[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 4
lnallllahi wa Ina Ilaihir rajlun, shi ne abunda Musbahu ke maimaitawa. Hajjo kuwa don rudu kasa kuka tayi, Musbahu yayi qarfin halin kiran maqota don a suturceshi Cikin awa da be wuce
daya aka kai Rabiu gidanshi na gaskia, kafin aka zo zaman makoki, Karime ta dan rude da farko amma daga baya sai ta gyagile wai Allah ke kama maqiyanta ta hanyar kashesu. Bayan Arbain Musbahu ya rungumi iyalan marigayi qaninshi, dukkansu ba wanda be zuwa makaranta banda Hassana da Hussaina.

Bayan wata 5

Aishalle kince kina son muyi wata magana? Tace eh Mallam, daman wani abu na hango, yace me ke nan? Tace Me zai hana tunda Yaya Hajjo taga ma Takaba me zai hana ka aureta? Ina ganin ta hakan ne zaka fi kula da ita kuma ka riqe amanar da qaninka ya barma, ya tsura mata ido, dama Chan yayi wannan tunanin amma yana tsoron abun da zaije ya dawo shisa be gaya ma kowa ba, kaii amma Allah yayi ma Aishalle albarka Akwai ta da kalfin tunani, yace Aishalle kin tabbata wannan shawarar taki har rankl? Don ni bana so nayi abunda zai bata ranki, tayi murmushi Maigidana kenan, kamanta hallacin Hajjo a gareni? K0 kirkinta da kular data bani ka mance wlh wannan abu har raina, don a qasar nan banda kamarku. Yace toh shkn, na amince, tace ka taso muje mu kai qoqon barar mu, yayi daria yace Aishalle baki da dama.
Karime dake labe bakin kofa tana jinsu idonta ya rufe tsabagen tashin hankali, kishi da Hajjo? Alko zaayi yaqin basasa na biyu a gidan nan, kaji wannan hegiyar mayyar, dan taga na barta ta zauna shine harda gayyato hajjo, ganin sun kusa fitowa ne yasa ta shige dakinta da gudu.
……
Hajjo jin maganartayi bambamraqwai, ya za,ayi ta auri yayan mijinta? Kuma Mijin yaya karime? Aishalle tayi sauri tace don Allah yaya hajjo kar ki baza mun qasa a Ido, kinsan duk wnda zaki aura a bayan mijina yake, kuma so kike kiyi aure wani gurin ya rabaki da yaranki? Auren mijina ne mafita gareki, hajjo ta harareta, hussain da ya shigo yace Umma dan Allah ki auri babanmu, shiru tayi sai chan tace Allah ya hada kawunnan mu. Suka amsa da Amin. Ji sukayi ance idan ka isa Allah ya tsinen, ni zaka ci wa mutumci? Hajjon zaka aura? Qanwata? Yayi murmushin takaici, yace yanzun kika san cewa qanwarki ce? Ai aure be haramta tsakaninmu ba, kuma kamar anyi angama, ta chakumo wuyanshi, yace kuran sai ka saken, ya ce so kike na sakeki? Wani dan guntun tunani tayi tace da sauri aa kar ka saken dan Allah, amma yasin da sake ba zata sabu ba. Daria yayi yaja hannu Aishalle sukayi qofa tajuyo ta fara zagin Hajjo, Musbahu ya leqo yace kika qara ce mata uffan a bakin Aurenki wlh kuna kika tafi kin tafi kenan. DIf kakeji kamar an dauke wuta, sai murgude murgude da harare hararen da takeyi, ba halin magana. Oh su karime ashe ana san aurene… Ana idar da Sallahn jummaa aka daure Auren Hajjo da Musbahu ………

Bayan Shekara 15.

A halin yanzu Hajia Babba (karime) Haihuwanta 10 Shida sun rasu saura Abida,Sadiya, Zainab, sai
Usman haushinta daya yaranta maza duk sun rasu daya kawai ya rage mata. Hajiya Ama (AIshalle) yaranta Aliyu, Umar,Abubakar, Maryam, Rabi’u sai Auta Nuratu. Tun Da aka yi Auren Hajjo da Musbahu ko batan wata bata taba yiba, Yaranta da Rabiu basu da bambanci da yaran Musbahu a cikin Gidan.
Dalilin da yasa na tara ku anan shine Na yanke hukuncin hada aurenku duka. kasancewar ku Maza duk kun gama makaranta ga Sanaar ku kunayi, ya kalle Mudassiru da Labaran yace matsayin qannai na kuke, amma aure be haramta tsakanin ku da ‘yayana ba, saboda haka
kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai Labaran Sadiya ce matarka, karime sai fara,a
kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai Labaran Sadiya ce matarka, karime sai fara,a take tayi, don tasan sai yanda tayi dasu mudassir Musbahu Zailani ya cigaba da cewa, Hassan Maryam ce taka Hussaini kuma Nuratu, Gambo kuma na baka Zainab. Aliyu kuma zaka auri Hassana, Umar kuma Hussaina, Abubakar kuma akwai diyarbAlhaji Mai dala’ilu Hafsat, yace ya baka ita charaf Karime tace Wa?? Ai kuran baku isa ba, Hafsatun dake son Usman fa Kuma mun gama magana da mahaifiyar yarinya tace taba usman Hafsatu, Wlh ba wani abubakar, karime sanin dukian Alhj me dalallu ne yasa take son hada danta da diyarshi, Shi dama Abubakar yana daban cikin gidan, yace Baba a bar ma Usman dun, duk daya ne, don be son Auren yanzu musamman na zumunci. ya cigaba da cewa ni dama ina son na qaro illmi, , yace toh shkn da kai da Usman din duk daya ne, Allah ya bada xaman Iafiya. Suka amsa da Amin gabaki daya, Karime tace yauwa Alhaji maganan Zainab da Gambo, ya xa,ayi ka hadata da gambo? Bayan kasan hajjo bata qaunar jinina? Wani kallo daya watsa mata ya sata nustuwa lokaci guda..
…..
Sunyi qoqarin fahimtar junansu, kowa yayi naam da hadin da aka mai, Zalnab kuwa tana son Gambo qwarai da gaske amma Karime tana laantar wannan hadin, Gambo ma yana danne zuciyar sa, don duk dakin Hajia babba ita kadai ce ta fita daban, Hajia Hajjo (mama hajja) da Goggo Ama suka lallasheshi kan yayi haquri yama babansu biyayya, Haka dai yayi haquri ya chusa ma kanshi son Zainab don ya lura tana sonshi.
A haka akayi aurensu, nan cikin gidan aka fidda ma kowa gidansa ciki da parlo, aka aje amare anan. Abubakar har ya tafi qasar Rasha (Russia) don karo karatu.
A qasar Russia ya hadu da Yarinya me suna Raijana, course mate dinshi ce, yau da gobe suka shaqu, har suka qullah soyayyah tsakankinsu, har Abakar ya yanke hukunCin aurenta, Raijana ta gabatar da Abbakar ga mahaifanta, dayake mamanta ‘ta dade da rasuwa, fir babanta yaqi wai bazai aura ma dan Africa diya ba, ta dage ta nace tace wlh sai ta aureshi, yace shiko idan ta nace sai ta aureshi, to ba ruwanshi da ita, ya yafeta, da yake su yan chan sun dauki soyayyah da mahimmanci ta tsallake mahaifinta taja hannun Abbakar, Haka sukaje wani massallaci aka daura aurensu.Haka suka gama karatunsu, sukayi shirin dawowa NIGERIA, yace suzo suyi ma babanta sallama, suka nufa gidanshi amma yana ganln su ya musu korar kare, yace beson qara ganin Raljana, haka suka wuto Nigeria guiwa a sake.
Zaune suke a parlorn M.Zailani gabaki daya ana cin Abincin Gandu, yayi sallama hannunshi riqe dana Raljana, duka suka zubo musu idanu, Umma Ha ta fara ganeshi da sauri ta miqe tana tafa hannu ga Abbakar ga Abbakar, gunta ya nufa don tun kafin ya girma ita yafi sani don tana sonshi kamar ita ta halfeshi, ya rungumeta ta shafa sumar kanshi, ya nufa M.Zailani ya zube yana kwasar gaisuwa, kafin ya nufi Hajia Ama yana gaidata farinciki ya mamayeta amma kawaici ya hana ta nuna, ta amsa, sannnn ya Gaida Hajia Babba ta amsa Cikin yatsina. Ya gaida yanuwanshi, Idon M,Zallani kan Raijana da take tsaye bakin qofa, yace Abbakar wacece wanchan, yayi murmushi ya kamo hannunta ya kawo ta gab da baban nashi. cikin turanci tace Good Afternoon Papa, cikin turancin yace how are u? Tace fine papa, Yace Abu bakar wacece wannan? Abbakar ya murmusa yace Matata ce, Duka dakin suka hada baki wurin cewa MATARKA?


Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]