[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA


CHAPTER 5
HaJia babba ta tafa hannayenta blyu tana salati, Abbakar kafira ka auro ka kawo ta cikin gidan nan?wani mugun harara ya jefeta dashi, Hajia Ama tace yanzu daman baka da wayau, Abbakar ya dafe kanshl, Umma hajja tayi saurin miqewa ta ja hannun Raijana tayl waje da ita, sassan ta ta kaita ta shigar da Ita daklh, ta debo mata abinci ta mata alamun taci sbd bata iya turanci ba, Raijana tayi murmushi tace thank u, Umma hajja ta komo cikin babban parlo, Abbakar xube gaban babanshi, yace Baba ka yafe mun. bana son aikata sabo ne yasa na aureta, kuma musulma ce, ta rabu da mahaifanta saboda ni, baba idan na rabu da ita ban mata hallaci ba, na kuma ci amana, shlru ya glfta na wasu yan Iokkuta M. Zailani yace shikenan Allah ya maka Albarka, na yafe maka, amma daga yau ba wanda zai qara auren bare, kuma ni zan zaba ma kowannenku mataye da mazaje, yace nagode baba. Abbakar ya matsa gun mahaifiyansa Hajia Ama, yace Ama dan Allah ki yafe mun, tace bakomi Abbakar Allah ya bada saman lfy. Yace Umma hajja ina raijana? Tace tana chan daka, ya nufe dakin tana ganinshi ta fashe da kuka, Abbakar ur family is against our marriage ryt? Ya rungumeta yace dont cry, dey are not like dat, i explained evrything to dem, and dey understood me, u have nothing to worry abt. 30 years later..
Baba Mudassir da Aunty Abida (first daughter karime) na da yara 7, Tahir, Fatima, Noorayne, Zayd, Farida, Haneefa sai auta Ahmad, Baba Labaran da Aunty Sadiya na da yara 5, Yusuf, Khamis, Mu’ammar, Yusra , Bulkisu. Yaran Aunty zainab(diyar karime) da baba Gambo(dan Hajjo) 2, Samir, Samar. Baba Usman kuwa da Aunty hafsat diyarsu daya NI’Ima sai da suka shekara 15 da aure suka halfeta. Baba Hassan (dan Hajj)da Aunty Maryam(diyar AIshalle) na da yara 4, Imran, Faisal, Munira, sai auta Nasir, Baba Hussalni da Aunty Nur yaransu 3,Irfaan. Zayyad da Raffiyah, Baba Aliyu(dan Alshalle) da Aunty Hassana (diyar hajjo) nada Yara 3, Aisha. Nabila saI fadlla. Baba Umar da Aunty Hussalna na da yara 2 daga sai Islahulkhair. Uncle Abbakar da Aunty Raijana(yer mutanen Russia) diyarsu daya tilo Rumaysa’u….””‘““
Yawancin jlkokin M,Zallani sunyi aure, shike hada auren jikokinsa, Be hada auren jlkan dakin Hajjo da jlkan karime kojikan karime da na Aishalle. hada yan daki yakeyi (misali dan baba hassan da diyar baba Hussaini) k0 kuma diyar (Baba labaran da dan baba mudassir) shi a ganinshi hada auren jlkokin Karime da jlkokin hajjo kona Aishalle matsala zai haifar don yana sane da gaban dake qulle tun kafin a halfi yaransu, amma ya kan hadajlkokin Aishalle da Jikokin hajjo aure don su yasan Akwai yarda da amincin junansu. A qaidar gidan M.Zailani namiji daya gama karatun degree dinshi za,a mai aure, sai ya dauki matarshi ya tafi da Ita duk Inda zan kaita, mace kuwa data gama sakandire ake mata aure ta qarasa gidan mijinta. Jikokin gidan kama sukeyi don da wuya kaga wannan kace yana da kyau wannan be dashi, duk kakansu suka dauko wurin kyau da haske, Sai dai kowa da halinsa, suna gaban da suka ga kakanninsu sunayi, yan dakin Umma hajja da haJia Ama kadai ke zaman lafiya, Amma baka ra’ban yan dakin hajia babba, don da kun wuce sai ta zagi kakarku. Maza 7 zasu kammala degree dinsu ko wa da fannin karatunshi, gabaki dayansu suna Oxford University, Mata 6 kuma kejarabawar qarshe, kuma da sun gama za a hadasu Aure, matsalar gidan baka soyayyah don baka san dawa za,a hadaka ba‘ amma ba za,a rasa wanda kake burin a hadaku dashi ba.. Wannan kenan.
Kowa da halinsa, Islahulkhalr ba ruwanta da kowa, maganaa be dameta ba, Yan dakin Hajj babba ke mata laqabi da erjiji da kai, Fadila kuwa ba tada haquri k0 kadan, idan ka mata lalfi nan zata wanke ka tas, shisa Haneefa da bilkisu ke shakkunta, NI’Ima kuma gata nan dai laflyarta lau amma idan ta maka abu sai ka zata me Ciwon hauka ce. abunta dai kamar sakarya, kuma Qalau take, Rumaysah kuwa haqurinta yayi yawa, matsalarta daya Nawa, bata abu cikin hanzari, ko abinci su keci kowa sai ya gama ya barta. yan dakin Hajia babba ba irin zagin da basa ma mahaifiyarta kasancewar mahaifiyar ta yar wata qasace. kyanta dai yafl tada musu hankall, suce mata mayya Aljanna, k0 su zage kakanta Ama, tafi duka jlkokin gidan kusanci da Tsoho(M.Zarlan|) saboda yanda take kuka dashi,tayi mishi tausa, da hira. har yaqi cin abincin sa yace Nata zaici..
A halin yanzu suna ta fama da Jarabawa ta NECO…
Gida ya kachame, yau baqin turai zasuzo, shiri ake tayi ba babba ba yaro, shekara 5 kenan rabon su da gida, Har masu aure ‘yan nesa da kusa sunzo, misalin Qarfe 2 daidai suka shlgo gldan, Waiyo Allah, Akwai mazan Hurul Ayn dama? Ko wannensu najin kanshi, sai dai su basa yar tsama dajunansu, ba ruwansu da beef dln iyayensu ko kakaninsu, son junan su suke kasancewar sunyi shekara kusan 6 guri daya inda basu da uwa ba uba… Sallama sukayi a parlorn Tsoho, Murna ya lullube iyaye da kakaninsu, zube wa sukayi gaban tsoho suna kwasar galsuwa, kafin kowa ya nufl iyayensu, aka gaggaisa.. Tsoho yace Sarkin Gida ka kaisu cikin Sashensu kowa ya zabi daki, yace ku biyoni suka ja Akwatinnansu suka nufa sashensu, ko wannensu ya dauki daki suka shige don huta gajia,.Wurin 5 yanmatan Gidan suka shlgo don yau evening paper sukayi, Babban parlo suka shlge suka ga yayyinsu suna fira da tsoho, kowacce ta nufl yayanta ta rungume, Tsoho yace oh Allah, k0 Sallama babu? Ku tashi kuje kuyi wanka kuci abinci kafin kuzo a gaisa k0? Suka ce toh, suka fice. harta kusa bakin qofa yace Rumah, tajuyo tace naam tsoho, idan bakl gajiba zuwa anjlma ki min wannan hadin shayin tace angama tsoho bari nayi Iaasar, yace yauwa er albarka. Zayyad ya bita da ido, wacece wannan tsoho? tsoho yace duk baku san juna ba, zumuncin ku ya tabarbare, kowa nashi kawai ya sani, dan wannan daki be san dan wannan dakin ba, Zayyad yace ayi haquri tsoho, ayi mana uzuri shekara 5 rabon mu da gida, mun san juna matsalar baza mu shedajuna ba, Tsoho yace Allah shi kyauta. A ranshi kuwa yace dole zan chanza wannan rashin zumunci, na san abun da zanyi, k0 kunqi ko kunso saikun zama TSINTSIYA MADAURINKI DAYA, Ya kalli Mu’ammaryace yaushe Zaidu din zai dawo? Muammarya tabe baki chan yace nan da wata 3, tsoho yace wai saboda mene baku dawo tare ba? Inace duk tare kuka fara karatun? Samlr yace kwantar da hankalinka nan bada jimawa ba zai dawo cikln yanuwanshi. Tsoho yace akwai abunda ba kwa so na sani, Suraj yace kasan ko sun boye ma ni me fada mane, yace toh Allah sa dagaske ne, suka ce hakan ne ma. Yauwa da kunyi bautan qasa sai Aure k0? Muamaar yace Alfa maganar kenan Aure Aure mundawo gidan gandu kenan kenan. duk suka sa daria….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]