TAGWAYE CHAPTER 32

TAGWAYE
CHAPTER 32Sai tafiya ake dashi cikin mota, zuwa yanzu Zaid baisan ko awace duniyar sukeba domin Motartasu tayi tafiya mai nisa, kuma duk wannan uban tafiyar dasukayi cikin duhu yake, idanuwarsa a rufe da bakin kelle, Mutanen sun damkeshi sosai, dakyaryake nunfasawa.
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ itace kalmarda Zaid yaketa maimaitawa yana neman tsari daga Allah mahalillici. Bayan sunyi tafiya mai nisa,Awani wuri suka saida motar, Zaid na matukar mamaki, ko a ina suke, awace duniyar suka kawoshi, kodei masu yankan Kai ne. “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ ‘Kara zabga addu’oi yafara aransa,jikinsa na karkaruwa yanakuma had’a gumi alokaci d’aya tsabar irin tsinkewar da zuciyarsa tai ayanzu.
Mutanen sunamasa jagora har tsaida suka haura wata matakala tamkar gida suka shige, Ka’na suka sashi a kujera Sanda suka tabbatarda cewa ya zauna sosai, sannan aka bud’e Masa fuska. Ahankali yabud’e idanuwarsa kuma a tsorace. Sai dai awannan lokacin jiri ya debesa dakyar yataso aka kawomasu ruwa yawanke fuskarsa sannan ya‘kara ganin wajen sosai, Falo ce hadeddiya saidai babu kowa aciki, Zaid yaduba ko ta ina Amma baiga alaman bil adama acikin falon ba Nan ne zuciyarsa ta’kara tsinkewa.
“Shushu Zaid” Muryar Munah yajiwo tun a nesa ta kwala masa kira, Cikin hawaye Zaid ya juyo aguje tafad’a jikinsa tanacewa’ Daddy mugudu tafiya zusuyi damu. “Tafiya Kuma? Ya tambayeta cikin rud‘ani. Gyad’a Kai tai muryanta na karkaruwa yayinda take nuna masa windonan wajen tanacewa’ Ci Cik Cikin jirgi muke zasu tafi damu.
A wannan lokacin ne Zaid ya lura da windonan wajen kamar yedda tafad’a hakane cikin jirgin suke “What, No, No… Ya sula ihu, yayinda yad’auketa sama suka nufi kofar exit, yana kawo kafa yai kacibus da Mahaifiyarsa Hajiya Turai tareda wasu ma’ka ma‘kan sojoji. Afirgice Zaid yafara ja da baya. Hajiya Turai tanabin sahunsa har ksaida yakai ba’kin kofar sannan ta rungumeshi tareda cewa”A rufe kofofi sannan kowa yasany’a seatbelt nasa jirgi ta’kusa tashi, daganan babu inda zamu tsaya sai Beijin (China), ‘Dana karkaji komai mahaifiyarka zata maida ka inda ka taso, where you actually belong my dear.
……………………..
Saminu ya tattara akwatunansu birjik yafito dasu waje inda yazauna anan yafara rusa kuka
yana tunanin halinda Maisha zata shiga bayan ta’ dawo gida ta tarar dasu cikin wannan halin, Hajiya Turai takorosu daga gidanta ta kumace kada su’kara nuna mata fuskokinsu.
Babban abun tashin hankali Kuma shine basuda halin komawa wanchan gidan nasa ta Maiduguri sabida duk akewaye da y’an Sanda yake ana neman Maisha ruwa ajallo. Yana wannan lissafai aransa kwatsom Sallamar d’iyartasa ta doshi kunnuwarsa. “Hello Saminu lafiya naganka anan da akwatuna. Shiru yai tamkar ba dashi ake ba, Maisha taja masa d’an guntun tsaki tareda cewa “Halinku kenan talaka sam baku saba da dad‘i ba, if not meyesa zakabar AC cikin parlour kazo nan varanda kana kashe kanka da zafi? Mikewa yai yafara kame ka’me, gaba d’aya baisan ta inda zai bullomata da zancen ba.
Maisha ta share shi awajen tanufo falo, anan ne taja kofa Kuma akulle take babu hanya, ta‘karajan kofar shiruu haryanzu. Awannan lokacin ne zuciyarta Tai masifar tashi inda takoma wajen Saminu cikin tsananin tashin hankali da damuwa take tambayarsa “meyesa kofar take a rufe? Kuma Ina madam take? fadamin Saminu. Ta d’akamasa tsawa. “ Saminu yamike cikin sany’injiki ya kwaso akwatunansu yanacewa’ Biyoni mutafi, Madam ta koromu daga gidanta.
Anan wajen Maisha ta’kasa controlling balance d‘inta ta’ke tazube kasa “shikenan abinda take gudu ya samesu. Fashewa da kuka tai awannan lokacin “Saminu saida nagargadeka batun Matan nan, na cemaka ka bita a Sannu amma ka‘ki, to ga sakamakon Saminu, Allah wadaran Uba irinka ka hana Y’arka Zama awajenda ranta keso, Saminu na tsaneka Kuma daga yau kada ka’kara kirata y’arka har abada Sambo shine ubana ba kai ba, shashasha ragon banza kawai, Namiji ba zuciya …….
Bata ‘karasa kalmarda take kokarin furtawaba, Saminu ya’kasajure sauraron wa’innan bakaken maganganun da takejefomasa, duk duniya babu wanda ya isa yafad’a masa ba’kaken maganganu irin haka ya kwana lafiya barrentana Maisha Y’ar cikinsa. ”Baki isaba wallahi’ Ya fad’i wannan kalmarne adedei lokacinda yasa hannu a fuskarta babu tsoro,ko da’nasani ko fargaba a idanuwansa, kai tsaye ya shareta dawata d’an banzan Mari taredacewa “Shashasha kawai k0 don kinga ana binki a Sannu shiyasa kike kokarin wuce gona da iri, To kisani babu wanda ya isa yafad’amin ba’kaken maganganu yakwana lafiya?
Tamkar a mafarki Maisha ta tsaya chak!!! shiru! tana binsa da kallo cikin tsananin mamaki “Saminu kanada hankali kuwa?. Babu abinda yafad’a hannayenta yariko kurun” Maisha kada kibata Mana lokaci, kuma kada ki’kara furta Koda kalma gudace, ta’so mutafl. Da ‘karfi ta kifto hannayenta cikin hawaye ta maidamasa da martani” Saminu ka mareni how dare you, bakada hankali koh. Babu tsoro ta d’aga hannu sama zata rama marinda yai mata, yariketa tun kam ta’karaso fiskarsa, Sannan ya‘kara shareta da wata shegiyar mari ad’ayan gefen kumatunta, ransa abace yayinda ya damke wuyanta sosai yanacewa’ Maisha sai na koyamiki tarbiya sabida naga alama kina bukatarta.
A tsorace Maisha tafara magana, Awannan karon ta tabbatar dacewa wannan mutumin ba hankaline gareshiba kuma zai iya hallakata anan babu kuma wanda zai sani. Muryarta na bala’in karkaruwa tace “B Ba Bana iya nunfashi sakemin wuyata. 
‘Kara damke wuyan nata yai da ‘karfin gaske yace’ Zaki bini mu tafi ko kuwa? Jikinta na karkaruwa ta amsa masa kai tseye “Ehh mutafn, sakemun wuyata Saminu zaka kasheni. 
“Saminu? Ya d’aka mata tsawa “meye sunana? Dasauri ta amsa, in a shakky voice “S su sun sunanka B b be baba, mutafi baba. Maisha ta’kara rusa kuka tana nanata “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun tareda Astagfirullah’ aranta. 
“Wawiyan yariny’a kawai sai na koyamiki hankali. Cewar Saminu ‘Kawai don kinga ana ragemiki toh baki isaba wallahi, uwarki wacce mukazauna tare shekara da shekaru itama yanzu narabu da ita nasaketa saki Uku barrentana ke Karan kad’a miya. Maisha ta’ji zafin wannan maganar matuka sedei ayanzu babu yedda za’ayi ta maidamasa da martani sabida tsoronsa tarigada ta shige zuciyarta sosai, lta ‘kanta batasan dalilin hakanba kasancewar tinda take rayuwa bata taba tsoron wani mahaluki ba duk girmansa Sai Saminu. Wasu zazzafan hawaye ne suka fara zubowa a idanuwarta sai yanzu tafara kewan iyayenta Momcy da Daddy, awannan lokacin jitake tamkar tafi’re takoma gida taredasu su cigaba dazama kamar yedda suka Saba. Saminu ya zuba mata akwatuna duk ita ta d’auka, shiko yayi gaba,yana matukar mamakin irin bacewar da Maisha tai, “wai ace kamar shi, ta dubi girmansa tafad’a Masa wannan bakaken maganganun harma ta d’aga Masa hannu. Daga yau yadena wa’sa da ita kenan, Welcome to hell Malsha Saminu Maldugu”. “ 
Zayyad ya fa’do mata awajen yana barci dayake abige yake sosai kuma dagani giyar ta’haura kansa. Nan ne Miemah tasamu damar komawa gida, ta’karaso tamkar daga sama inda cikin nunfashi d’aya ta tsanar dasu dikkan abinda kefaruwa “Zaid baya cikin hankalinsa kuyi sauri kuje kudawo dashi gida, abige yake sosai sabida har sunansa mantawa yai giyarta’haura kansa, zatayi masa illa. 
Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ suka ambata alokaci d’aya. Fad’uwa tazo dedei dazama daman tun tuni nemansa ake. Basu bata lokaci ba nan da nan suka shige motocinsu, kai tseye Miemah takaisu har zuwa wajenda tahadu da Zayyad,Amma abun mamaki babu wanda suka gani awajen ko tsunsu baya wajen barre d’an Adam, hakan ya tabbatar musu cewa Zaid ya’kara gaba. 
A tsorace Miemah ta’karaso har inda tabarosa tanacewa’ Wallahi Baba anan wajen nabarosa yana barci har cewa yai kadanafad‘a muku had’uwarmu dashi, yakuma cemun sunansa “Zayyad”. 
Zayyad? Daddy, Mamy da Aunty Nasiba suka hado baki cikin tsananin mamaki, fiskokinsu ta’nuna matukar kad’uwar da kunnuwarsu tai bayan jin sunan wannan mutumin juyowa sukayi alokaci d’aya suna bin junansu da ido tamkar marasa Gaskiya. 
,,,,,,,,,,,,,,,,,

Sai tafiya suketayi sunata pasowa cikin daji, Maisha ta gaji sosai amma dayake Saminu bai saukoba har yanzu babu abunda tafad’a masa sai binsa take abaya tanakuma kuka. Harga Allah Ba’tason wannan binna’sa datake amma dayake ta’san cewa idan bata biyosaba y’an Sanda zasu ganeta aduk inda tashiga shiyasa ta daure tana binsa a Sannu. Saminu bai tan’kamata ba har sanda suka iso wata lalatacciyar gidan ‘kasa sannan yanufo cikinta yanacewa’ Anan zaki ciga  da rayuwa k0 kinaso k0 bakiso sai dai kiyi hakuri mahaifinki bashida k0 sisi this is where you actually belong Maisha Saminu Maidugu” yafad’a yayinda yake nunamata gidan 
‘Audhubillahi Mina_Shaidani Rajim” Maisha ta’kara bud’e idanuwarta sosai tazubama gidan kallo. Dasauri tamaida idanuwarta kan Saminu tanacewa’ Wallahi sai dai ka kasheni Saminu, ba’zan zauna anan gidan ba.*'” 


Hmm 

About Ismail

Check Also

TAGWAYE CHAPTER 35

TAGWAYE CHAPTER 35 Tukin awa guda ce takai Miemah gida, afusace taflto cikin gaggawa tanemi …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *