[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 26 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE

CHAPTER 26“Tana cikin mota” Asad yabude kofan kai tseye yana inviting dinsu. Mainah kam dasauri tai ciki, ai ko tana shiga taga Zaid zaune akujeran baya Yana Shan Tayi mamakin ganinsa awajen shiko ba alamun mamaki a fuskarsa, dan karamin bakinsa yaturo yanacewa Driver kaja mota mutafl.
Miemah bata kara’sa cikin Motar ba, tatafl tabarosu tareda Asad suna tseye awaje, juyowa tai tana tambayarsa lafiya aka tafi da Mainah? Ya kada kai “Zaid ne aciki ba matsala.
Murmushi ta sakar masa “Alryt to sai anjima. Tana fadan wannan tajuyo tafara tafiya.
Asad ya‘kasa furta mata abinda ke cikin ransa har sanda tai nisa dashi sosai sannan ya
sauke ajiyar zuciya ya ambaci sunanta “Miemah”. Tajuyo dasauri tafiskance shi.
Sanda ya rintse idanuwarsa, yasaukar dawata doguwar nunfashi sannan yace’ I love you Miemah.
Sai tafiya suketayi tun tuni, Ma’inah ta rasa gane inda Zaid zai kaita ayau, After a very long drive suka shige ‘Wantamele Police station, ko me yakawosu nan oho. Suna fita ya rike hannayenta tamkar d’an jagora take biye dashi abaya babu mutsu, Basu tsaya ko inaba sai cikin Cell inda kuma akasa Maisha,Alokacin Maisha tana kwance tamkar ba itaba amma da’kaga fuskarta zakasan akwai gagarumar matakinda zata dauka akan Zaid. Zaid ya rike hannayen Ma’inah kai tseye suka shige dakin, yakaita hargaban Maisha sannan yadurkusa har ‘kasa, Ma‘inah ta’rasa gane abunda yake kokarin yi har sanda ya’zaro wata zoben (Diamond) yanacewa”Mainah Sambo Maidugu will you marry me????
Cikin bacin rai Maisha tamike, tamkar a Mafarka ta’kara goge idanuwarta sosai tana ‘kara ganinsu “Zaid me ya kawoka nan? Sha’re Mainah tai tamkar bata ma wajen. Ta’kara matsowa har kusa dashi tanacewa” Zaid ka’san ban sa ba da rayuwar wahala ba, amma kawai sabida San da nake maka yasa na amince aka kawoni nan aka rufe Wallahi duk
duniya babu wanda ya isa yai min haka ba’yan kai, becausel love you ……
Katseta yai nan ta’ke ya’kara turo hannunsa gaba yana mikowa Ma’inah zobe “Will you marry me? Kwata, kwata ta rasa amsar da zata bashi, farin ciki da fargaba duk sunzo Mata alokaci d’aya. “Mainah Sambo Maidugu will you marry me.” Ya’kara tambayarta in a lower tone.
Ihu Maisha ta rapka alokacin, “Nooo this can’t be. Take ta damke hannayen sa tana hawaye “Zaid bazaka taba cin amanata ba please don’t decieve me Zaid I love you so much, kuma na rigada nai wa Kai na alkhawari cewa babu wani namijinda zan iya rayuwar aure dashi ba’yan kai, Zaid dan Allah kace kanasona.
Ganin babu amsarda Zaid yabata ta juyo nan ta’ke takoma Bangaren Mainah, Sanda ta share hawayenta tas! Sannan tafara magana. “Keh Jaka, wallahi Allah, rantsuwar musulmi nai miki, Mainah idan kin auri Zaid sai kinyi babban da’nasani arayuwarki….
Bata ‘karasa furucintaba yayinda Mainah ta katseta, Kai tseye tamiko hannunta” Yes Zaid
I‘m ready to marry you na amince zan aureka Wani irin murmushi ne ta bayyana a kekkyawar fiskar Zaid awannan lokacin  Sonshi da sha’awarsa ta’kara shiga Zuciyar 
Maisha sosai. 
Dimples din fuskarsa ta’bayyana sosai yayinda ya rike hannayenta dasauri yaturo zoben a yatsarta “Thank you Mainah, Thank you so much. Babu fargaba ya rungumeta yanata 
murmushi itako hawayen farin ciki ne ke zubowa a idanuwarta awannan lokacin. 
Zubewa a ‘kasa Maisha tai, duk da uban bala’inta ayau ta’kasa fad’an komai tana kuka nafitan hankali, abu d’aya Tak! tasani azuciyarta itace ‘ba’zata jure rashin Zaid ba ko tawani hali, sabida tana mutuwar Sansa harma tafi San shi fiyeda yedda takeson kanta Kuma yazama dole ta aureshi sukuma kwana a shimfida guda, Sabida wannan shine Babban burinta kenan. 
Meyesa kakawoni nan? Miemah ta tabe baki tana tambayarsa. Sai yanzu tai magana ba’yan wannan kalmarda yafurta mata dazun cewa Yana San ta. Asad ya durkusa har ‘kasa fiskarsa kamar kuka zaiyi, ya’kara tambayarta “Please Miemah Sanki nake har cikin zuciyata ki taimakamin, Zan iya rasa rayuwata idan kinki amincewa dani, ki taimakamin Miemah please. 
Kayi hakuri Asad. Ta katseshi, bana tareda iyayena ayanzu, zaman taimako nake anan gidan sabida haka inaga wannan bukatar ta’ka bazata taba yiyuwaba I’m sorry please. 
Tanafadan wannan tajuyo dasauri tana tafiya. 
Aguje Asad yashige gabanta, awannan lokacin hawaye ne suke zubowa a idanuwarsa 
tamkar dan karamin yaro, har ‘kasa yadaura guiwowinsa. “Miemah please ki taimakamin kiyi hakuri. 
Shiruuu ta tseya tanabinsa da kallo har tausayinsa taji yashige zuciyarta, dasauri ta rike hannayensa, Kai tseye yami’ke yana wani share hawayensa tamkar daddy’s Bom_boy ya 
tseya chak! yana jiran abunda zata fada. 
I love you too” abunda tafad’a kenan…. Nunfashin kwanciyar hankali yasaukar inda yaiwa 
Allah sujjada sannan yamike nan ta’ke ya rungumeta yana farin ciki da godiyan Allah…. 
Subhanallahi meye nake gani haka? Maganar Momy ce ta tsorace su, alokaci daya suka juyo. “Miemah karuwanci kikazoyi anan gidan daman wato anga’ji halin uwa shashasha Yar iska kinason kibatamin suna a duniya koh toh Wallahi ta Allah ba Taki ba. Karasowa inda suke tai Kai tseye tafara janyo Miemah, ta rike ‘kanta tana janyota da gashi sosai take zubar da hawayen zafi, Asad na faman magana amma babu Hali tuni Momy ta 
jefo Miemah a mota sun tafi.
Kuka take sosai tana Ihu wanda harjijiyoyin wuyanta suka bayyana, idan kaji irin sautin dake fitowa daga dakin, se’kace gidan mahaukata kake tsabar ihun da Maisha keyi tana kuka harma da birgima. Ma’inah da Zaid sunbar wajen tun tuni itako sana’a guda take tun bayan tafiyarsu tana sula kuka, tanakuma bibbige kofar d’akin tamkar Balleta zatayi; “Shegu yan iska Kubude mun kofa yau wallahi Mainah bazata kwana da ranta ba sena hallaka’ta, itace sanadiyar wannan wahalhalun danake ciki a yanzu she must pay wallahi sai na kasheta na kashe Miemah muga k0 wa Zaid din zai aura ba’yanni”. Wannan ne irin maganganun datake fadi tun tuni tana kuma kuka at thesame time take ihu tana bibbige kofa. 
Yan Sanda sunajin duk wannan haukan datake amma babu wanda yadamu da ita sabida Zaid yarigada yafada musu cewa koma menene tai kada a tanka mata, kada Kuma a saketa ko uban wa yazo neman Belinta. 
After a very long drive, suka ‘karaso Alhaji Sambo Maidugu residence, Miemah nata kuka cikin mota har Sanda Momy tai parking, Babu sassauci ta bude kofan “Baaaaaf ta rufeta da ‘karfi. Jikin Miemah na rawa sosai irin yedda taga zuciyar momy ta baci ke ‘kara tsorata ta ahankali tabude kofa tafitce. Aiko babu abinda taji sai saukar Mari a fuska “Shashasha Y’ar iska sharri zakimun wurin Mijina, salon yadawo kicemasa ni nabaroki kikaje kika kwaso cikin Shege Sannan ki dawomana gida da ita murasa inda zamu jefe ki, Banza mai halin uwa. 
Duk wannan hawayenda Miemah keyi batasa tausayinta tashige zuciyar momy ba haka ta ringa jibgarta tana dukanta sekace dabba, Mai gadi ne yazo yakarbeta dakyar ta gudu dakin shi. Aww iskancin naki harma da talaka mai gadi zakiyi? Shikuma me zai Baki Yar iska kawai. Fushi momy keyi tamkar kare tana magana muryarta sama sama tsabar irin dukanda taiwa Miemah itama kanta ta gaji,juyowa tai bangaren Mai gadi tace’ Kai kuma na sallameka, daga yau an koreka daga aiki, ka tattara a koma kauye matsiyacin banza da wofl. 
Yana bata hakuri Taki tanka masa haka tai cikin gida kai tseye tana shiga wayarta tafara ‘kara sunan kawarta Hajiya Naja tagani a fuskar wayan “Hajjaju Makkah da Madinah an dawo daga Dubai d’in neh? Tai Jim kad’an tana sauraronta, Hajiya Naja na gama magana Momyta sake wayar tafad’o kasa takama Salati “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Lailaha illahu Muhammadu Rasoulul Allah (SAW) Yattawa ce Zaid yakamo a cell lallai ko wannan yaron yacika Mara mutunci Maisha ta zai kamo how dare him, yarinya karama irin Maisha, toh ma shin meye tayi masa. 
Da wannan Momy tamike aguje tafito babu inda ta tsaya sai garrage anan tashige mota cikin matsifar bacin rai Ta’kama hany’an Zabirs Mansion “Zaid wallahi duk karancin hankalinka yau dei sai na koyamaka, an bataka da kud’i Koh don ubanka duk kudinka sai ka tsakar min yarinya shashashan banza shashashan wofl. 
Horn taketa bugawa babu sassauci, aguje mai gadi yafito yabude mata gate sai shashare hawayensa yake yana goge hanci yanasa ran ko Momy zata chanza ra’ayi yacigaba da aiki a gidan, Glass d’in motarta tazuge zuwa ‘kasa “karurrufe mun ko ina kada kabari Miemah tabar gidan nan, Kuma kada kabata abinci this is her punishment gobe bazata ‘kara zuwa d’akin na miji ba. Tsaramasa tayi “Angama Hajiya Allah yadawo dake lafIya. 
Bata tan’kamasa ba, Jan motarta tai ta’kara gaba. Awa guda ce takaita gidansu Zaid tsabar gudunda Tai da Motar, mutane sai bata hany’a suke suna ganin ikon Allah. Tana zuwa first aka bude mata kofa kai tseye sabida masu aikin sunrigada sun waye ta, ahaka tashige da motarta har zuwa bangaren Zaid. Wata ma’aikaciya ta tambaya “Ina Mai gidan nan yake? Yana chan ZMZ Villa ranki shi dad’e. 
Matar bata ‘karasa abinda take fad’i ba, Momy tabankadota tawuce sai wani sauri take tana ta’ku, ZMZ Villa tashige Kai tseye tana kwala masa ‘kira, “Zaid Muhammad Zabir, Zaid ina kake? Kafito don ubanka, ubanwa yabaka daman Tsare Yata wallahi Maisha tafi karfinka. 
Irin wannan maganganun datake yasa y’an sanda suka taho, inda aka hanata ‘karasowa ciki, sai hayaniya suketayi da surutai har sanda sautin ta iso falon Zaid, cikin barci ya taso da Salati a bakinsa “Lailaha illahu Muhammadu Rasoulul Allah (SAW). Wata karrawa ya danna nan da nan Chief security yashige, tsaramasa yai tunkam Zaid yabude baki yayi magana yace’ we are sorry sir mun tasheka daga barci. 
Excuse me, ‘Daga masa hannu Zaid yai taredacewa” wace irin hayaniya nakeji haka? Mahaiflyar Madam Ma’inah ce sir wai tanasan ganinka. Tabe baki yai” Toh sabida me kuka hanata shigowa? You guys are not serious, kaje kabud’e mata kofa ta’karaso. Yes sir! 
Da fitansa, bai ‘kara k0 minti guda ba, sai ga Mommy cikin falon ko sallama babu tafad’o 
kamar daga sama tanacewa “Kud’inka, Arzikinka, Darajaka da akeyi Wallahi bai taba 
tsoratani ba. Zaid ubanwa yabaka damar tsaremin Y’a? me tai maka? Ta ‘kara murya sosai 
ta daka masa tsawa nace me Kai maka? Kai Kurman Ina ne, ina maka magana kana bina da 
ido haka se’kace tsohon barawo. 
Duk wannan surutan datake babu abinda Zaid ya amsamata, binta da ido yake kurun bai fasa’ ba, Ta’yi magana iya magana Zaid na nan shiru kamarwanda ba’ya wajen, har Sanda ranta yabaci takoma baki Kirin, ta rasa me zatayi masa ayanzu haushinsa ta’kai makura har zuwa ma’kokoronta, Haka ta daga hannu zata Kai Masa Mari kenan aka damke hannun nata, Zaid k0 saukar da Idanunsa ‘kasa yai yana jiran saukar mari yaji shiru. 
Dasauri momy tajuyo domin taga kowaye ne wannan shegenda ya rike hannun nata, Wata Mata ce, ‘kirar Naira, tana sa matar a idojikinta yai sany’i sabida takoma talaka putuk! Kayan dakejikin wannan matar zata sai irin kayan dakejikin momy sau d’ari da golagolenta, takalmarta dama komai na jikinta masu tsada ne na bugawa ajarida. 
Wacece keh? Momy tafad’a atsorace. Zaid najin haka ya daga ido, da mamaki yami’ke yanacewa “Ammi meye yakawoki Nan? 
Aduk inda nake bana rabuwa da Kai ‘Dana Kuma kasani ko a Ina kake ina nan kusa da kai Wacece wannan? Hajiya Turai ta tabe baki tana nuno Momy da dan yatsa. Cikin sany’in murya ya amsa mata‘ Mahaifiyar matarda zan aura ce. 
Bata fuska tai” Zaid kana nufin wannan zuri’ar matsiyatan zaka kwaso mana wallahi ban 
yarda ba gwara ka chanza shawara. Kai tseye tajuyo ta bangaren momy’ Keh Kuma, yau da kin kuskura hannunki ya taba fuskan d’ana wallahi da rayuwarki a duniya ta‘kare, Ba’a tabamin d’a a kwana lafiya he is my son jinina ne, Nice nan Hajiya Turai Mafiya, na sunkuya na haifi abina
Ammi ya Isa haka, don Allah kitafl y’an Sanda zasu iya shigowa nan at anytime. Zaid ya katse ta. Ahankali momy ta rabo tabar wajen sabida daganin Hajiya Turai zata iya aikata komai. 
Tana fita Ammi ta janyo Nikapinta ta rufe fuska, Bata ‘kara wata kalma ba kai tseye tafara tafiya. “Ammi”…. 
Wannan kiranda Zaid yai mata ne yasa ta tsaya chak! Saukar da ldanunsa ‘kasa yai yace l miss you. Juyowa tai tadawo inda yake tarungumeshi “I miss you too son, I love you so much”. Ahaka suka tsaya sunata zubda hawaye har sanda sukaji motsi, nan ne Turai tabar wajen nan take. Zaid koh fitowa yai alokacin dreba yakaisa Wantamele station inda yasa hannu a tarkandan beli aka sake Maisha. 
Tun tuni take labe gindin wata flawa tana kuka, Miemah ta’rasa meke mata d’adi a duniyar gaba d’aya, kai ta gwamace ta mutu akan rayuwar nan datake ciki ayanzu, ‘Karar 
kwankwasa kofar da’ake tayi ce ta addabeta, Ta’kira Mai gadi shiru bai amsa ba, haka ta taso tanufi wajen; 
“Miemah kibudemin kofa ni neh. a 
A tsorace ta zaro idanuwarta” Asad meye kazoyi anan? ‘dan Allah katafi, Karufamun Asiri Aunty Safeenah zata iya kasheni idan ta dawo ta tsamemu tare awannan lokaci. Cikin muryar kulawa yace” Zuwa nayi nadaukeki mutafi tare banasan zamanki anan gidan Safeenah zata iya hallakamin keh, Miemah please ki amince dani. 
Ahankali tace’ Asad wallahi na amince da kai Kuma Na’gode da irin soyayyar da kake nunamun, Nima inaji ajikina zamuyi soyayya mai zurfi dani da kai amma ba yanzu ba,This is not the right time Asad please go I love you. 
Asad na’jin wannan ya hauro katanga ya haye, sai gashi cikin gidan, agaban Miemah ya durkusa har kasa yana hawaye “Miemah kibiyoni mutafl, Wallahi bazan taba barinki a hannun Matan nanba. Tausayin Asad tasa Miemah ta amince da bukatarsa,ya mike cikin sannanin farin ciki ya rungumeta thank you so much, Miemah na gode. 
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Momcy kishigo gida kika abundake faruwa acikin gidanki. Mommy na cikin mota tafito kai tseye ta’karaso cikin gida “Laa haula Wala kuuwata illa billahil azizul hakeem’ Wato Miemah idanu sun bude Koh, Iskancin naku har cikin gidan nawa, in my husband house, cikin gidan Mijina. Tabe baki Maisha tai “Cikin gidan uba na, you guys are not serious momcy kada kibarsu Daman nafad’a miki wannan Yarinyar Yar iska ce, Miemah Karuwa ce gaba da bay …… 
Bata ‘karasa kalmarda take kokarin furtawaba taji saukar Mari a fuskarta. Mommy, Miemah harma da Maisha baki suka sake suna binsa da kallo. “Asad meyesa ka mareta? Miemah tafada cikin rawan jiki. Bai furta musu ko kalma guda ba,juyowa yai yafitce alokacin. 
Maisha na kuka ayayinda tafara buga ihu tanacewa’ Momcy wallahi wannan yarinyar da kike gani Karuwa ce gaba da baya, da ita da Mainah duk layinsu daya yan iska ne na’kin ‘karawa…. 
‘Daga hannu Mommy tai alokacin zata kaimata Mari kenan ta tsei da hannun nata, inda ta’kara kurewa diyar tata ido “How dear you Maisha, kada ki ‘kara zargin Mainah da wannan muggayen dabiun, Kamaryadda kike diyata haka Mainah takejinina sabida haka ko da wasa banson ki Kira furta wannan maganganu gameda ita. 
Shiru tai tanabin Momcy da ido bacin rai kamar tasha’ke kanta ta mutu alokacin ko ta huta da irin wannan wahalhalun datake fuskanta ayanzu. 
Karfe Goma Sha daya na dare, Maisha na tseye gaban mujallar Hoton Zaid tana kuka “Wai shin ahaka rayuwarta zata ‘kare? Kowa najin d’adi, kowa na sa’mun abinda yakeso amma banda ita why? Why? Why? wani laifi ta aikatawa uban giji? Hoton ta runguma tana ‘kara wata sabuwar kalar hawaye” Zaid wallahi kai mallaki na ne, I can sacrifice everything Amma Banda kai, Ma’inah ta shiga tsakanina da iyayena, tayi tsanadiyar rabuwata da kowa. 
Mainah sam farin ciki bata kamaceki ba, hakama Miemah dukkannin ku baku dace da Farinciki irin hakaba, wallahi wallahi wallahi sai na gurbata rayuwarku harma da Zaid din shi kansa sai yayi da’nasanin rabuwa dani, Rayuwarku bazata taba tafiya yedda kuka tsarata ba dazaran Ina nan raye a doron duniya. This is a promise. 
Asad ka’zauna shiruu kamar gunki tun tuni magana nake maka ba’ka ansawa. Zaid ya’kara matsowa har kusa dashi “are you Okay? Talk to me please so fa ba hauka bace. 
Sai yanzu yabude baki yafara magana cikin sanyin jiki” Abokina kaga irin wahalhalun da wannan baiwar Allah take sha ahannun matar Kawu Sambo, Gaskiya I’m sorry to say wannan surukar taka shedaniya ce. 
Babu martaninda Zaid ya maida masa, Tabe Baki yai yanacewa” ls too late Asad karfe Sha biyu ta’yi ya’kamata katashi kaje daki kai barci. Dasauri ya girgiza kansa “lnaa ai barci bata ganni ba Miemah tana bukatata kusa da ita ya’kamata ………. ‘Karar wayarsa ce yakatse shi, yana duba fuskar Yar Halak Miesad ce, Sanda yami’ke tseye sannan yaisaurin d’agawa “Hello Miemah I hope Babu abunda yafaru dake, are you ok. 
Asad kazo Gamji Hotel yanzun nan kasameni dan Allah Kayi sauri za’su kasheni. Abunda tafad’a kenan sannan ta katse wayan. Zaid na faman tamabayan Asad meke faruwa amma inaaa rugawa yai aguje yazaro key motarsa “fuuuuu” ya fita, irin gudun dayakeyi akan hanya kace tashin tuniya ake. Minti hamsin kacal ya iso Gamji Hotel, adreshinda tafad’a masa yabi har cikin wata daki kebabbiya, Yana shigowa ya tsameta awajen ta’sha kwalliya Shar! Ta hadu iya had’uwa. 
Dasauri Asad ya’karaso inda take “Miemah are you 0k? Mikewa tai kai tseye tasa ba’kinta a lebbansa, Asad yana kokarin Magana ta zaro wuka cikin Jakarta aiko babu abinda yaji sai chukin wuka a cikinsa. Nan ta’ke yazube “Miemah komenene kikayi mini wallahi bazan taba Dena sonki ba har abada, Jini na bulbulowa a bakinsa yayinda yakecewa Miemah meye nai miki? 
Du’kawa tai har ‘kasa, tasa ba’kinta a kunnensa tanacewa; Ba Miemah bace, Maisha Sambo Maidugu ce, na dau alkhawari sai na hallakaku duka yanzu dei na gama da kai da Miemah sabida gidan yari zata kare sauran abokinka Zaid dakuma Yar Uwata Ma’inah. 
Cikin wata duniyar zafl da Azaba yace’ Maisha dan Allah ki isarda sa’kona zuwaga Miemah kifadamata cewa Ina Sonta. Bai ‘karasa kalmarsaba, ta’kara choka masa wukara kirji, nan ya’karasa maganarsa da “Lailaha illahu
Muhammadu Rasoulul Allah (SAW). 
Mommy ta’kara hasko wuta a dakin Maisha, Nan tabbatar idanuwarta ba gizo sukemata ba, Miemah ce kwance akan gadon Maisha Kuma da kayan Maisha a jikinta, Ruwa ta debo daga waje ta zubo Mata, A firgice Miemah tamike tana Salati. 
Meye kikeyi a d’akin Maisha? Mommy ta daka mata tsawa. Sai yanzu Miemah taga’ne inda take, lta kanta batasan taya tashige d’akin ba Kai har kayan dakejikinta duk batasan lokacin da tasakosu ba. Rasa amsarda zata baiwa momy tai sai zura Ido take a tsorace tasauke daga gadon tazauna a ‘kasa. 
Ina Ma’isha? Momy ta duba agogo karfe Sha biyu da rabi. “Nace ina kika kaimun ya cikin wannan Bakar Daren? Ta ‘kara tambayarta cikin damuwa. Ina Ma’isha ta take? 
Bata rufe ba’kinta ba, sai ga Maisha ta shigo sanyeda kayan Miemah da wayoyin Miemah a hannunta. Shiru momy ta tsaya tana binta da kallo sabida daganin haka ta rigada ta tabbatar dacewa akwai wata gagarumar sharinda ta aikatawa Miemah. 
Mommy ta‘kasa furta komai, janyota tai sukaje falo “Maisha daga ina haka cikin wannan uban Daren? Ganin irin fargabanda ta bayyana a fuskar Ma’isha tasa hankalin momy ta’kara 
tashi. Tayita tambayarta itako shiruu take tamkar gunki, Har Sanda momy ta kunna mata wuta dajajayen ldo sannan tai magana. 
Muryarta na karkaruwa tace’ Momcy ki gafartamin wallahi ni kaina ban taba aikata
Irin wannan laifin dana aikata ayau ba, Momy zuwa nai na kashe Asad Kuma nabi duk hanyoyin da za’a tuhumi Miemah da laifin Yan Sanda zasu iya zuwa nan at anytime. 
Tana ‘karasa furucinta, Babu abinda taji sai saukar mari afuska “Maisha nice na haifeki kuwa? Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun’ Zubewa momy tai akasa tadafa kai sai kuka take ” Maisha Yaushe kika fara kisa? Maisha daman rashin hankalin taki, ta’kai haka. 
karya kuke Asad bai mutu ba, yana nan da ransa. rungume Mahaifinsa yai yanata kuka abun tausayi. 
Yan Sanda sun’kai Gawan Asad, Zabir Mansion, kowa ya’taru awajen, yanjarida sunata aikin d’aukan hotuna ayayinda yan Sanda suka kewaye wajen suna ‘kara investigations. Ma’inah na labe ajikin Mamytana kuka yayinda Anisa ko kejikin mahaifiyarta itama tana kuka, Kowa kuka yake dashike Asad yanada Fara’a har masu aikin gida suna jimami da kuka. 
Alhaji Zabir ya’koma falo tareda Zaid yana kokarin kwantar masa da hankali amma inaa shi dai kawai afadamasa Wanda ya aikata wannan laifln ko wanene ayau shima sai ya dandani azaban duniya. Yan Sanda sunrigada sun tsanarwa Mahaifinsa batun Miemah ce real culprit din amma basu fadawa Zaid ba tukunna sabida irin Halinda yake ciki ayanzu. 
Tun dasafe Miemah taketa Mamaki, Bata taba ganin momy da Ma’isha cikin irin wannan yanayinba, yau tin safiya suna zaune a falo shiru ko TV Basu kunnaba bare ace kallo suke. Cikin wannan mamakin ta labe ba’yan kujera chan karshen falo itama tazauna. Zamanta ke da wuya saiga y’an Sanda sun ciko falo, Miemah ta’rasa meke faruwa. Yan sandan suna shiga Momy da Maisha duk suka mike alokaci daya suna nunota “Ga’tanan itace Miemah ita ce ta kashe Asad Abdallah. 
Miemah ta rasa ga’ne abinda ke faruwa har Sanda Yan Sanda suka rufe hannayenta da “Anko” anan tafara kuka tana tambayarsu laifinda tai. Babu Wanda ya tankamata cikinsu, kwasota sukayi daganan Babu inda suka sauketa sai cikin motarsu. “Innalillahi wa Inna 

®NEXT CHAPTER SPOILE R® 

Wace irin magana kakeyi haka Alhaji dan Allah nidei kawai kahado Mana Urgent flight dani da Maisha da Mainah zamu taho America mu tsameka. Muryar Daddy ya‘nuno mamaki sosai yayinda ya’kara tambayarta’ Safeenah wallahi na’san 
akwai abunda kike Goyemun, sabida babu yedda za’ayi haka kawai kicemun zaki dawo America tareda Yara kusameni ba Gaskiya akwai matasala, fadamin menene? Momy ta’rasa inda zata fara bullomasa da Maganar” Bukatarka nake kuma Gaskiya bazan iya jurewa ba. 
Ya‘rigada ya’gane wannan maganganun datake duk karya takejeromasa, “Toh why not kizo ke kadei banda Yara, sukuma meye zasuzoyi? Jikin momy na rawa awannan lokacin ta rasa inda zata bullo Masa, gabanta har fad’uwa take koda tagane cewa Daddy ba’zai taba gamsuwa da wannan fake maganganun datake tsaromasa,ba ajiyar zuciya tasau’kar kai tseye tafara furta Gaskiya d’aya ba’yan daya har Sanda ta’kai inda y’an Sanda suka kamo Miemah Sannan Daddy ya dakatar da ita. 
Ma’isha ce tai kisan sannan kika rufamata asiri aka kamo Miemah? Cikin hawaye momy ta gyada Kai “Toh yazanyi kaima kasan bazan tonawa Yata asiriba na gwammace duniya nan duka su wahala akanjinina Ma’inah da Maisha su wahala…. 
SAFEENAH, MAISHA BA JININKI BACE, Daddy ya katseta, ki gafartamin na boyemiki sirrinda baikamata na boyemiki ba amasayinki na MAHAIFIYAR MIEMAH …… Dakata Alhaji, chak hawayenda suke zubowa a idanuwan momy suka tsaya “Meye kake nufi Alhaji kada son Miemah yasa ka aikata laifinda Allah zaiyi fushi da kai, wace irin magana kakeyi haka? 
Akwai wata tsohuwartakardar da na ijiye cikin wata kwali a karkashin gado na, wannan takardan tun ranarda kika haihu na rubutata kuma ina ganin ayau ce anfaninta tazo, wannan takardar ce kadei zata iya gwada miki gaskiya ayanzu. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]