[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 1Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu, yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti? Bilqeesu tace Alfah. inda sabo ai yaci ace mun saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu Tsoho mu gaya mishi, lslahulkhair dake gefen su bata tanka musu ba, cikin damuwa Fadila tace Mallam Audi don Allah ka qara mata horn, kam Mallam Audi ya qara Horn suka hangota tana sauri cikin yanayinta na sanyi ta fada cikin mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja mota ya bar haraban wakeken gidan da ke qunshe da sashe sashe..
Kusa da lslahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce riqe da keypoint tana karatu, Tace hey Sisters, sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta, cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da zamu dainajiran Maysah, kin cika nawa, tace wlh banga safata bane ta kalli lslah tace yadai sisi? Murmushi ta mata tace lafiya u will never change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe tare duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki tare da hararanta, bata damu ba don idan da sabo ta saba. Mazan dake zaune su hudu a chan baya tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na’imah da bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din, sa’idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau suke fara NECO exams…
Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu rubutan Jarabbawar qarshe ta makarantar Sakwandire na Top Onwards Science College Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana… Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon dake zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne, kadan ya rage ya cika shekaru chasa’in cif a duniya,tsufansa me kyau ne, gyara zaman gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune, amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace ja’ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi, duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun kasa magana, ku fada matsalarku a magance maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu tace daman Tsoho qara muka kawo ma, Haneefa tayi charaftace tsoho mu dai mun gaji, wato kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun farajarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba wata rana sai an hana mu zana jarabawar saboda latti, Mu gaskia da sake, a san yadda za,ayi damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri, kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma maganar raba tafiya duk bata taso ba,tun lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu makaranta kunga lokaci guda ba za a bar wannan aqeidar ba, Hmm ai daman munsan baka san laifinta kafi sonta cikin jikoki, da sauri yace haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku, ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni kunji? Sukayi godia suka mai Sallama.
Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA’U Meyasa kike sa ‘yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da fuska tace, kayi haquri lnsha Allah zan daina, yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da bansamu latti ba, yace don Allah ki daina kinji? Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta miqe ta fita,a ranta tace InshaAllah sai na riga kowa shirin makaranta jibi, ba za a qarajirana ba saidai najira Tayi Sasan Matan tsoho domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa) a dakin, suna ganinta suka bata fuska, ta gaida su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho na kiranki, ba tajira tace komai ba, ta Fice don bata sonjin zagin da za a jefi kakar ta dashi Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai‘ Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho.
Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da
GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne, me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna Rabi‘u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan Shuwa Arab, Shekara 2 kachal yaba qaninshi. iyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin Maiduguri inda suke sana’ar sirfani da dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu ilimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka zama matasan Attajirai.
A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata yarinya Karime dake kawo musu tallan fura fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin qaninshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya wannan yarinyan ta man, bansan k0 babanta ze ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta daman gwara kayi auren kaima, ko da baban ya dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa, Mallam yayi shiru yace banqi taku ba, amma Hajjo bata da kowa sai Allah sai ni, Hajjo tasha wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati 2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan su…
Da daddare Mallam ke gayama maman karime yadda sukayi da meson Karime, murna fal ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take Annurin fuskarta ya dauje dIf, tace bangane ba,yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na bashi ita, maman karime ta daka tsalle tare da riqe qugu tace Kam babban balaeen chan….

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]