[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 27 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE
CHAPTER 27
Sai addu,oi mommy keta nanatawa tun zuwan su gidansu, tana tsaye a bakin kofa kafafunta duk suna ‘karkarwa, ayau jitayi tafara da’nasanin shagwaba Maisha dakuma bin bayanta datakeyi tun tana kankanuwa, A zuciyarta take ‘kara sanyawa Ma’inah Albarka yedda halaiyarta duk suka banbanta data Yar uwarta.
Cikin wannan zunzurutun damuwa da tunani momy takoma daki. Sai aikin leke leke take tana Allah Allah aranta kada sojojin nan sugano Gaskiya adawo gun Maisha a kamo mata ya. Wannan tunanin take har sanda ta kwaso dukkanin kayayyakinsu tana kammalawa wayarta ta laluba jikinta duk rawa take yayinda tasa layin Ma’inah Kai tseye tadanna, abugu daya Ma’inah ta daga “Yi maza kitaho gida,” abunda tafada kenan. batajira amsarda Ma’inah zata maido mataba ahaka ta katse wayarta.
Daga nan d’akin Maisha tawuce arazane tafado ciki aiko babu kowa cikin dakin Maisha
ta’kara tsere mata “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Zama tai anan tafashe dawata sabuwar kalar hawaye, Maisha zata daura mata hawanjini takuma yi sanadin mutuwarta. Ko Ina taje? Ko me taje kullawa kuma???. ‘
“Dallah Malama kada ki raina mana hankali mana wannan uban aikin damukayi miki yaci ace kinbamu dubu hansin amma meye zamuyi da dubu ashirin”? Cikin tSananin sauri Maisha tace’ Dan Allah kuyi hakuri dubu ashirin gareni wallahi amma idan na’samo cikon zan biyaku, kun tabbata dei aikin yayi kyau.
Wani kato cikinsu ne yafashe da dariya ‘ai yanzu na shedamiki Hajiya Turai babu wanda tafi tsana a duniya irin danta Zaid sabida dasunansa mukasa yan Sanda sukaje suka kamota yanzu hakama nasan bata gama mamakin butulcinda danta ya aikata mata ba sabida alokacin da aka kamatanma cewa take Zaid da mahaifinsa zasuyi da’nasanin idan tafito. Tapi Maisha tabuga, tapin Farin ciki, washe hakora Tai tanacewa’ Shegu d’aya ba’yan d’aya sai na gurbata rayuwarsu ba’zasu tasa zama cikin farin ciki ba har abada yanzu kuma saura babbar shedaniyan MA’INAH nagama da Miemah nakuma gama da Zaid.
Cikin wata barkaceciyar daki aka jefo Miemah, dakin duk datti ga wari da kazanta, tinda aka kamota babu wanda yataka wajen bare tasamu damar tambayan abinda ke faruwa, abinda ke Kara daure mata kai Kuma shine sauyawarda momy da Maisha sukayi ayau ta tabbata basuda Gaskiya,Azaune take shiru a bakin kofa Babu abinda yacika zuciyarta sai tsanar Mommy da Maisha tana Kuma mamakin sharrin dasuka Kara ‘kala mata awannan karon.
Tun lokacinda Mainah taji cewa Miemah ce tayi kisa ta’kasa yarda da batun, kwata kwata ta ‘kasa gaskanta maganar hakan yasa sukayi fada da Zaid sosai sukayi hayaniya agida yace idan zata kara musa maganarsa tabar masa gida sabida yafo karfin yafada tafada, Wannan yasa Ma’inah tabar gidan kamar yedda ya umarceta. Aunty Rahila dasauran mutanen gida duk basuda bakin magana, daman idan ran Zaid yabaci babu mai chanza masa shawara.
Tana ofishin lawyer ayayinda momy Ta’kira cewa ‘tai maza tazo gida”Amma bata damu da maganar ba. hankalinta duk nakan Yar uwarta wacce aka kama batasan hawaba bare
sau’ka.
Momy tashafa awowi dadama tana zaman jiran Ma’isha Amma Babu alamarta haka ta lalubo wayarta ta’kira Daddy, kame kame takama batasan inda zata fara ba bare ta bullo Masa da maganar ba.
“wace irin magana kakeyi haka Alhaji dan Allah nidei kawai kahado Mana Urgent flight dani da Maisha da Mainah zamu taho America mu sameka. Muryar Daddy ya’nuno mamaki sosai yayinda ya’kara tambayarta‘ Safeenah wallahi na’san akwai abunda kike boyemun, sabida babu yedda za‘ayi haka kawai kicemun zaki dawo America tareda Yara kusameni, Gaskiya akwai matasala. fadamin menene? Momy ta’rasa inda zata fara bullomasa da Maganar“ Bukatarka nake kuma Gaskiya bazan iyajurewa ba.
Ya’rigada ya’gane wannan maganganun datake duk karya takejeromasa, “Toh why not kizo ke kadei banda Yara, sukuma meye zasuzoyi? Jikin momy na rawa awannan lokacin ta rasa inda zata bullo Masa, gabanta har fad’uwa take koda tagane cewa Daddy ba’zai taba gamsuwa da wannan fake maganganun datake tsaromasa ba, ajiyar zuciya tasau’kar kai tseye tafara furta Gaskiya d’aya ba’yan daya duk ta fad’a Masa har Sanda ta’kai inda yan Sanda suka kamo Miemah Sannan Daddy ya dakatar da ita. Dakata Safeenah,Yai saurin katseta Ma’isha ce tai kisan sannan kika rufamata asiri aka
kamo Miemah? Cikin hawaye momyta gyada Kai “Toh yazanyi kaima kasan bazan tonawa Yata asiriba na gwammace duniya nan duka su wahala akanjinina Ma’inah da Maisha su wahala….
Daddy yayi shiru nawasu lokaci, sannan yasaukar da ajiyar zuciya yace’
SAFEENAH, MAISHA BA JININKI BACE, Ki gafartamin na boyemiki sirrinda baikamata na boyemiki ba amasayinki na MAHAIFIVAR MIEMAH …… Dakata Alhaji, chak!!! hawayenda suke zubowa a idanuwan momy suka tsaya ”Meye kake nufi? Alhaji kada son Miemah yasa ka aikata laifinda Allah zaiyi fushi da kai, wace irin magana kakeyi haka? 
Akwai wata tsohuwar takardar dana ijiye cikin wata kwali a karkashin gado na, wannan takardan tun ranarda kika haihu na rubutata kuma ina ganin ayau ce anfaninta tazo, wannan takardarce kadei zata iya gwada miki gaskiya ayanzu. 
Sake wayan momy tai jikinta duk na rawa yayinda takoma d’akin Daddy, tana gumi sosai ayayinda tabude wannan kwalin. 
Karfe biyar da rabi ta yammaci Ma’inah da Barrister Ibrahim suka karaso police station, Sunko isa adedei lokacinda yakamata. Zaid dasauran abokanansa da Yan uwa harda sojojin kasashen waje duk sun kai ziyara wajen, inda sukasa Miemah asakiya Yan jan’da sunata tapka rahotuna tareda aikin d’aukan hotuna masu yawa, awannan zuwansu ne Miemah tasamu damarjin laifinda ake tuhumarta da shi. duk dacewa ba’ tada hannu wajen kisan Masoyinta Asad. Miemah batamu’sa ba, Kai ko kalma guda bata ‘kara furtawaba, jikinta yayi matukar sanyi tamkar ‘kankara, kwakwalwarta tayi matukar kad’uwa dajin wannan mumunar labarin. Tsabar mamaki da kaduwar da tayi ko hawaye basu sauka a idanuwarta ba tsit take zaune a tsakiyarsu babu abinda ke motsi ajikinta sai zuciyarta dake matukar bugawa tamkar ganga, idan kayi mata kallo daya zaka sheda tana dab da kamuwa da masananciyar ciwon zuciya idan ma ba’ayi sa’aba bugawa zuciyar tata zatayi tabar duniyar gaba d’aya. 
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Furucin Ma’inah kenan ba’yan ta shige cikin ta’ron 
mutanen taga irin Halinda Miemah ke ciki, ihu tafara bugawa tana neman taimako “
Allah ki taimakawa yar Uwata. Tana kuka sosai yayinda tarike hannayen Mamy tanacewa’ Mamy ki taimakamata wallahi mutuwa zatayi, yanzu ma hankalinta bata jikinta Mamy please Dan Allah ki taimakamata Miemah ce fa yarki wacce kike alfahari da ita. ‘ 
Duk ta’gama surutanta Mamy bata tankamata ba, juyowa tai tana nunamata Zaid yayinda hawaye suke sirnanowa a idanuwarta tace” Y’ata kije wajensa kinemi alfarma kila ko kya dace yabari akaita asibiti. Sam Ma’inah ba’tasan zuwa wajensa sabida abubuwan dasuka faru tsakanin su, Wanda har sanadiyar hakan yakorota daga gidansa, Amma awannan karon yazama dole taje domin taceci ran Yar uwarta Miemah. 
Sunkuyowa tai adedei inda yake” Zaid. ‘ Excuse me Ma’inah get the hell out of my side I don’t have your time. Da wannan shima yajuye yai tafiyarsa inda hawayenda suka dade cikin idanuwarsa suka fara gangarowa kai tseye. 
Barrister Ibrahim ne yataho wajen adedei lokacin inda yake rarrashin Ma’inah “Ba komai Ma’inah yanzu zan barki anan, Niko zan koma office domin na’samo mana Urgent appel idan nasamo wannan yazama dole ayi mana uzuri duk lokacinda tai rashin Iafiya shari‘a tabamu damar kaita asibiti. 
Mikewa Ma’inah tai kamar yedda ya umarceta inda takoma chan gefe tazauna abar tausayi tana kuka jijiyoyin wuyanta duk sun fito suna nuna irin bakin cikin datake ciki awannan lokacin. 
Zaid ya’kasa matsowa daga inda ya tsaya tun tuni yake tsaye wajen motarsa yanabin Ma’inah da ido, kamar yedda take ‘kara zubda hawaye haka shima yake zubarda nasa hawayen tamkar dan karamin yaro. Kasa jurewa yai “I can’t see her in pain, Tseyawa yai ya’kara kuramata ido “Ma’inah meyesa kike daurawa kanki laifin wani, Ina sonki Ma’inah kuma ba’nasan ganinki cikin damuwa. Ahaka ya’karaso inda take. Yana isa ya daura kafafunsa a kasa babu fargaba yace “Ma’inah please forgive me, I’m sorry*, Cikin sassanyan murya kamar yedda ya’saba. 
Duk dacewa Ma’inah taji abinda yafada kauda kanta tai, takoma dayan bangare tacigaba da kuka. Mikewa yai yabiyota “Ma’inah please talk to me meyesa kikemin haka? Mikewa tai 
tana kokarin barin wajen kuma, Nan ya rungumeta tamkar ‘Da da Uwarsa “I love you Ma’inah. 
Bai rufe bakinsaba ta bankadosa daga jikinta “And I hate you Zaid, Da karfi ta’kara fada” I hate you Zaid Muhammad Zabir ko a hanya kaganni i plead with you kada kanuna ka taba sanin Ma’inah Sambo Maidugu and that’s Final. Tana fad’in wannan tajuye da niyar tafiya inda ta‘kara jinsa a jikinta ya lafe tamkarjinjiri, sabuwar hawaye yafashe dashi”Ma’inah please tell me how can I live without Asad, Ma’inah how? Asad ya tafi yabarni, Ma’inah bazan iya rayuwa batareda shiba. Kema so kike ki gujeni sabida yar uwarki ce ake tuhuma wajen kisan aminina. Yes na rabu da Asad amma bazan iya rabuwa dakeba, fadamin sokike abar Miemah tatafi haka kawai batareda an dau hukunci ba? kiyi tunani sosai Mainah idan munyi hakan munyiwa Asad adalci kenan? 
Babu abinda Ma’inah tafada tsit ta tsaya tanabinsa da kallo cikin sany’injiki. Jin babu amsar databasa yajuye nan take “Fine tunda Kinga hakan shiyafi dacewa shikenan zanje insa asake Miemah, I think Asad deserve this, he doesn’t deserve justice at all, Zanyi magana da commissioner of police ayi cancelling case din kinga shikenan zamu koma gida mucigaba da rayuwarmu. Da wannan magana Zaid yajuye Kai tseye yafara Tafiya. 

“FLASH BACK 

” Wannan ba abun tada hankali bane Miss Ma ‘inah, Zaid haka yake yanada tsananinn farin jini da d’aukar hankali Wanda idan kana taredashi kamar yadda kika fad’a you will not feel comfortable ‘Asad yakatseta, Kai tseye yashigo suka gaisa da Daddy sannan yajuye bangaren Ma ‘inah yana zolayarta: Miss Ma ‘inah Zaid is really amazing isn’t he? 
Shiru Ma ‘inah tayi tana masa kallo da idanun mamaki, daganinsa akwai fara’a kuma yanada hankali, toh amma taya akayi sukayi hannun Riga da dan uwansa Zaid Kodei shi wannan ba ‘dan anan gidan bane? Gashi se wani dariya yake yana washe hakora.. 
“Miss Ma ‘inah don’t think too much. Asad yakatse mata tunanin, inda yajefo mata wata doli dolin yara yanacewa: zaki iya wasa dashi it’s really fun idan kinmasa magana zai bibbiye ki, Kinga kenan shi zai ringa debe miki kewa akoda yaushe and trust me you won ‘t feel lonely around him, l mean the Teddy. Yafada Yana nuna dolin dake hannunta. 
Murmushin karfin hali tayi ‘nagode sosaii Never mind miss, sunana Asad babban abokin, the almighty Zaid, karki damu dahalinsa dazaran Ina nan taredake babu abinda zai ’kara miki da yardan Allah, And nice to 
meet you Miss Ma ‘Inah. Yamika mata hannu domm su gaisa. 
Dasauri’ tabasa hannu “nice meeting you too Asad. 
Ma’inah tana gama wannan tunanin tafashe da kuka, lokacinda suka fara haduwa da Asad a gidan Zaid kenan tun alokacin Asad yanuna mata so da kulawa matuka bai kamata ta saka masa da wannan ba. Da karfi: ta kwalawa Zaid kira daman a hankali yake tafiya baiyi nisa da ita sosai ba. Waiwayowa yayi babu mamaki a fuskarsa kamar daman ya’rigada yasan za‘a ambaci sunansa. Aguje ta‘karaso wajensa babu tsoro ta rungumeshi cikin tsananin hawaye tace’ I’m sorry Zaid Dan Allah kada kasa ayi cancelling wannan case d’in please he deserves Justice na amince abar Miemah anan akuma zurfafa bincike har zuwa lokacinda za’a gane Gaskiya, idan ma an ga’ne itace tai Kisan wallahi na amince azabar Mata da hukuncin da zatafi dacewa da ita. 
Ta’ke Zaid yasake murmushi Wanda ta’kara Masa kyau sosai yace’ I know my Wify is the best among the best thank you Ma’inah. Shima Haka yasa hannu ya rungumeta. “ 
Maisha ce ke zaune agefen momy dake kan gadon Asibiti, a kwance take ba’ta magana bare motsi, jikinta tsit! Tamkar matacciya, likitoci sai aiki suketayi akanta Amma sunyi iya bakin kokarinsu babu mafita. 
Hannayenta dika biyu Maisha ta damke tana hawaye”momcy Dan Allah kitashi kada kimutu kibarni Dan Allah momcy Ki‘tashi sabida ni. Cikin wannan yanayin suke har tsaida hankalin momy tadawo jikinta Amma abinda ya daurewa Maisha kai shine umartar likitocin tayi cewa akoreta daga wajen ba’tasan ganinta kusa da ita. 
Maisha ta rasa gane dalilin hakan, lissafi duk  a ‘kanta amma bata gano dalilin dazaisa momcy ke gudun Maishan taba. Sai dai idon gamuwa tai da tabon hankali. “Doctor bangane abinda ke faruwa ba, cikin duhu nake don Allah kafitardani what happen to my Mom meyesa take guduna why? please tell me. 
Doguwar nunfashi likitan yasaukar tareda cewa “Amma Hajiya kin tabbata babu abunda kikayi Mata? ko dei kin bata mata rai batareda saninki ba? 
Mikewa tai cikin tsananin damuwa tace’ koda ma na aikata laifl Momcy Bata taba nuna bacin rai akaina ba because I’m her favorite daughtet, Baby Isha take kirata babu abunda yataba shigewa tsakanin mu tunda ta haifeni akasarima k0 kadan ba tasan ganin bacin rai na, try to understand me Doc I am her little princess. 
Kad’a Kai likitan yai cikin d’aurin kai yace” Look Madam I’m so sorry kawai kifita kibarta ita kad’ei, And I’m sorry to say she doesn’t need you here. 
Babu tsoro tashare shi da mari a fuska, sosai taji haushin wannan Furucin dayayi ayanzu, Nan da nan tafara zubarda hawaye “No, Noooo, how dare you say this to me. Dasauri tajuye bangaren momy tanacewa” Momcy you need me right please tell him I’m your,,,,,,
Momy tamike cikin tsananin hawaye ta daga mata hannu ma‘ana batasan jin komai daga gareta “Astagfirullah” ta fada cikin muryar marasa lafiya sannan takara dacewa” Idan da’ace Allah zaice mu bautawa wani bayansa to fa babu shakka yayana zan bautawa, idan nace yayana kuma ina nufin jinina yaranda ni nadurkusa na haifi kayana. 
Mutuwartsaya Maisha tai tana sauraronta, tunma bataji karshen maganar da take kokarin furtawaba hawaye suka cike mata ido dominko ‘ta tabbata ayau kashinta ya bushe damuwarda ta dade aranta tun tana Yar karamar yarinya ta bayyana kuma da dukkan alamu ta’kusan rasa rayuwarta nan bada dadewa ba. 
Muryarta na karkaruwa ta matso kusada gadon momy tanacewa’ Mo mom momcy babb babab ban gane abunda kike nufi ba. 
“Maisha you decieve me, kin zalunceni kinci amanata Kuma bazan taba yafemiki ba har abada” …… A fusace Maisha ta dakatar da ita “Me kike nuf”: Momcy dan Allah kifadamin yedda Zan gane, What do you mean? 
Saukar Mari taji a fuskarta tun kam takarasa kalmarda take fadi, Babu shakka Mommy ta sauke mata Marin abun mamaki. Korokoro ta zaro idanuwa tanabin Momcy da kallo ‘Lallai k0 yau Gaskiya ta bayyana’ tunaninda Maisha Tai aranta kenan. Har kasa ta durkusa tana neman afuwa “Momcy duk dacewa ba kece mahaifiyata ba Dan Allah kada ki gujeni kuma kada ki fadawa Ma’inah da Miemah wannan zancen ai ‘Da na kowa ne. Saukar Mari ta’kara ji a fuskarta har guda Uku “Shut up Maisha daman ashe tun tuni kinsandacewa keba jinina bace Amma kin kasa tsanar dani, Ashe shiyasa kika daurawa Ma’inah ta kiyayyarda babu lissafi, shiyasa kike neman rabani da yata Miemah wacce ta taso cikin akurkin gidan mahaifinki wanda sam batadace da hakan ba kema kin sani Yar Sambo Maidugu ba sa’ar bugawar Yar Saminu Maidugu bace Maisha kin cucemu dani da yayana, Kuma wallahi tallahi bazan taba yafemiki ba ko don Yata Miemah domin nasan ita kanta koda zatasan Gaskiya ban taba tunanin zata yafeminba har abada. “Momcy please.  Kada ki Kara kirata da suna Momcy daga yau babu alakar dake tsakanin mu, sabida Maisha ke shedaniya ce wacce tashige duniya da ‘siffar bil Adama. Yanzu haka Mijina. Kuma mahaifin yayana wato Ma’inah da Miemah ya’zo yana Maiduguri, anyi bincike Kuma angano cewa kece kikayi sanadiyar shigewar asalin iyayenki gidan yari sabida kinsa ankashe Mai gadin gidunsu domin Yan Sanda su daurawa mahaifinki da mahaifiyarki sharri akashesu sabida ko da Gaskiya ta bayyana su kasance basa Raye,tir da halinki Maisha Kuma karshen bazatayi kyau ba, Kina …… 
Enough Ya Isa haka Safeenah Sambo Maidugu keba mahaifiyata bace sabida haka banga dalilinda zaisa kiringa zagina hakaba, kinrigada kinfada daga yau bani bake fine,l can live my life alone daman da dukkan alamu Allah ya hallicceni ne kawai sabida na wahala. 
Momy tayi matukar mamakin Jin ambaton sunanta Kai tseye da Maisha tai “You can live your entire life in jail not alone point of correction. Yazama dole intashi yanzu yanzu inje gidansu Zaid domin nakai sheda akanki Maisha kece kika kashe aminin zaid Asad. How dare you” Sandan drip dake gefen gadon mommy Maisha ta zaro Kai tseye ta sauketa a kan Momy nan da nan jini yafara zuba awajen “Babu Shakka babu wacce nafi kauna a duniya irinki amma ayau yazama dole na gujeki sabida ke kanki kin gujeni I’m Sorry Momcy kafin kibar nan asibitin sai na tabbata Ma’inah da Miemah sunbar duniya this is a promise. 
Tana gama maganana tabude kofa aguje tabar asibitin “I’m sorry my former Mommy I’m so sorry yazama dole na aikata abinda nai niyan aikatawa, bazaki taba zama tareda Yayanki  I’m sorry. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]