata sedei halinsu ya 
banbanta, shi Zayyad tunda yataso babu abinda yafiso irin dukiya shidei abashi kud’i yata kashewa yana more rayuwarsa shine duniya awajensa. 
Da wannan masananciyar son Duniya ya taso har ya girma, Zaid shine yake kula da dukkan kasuwancinsu shiko Zayyad yana rayuwa a kasar amurka sedei ya kwasa du’kiya yacigaba da more rayuwarsa. 
Ammi ce take goyamasa baya yake kara sakalcewa, sabida harma tafi sonsa fiyeda Zaid, Zayyad yazama shine komai arayuwarta. Baba koh tunda suka taso yafi shukuwa da Zaid ako yaushe burinsa shine yaga shriyar Zayyad, Sam bayason abubuwanda Ammi take nunamasa na rayuwa, ita koh aganinta ga’ta ne ahaka Zayyad ya sakalce yadawo hatta Sallah bayayi yakoma chan Amuka yana rayuwa da turawa, wannan irin halaiyar nasa ne yajanyowa Baba hawanjini. 
Ganin Zaid ne ke kula da dikkanin kasuwancin mahaifiyarsu kishi dason dukiya yasa 
Zayyad dawowa gidansu dake cikin babban birnin China nan ne yafara farautar rayuwar Zaid, burinsa yakasheshi domin yakoma matsayinsa a kasuwancinsu. Ahaka yacigaba da farautar rayuwarsa batareda sanin kowa ba yasa guba cikin abinci yakaimasa har wajen aikinsa Amma amaimakon Zaid yaci abincin Baba ne ya ziyarcesa a ranar yana zuwa daman da y’unwa acikinsa haka yazauna yagama da abincin tas! Daga nan ne yasume aka kaishi asibiti likitoci suka tabbatar musu cewa guba aka sakamasa cikin abinci, dakyar baba ya rayu. CCTV camera ce ta tabbatar musu cewa Zayyad ne yasa guba cikin abincin. Tun daga wannan ranar Hajiya Turai tafara boye Zayyad a kasashen duniya daban daban. Yan Sanda sunyita nemansa amma babu labarinsa, Bai ‘kara bayyana kansa ba kuma sai Sanda Baba ya’kara aure anan ma yadawo yai yunkurin kashe Matar Allah baiyiba ahaka ya’kara komawa inda yafito daga wannan ranan babu labarinsa har izuwa rana itayau daya bayyana agidanmu. 
Wannan kenan. “‘End of Flashback “‘ 
Baba ya gama basu labarin ne idanuwarsa a jike chakap! Hawaye sun ‘kasa tsayuwa daga idanunsa “Wannan kad’an ne daga cikin munanan halaiyar Zayyad, wannan d’an labarin danabaku kad’ei nasan zatasa kowannenku yacire tausayin Zayyad daga cikin zukatansa. “Banda ni” Miemah tai ajiyar zuciya ta furta kalmarda takeson furtawa tun tuni. Juyowa sukayi dukkansu suka maida idanuwarsu akanta “Tabbas Zayyad ba mutumin arziki bane amma kamar yedda Hausawa sukace yatsu basa tsayuwa tsayi d’aya maganarsu gaskiya ne, don Zayyad yanada mugun hali aimu ba haka mukeba ya’kamata mutaimaka Masa inyaso na yarda nakuma amince idan yasamu lafiya ku hukuntashi iya son ranku. 
Baba yabud’e baki zaiyi magana, Zaid yadakatar dashi” Baba kyaleta na amince amaidashi d’akin ba’ki. Babu kalmarda Baba ya’kara furtawa fuu!!! Ya bankado kofa yabar wajen cikin tsananin bakin ciki. Y‘an Sanda sun maidashi d’akin ba’ki kamar yedda Zaid ya umarcesu. Miemah kam sai kukan farin ciki take tana dad’a gode masa. 
Ma’inah ma ganin Y’ar uwarta ta damu da Zayyad d’in sai tayata farin ciki take itama tana godemasa da kokarin amincewa da maganar yar uwarta dayayi. 
Shima flskarsa sam babu walwala, murmushin karfin hali yake sakomusu kurun, bai bata lokaciba ya’kira layin Likita. Sunyi zamanjira karfe 10 da rabi dare likitan ya karaso. Zaid yaimasa jagora zuwa d’akin Zayyad yadubashi iya iyawarsa jikin sai Kara tsananta yake Yana dap da loosing brain nashi dazaran anbarsa ahaka harzuwa wayewar gari ba’a kiramasa babban likitanda zai dubashi ba. 
What? Kai fa meye aikinka why can’t you treat him? Kad’a kai likitan yai “Gaskiya wannan Kam yafi karfinmu bama ni kad’ei ba yafi karfinmu dukkannin mu sedei anemi 
shugabanmu Doctor Manav Muhammad Al’slddlque na tabbatar maka cewa shine kad’ei wanda zai iya treating nashi cikin mintuna kalilan idan Allah ya yarda daransa agaba zai warke, sabida yafl duk likitocin Duniya kwarewa tafannin magance kowani irin ciwo. Doctor Manav? Zaid yamaimata sunansa ahankali, Sannan yace” Tabbas his name is familiar sedei a ina yake kuma taya zan nemeshi? Doctor Manav baya zama anan duk dacewa nan ‘kasarsu ne, yakan ziyarci kasar nan kusan ako wace mako, Yana Kasar USA anan yake aiki awata babbar asibitinda yafl kowani asibiti kyau aduniya “Manav_Clty_Hospltal kenan wandake cikin Sanfransisco. Dakata , I don’t care about his life. Zaid ya katseshi ‘Fad’amin taya zan samu ganinsa cikin gaggawa before wayewar gari. “Allah dei yasa yana ‘kasa inada layin PA sa bari na Kira muji daga bakinshi. Ran Zaid abace yafito falo yashedamusu yedda sukayi da Likita, razzz! Zuciyar Miemah ta tsinke batasan sanda taji hawaye a idanuwarta ba. “Ya Zaid please do your best, please save him. Tafadi hakanne yayinda hawaye masu tsananin zafi suke gangarowa kan tattausar kunshinta. Congratulations Sir, Likita yaflto da walwala a fiskarsa yashedamusu cewa sunyi magana da PA Dr Manav Kuma sun tarbi babban sa’a yana nan ‘kasar dama gobe zai koma Sanfransisco, ya shedamusu adreshin gidan zasu taho nanda awa biyu duk dacewa booking dinsa akeyi sunci darajar Sanin mahaiflyarsu (Hajiya Turai) dayai shiyasa ya amince dazuwan. Million biyar yake duba kowani booking patient, Emagency kuma million goma yake dubasu. 
Babu matsala, Zaid yafad’a cikin sanyin murya ‘Kud’i basune abun damuwa ba, burinmu kawai yazo yadubamana shi ko Allah zaisa adace. lnsha Allahu za’a dace kuwa. Likita yafad’a da tabbacin maganarda yai. “Michael kujerun zaku tattara ku tabbata kun kwaso komai na falon mu zamuje d’aki mufara tattare”. Babu sallama sukaji dirkowan kattin maza cikin falon basusan hawaba bare sau’ka kurun suka Fara fito da kujerun falo dasu TV dasauransu. Zaid yaimusu magana amma babu mai sauraronsa Saida suka kwaso komai suka kai waje sannan d’aya daga cikin mutanen yanuna Masa ID Card dinsa “Sunana lnspector Adebayo Okorocha kotu tabamu damarzuwa nan gidan mukoreku sabida Mai fili tana bukatar wajenta, Account dinka na banki duk munyi hacking nasu sabida ba kud’adenka bane kotu tamaidawa mai kud’i dukiyarta atakaice dei Zaid Muhammad Zabir ayanzu babu abinda Kotu tarageku dashi dakai da mahaifinka sai suturun dakejikinku suma din ka’ra ce kotu tayi muku sabida haka before sojoji sushiga wannan maganar gwara kawai kufita ku bar mata gidanta. 
What? Rud’ani da mamaki ne ya bayyana nan ta’ke a fuskar kowannensu awajen barin ma Zaid. Babu shiri hawaye suka fara saukowa daga idanuwarsa,jikinsa na bala’in karkaruwa yayinda yabud’e baki zaiyi magana kenan yaga shigowar Hajiya Turai tareda Maisha da Saminu cikin falon. 
“Ma’isha’ Mommy ce ta ambaci sunanta cikin sananin mamaki tamike wuf! Hawaye suka fara gangarowa a fuskarta “Maisha sam wannan ba halinki bane don Allah kada ki biyemusu. 
Jikinta yai sany’i nan ta’ke tana kukan zuci Harga Allah tana kewar Momcy da Dadinta sedei babu damar nunamusu hakan sungujeta alokacinda tasha’ku dasu fiyeda kowa a duniya. Waina idanuwarta taimusu cikin gadara da Isa. Zuciyarta na tafasa amma bata nunamusu haka ba. 
“Sojojinku, y’an Sanda da Bosawanku duk sun zama mallaki na dama Hausawa sunce kayan aro baya rufa asiri, Cewar Hajiya Turai cikin ta’kun ka’saita ta’karaso har kusada d’an nata tanacewa ” Sorry Zaid you loss sai yanzu zakasan amfanina a duniya, yanzu ne zakayi da‘nasanin fiflta mahaifinki akai na, Kuma yanzu ne zakasan ma’anar Rayuwa. Enough ‘ , Ammi you are too much. Baba ne ya shigo adeden wannan lokacin ya katse masa maganar “Zaid kada ka tan’ka Mata kuzo mutafl, mubar mata gidan wallahi Tallahi sai tayi da’nasani kuma da’kanta zata nemomu. 
Daddy kam tunda sukashigo Saminu kad’ei yakebi da Ido mamakin halinsa ne yakeyi tun tuni ya’kasa furta komai, tsaban bakin ciki shi ko digon hawaye basu zubanmasa ba. Miemah ce taketa kuka tareda Umma Aisha. Sun tattaro kamar yedda aka umarcesu harda Zayyad akasashi a motar Daddy, Aunty Nasiba girma ya fad’i ita da Y’ayanta sai kuka suke suma harda Mamy duk motocin Daddy ne ya kwasosu duka. 
Daddy yace sukoma gidansa suyi maneji kafin su samo wani gidan wacce zata daukesu. Sun shigo Motar dukkansu, Daddy ne yakejansu, a d’ayan motan koh Zaid d’an Aunty Nasiba ne yake tuka su. Sanda sukayi nisa da tafiya wayan Zaid tafara ‘kara dasauri yad’aga ganin Likita ne yake kiransa. “Zan tura maka adreshi yanzu nan kujuya da motocinku ku taho. Likitan bai tsaya Zaid ya amasaba haka ya katse wayan. 
Babu musu Zaid yabi adreshin daya turo awayansa suka juya da motarsu zuwa chan, Karfe biyu da rabi tsakar dare suka karaso. Gini ne zafaffiya mai d’aukan ido, Sun rasa dalilin dayasa Likitan yagayyatosu nan har saida suka karaso ciki wani ne yai musu jagora har izuwa sitting room, Mutum d’aya tak! suka tarar a falon Kuma k0 shakka babu Doctor Manav ne sabida duk wannan bayanan da Likita yai akansa sunje dedei da wannan hadedden bawan Allah dasuka gani. 
“Zaid kaduba Gidan Sosai idan yayi maka na bakashi har abada’ Abunda Dr Manav yafad’a kenan cikin sassanyar murya irinna likitoci. Tun kam Zaid yayi wani furuci Aunty Nasiba tafara shigowa ciki tana duddubawa “Bawan Allah mun gode Allah ya biyaka da gidan Aljanna thul Firdaus wannan irin gida haka Masha Allah. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]