[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 28 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE
CHAPTER 28Karfe shida da rabi, adedei lokacin Sallar Maghribajirginsu tai landing a babbar international airport ta Abuja wato Nnamdi Azikwe Airport. Daddy ne yafara fitowa sannan Saminu da Matarsa suke biye a baya, fiskokinsu duk ba kyan gani musamman ma fiskar Saminu kwata kwata baiji dad’in bayyanar wannan sirrin ba, abinda ke kara sosa masa zuciya kuma shine tonuwar sirrin Maisha, ayanzu yan sandan Maiduguri suna nan suna nemanta ruwa ajallo, shiko Saminu yasha alwashin cewa zaran yana Raye babu abinda zai faru da y’arsa zaibi ko tawace hanya domin ya ceci yarsa Maisha Saminu Maidugu.
Bismillah, Bismillah , Hi ‘Saminu lafiya meye kake tunani haka? Sai yanzu yadawo cikin hayacinsa inda yaga ashe tun tuni anbude masa kofar mota, Daddy da Matarsa duk sunrigada sunzauna shi kad’ei akejira. Dasauri yasa kafa yashige, shiru suke cikin Wannan motan babu wanda yai magana har Sanda suka kai gida saukesu Daddyyai shiko Kai tseye yanufi asibiti gun Matarsa daman ya matsu yadawo gunta sabida yana kewarta sosai ya kuma san duk yedda akayi ayanzu tana cikin kad’uwa da matukar ciwon zuciya domin wannan sirrin zata iya tsanadiyar rasa rayuwarta gaba d’aya sabida ta dad’e tana bautawa Y’ar daba jininta ba, wacce Kuma tai sanadiyar nisantata da yayan cikinta “Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’.
Dayake sunada d’aki a gidan Sambo, Kai tseye Saminu ya janyo Matarsa suka shige tamkar fad‘a ya fisgO jakarda ke hannunta ya wullota kan gado da jajayen ido ya tsawatarmata” Aisha, Maisha yarki ce Kuma jininki amma meyesa kikebin bayan Dan uwana kuna zarginta, how dare you? Aisha wallahi idan kika kuskura nagano kinabin ba’yan Sambo da matarsa Aisha zan gujeki kuma karshen igiyar auren mu kenan sabida babu bata lokaci zan datse ta….
Toh sai me? Ta katseshi babu fargaba tace’ Saminu ka sakeni mana wallahi tamafi nono
fari, sannan tun da wuri kasani bazan ta6a bin Bayan Mara Gaskiya ba, Maisha tayo halinka Saminu batada Hankali bare imani fad’amin me Zanyi da y’a irinta Allah wadaran halinku dakai da d’iyar taka ba’ki d’aya, Nidei har gobe banida wata y’a datawuce Miemah, itace jinina, bazan ta6a karban Maisha amasayin y’ata ba Allah sauwake yariny’ar datai niyar kashemu iyayeta kawai sabida tasamu damar cigaba dazama agidan ya Sambo bayan bayyanar gaskiya… Bata karasa wannan Furucin dake bakintaba yayinda Saminu yakai hannu fuskarta, alokaci d‘aya yakai mata mari har guda Uku “Toh kisani wallahi zamana da
ke ya’kusan karewa shasha kawai wacce batasan ciwon kanta ba. ‘
Toh Sannu Wanda yasan ciwon kansa, nidei kamar yedda nafad’a ban fa’sa ba, Miemah itace Y’ata har abada, kaje kadauki d’iyar ta’ka kuje bangon duniya bata shafeniba wallahi. Girgiza kansa yai yanabinta da kallo, ganinta yake tamkar mara hankali, Babu abinda ya’kara fad’i bud’e kofar d’akin yai Zuuuu!!! Yafitce a guje kamar wanda aka koro.
Innalillahi wa Inna iIeihi rajiun‘ Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’. Kalmar dake fitowa abakin Daddy kenan bayanjin abubuwan da Maisha ta aikatawa Matarsa a asibiti dakuma kudirinda tai niyar d’auka wato kudirin kisan y’ayansa Moemah da Maisha.
Tasowa yai cikin tsananin damuwa ya rungume Hajiya Safeenah “A Gaskiya nima yanzu hakuri na ya’kare, Maisha ta turani bango she must pay for all her crimes Insha Allah, I’m sorry Safeenah ki yafemun tun tuni na’san Maisha tasan cewa mu ba asalin iyayenta bane sedei ita kanta batasan cewa na’san da hakanba, Nikuma don gudun bacin ranki yasa nabarki cikin duhu ban sanarmiki da komai ba na’san kuma na aikata babban laifi don Allah ki gafartamin. Dasauri momy ta‘rike hannayensa “Mijina na yafemaka har abada
sedei inason kafad’amin yaushe Maisha tasan da wannan maganar?
Tun lokacinda muke America tanada shekaru bakwai alokacinda muke shirin dawowa ‘kasa Nigeria, kinsan Maisha da shiririta cikin jaka’ta tagano wannan takardar yarjejeniya damukayi tsakanina da D’an uwana dakuma Likita …….

“FLASHBACK”

“Alryt sir i will call you back thank you so much” Cikin tsananin sauri Daddy ya katse wayarsa sannnan yafita tsakar gida da harshen turanci yakecewa” Clifford akwai akwatunana dasuka rage cikin d’aki sai kai sauri kazo kukai mota mutafi saura minti talatin jirgin namu ta tashi. Bai jira amsarda zai basaba haka yakoma falonsa aguje yana tatttara sauran littatafansa dasuka rage cikin sauri, Alokacin Momy tashige “Sweetheart kayi sauri don Allah muna jiranka A mota.
“Kuje mota tareda Isha ina zuwa just wait for me there. Nan momy takama hanyarta taje mota, Daddy koh yana kammala shirinsa d’aki ya nufo nan ya hango Maisha a cikin d’akin nasa tana rigima gaban madubi.
“Daddy’s princess, Momcys Heartbeat, Maidugu Family face Maisha Sambo Maidugu I’m so much proud of myself. Magana take ita kad’ei takeyiwa kanta kirari dayake kowa ya’san Maisha ta Saba da wannan tana matukarji da kanta dakuma iyayenta.
My little princess dama bakije Mota ba? Tun tuni Momy tatafi tanakuma jiranki achan maza zo mujejirginmu ta kusan tashi. Shigewar Daddy d‘akin Maisha ta rungumeshi “Daddy please kayi hakuri na’san zanyi kewar d’akin idan muka koma Nigeria shiyasa nake ganinta for the very last time. Daddy ya kwaso sauran akwatunan yakai mota yana dawowa ciki sautin kukan Maisha yaji daga waje cikin sananin mamaki yalaSe aba’kin kofa, Nan ne yaganta da wannan takardar yarjejeniyarta gama karantata tas! Sannan ta boyeta cikin rigarta batareda sanin Daddy yana nan tseye Yana ganin duk abinda takeyi ba. Daga nan tashare hawayenta tafito tamkar babu abinda yafaru ……

“FB END”

Wannan kenan. Bayan ya gama bata labarin girgiza kansa yai yanacewa: How can you imagine tun lokacin Maisha tasan Gaskiya amma ta boyeta azuciyarta ta yaudaremu kamar babu abinda tasani gameda sirrin, shiyasa take bin hanyoyi domin ta rabaki da Ma‘inah wato kiji kin tsaneta harma bakyasan ganinta gaba d’aya.
Maisha bata taba sanin cewa na’san ta’gano wannan sirrin ba, Nikuma ko dawasa ban taba fito mata a flli nanuno Mata cewa akwai takardata wacce tabacemin ba, haka takone wannan littafin Sanda na’kara zuwa wajen Saminu nai photocopy tasa. Amma kiduba kigani yau Maisha ta zuba mana kasa a Ido dakda irin hallacinda mukanuna mata. 
Dasauri momy tamike “Alhaji kabar wannan zancen anan, idan munce zamu lissafa irin butulcinda Maisha tai mana zamu iya shafa tsahon shekaru munakan abu d’aya. Bazan iya zamaba Alhaji zuciyata tana bala’in konuwa Y’ata tana gidan Yari tanashan wahalar laifinda babu hannunta aciki, Alhaji muje mukai shedar Maisha, I want my child with me, babu abinda nakeso ayanzu irin kasancewa tareda Miemah da Mainah, Alhaji inason inroki gafararsu musamman ma Miemah she is my beloved daughter kun rabani da ita tun tana Y’arjinjira meyesa kukayimun haka?. 
Daganan zubewa tai akasa tana rusa kuka, Daddy ne yariketa sannan tamike “Kiyi hakuri kaddarace arubuce take, but I will promise you one thing, You will soon be with your daughters again, Our Family will soon be complete, I promise we will live happily ever after with our own flesh and Blood that‘s Ma’inah and Miemah. 
Dawannan Daddy yakarbi takardar sallamar Safeenah daga asibiti, Sanda yasa hannu sannan aka sallamesu. Daganan babu inda suka wuce sai Wantamele police station sabida 
momy ta matsu taje gun y’arta. 
Saminu? Idanuwarta cike takeda mamaki yayinda tamike wuftana binsa da Ida “Meye yakawoka nan, What the hell are you doing here at my house you bloody fool, Good for nothing. 
Idanuwarsa suna matukar zubda kwalla yayinda ya matso haryakai inda take, a kasa yasa gwuiwowinsa sannan ya had’e hannayensa duka biya “Maisha karkiji komai Kuma banason kikara zubarda hawayenki sabida Zuri’ar Sambo sun gujeki Y’ata gani nan Mahaifinki wandake matukar alfahari dake bazan taSa barin bayankiba Maisha, Do you know why? Because I’m your real Father my dear ….. 
Enough Saminu enough , Ta katseshi a tsawace tafara magana Kuma cikin tsananin kuka da bakin ciki ” Saminu kai ba Mahaifina bane Kuma babu alakar dake tsakanin mu, ka duba girman Allah karabu da dani, Sabida na gwammace na mutu akan wannan lalatacciyar ruyuwar danake ciki a yanzu, Saminu just live I really want to  be alone kafita kabani wuri sabida nidei har gobe ‘Dan uwanka shine mahaifina…. 
Mikewa Saminu yai” Maisha, Sambo ya yaudareki tun tuni idan zaki kula sosai Samba yana fifita Y’arsa Ma’inah fiyeda ke, Bai taba sonki kamar yadda Uba ke nunawa yarsa soyayya ba, shiyasa kikaga yabaiwa Ma‘inah tarbiya mai kyau ke ko yabarki kika gurbata rayuwarki dasunan soyayya. 
Shiru Maisha tai tana sauraronsa, inda yacigaba dacewa” Sambo yabarki agidan kanki tun kina Y‘ar shekara bakwai, kinsan meyesa yayi haka? Cikin sassanyan murya Maisha ta kad’a kai ” A’a. 
Murmushi Saminu yasakar mata sannan yacigaba da magana” Sabida shi da Matarsa susamu damar Zama da ‘Diyarsu Mainah, su samu damar kusantarta, Sun san cewa idan kina taredasu koma menene sukayiwa yarsu yazama dole suyimiki the same thing. ldan Zaki tuna soyayya Matar Sambo tana nuna miki soyayya nejust to earn your trust Maisha your foster Mother never love you …….. 
“Ba Gaskiya bane, soyayyar mumcy Gaskiya ce ta Soni tsakani da Allah. Cewar Maisha. Girgiza kansa yai” ldan itace mahaifiyarki kina ganin zata gujeki a rana guda? Yayi shiru Yanajiran amsarda zata bashi. 
Tayi shiru na tsahon lokaci tana tunani sannan ta gyada Kai “you are right Saminu duk 
maganganun da kafad’amin Gaskiya ne. 
“Kin amince dani kenan, Ina rokanki dan darajar annabi Maisha ki amince dani, ki karbeni amasayin mahaifi ba’zan taba zuba miki kasa a ldo ba kuma wallahi har abada Ina bayanki Maisha. 
“No Saminu never”. Tafad’a kai tsaye, ta’kara fad’a “Never God forbid bazan iya ba. 
“Please Maisha trust me, ki amince dani ko don mu gurbata zuri’ar Sambo, lets destroy them Maisha please. 
Share hawayenta tai kai tseye tamatso kusa dashi suka hade hannayensu “Na amince dakai kuma nayarda muhad’a kai wajen gurbata rayuwar Zuriar Sambo. 
Cikin tsannanin farin ciki Saminu ya rungumeta “Thank you my child, yanzu ta Ina zamu fara??. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]