[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 31 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE


CHAPTER 31Karfe Sha biyu ta Rana, Ana iska sosai agarin Abuja Sany’i da kanshin ruwan sama kakeji abar sha’awa, Hadari ta hade bakikkirin garin takoma. A wannan lokacin ne Zaid ya fito daga ZMZ Builders bayan sun kammala meeting kan nad‘in sabon manajar Confanin Wanda zai maya gurbin marigayi Asad. Zaid ya shedamusu cewa awannan karon macece zai d’auara a kujerar, kowa na mamaki suna kuma kokonto shin waye za’abaiwa wannan gagarumar kujeran, ahaka yabarosu suka watse daga wannan zaman.
Shi kad’ei ya fito sai sauri yake yanata zumudi, Parking lot yanufo cikin wannan saurin yashige abar hawansa, Sosai yake ta’ka Motar in full speed ahaka har saida yakai babbar Super marketta Maitama.
“Jiya akayi birthday Munah a makaranta yau kuma da yardan Allah zaije makarantar su yad’aukota sudawo gida domin zai shiryamata gagarumar liyafa anan Zabir mansion. Ya gayyaci mutane dadama domin ataya Y‘ar uwar nasa murnar cika shekara shiyasa yakeson komai yayi dedei yedda ake bu’kata …..
“Ranka shi dade meye za’a baka? Wannan mutumin yayi matukar mamaki, ganin tun d’azun yake kokarin masa magana amma bai kulashiba “Amm Ranka shi dade meye kake bu’kata tun d‘azun nake maka magana amma kana wata tunanin daban. Sai yanzu Zaid yadawo cikin hayacinsa “Sorry sonake kabani …… Haka ya lissafo masa abubuwa na bu’kata duk masu tsananin tsadar tsiya.
Gida an chanzata ba’ki d‘aya ko ina flawowi kake gani da decorations masu d’aukan ido, ma’aikata ne suketa zirga zirga a tsakar gidan suna aiki, DJ yayi playing music already sai tashi take gwanin birgewa.
Aunty Rahila, Umma Aisha da Mommy duk aiki suke suma sunata zirga zirgan, Aunty Nasiba ce kad’ei ke zaune a falo tana waya da danta Zabir; “Hello kanajina? Aunty Nasiba ta ‘kara murya “Babu matsala Babana Momy tana nan zuwa Airport ta d’aukoku yanzu kuwa Ashe harma kun karaso, Alright sweetheart wait for momy there, momy is on her way. 0k bye sweetie pie.
Tayi shiru nad’an wasu mintuna sannan tace’ Sorry my chocula‘ie dayake kasan akwai liyafa agidan namu yau mutane sunyi yawa Kuma kaga zuwan naku kunyita ne as a surprise, ai kaima kanka kasan cewa da Momy ta’san dazuwanku a Airport zata wuni. Shiru Tai tana sauraronsa Sannan tafashe da dariya “Ohh my sweetie pie sai anjuma ina nan tafe.
Daganan ta kwaso gelenta tai gaba. ………………,…….. Anisa, Miemah da Mainah Sun wuni a Diamond Beauty Parlour suna gyaranjiki, kwalliya
da gyaran gashi, sosai sukayi kyau tamkar amare. Sun kammala adedei lokacinda yakamata sannan sukawuce dressing room, kowannensu da kalar kayansa.
Ma’inah ta Sanya doguwar riga kalar pink, kasancewar itace kalarda tafiso aranta, Kuma Zaid kansa yace kalan na matukar karban jikinta, shiyasa take matukar san pink colour.
Blue itace kalarda miemah tafiso aranta, wannan yasa ta sanya doguwar riga mai kalar
bula, Kuma dayake alokacinda Asad ke raye yafad’a mata cewa shima yafison kalar fiyeda duk sauran kaloli.
Anisa ta Sanya farar riga wanda tai dedei da tsarin jikinta, tayi kyau ba karya. Kamar yedda Miemah da Ma’inah suma sukayi muguwar had’uwa ayau. Ma’inah ta matsu tahadu da Zaid domin yaga wannan kwalliyar wacce tai mussaman domin sa. Itama Anisa tsayawa tai akayimata hotuna ta turowa saurayinta Fazhab Khan, wani matashin saurayi ne d’an India wanda suka had’u a Dubai lokacinda take karatu,tana matukarji dashi ba wasa.
Tun tuni Miemah take kokarin rike hawayenta amma inaa, ta’kasa, kai tseye suka fara zubowa, Anisa da Ma’inah suna chan suna waya da samaransu itako tunanin Asad kawai yake zuwa aranta, “Shikenan na rasa saurayi Mai Sona so na gaskiya, na rasa Asad. Tsayawa agaban madubi tai yayinda take cewa, Duk wannan kwalliyar nayita ne abanza, babu wanda zai ganni yace’ Nayi kyau bayan Mommy, Umma, da Daddy. Banida Saurayinda zaiyi sha’awar wannan kwalliyar tawa. 
Da wannan tunanin Miemah tafara tafiya ahankali ahankali babu wanda yaganta cikinsu har saida ta’kai ba’kin gate tabar motocinsu awaje sannan tahau adeideita tayi tafiyarta. 
0k my dear love you, bye. Dawannan maganar Zaid yakatse wayarda suka dade sunayi tareda Ma’inah, Kai tseye ya’karaso cikin makarantarsu Munah adedei gun parkingya baro motarsa, Sedei kuma abun mamakin shine makarantar shiruu take babu d’alibai, yafara mamaki aransa “Yau take ranar bada hutu, shin meyesa makarantartasu tai shiru haka tamkar ba Yara. Da wannan tunanin ya’karaso ofishinsu, ya tarbi sa’a matuka sabida yatarda mutane aciki. “Sannu sir, how may we help you? Cikin sany’in jiki ya amsa cewa” Actually I’m here to pick up my daughter Maimunatuh Muhammad Zabir. HOD ya mike tseye yana binsa da kallo har tsaida yagama maganarsa sannan yazaro idanuwa cikin rudani yace”Jiya akayi hutun makaranta Kuma mahaifiyarta Hajiya Turai tazo nan da’kanta ta d‘auki Maimunah bata fad’a maka ba?. “What Munah na tareda Ammi impossible, Yaushe aka sakota daga gidan yari?” Zaid ya 
fad’a ahankali inda yahad’e hakoransa cikin tsananin bacin Rai ya bankado kofard’akin ko sallama babu, haka yafice aguje a zuciyarsa yaketa nanata sunan mahaifiyar nasa “Ammi you are too much. Fitowarsa keda wuya ya zaro key motarsa inda kai tseye ya nufo Parking lots, Yana 
karasowa saiga wani Kato yafito cikin wata katuwar mota mai tint. Zaid baisan hawaba 
bare sau’ka, jinsa kawai yayi a kafad’ar wannan mutumin anrufemasa Fuska harda baki Kam kace Kobo ansakashi cikin wannan motar sunyi gaba dashi. 
Aunty Nasiba taje Airport kamaryedda sukayi da Zabir, ayau y’ayanta duka sun taho Abuja hutu, Dad’i ya isheta sai zumudi take tana mamakin yedda yaran duk suka girma cikin d‘an wannan lokacin da basa tare. 
Dreba na tuki, ayayinda Zabir yazauna agaba gefensa, Zaid, Zayyad da Auta Hani ko suna zaune abaya tareda mahaifiyarsu. Aunty Nasibah ta sa Hanifa akafanta tamkarjinjira tariko autartata, Tad’aura hannun damarta a kafad’arZaid, Hannun Hagu ko tasaka kan kafad’ar Zayyad ji take tamkar ta had’iye su tahuta tsabar yedda zuciyarta tayi matukar farin cikin ganinsu duka ayau. 
“Dan Gaye na ya girma jibi yedda ya ijiye tunbi tamkar alhazawan sokoto” Aunty Nasiba tafad’a tana kelkelewa da dariya, awannan lokacin ne kowa yafara dariya suna zolayan Zayyad. ‘Ai wannan mayen abinci ne” Zaid yafad’a cikin zolaya. Zabir koh juyowa yai suka had’a Ido da Zayyad sannan ya maida idanunsa. shiru Zayyad yake zaune tunda suka shige motar Bai tan’kawa kowaba dayake Daman shi bashida yawan surutu akwai shi da girman 
Kai, rigima dakuma tsafta shiyasa Aunty Nasiba take masa kirari da ‘Dan Gaye. Awa Uku ce kacal takaisu  Gida Koh sun tarar da ita babu d’adi, tun lokacinda Zaid yabar gida dasassafe bai ‘kara dawowa ba, an shirya fili, mutane duk sun taho, Y’an jaridu dama sauran baki duk sun taho taya murna, Zaid ko shiruu babu labarinsa har zuwa yanzu da la’asar takawu goshi, Manyan Baki kowa na watsewa ahankali, ahankali, Y’an jaridu duk sun rud’e daga rahotannin murna sun koma rahoton cigiya. Mahaifin Zaid sun fito cikin gari tareda y’an Sanda suna aikin nemansa. Ma’inah dasauran mutan gida kuwa babu abinda aka ragesu da ita Sai kuka dajimami daga murna wannan damuwarce tabiyo baya Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’. 
Fitowar Miemah daga Salon, Ta’kira Ma’inah awaya ta tsanar da ita cewa zata biya kasuwa ta sai abu idan sun kammala suwuce gida kada sunemeta sabida daganan itama gidan zatayi. Babu musu Ma’inah ta amsa mata, sedei kuwa tasha masifa gunta akan meyesa bata jira sunje kasuwan tareba. ‘Karya Miemah tapesa mata, Restaurant ta nufa ba kasuwa ba, zuwa tai musamman domin tasha kuka yedda ranta keso, ta’san cewa agida idan tana kuka mummy, Umma, daddy harma da Ma’inah zasu shiga damuwa zakuma su tambayeta dalili, shiyasa tazabi zuwa nan domin tasauke duk abubuwanda suke damunta. Tasha kuka sosai awannan wurin har saida dukkan damuwar dake addabarta suka sauke sannan tayi hanyan gida. 
Ana sallan magriba Miemah ta karaso, duk wannan wainar da ake tauyawa agida batasaniba, ahankali ta sauko daga adeideita chan idanuwarta suka hango Zaid tsaye awata lungu kusada gidan nasu “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Zaid meye nake gani haka? Miemah ta’karaso kusadashi a tsorace ta kwato kwalbar giyan dake hannunsa ta wullota kasa tanacewa’ Zaid ashe kaima kana wannan shaye shayen. Cikin maye ya shareta da Mari a fuska inda yakecewa” Meye ya yaya yyy yasa kika kwacemun abuna. 
Zuru zuru Miemah tazaro idanuwa tana binsa da kallo, “Zaid wannan halin sam bata kamaceka ba. Tafada cikin tsananin hawaye. 
Damketa yayi tana kokarin tserewa yariketa sosai shima yafara zubda hawaye yanacewa” Protect me please kada kibarni, banida kowa. Awannan lokacin babu abunda zakagani a fuskar Miemah face rudani” Zaid Muhammad Zabir are you ok”. 
Kai tsaye ya katseta “Sunana Zayyad Muhammad Zabir. “ZAYYAD???? Miemah ta’kara bud’e idanu a tsorace tana binsa da kallo…. Ta zaro wayarta cikin sananin rawan jiki tasa layin Ma’inah. lnda take ya kwato wayar idanuwarsa cikeda kwalla yayinda yafa’do har kasa yanacewa don Allah kada kifadawa kowa cewa kinhadu dani anan please. 
“Meye yasa? Miemah ta’kara tambayarsa cikeda rud’ani. “Babu komai“ amsarda Zayyad yabata kenan sannan yami’ke Kai tseye yafara ‘tafiya. Miemah tana binsa da kallo har saida yai nisa da tafiyarsa ta ambaci sunansa da Karfi”Zayyad”. Haka ya tsaya chak! ya waiga shima yana binta da kallo. Aguje ta’karaso wajensa, Zayyad yana tsaye tamkar poster yanajiran abunda zata fad’a masa, Saiko yaga ta riko hannayensa duka biyu cikin sassanyan murya takecewa’ Don Allah kar katafi Zayyad. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]