[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 8
Tsoho yace ku tashi zan ne meku, Duk suka tafi, Tsoho yace Hassan da Hussaini da Gambo ku tsaya akwai magana, Su suka koma suka zauna, Tashin hankali, in akwai abunda Hajia babba ta tsana be wuce yanda M.Zailani ke nuna wariya ga yaranta ba, tayi mitar tayi masifan amma shirun, A cewarshi sune manyan yara maza a gidan, duk da bashi ya haifesu ba ammajinin qaninsa nashi ne kuma yana auran Uwarsu, Yo su Mudassir da Labaran fa? Ai in akwai Manya be wuce su ba ko? Yace toh bana buqatar shawararsu, idan ina da buqatar hakan zan nemesu, haka zata zauna ta tara yaranta ta chusa musu tsanar Qanwarta Hajia Ama. yaran Umma hajja ne abokan shawarar Tsoho, k0 yaransa na cikinsa(‘yan dakin Hajia Ama) be neman shawararsu, da yake su masu fahimta ne basu taba damuwa da hakan ba. Tsoho baya yanke hukunci sai ya nemi shawarar Baba Hassan, Hussaini da Baba Gambo. Yace Ya kamata yaran nan a aurar dasu don naga har wasu daga cikin su sun fara magana, Baba Hassan Yace Tsoho ina ga kamar a bar yan samarin su gama bautar qasarsu su kuma matan ko Dan Computer skul a sasu na shekara 1, Tsoho yace amma ka san da sun gama ba a jiran komai sai a aurar dasu, in yaso su tafi dasu chan wurin bautar qasar tasu. Baba Hussaini yace Ehtoh Baba haka ake yi a da. Amma yanz ina ga a dan qara musu shekara 1, lokacin sun gama bautar qasan har sun fara aiki kowa ya samu na kanshi, sai ayi auren su dauki matansu su tafi dasu chan. Tsoho yace toh Shikenan Allah ya shige mana gaba suka amsa da amin.
A hanya Samir ya samu Ameerah, yace Amira meyasa kikayi rashin kunya gaban tsoho? Ta kalleshi da niyyar mai masifa taga ya tsureta da ido, tace kaga dai ina jin kunyar ka ko? Meye rashin kunya a ciki? Son Ya zayd ko ce musu da nai ai mana aure? Ai nasan kowa nason auren nan, don na ari bakinku nayi magana sai ace nayi rashin kunya, da yake yana da sanyi yace Ba haka nake nufi ba lil sis meerah, waiyo Allahna wannan sunan yayi dadi yasamir, dan qara fadih muji, yayi smile yace Lil sis meerah, ta saki ihun da ya tsoratar dashi, taja hannunshi kamar wani soko ya bita suka zauna, Dan Allah Yasamir ina son sunan nan ka dinga kirana dashi kajih? Yace toh ynz kinsan me nakeso dake? Ta girgiza kai, yace inaso ki zama me kunya, kinga dai da babanki da mamana ya da qanwa ne k0? Ta daga kai, to inaso ki zama me kunya da kawaici, idan kina da problem ki fada mun kinji? We’ I’ll solve it togeda, nd if u nid someone to talk to, i’ll b ryt here, tace ba zaka gujeni ba? Don mutanen gidan nan na cewa na cika damu nd ina da saurin ginsa yace bazan taba gajia da maganganun lil sis meerah ba ko da kuwa zamu kwana tana mun labari ne, tayi murmushi tace to big bro samir, yayi smiling zaiyi magana wayar shi tayi qara, Islah ce ya dauka hey babe gani nan zuwa, Amira ta kalleshi tace waye Babe? Yace Islahulkhair, tare da miqewa yace bari naje, tace big bro samir ya juyo yace naam lil sis meerah? Tace u think Yazayd will like me? Jar uba yace a ranshi a fili kuwa ce mata yayi he will love u. Tsalle ta daka tana tafi yace i gotta go, oryt bye, ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da kallo, dabadan Yazayd ba da tace tanason yasamir…
Yanzu ku haka xaku tsaya wasu bare da basu fiku da komai ba su mallake muku malam? Kune yaranshi gudanjininsa, Aunty Zainab (matar Baba.Gambo) tace haba Hajia wai kullum sai an nanata maganan nan, wannan magana an dade anayinta fiya da shekaru 30. Ni banga laifin baba ba, Keee Zaynaba, yi man shiru mutuniyar banza da wofi inji hajia babba, kai Allah ya isa tsakanina da Hajjo, ynz sai da ta shanyeki? Ta gama dake, takai sunanki gaban boka da yan tsibbu, tashi ki ban guri banza sususu wanda bata kishin kanta da yanuwanta. A. Zaynab ta miqe sumsum ta bar dakin yanuwanta suka rakata da ido, ita ko Addu,a take musu Allah yasa Ta gane. duk dakin karime ita kadai ta fita daban. Amira ta shigo sasan taji Muryan Babanta (Baba Usman) yace Yanzu Hajia meye abinyi? Yauwa mafita dayace, hankalin Musbahu ya karkato kanmu, ni da ‘yayana da jikoki na kadai, yayi watsi da lamuran ‘yan dakin Aishalle da Hajjo, ya zamana muka dai ke gabansa, Aunty Abida tace taya zamu sa hakan ta kasance? Hajia babba tayi murmushi tace ku bar komai a hannuna… Zan shayar dasu Mamaki, da nayi sanya amma yanzu ko ni ko su. Ku tashi ku tafi. Duk suka miqe Amira naJin haka tayi saurin barin gurin, da niyyarta tashiga tace Allah ya tona Asirinku, sai kuma ta tuna da mgnr Big bro samir na dazu. Tayi sassan su Islahulkhair da gudu, zaune ta iske su suna shan lov, ta zauna gabansu tana haki, Islah ta miqe da sauri lafia Amira? Samir cikin damuwa yace lil sis meerah wats wrng? Ta fara zuba zance, ba wanda ke gane me take cewa, Samirya dagota yace kallenih, ta kalleshi yace fada mun me ya faru a hankali, a hankali kuwa ta dinga zaryo duk abunda tajih, hankalin Islahulkhair ya mugun tashi Tace yanzu me zamuyi? Muje mu sanar da Tsoho, Samir yace wait. Islah na, no one must know abt dis? Tace heyy we are talking abt my parents nd grandparents i can’t just stnd here and do nthn, wel yea my father too is involved my grandma olso, meye amfanin gaya musu? Suyi ta tashin hankali? Su rarrabu? We are going to stop dis frm happening, mu 3 dinnan! I dont trust Amira, kasan bata-Amirah ta chakumo islah tace banida me? Samir ya shiga kwatar Islah data qi cewa komai, don ita ko chachan baki ake da ita bata daga kai ta kalleka balle ta tanka maka. Amira ta saketa tace U dnt trus‘ me? Yo trust dinki nakeso dama? I am telling on my dad nd his siblings, yet u dnt trust me, ke a tunaninki ban san abun da nake ba, Bani da hankali? Toh da uwarrrr-samir yayi saurin rufe mata baki tare da
cewa ya isa lil sis meerah. ldan har kuna so plan din mu yayi aiki we will have to work together, ku ajiye differnces dinku aside. Amira tace Ni bro banda matsala itace dai ke da ciwon qwaqwalwa shisa bata san who’s on her side ba, Islah tayi murmushi tace kiyi haquri Amirah i dnt mean to, tayi murmushi tace toh shkn ya wuce, big bro samir me zamuyi??? Yace Yauwa sisters abinda zamuyi shine musa musu ido sosai, duk moves din da zasuyi muna sane, Islah tace How? Yace yauwa we’ll kip a close watch on dem, ni da Amirah mune ‘yan ciki zamu san me su keciki, barin ma ke Amirah ke macece, zaki fi kutsawa ko ina kingane me nake nufi? Tace nagane i’ll prove to u m not crazy as dey think i am, yayi smile yace i know, My lil sis meerah is’nt crazy. Tace yauwa Yayana kama wannan budurwar taka warning ta qara ce mun mahaukacyi sai na zaune mata ruwan Hanji, suka fashe da daria duka, islah tace Oh Ai fa na bani da mita, ba kince kin haqura ba? Ameerah tace wai misali nake baki, Samiryace Amirah kar ki manta, kar ki gaya ma kowa kinji? Tace ba wanda zai sani, Okay i will leave u too ku dan sha soyayyah ta fada tana kakkashe musu ido tare da tafia duk suka sa daria. Ooo Amira halinki sai ke.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]