RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 2

Advertisements

_____

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 2 Sai kuma ta fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asin’ ba, dan kaga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi aure wazai na kai min talla? Ko ni kakeso na fota tallan da kaina? Takaici ya hana mallam magana sai kawai ya fice ya bardakin… 
Tadi su sukeyi irin ta masoya, Hajjo ta shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan karime ta hada gabas da yamma, tace wato Rabiu ba xaijanye ba koh? Me zaayi da wanda ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata rai yace haba karime me yasa kike haka neh? Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban, Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola ce, kuma data rasu, shine babana ya riqeta, ni kadai mahaifana suka haifa, Musbahu yace najih dai’ be kamata kina nuna qyamarki gareta a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiki kyau, wani mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe zasuje Chadi don sanarda kawunninsu auren su, ta mai Allah ya kiyaye 
Ko daSu Musbahu suka isa qasar Chadi suka tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi dasu Mudassir da labaran Nigeria, yara ne basu fi shekaru 10 basu da kowa yanzu sai mu, yace Yaya duk yanda kace hakan zaayi… 
Haka kuwa akayi Washe gari suka kama hanyar Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo. Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru, Musbahu yace Karime ta riqe su, firtaqi ita bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo su, ta amshe su hannu bibiyu. Bayan Shekara daya. 
Adaddafe ta iya zuwa ta kai kanta bangaren Karime, kuka takeyi tana kiran Yaya ki taimakeni, bayana zai balle, Karime dake zaune tana tamnar cingam ko kallo bata isheta ba, nan Hajjo ta xube tana murqususu, amma karime bata ce mata ci kanki ba, Tunda Hajjo ta samu ciki Karime taji wani tsanarta ya shigeta,jin haushinta daya ya zaayi hajjo ta samu ciki? lta bata samu ba? Ta sha kai ma cikin hari tun yana qarami amma bata samu nasara ba, Kishinta takeyi Sai kace kishiyoyi, ta dinga juyi a qasa amma ko kallo bata samu ba daga karime, maqociyarsu ce Umm Afeef ta shigo gidan da Sallama, ganin hajjo a qasa yasa ta qarasa gunta tana sallami, me ya sameki haka? Ko naqudarce? Sannu, ta kalli karime tace kedai bakiji dadin rayuwarki ba, wai shin miji daya kuke aure da zaki nuna mata wannan halin ko in kula? Karime tace Maman Afeef wlh ki fita idona zamu kwashi yan kallo dake. Cikin wahalaliyar muryan hajjo tace umm afeef marata, bayana, ta fita da gudu tana fadin ina zuwa Bata tsaya k0 ina ba sai gidan Unguwan zoman garin Ummu Anisa, tace ki temaka haihuwa tazo ma hajjo, ai ko da gudu suka fito suka nufa gidan, har ynx hajjo na qasa tana mutsu mutsu, maman Anisa tace kamata mukaita ciki, Karime tace Waaa? Ai wlh ba za,a shiha da najasa dakina ba, ummu Afeefta buga tsaki tace in fitsari banza ne, kaza ma tayi, Ummu anisa tace rabu da marartausayin nan kamata mu kaita bangarenta, nan suka bar karime na ta zazaga masifa. Suna ko shiga daki Hajjo tayi wani yunkuri ta santalo danta, Kai Masha. Maman afeef bata rufe baki ba sai ga wani dan ya fito, cikin murna tace yan biyu-sai ga wani dan ya kuma fitowa, Guda maman afeefta sake  ummu aneesa sai sannu take ma hajjo, kafin aka gyara hajjo. Da yaranta maza kyawawa kamar babansu. 
Ummu Afeef ta fita waje da sauri taga karime na labe tana leqe, ummu afeef tayi shewa tace samun Yan uku sai ‘yar baiwa, Karime ta dafe qirji tace na shiga uku, Yan uku? Maman afeef na fita ta samu almajiri kayi maza kaje kasuwa kace ma malam Rabiu hajjo ta haihu ta samu yan uku. Da gudu almajiri ya ruga. 
Karime kuwa kamar tayi hauka, sai sambatu take tayi, Hajjo ta haihu? Ta samu yan uku? Kuma maza? Jar ubanchan, wlh bazata sabu ba. Da balaee nima sai na haihu cikin watan nan hka ta dinga haukanta… 
Da gudu Rabiu da Musbahu suka shigo gidan, kallo daya zaka musu zaka san suna dauke da tsantsar farin ciki, Hajjo har tayi wanka tayi kyau abunta, Rabiu ya kwaso yayan ya rungume, ya miqa ma yayanshi, Musbahu ya amshesu tare da musu addua, Allah shi rayaku.. Nan ummu aneesa tace a bar hajjo ta samu bacci, Yan gidan kuwa Labaran da mudassiru sai murna suke tayi Nene Hajjo ta haihu. 
Musbahu ya shiga cikin Gidanshijiki na rawa yake ta kwalawa Karime kira yana Karime karime, Hajjo ta haihu har daki ya bita yana gaya mata, Yan uku ta samu, kuma duka maza, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, shi be ma lura da yanayinta ba, yace wai baki san hajjo ta haihu bane ba? Cikin tsawa da masifa tace Tou Sai Me? Ya dan kallota, karime lafiya? Ta miqe tace ita ta kawo hakan, ta sabi zaninta ta bar gidan, shiko Musbahu tunani yake me yayi zafi haka? 
“’Ranan suna Yara sukaci suna Hassan Hussaini da Gambo, Yaran nan abun so ne gurin
Jamaa, har yau Karime bata leqo ta gansu ba, Rabiu wani kula ta musamman yake ba matarshi, Hajjo na shan wahaln yan ukun nan, ba wanda ke tayata da rainonsu, sai Mudassiru da Labaran, ganin hakan ne Karime ta sami Rabiu da kuka wai ita dai 
a kawo mata mudassir da labaran, ita tana cikin kadaici, waye waye, Rabiu bece komi ba yace su koma gun karimen, Musbahu ya so tambayar ba aSi kawai sai ya share. Karime ta cigaba da riqonsu don kawai kar Hajjo ta moresu, a hankali a hankali ta dinga chusa masu tsanar Hajjo. 
Abu na Allah cikin Shekaru yaran hajjo 6 har da yanuku kasancewar duk shekara take haihuwa wani abun Allah yaranta duka maxa, Bayan Yan uku ta samu Ahmad da Ibrahim, sai auta
 Hafiz haryau Karime ko batan wata ba tataba yi ba, an bi Malaman anbi yan tsibbu da bokaye amma a banza. Musbahu na san Yaran Yanuwansa sosai,ya sa yan uku da Amad makaranta Islamiya.. 
A bakin kogi me kallon boader ya hango yarinya na kuka gashin kanta ya rufe mata fuskarta da sauri ya qarasa yace ke me akayi maki? Dago kanta tayi Ya Salam Aljana ce ko mutun? Cikin hausarta dabe fita tace wlh mutun ce ni, ya sunanki? Sunana Aishalle daga ina kike? Masu kamen bayi ne suka kamo mu shine ni na gudo nayo nan, ke er wace qasa ce? Tace kamaru, yace ina iyayenki? Ta matse qwallah tace sun rasu da dadewa, yace ta shi na siya miki abinci, na saki kwalekwalen da zai kaiki har kamaru, da sauri ta girgiza mai kai,Tace wlh ba zanje ba, banda kowa a chan, bauta mukeyi a gidan sarki, kuma na gudu da na koma zaa fille mun kai. Ka barni a nan kawai, Musbahu ya tausaya mata qwarai, yace zakije gidana? Da sauri ta daga mai kai, yace toh biyoni, ba gaddama ta bishi, sunyi tafiya kadan kafin suka isa gida, tun daga soro yake qwala ma karime kira, ta fito, kai mallam ya kake kwala man kira kamar wani watan ramadana-turus ta tsaya ganin Alajana da gudu tayi daki ta na fadin bayanka Musbahu bayanka Aljana, yayi daria yace keee mutum ce, ta dan leqo tace daga ina? Ya kwashe komai ya gaya mata, shine nace tazo ta xauna a gidan nan, Ashar ta saki, Wannan Alajanar zata zauna dani? Wannan Mayyar? A gidan nan? Wlh ba dai gidan nan ba, Musbahu ya fusata yace Gidan ki ne ko nawa? Toh sai ki hanata xama gidan nan idan kin isa.. Zuciya taci karime ta daka tsalle ta damqo gashin Aishalle 

Hmm

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Advertisements _____ Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *