RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 3

RIKICIN WANI GIDA


CHAPTER 3Aishalle ta saki ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya hadata da bango, yaja hannun Aishalle yayi waje da ita. karime na kwance kasa amma bakinta be daina furta zagih da batanci ga Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi saurin lullube jlkinta da zani. yace hajjo ga yarinya nan dan Allah aba ta abinci kuma tayi wanka a bata kaya, Hajjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga qanwata nan zata kula dake kinjl? Aishalle ta gyada fuska,musbahu ya saketa ya fice,Hajjo tace zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincm nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka.
Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta, ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo yaga ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gidan, don ba shiga sassan hajjo takeyi ba balle ta ganta. Kuma ta hana su mudassir shiga balle su kawo mata rahoton gulma.
Wasa wasa har Aishalle ta samu wata 2 a gidan Rabiu, tayi clean ta qara wani irin kyau me firgitarwa. Kuma tana son yaran Hajjo har ranta, da taimakon Hajjo A|shalle ta iya abinci da wasu gyaran da ya kamata ace mace ta iya. Haka suke zaman su Cikln aminci da yarda da juna..
Yaya kana ganin karime baza ta bamu matsala ba? Musbahu yace Rabiu ni ba raggon maza bane, na isa da gidana, Kuma bawai zan auri Aisha bane don naci mutuncin karime ko sbd bata haihuwa ko wani abu baneba, aa zan auri Aishalle ne don ina matuqar sonta kuma dan raya sunnan manzo. Rabiu yace toh shkn Allah shi sa a dace.. Hajjo ce tama Aishalle bayani,tace Maman Hassan ba wai zan muku musu bane, amma wallahi ina tsoron matarshi, hajjo itama cikin damuwa tace karki damu kowa da halinsa zai zauna. Allah dai yasa mu dace.. Yau ana sallahn juma’a aka daura auren Musbahu Zailani da Aishalle, bisa sadakin silallan zinari 5, Hajjo ta gyara Aishalle, da daddare Musbahu ya shigo Sashen qaninshi yace ma Hajjo ta shigo da Aishalle sashen karime zai hada su, sai da gaban hajjo ya fadi kafin tace toh Yaya gamu nan zuwa. Wuce wa yayi sashen karime, tana xaune tana shan rake ko Isha’i ba ‘ayi ba. Mallam sannu da zuwa, tace yauwa karime rake ake sha. e wlh zaqin tsiya kana sha? Yace aa, yo daga ina kake haka sai uban qamshi kake zubawa, rabon dana ganka tun safe? Kafin yace komai su hajjo suka shigo da sallama ya amsa, karime tace wai meye? Da daddaren ma ba za a barka ka zanta da mijinka ba? Hajjo dai bata ce komi ba, Aishalle kuwa gabanta ya tsanta bugu, hajjo wace ce wannan sai noqe noqe take kamar munafuka? Musbahu yace Karime, tace na,am mallam, zaki tuna fuskar nan? Hajjo bude mata fuska, Hajjo ta bude mata fuska, karime tayi zumbur ta miqe, oh Allah Musbahu wai kai ina kake samo aljanai masu tsigar mayu ne Haka kwanaki ka kawo wata mayyar, ai gwara wanchan akan wannan! Wannan ai kynta ya shahara, dan Allah kiyi haquri baiwar Allah, ai kuma Allah ya hallice ku Duk da bansan me mijin nawa ya miki ba amma kiyi haquri, taba musbahu daria sai daya dan dara, yace Karime wannan ce na kawo miki ita kwanaki sunanta Aishalle, kuma a yau ta zama matata saboda na aureta, Karime ta daka tsalle ta chakumo wuyanshi, Ni zaka munafurta ni zaka cima amana? ldan ka isa Allah ya tsinen, babban balaeen chan, saita sakeshl ta wawuro sandan rake ta maula wa hajjo a baya, hajjo ‘ta gantsare baya, tayo kan Aishalle, yau sai na daddaki kashin babba buraubaki, Cikin zafin nama musbahu ya damqota ya jefar ya nuna ta da yatsa, karime ki kiyayeni karime ki fita idona, ta yo kanshi ta chakume shi na rantse yau sai ka sakeni idan baka sake niba ba ka haifu ba, wlh sai ka saken, yace karime na sake ki saki daya, ihu ta sake da qarfi tace na shiga uku, daman basona yake ba? Shege tsinanne laananne, ta figi zanenta ta bar gidan da gudu k0 tsoron dare batayi.
Ya kalli Hajjo yace Hajara kiyi haquri ni na jamaki k0? Tace bakomai Yaya. yace nagode kije ki wanke fuskanki kar ki sa su hassan damuwa tace to yaya nagode saida safe, Aishalle Allah ya tashe mu lafiya. Bayan Wata Biyar
Zama suke cikin so da qaunarjuna, abu na Allah Aisha na dauke da cikin Wata 4, Hajjo na kula da ita sosai, su Hassan na sonta Goggo Amarya suke ce mata, Hafiz na ce mata Goggo Ama sbd shi yana da tsamin baki, haka kuwa kowa kece mata Goggo Ama, su Mudassir kullum suna gidansu karime suna kai mata rahoton abun dake wakana cikin gidan, ta dau alwashin raba Aishalle da gidan nan amma bokanta ya shaida mata Alshalle ba zata taba barin gidan nan ba, kuma ya hango yaranta da jikokinta cikin wannan gidan, kuma duk wanda Musbahu zai aura a bayan Aishalle yake don sonta a cikinjininshi yake, Hankalinta ya tashi ainun, babban baqin cikinta be wuce yanda Musbahu yayi watsi da ita, a tunanin ta zaizo yace a maida aurensu ba amma shiru, gashi uwarta ta rasu, abinci ma gagaranta yakeyi, haka ta samu babanta tana kuka tace sai dai yaje yaba Musbahu haquri a maidota, yace shifa ba inda zaije, ba zata maidashi tsohon banza ba Nan ta fashe da kuka tana tirje tirje, don yaga uwarta ta rasu shisa be damu da ita ba, yafi son hajjo, duk da Hajjon ba diyarsa bace, tsakanin da da mahaifi sai Allah, zuciyarsa ta karaya, yace zai ma Musbahu magana. Da kanshi yaje kasuwa gurin Musbahu, Musbahu yace haba baba ai da ka aika an kirani yace babu komi, nan ya gaya mai abunda ke tafe dashi, ya danyi jimm baba yace idan baka so dole ta haqura bawai ina maka dole bane, yace lahh bakomi wlh ni ko ynx a shirye nake a maida auren mu. Haka kuwa akayi ba a jima ba aka maida auren, bayan ya samu Aishalle ya mata bayani ta nuna mai bakomi, amma ta shige daki taci kukanta hajjo na lallashi,. Daga bangare wani bangaren aka fidda ma Karime daki ciki da parlo, rananr da karime ta dawo su Mudassir dadi kamar ya kashe su uwar dakinsu ta dawo, nan ta rada musu wani abu kunne suka hau shewa…
A yau Aishalle ta suntulo danta kyakyawa me kama da babanshi da taimakon hajjo . ko kallo basu ishe karime ba. amma hauka ne kadai batayi ba, takaicinta ya akayi Ama ta riga ta haihuwa kuma namiji? Musbahu baki har wuya yau ga gudanjininshi. Ranan suna da yaci suna Aliyu. A rannan ne karime ta tashi wani iri wai ita bata san qanshin ragon da ake soyawa, maqota basu bi kanta ba don sun san halinta sai da suka ga tana amai suka temaka mata, aka kira ummu aneesa don ta dubata, gwajin farko ta gane karime na dajuna biyu. Aifah tun lokacin karime aka fara salon iyayi da kankamba, bata san wannan bata san wanchan. Har Allah ya sauketa lafiya. amma tayi baqin cikin ganin mace ta haifa, Musbahu ya nuna farincikin shi ranar suna diya taci suna AbIda. To daga nan Aishalle da karime suka fara gasan haihuwa, duk shekara sai sun haihu, sai da Karime tayi mata 2 Sadiya da Zainab kafin tayi namiji daya Usman, ita kuwa Aishalle bayan Aliyu ta haifi Umar da Abubuakar sai mace daya Maryam tun daga maryam Basu sake haihuwa ba. Maryam din Ama nada shekara 7 Hajjo ta qara halfan Yan biyu mata Hassana da Hussaina, Aishalle kam kamar ita aka ma haihuwan nan murna kamar mene, tace wlh Yaya Hajjo ke yer baiwa ce, daga yan uku sai yan biyu dama ni, tace kema Allah xai baki.,..
Hannun hajjo saqale da nashi, kuka take tayi jin abun dake fita daga bakin mijinta, Hajjo naso na zame miki Gata har qarshen rayuwarki, amma da alamu kwanana yana gab da qarewa, tace wai rabiu me kake cewa haka? Cuta ba mutuwa bacefa? Hajjo kenan sati biyu kenan ina fama da ciwon cikin nan, nidai dan Allah kayi shiru, Hassan ne da qanenshi suka shigo dakin ganin mahaifansu na kuka yasa suma suka fara kuka, Da qyar rabiu yace hassan Allah muku Albarka, jeka kira mun babanka, da gudu ya fita sai gashiya dawo da Musbahu da Aishalle a rude, Asha Rabiu ciwon ne haka? Sannu yace yaya ka yafe man idan na taba bata maka, Yaya ga Amanar iyalai na, na san zaka kula mun dasu, Kafin Musbahu
yace wani abu rabiu ya cika yace ga garin ku nan, Tashin hankalI.

Tofa da alamun karime hajjo da Aishalle za,a zama kishiyoyi kenan?

About Ismail

Check Also

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 9

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 9 Zayyad da Rumaisa zaune a parlorn tsoho, Yazayyad na basu …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *