[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER6 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 6Yau basu da paper, suna gida, Fadila ta shigo Sashen Uncle Abbakar, Aunty Raijana na zaune na kallon wani Fim, Aunty Maisah fa? cikin hausarta da haryau be fita tace ki dubata dakih, ta shiga, tsakih ta buga da qarfi, Oh Allah haka zaki qare dai, don fa kiyi sauri ki shirya yasa na kiraku tun dazu, amma jibeki shafa ki keyi, Maysah tace sorry riga kawai zansa tace wlh ki same mu sassan Baba Hussaini, bari naga Islah ta shirya, ta iske Islah ta shirya duka dai ita ake jira, Islah tace lemmie guess maysah bata shirya ba, Fadila tayi dan guntun tsaki tace ke da kika san komi, yaya Suraj ya shigo dakin yana Sisi bani earpiece dina, islah tace bro don Allah bari mu dawo zan baka, yace kinga dai ki-shiru yayi da idonsa ya kalli fadila, murmushi ta mai tace Ya suraj ina wuni, ya mayar mata da murmushin yace wacece wannan? Tace fadila ce, lalala haka kika qara girma, kai murmushi ta mai, Yace ina zaku ne? Islah tace walimar Quranin qawarmu, ya kalli fadila yace tohm muje na kaiku koh? Ta dago kai suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta, Islah tace wai sarkin Nawa mukejira, wacece sarkin nawa kuma? Maysah ta shiga dakin tace iyayen mita gani nan, Ya suraj ina wuni? Ya sakar mata murmushi ya ganeta don fuskar aunty Raijana gareta, yace Rumaysah wai duk kun zanqale banda su o’oh Islah ta turo bakih tace kai koh yaya? Ban mayi missing dinka ba, yace liar, ku tashi muje, suka nufa parking lot motar da Tsoho ya ba kowannensu bayan dawowarsu, ya bude ya shiga Islah ta bude gaba zata shiga yace ke zaki shigo ki isheni da surutu koh? Koma baya Eeelerh dawo gaba kinji suka tsaya kallon kallo waye kuma eelerh anan? Ganin Fadila yake kallo yasa ta gane da ita yake, ba musu ta shiga gaba, Maysah da Islah suka shige baya, Ya kalleta eeelerh ina zamu ma? Jikin ta yayi sanyih ta gaya mai, bini bini yakejan ta da hira, Islah cikin rada tace maysah kin ga abunda na gani? Ita ma cikin murya qasa qasa, tace nagani, Ya suraj ya fado suraj ya kallesu ta mirror yace gulmanmu, me kuke cewa? Sukayi daria, suka iso gidansu Fatima Bobboi wace ake ma sauka din, fita su Islah sukayi, fadila zata fita taji Ya suraj ya riqe mata hannu juyowa tayi cikin tsiwa taga yana kallonta ba shiri ta kai kanta qasa, a hankali yace I love you fadila, Kallonshi tayi da sauri yace Fadila will u marry me? Murya na rawa tace, Ya suraj kasan dai we are not allowed to fall in love koh? Kayi sauri’ ka cire wannan tunanin don baka san wacce tsoho zai baka ba, yace fadila, yanzu ba a auren dole, all am asking is for u to let me love u, nd i promise u, u wont regret it, ya qare matse hannunta, yace pleaseee, a hankali tace i love u ya suraj, ya sake ajiyar zuciya. Islah ce ta durquso ta window, hey are u coming or not? Suraj yace shes not bye bye, Fadila tayi mata gwalo, Rumaysah tace kema dai ina ruwanki kizo mu shiga ciki, in yaso sai muce ma bobboi tana love cikin mota. Sai da Suraj ya tabbatar ya gina sense a ziciyar fadila kafin yace ta shiga ta mata Allah sanya Alheri ta kira su Islah suzo su wuce.
Nikam Mu’ammar ka gaya ma hanifan? Ya dan tabe fuska yace kasan bana son raini, but zan aika Bilkis, Jawad yace kana bani mamaki wlh, kana son abu amma girman kai dinka ba zai barka ka furta ba, kuma idan gudu kake kar tsoho ya hadaka da wata, dama ka bar tunanin nan, dan a kanmu Culture dinnan na auren hadi zai tsaya, fine ba xa mu aura bare ba, but a bar mu mu xabi na cikin gidan da kanmu, amma idan kaga zaka tauye ma kanka haqqi ka auri wacce baka so den goodluck wit dat, Guy, yaka dauki zafi ne haka, yace Allah bana son bacin rai, wai hadin Aure kawai sai a hadani da wacce banaso, yace wlh akwai matsala don ba yarda zanyi ba, yanzu ma Bilkis zanje nayi approaching, Muamar ya kaimai duka, kaii careful! dats my lil sis, Jawad yace na ga nima hanifan sista tace, hurt my sis nd i will hurt urs, sukayi daria daga nesa suka hango haneefa ta fito daga sassan su tana yauqi, Jawad ya miqe tare da cewa man up and tell her wat u feel, yakwala mata kira Hanee, ta qariso tana wannan yauqi, Yajawad yadai? Yace Yayan ki ke kira, wane yayan? Ya nuna mata mu’ammar tace 0k, ina Bilkisu ne? Tana sassan hajia babba, yace ok yayi gaba ita kuma ta nufa Yamu’ammar how far, yace hanee am in love, jin maganar tayi wani bambaraqwai, tace with who? With you ta zaro kyakyawan idonta tace what? Shima ya zaro mata nashi yace Yes i love haneefan Baba Mudassir tayi rau rau da fuska, Yamu’ammar namiji ne da ko wacce mace zata so, haneefa tace amma Yamua’ammar kasan tsoho-~shh ya dakatar da ita, i dont care abt tsoho‘s decision ol i know Is dat i lob u, unless ban miki bane ba, tace Aa fa ba haka bane, yace nasan me kike tsoro, but its high time su bar wannan Culture din, munji ba zamu auri bare ba, amma a bar mu mu xabi na gidan da kanmu. Bazan taba iya auren yarinyar da bana so ba gaskia, Tace toh shkn, Allah ya bamu saa, ya dan kallota is dat a yes? Ta kashe mai ido daya nan suka zauna suna firar soyayyah..
Hajia Babba tace Ahh yau Jawad a sashe na? Tunda kuka dawo so daya ka shigo dakin nan da ba ni na haifi uwarka ba kuma na riqi ubanka ba da nace kai bajikana bane ban san ko Aishalleta shiga tsakani da kai ba, yayi daria, kin cika mita wlh, wai ni meye matsalarki da Hajia Ama ne? Ko don ta aure miki miji?Tsohon ma ya tsufa amma kina kishinsa haryau, ko don ta fiki kyau ne? Da yarinta? aiko ya zunguro ma kanshi, nan ta fara zagezage da tsinuwa,yo indai kyau irin na mayu ne wlh na yarda nafi duwawu muni,Allah ya tsareni da kyaun Mayyu da Aljannu, nan ya shige dakih yana daria zaune ya ga bilkis tana ninke kayan Hajia Babba, yace Sis ya dai? Ta fadada murmushin ta, duk cikin causins dinta Yajawad ya fi burgeta, tana mugun sonsa Yajawad ina wuni, yace me kikeyi? Hajia ta sani ninkin kaya, yace duk cikin yaran gidan nan Hajia ta rasa wanda zata sa aiki sai matata? Dadi kamarya kashe bilkisu amma ta wayance tace matarka kuma? Wace matarka? Yace ke mana. ko ba zaki aureni bane? Tayi mai far da ido, tace Dan tsoho zai baka mata, Yajawad yace ke ni rabani da wannan hadin zumuncin, ni ke nagani nakeso inaso sai dai in kece ba kyasona, da sauri tace ina sonka fa Yajawad, yace lets stick togeda, bame rabani dake kinji? Ta gyada Kai tana murrnushi. Sanye yake da 3quarter hannunshi riqe da basketball ball, leqawa dakin Jawad yayi yaga bayanan, ya leqa dakin mu’amar beyanan, tsaki yayi yaga suraj kwance yace guy muje muyi basketball, Suraj yace uhm uhm not in d mood, Zayyad muje muyi, zayyad yace No thanks tsaki yayi yace Kar Allah yasa kuyi, haka ya isa field din da ke bayan Sashen Hajia Ama yana bouncing ball din. Da ya hango basketball court dn ya wurga ball din, daga chan nesa Islahulkhair ce ke skipping,ji tayi saukan Qwallo a kanta, qara ta sake na shagwaba ta dafe kanta tana kallon wanda ya jefeta da ball cikin tsiwa tace baka gani ne? Ya kalleta yace da kika ga ball me yasa baki matsa ba, Miskilancin Islah ya tashi, taga idan harta tsaya tanka mishi tana iya sakin kuka ta duqa ta dauki rope dinta tai wuce warta, har ta kusa barin field din ya daga murya yace Islahulkhair tsaya wa tayi bata juyo ba, yace kin iya B.Ball? Juyowa tayi tace wat if na iya? Yace i want u to play wit me pls, kamar ba zata tanka ba sai kawai ta qaraso tace lets do dis, ya fara bata ball din suka hau bugawa, sai da yayi mata 120 wai ita ojoro yayi haka zatace bata yarda ba sai a sake, haka suka dinga yi ko daya bata ci ba, tace a qara one last time, yace Nooo nan tayi wayon kwace ball din taje ta sa a ragar sa, yabita ya qawace ball din ta yi tangar tangar zata fadi ya tallabota suka zube a qasa suna daria sosai, yace Islahulkhair I need someone da zan dinga games da ita bayan nayi aure, i love games, nd u fit wat i like, so u want to be my game partner nd my life partner? Ta tsureshi da ido, yace zan fahimceki idan kika ce aa don nasan beef din dake tsakanin Grandma dina and ur grandma, but karfa ki manta mun hada kaka dake da babana da mamanki Uwansu daya ubansu daya nima ina dajinin Umma hajja atare dani so ban ga dalilin da zaisa ki qini ba, oh maybe ban miki ba, ya miqe ya barta kwance har yajuya, Islah tayi saurin cewa Ya samirrr yajuyo ta miqa mai hannu da ga kwance, yasa hannu ya dago ta, cikin sanyin muryarta tace Yasamir am scared, yace i knw wat u are afraid of, dis Culture has to stop now, ba Zamanin daaa muke ba, trust me pls, ta daga mai kai tace ok. Yace l love u Islahulkhair cikin kunya tace ilove u too ya samir

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]