[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 34 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE
CHAPTER34
“Wuukaa. lhun da Maisha ta daka kenan yayinda ta sake baki, tawangala idanuwarta kororo kororo, cikin sananin rawanjiki ta d’aura guiwowinta a ‘kasa tana ko’karin neman afuwarsa.
“Baba kaya’femun, wallahi na amince kai ne mahaifina, Baba na tuba dan Allah kabarni da rai na, kada ka kasheni har sai na tarwasa rayuwan Ma’inah domin shine babban buri na a duniya idan kuma ka kasheni Ma’inah zata sake ta wala tareda masoyina Zaid su aikata dukkan abinda sukeso karshentama Y’aya zasu samu, idan hakan yafaru kuma kaga na shiga uku. ‘
Cikin nunfashi d’aya ta jero Masa duk wa’innan bayanan, Ahankali Saminu yajanyota. A tsorace tamike tana sauraron abinda zai ‘kara fad’i. Saiko ya rungumeta sosai shima yafara zubda kwalla yanacewa’ Maisha duk wa’innan musgunawar dakikaga nai miki wallahi ba’ason raina nai hakan ba, so nake naga taurin zuciyarki, ko zaki iya kasheni sanadiyar farin cikin ki. Kinga kenan ayanzu na’fl kowa farin ciki a duniya, Y’ata ta d’auki halina sak! Daman Hausawa sunce kyaun ‘Da ya gaji ubansa, Maisha sai yanzu na tabbatar dacewa ke Y’ata ce ta hakika. Allah yai miki albarka.
Nan ta’ke farin ciki ya mamaye fuskarta, itama d’aura hannayenta akafad’arsa tai tanacewa’ Baba ayanzu Ma’inah ce matsalata so nake mu gurbata rayuwarta gaba d’aya sannan ni nakoma gidan Mommy da Daddy nacigaba dazama tare dasu amasayin Y’arsu.
Murmusawa Saminu yai” wannan ai tafi komai sauki, komawa gidan Turai Mafia zumuyi munemi gafararta na tabbata zata yafemana Kinga daga nan ahankali ahankali zamu gurbata rayuwarsu duka cikin dabara zamu mallaki dukkan dukiyarsu mukoma chan ‘kasar waje mucigaba da rayuwa.
Ta tsaya shiruu tana tunani har saida ya kammala bayanansa sannan ta sauke nunfashin kwanciyar hankali tanacewa” Lallaikam Saminu akwai ilima, hakan za’ayi.
“Kekkyawar fuska? Zayyad Muhammad Zabir?. Maganar da Zaid yaketa nanatawa kenan bayan rabuwarsa da Miemah. Abinda ya’kara d’aure masa kai kuwa” a ina Miemah tasan Zayyad kuma wace alakace take tsakanin su?. Damuwa da bacin rai ce tahanashi sakewa awannan lokacin. Nan da nan yasa ki a motarsa da ‘karfi yafara tuki. Motoci a hany’a sai basa wuri suke, babu wani d’an sandan da ya isa yai masa magana, dayake motocinsa duk
tana daukeda sunansa a plate Number kamar haka.ZMZ101.
Ofishin mahaifinsa ya nufo kai tseye, yana isa aka tsanar masa cewa Baba yafita yanzun nan ya tafi asibiti gun Mainah, Shi Zaid baimasan masoyiyar ta’sa tana asibiti ba. Rikicewa yai nan da nan yafara ambaton sunan Allah fuskarsa na had’a gumi, ta’ke ya mance abinda takawoshi wajen Baba. Zuciyarsa ce tafara bugawa du’kan uku uku Yayinda ya’kara Jan Motar “Kiiii” yai hanyan ZMZ Private hospital, layin Mami yaketa trying sedei yayita ‘kira ba amsa, Hakan yasa Zaid ya’kara rikicewa sosai. .
Zayyad yana taflya ahankali ahankali yake biyeda Baba yayinda suka ‘karaso cikin asibiti. Ya d’aga ldo cikeda takaici yazubama asibitin ldo.
Nan da nan hawaye suka taro masa a ido “ZMZ Private hospital” yakaranto sunan asibitin, ahankali yace “Zaid Muhammad Zabir Private hospital kenan”. Awannan lokacin ya kasa jurewa kai tseye yafara zubda kwalla.
Cikin tsananin tunani yake har sanda suka karaso cikin asibiti Yana biyeda Baba suna tafiya jugummm! Baba nata zuba Masa surutansa, shiko Yana baya baya jikinsa na karkaruwa jiyake tamkar ya ruga yabar wajen amma babu hali. Ahakan yai ajiyar zuciya aransa yake‘ zaro adduoi yana fatan kada Allah yasa Zaid ya bayyana anan wajen agane’shi.
Wata kantamemen d’aki suka shige, Zayyad yana faman rabe rabe a baya saiko yahango mara lafiyan ta taso aguje tayunkuro wajensa. Zaro idanuwa yai yanabinta da kallo yayinda tarungumeshi sosai tanacewa’ Sweetheart Ina ka shiga mukayi tanemanka. Rasa amsarda zai bata yai. Ya had’iye miyau a tsorace yace” ki kwantar da hankalinki, I’m fine.
Mamy, Aunty Rahila dasu Anisa duk zuwa wajensa sukayi sunata farin ciki Ma’inah ko ta’kasa komawa gadonta, Gam! Tarike Hannayensa sai shafa fiskarsa taketayi tamkar amafarki sai gashi ya bayyana agabansu “I love you Zaid kada ka ‘kara zuwa wani waje kabarni ba’nason kayi nisa dani daga yau, because I can’t live without you my Boo. Ta rad’a masa a kunne.
Nan ne Zayyad ya bankad’ota dasauri ya mike yana mulka Baki tareda girgiza kansa “Inaa lnaa bazaiyuba ba zan ‘kara aikata wani laifinba kuma, laifuffukanda suke Kai nama yaushe na’kare dasu. Abinda yafad’a aransa kenan, Ma’inah ta mike da mamaki afuskarsa yayinda take tambayarsa Zaid lafia? Babu abinda Zayyad yafad’a manna musu hauka yai sunata magana shiko yabud’e kofa cikin gaggawa yasa kafa waje daniyar barin d’akin,juwowarsa keda wuya sai k0 yai kacibus da Zaid alokacinda yataho aguje yana kokarin karasowa cikin d‘akin. ‘
Zaid ya’karaso aguje, yanazuwa ba’kin kofa sukaci karo da wani, ya bugeshi sosai kansa yahade da bango, Nan take idanuwarsa sukafara ganin bibbiyu yana kokarin danne wajen da yabuge sai ko yaga jini na diga yaji ciwo sosai ahaka yadaure, ya mike ahankali domin yaga kowayene wannan mutumin, Babu wanda yagani dagashi sai shi awajen da alamu mutumin yaji tsoro yagudu domin kada aganshi atuhumeshi da laifin rashin kula.
Dukwannan ciwon Sam bata dameshiba, shidei yaga halinda Ma’inah kece shike ransa ayanzu kwata kwata zuciyarsa ta ‘ka sa sukuni. Ahaka yabud’e kofa dakyar ya’karaso cikin d’akin. “Meye ya tsameka Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Suka had’a ba’ki alokaci d’aya suka taru akansa, Baba yana share masa jinin da cotton “Zaid lafia yanzu kabar nan lafiyanka kalau meye yasameka kuma?
Babu abinda yafad’a mikewa yai kurun yakoma bangaren Ma’inah, Doctor yana cire mata bandejin drip ahanun damarta, shiko yawuce ta d’ayan gefen, Yana hawaye yayinda yarungumeta sosai yanacewa” I’m sorry Love, I’m really sorry please try to forgive Habibeee. Ya turo Baki tamkard’an Karamin yaro.
Tana zubda kwalla sosai inda tafara shafa kansa, cikin muryar shagwaba tace “Habibee is already forgiven Amma dan Allah Habibee kada ka’kara nesa dani because habibtee wants to be very close to Habibee Everytime.
lrin wannan murmushin nasa dake ‘kara bayyana dimples din fuskarsa yasakar mata “0k my love lnsha Allah”. Doctor ne yaketa gyaran muryarsa tun tuni suko suna cikin wata
duniyar soyayya babu kunnenda yaji abinda Doctor ke fad’a. Har tsaida Baba yasoma bakinsa “You are not yet married please kada ku wuce gona da iri.
Nan ne hankulansa takomajikinsu, dasauri Zaid yaja dabaya “Tun tuni nake sauraronka k0 kana tsammanin banida kunnuwa ne’ yafad’a cikin launin Kore kunya da hau’ka. “Sorry sir’ Doctor yasunkuyar da kai kasa yanacewa’ zaku iya tafiya gida she is now perfectly fine.
Zayyad yanata godewa Allah da Allah yai Zaid baigansaba sai hamdala yake yafito aguje yanatajuyejuye kada wani yagansa. Ya fito babbar harabar asibiti Yana faman boye boye da gudu kenan yahaduda gagarumar tsausayi, Motace ta bigeshi anan yazube jinajina jikinsa. 
“” Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Miemah ta sake siterin mota arazine taflto,jikinta na bala‘in karkaruwa a tsorace ta leko mutumin “Allah sa yanada rai’ adduar da takeyi aranta kenan. Tana ganin fuskarsa zuciyarta ta‘kara bugawa razzz! Mafarkinta yakoma kan Zaid Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun‘ tana hawaye sosai yayinda tafara jijjigasa tanacewa’ Zaid katashi yanzu zan kira jama’a sushiga da Kai cikin asibiti zaka samu sauki lnsha Allahu. 
Wannan wani irin masiface zuwa nai domin naduba Halinda jinin jikina Ma’inah ke ciki gashi kuwa muguwar tsausayi ta riskeni, na lahanta mata jininjikinta kuma ‘dan gatan saurayinta wacce take matukar ji dashi, Zaid Allah dan karka mutu. Tamike domin tanemo jama’a saiko ya damke hannunta. Dasauri takoma gunsa tanacewa’ Ka ringa nunfashi babu abinda zai sameka kaji. 
Idanunsa a rintse ba’tareda ya’san ko wacece ta bigeshi ba, cikin wata irin duniyar azaba yace” Baiwai Allah na rokeki dan girman Allah ki kaini gida, inyaso sai ki Kira likitan achan adubani na tabbata idan kinshigadda ni cikin wannan asibitin mutuwa zanyi. Daga wannan kalmar sai ya sume mata awajen. 
Miemah tasha mamakin wannan maganarta sa, sai dai Kuma taji tsoron hakan sosai yazama dole takaishi gida da gaggawa domin tanemi likitanda zai dubashi. Ba tareda bata lokaciba tajawosa dakyar tashige dashi bayan motarta ita koh tayi gaban mota Kam kace Kobo sun haura kan titi. 
“Shikenan ba matsala’ Hajiya Turai ta jinjina kai taredacewa ” Na amince mucigaba dazama taredaku sabida na gamsu da dukkan bayananda kukayimun na fahimci cewa kunyi danansani matuka, Ba matsala na yafemuku. 
Mun gode Hajiya Allah yabar zumunci” Saminu yafad‘a kansa akasa. Hajiya yanzu kenan kina nufin kin rabu da Zuri’arki har abada bake Basu? Cewar Maisha uwar kisisina. “Kwarai da gaske ayanzu ki kaddarama ban taba aure arayuwata ba bare nasamu y’aya narigada na gogesu a littafina. 
Saminu Yana tsotsa keyarsa yayinda yasauke murya ‘kasa yanacewa’ Toh Amma Hajiya gani nai wannan daular dasuke mora ayanzu ta’kice, inaga ya’kamata ki anso kayarki domin na tabbata idan kin barmusu wannan dukiyar ba’zasu taba sanin zafin rabuwa dake dasukayi ba. 
“Niko nasan dahaka” Hajiya Turai tamike tana murmushin muganci taredacewa” Kada kudamu dabatun dukiyata Gobe da yardan Allah Zuri’ar Zayyad zasu koma Talakawa tubus! bayin Allah abin tausayi abinci ma rasawa zasuyi, zasukoma may’unwata almajirai. Na rigada na Kai ‘kara Kotu gobe da yardan Allah kotu zata maidamin da dukkanin 
ababena. Zaid, Munah da Mahaifinsa zasu nemeni su rasa karshentama akan titi zasu kwana. 
Cikin masifar farin ciki Ma’isha da Mahaifinta suka hade Ido tareda junansu suna 
murmushi. Kowannensu da kalar burin dake ransa. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]