[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 33 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE

CHAPTER 33
Karku matso kusa Dani’ ya kwato bindiga daga hannun sojan. Nan ne duk suka maida makaman yakinsu. Ammi ta’kama baki tana salati ‘Abarsa yata tafi ihun data maka kenan, ta’kara wata ihu tanacewa’ Abude musu kofa su tafi, kuma kasani Zaid daga yau bani ba kai har abada mun rabu kenan, Daga yau ka kaddara bakada wata uwa a Duniya. Ni kai na daga rana nayau nacire nauyun kowa akaina nakoma tsohuwar Turai wacce bata tabayin aureba bare tasamu y’aya. Kasani daga yau ni Hajiya Turai Mafiya Banda kowa aduniya sai dukiyata sun ku daraja sau dubu.
Ya zuba mata ido cikeda mamakin maganganunta har tsaida takammala bayanan ta tsagaita Shiko bai kara wata kalmarba haka ya rike hannun ‘kanwatsa suka fice daga jirgin. Duk kanin zuciyarsa saida yazub da kwalla awannan lokacin yana takaicin rayuwar duniya, atunaninsa yafi duk duniya rashin sa’a. shikuma jarabawarda Allah yai masa kenan. Munah itama shiru tai suna tafia jugum!!! tamkar tafiyar hawainiya.
Wani ne fuskarsa a duhu yake kwance gindin wata babbar bishiya ya Iabe anan jlkinsa na karkarwa sanyi na ‘shigeshi sosai, gashi k0 kayan kirki baisakaba sai dai mutane suyita wucewa suna zolayanshi ana masa danya. Shi ba mahaukaci ba’ amma ana masa kallon mahaukaci.
Hakan yasa wannan mutumin ya tashi ya chanza gurin zama, yayinda yazo Haye hanya CE tsausayi’ ta riskeshi mota ta bigeshi jikinsa duk jinajina.
Mimah ce ta fito daga wannan motan tana salati a tSorace, mutane aka taru wajen nan anata nanata mutuwa yayi, Allah yajikansa daman wannan mutumin anan wajen ya’saba kwana bashida kowa. Wannan irin maganganun da mutane suke akansa yasa Mlemah ta ‘karaso domin taga‘ne koshi waye tana zuwa kuwa fiskar Zaid tagani. ‘ZAID? Ta kwala ihu meyesa ake duk wannan maganganun akanka, kuma meyakawoka nan wajen? Wata tsohuwa ce tabata amsa cewa ‘ Baiwar Allah wannan saurayin sunansa Zayyad anan yake kwana anan yake tashi, Kuma naji ajikina kece Zaki taimaka masa,yana matukar bukatar taimakonki awannan lokaci.
“lnna lullahi wa Inna ileahi rajiun wannan wani inn mafarkine Mlemah tafarka ba shiri. sai had’a gumi take jlkinta na karkaruwa tana kuma nanata salati aranta. Tun ranarda tahad’u da wannan bawan Allah Zayyad, batasan koshi wayeba Amma yanzu ba dama Tai barci ko yaushe sai tayi mahafarkinsa yana bukatar taimako daga gareta. Wannan mafarkin datai ayau yasa ta gaskanta sauran mafarke mafarkenda takeyi ako yaushe, Babu Shakka akwai wata boyeyyen sirri gameda Zayyad kuma ko ina yake yana bu‘katar taimakoma na gaggawa.
Mutanen gida sun wuni cikin tsananin damuwa, y’an Sanda sai zirga zirga suketayi ko in an kafa tsaro ana neman Zaid da Munah. Ma’inah ta kasa ci bare Sha ayanzu burinta kawai shine taganta tareda Zaid, rashinsa zai iya janyomata babbar matsala arayuwarta sabida babu wani namijinda take gani amasayin na miji face Masoyinta Kuma abar kaunarta Zaid. Su Mommy sai ranashinta suke ayanzu sumanta biyu kenan, Nunfashi dakyar takeyi karshenma asibiti aka wuce da ita.
Cikin wannan tunanin Miemah ta lallaba tatashi, damuwa da rudani ne sukayi Mata yawa awannan Iokacin ga tunanin Satan Zaid da Maimunatuh, gakuma tunanin halinda Ma’inanta ke ciki, uwa uba Kuma tunanin wannan bawan Allah Zayyad. Kasancewar tana barci alokacin da Ma’lnah ta suma suka tafi asibiti babu kowa agidan, ita kad’ei akabari, ta fito falo cikin tunani duk dacewa babu wanda tagani a gidan bata damu da tambayan ko Ina sukajeba, samun waje tayi tazauna a kujera tacigaba da sana’ana ta tunani
‘Ina bukatar taimakonki Baiwar Allah ke kad’ei ce zaki dawomin da Farin ciki a rayuwata. Banida kowa a duniya. Wannan maganar data doso kunnuwarta ne yasa ta tashi bit!!! A tsorace tanacewa “Kai waye?
Zaid yayi matukar mamakin ganinta ahaka, ya rasa meke tsoratata daga tambayan Ina Mainah shikenan ‘Mlemah lafiya dai? Abinda ya’kara fadi kenan. Ita kuwa Miemah jitayi yace ‘Baiwar Allah ke kad’ei ce zaki dedeita tsakani na da zuri‘ata, ki taimakamin. Cikin hawaye ta nufeshi da runguma, tana shafa fiskarsa “Bawan Allah ban sankaba Kuma ban taba saninkaba amma yazama dole nashare maka hawaye.
Tabe Baki zaid yayi ‘I think this girI is crazy” abinda yafad’a aransa kenan, a bayyane yace ‘Are you Alright? Yafad’a cikin sassanyan murya inda ya’kara dacewa Ni nefa Zaid Muhammad Zabir yanzu muka kubuce daga hannun Ammi, Mlemah Baki gane ni bane? Ya’kara tambayarta.
Kwarai da gaske na ganeka man, wallahi naganeka, Kuma bazan taba mance wannan kekkyawar fuskar taka ba, alkawari nayo maka Insha Allah zaka dawo cikin yan uwanka Zayyad Muhammad Zabir.
Jin wannan sunan daga bakin ta yasa Zaid saurin bankadota kasa, awannan Iokacin fuskarsa cike takeda rudani bila adadin. Amma babu abunda yafad’a barin wajen yai nan take.
Azaune take gindin bishiya tun zuwansu tana rusa kuka babu ci bare Sha. Shi dei Saminu ya Saba da wahala babu abinda ya’kara fad’amata ahaka tacigaba da kuka har saida akayi sallan Isha, Sanda tajira garin yai duhu sosai sannan tamike domin ta aikata abinda tai niya.
Daman ta shirya duk plans d’inta, da daddare zata kone gidan nasu da Saminu duka zata had’a takonesu kowa yahuta, ta gaji da rayuwa da mutumi matsiyaci babu arziki sai tsiyar banza. 
Ta saman rufin d’akin Sarninu tafara konawa a Sannu asannu d’akin ta‘kama da wuta bal_bal, gobara cikin gida abun tashin hankali, ita kanta dakyarta tsere, gidan ta kama da wuta sosai saici take 
Yar gara Maisha koh tuni tashige daji aguje tana neman hanya domin kada wani yaganta azargeta dawani lafin 
Labewa kusada wata katuwar bishiyan mangoro tai tana Iekowa ko zataga anfito da gawan Saminu saiko taji an tabota ta baya. lhu tasaka awannan lokacin jikinta na karkaruwa dakyar ta bud’e idanunta tamkar a mafarki Saminu ne tseye agabanta da wuka ahannunsa. ’ 
Yana huci cikin hawaye, ahaka yacigaba da share hawayensa har sauda yakai ofishin mahaifinsa sannan ne yai ajiyar zuciya yakaraso ciki. Labewa yai aba’kin kofa, har saida ya tabbar dacewa Baba nanan cikin ofishin Nan ne yasauke wata ajiyar zuciya a tsorace yai ciki.Yana shiga Baba yamike I cikeda farin cikin ganinsa ‘My Son, zaid Ina ka shiga? ka barmu cikin damuwa tun tuni nemanka muke. Zayyad ya bude bakinsa a tsorace zai Masa bayani kenan Baba yarufoshi da runguma “Son I love you sooi much karka ‘kara barinmu ahaka kaji D’ana. Awannan lokacin Zayyad yarasa mezai Fadi jikinsa na karkaruwa yayinda ya gyad’a kai ‘Toh Baba Insha Allahu’ yana kokari’n barin wajen cikin dabara Amma babu hali. babban abinda ke tayar masa da hankali kuwa shine kada Zaid ya bayyana anan wajen aga’neshi. 
‘Ma’inah tana asibiti a dalilin batanka,  ya’kamata mutafi domin kaje kadubata Koh’ cewar baba. Tabe baki Zayad yai, ya zaro idanuwa a tsorace tareda had’iye miyau “ko wacece Ma’inah? Yafad‘a aransa, inda ya’kara gyad’a kai a fusace yace’ Toh Baba’ 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]