QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 2

QADDARAR SUMAYYAH

CHAPTER 2
Shi din ma a yau kallo daya yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin farinciki da walwalarta,sosai fuska da jikinta baki daya suka nuna gazawa da kasawarta,gabansa ya fadi saboda wani tunani daya darsu cikin zuciyarsa,a hankali qirjinsa ya dinga bugawa.
Yarinya ce amma a dabi‘unta sam ba zaka kirata haka ba,tana da halin manya da dattako da sanin ya kamata,sai tayi qoqarin cilla dukwata damuwarta gefe guda ‘ta tarbeshi yadda suka saba,a yau din ya sake sosai har ma yana tsokanarta,amma ta nan fannin sai ta samu kanta da gaza amsa masa,duk da murmushin yaqen da take ta qoqarin binsa da shi,wani abu ne cunkushe a qirjinta. Tana ta kai kawon shirya masa abinci yana ta binta da kallo,babu shakka iya kula da miji ba wai mace mai karatun boko kawai ta iya ba,shi ya yadda da wannan,komai na sumayya a nutse yake,ba zaka taba tunanin bata taba shiga aji ba face ajinsa,shi ya koya mata yadda zata yi karatu da rubutu,rainonsa ce shi ya raini abarsa,ko motsi sumayya tayi yasan me yake nufi,hakan ya sanya a yanzu kallon da yake binta da shi karantarta yake,duk wani motsi nata na gaya masa akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta. Hannunsa ya sanya ya ruqota lokacin da take duqe tana shirin zuba mishi abinci,sai ta dago idonta take idanunsu suka gamu,ko baiyi magana ba tasan meke yawo cikin idanunsa,sai ta narke qwalla ta cika idanunta,janyota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta da dukka hannayensa,kuka ne ya qwace mata ba tare data shiryawa hakan ba,baice mata komai ba har sai da tayi mai isana,ya fuskanci zuciyarta ta soma sanyi sannan yace da ita cikin murya mai sanyi “Me ya faru my sumy,me ya sameki?” Cikin muryar kuka maganar na kakkatse mata saboda shishshiqar kukan dake kawo wa muryarta caffa
“Yaa mukhtar,yanzu saboda zakayi aure kake boyemin?,me yasa baka gayan ba ya mukhtar saidai na tsincin zancan a waje?” Shiru yayi wuta ta dauke masa lokaci guda,zancan da yake ta faman boye mata kenan,shi kansa cikin awanni kadan maganar ta dagulamasa dukka wata nutsuwa tasa,ina ga sumayyar tasa,ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Sumayya,bana son ki tada hankalinki kan wannan maganar,ni mukhtar a yanzu bana sha’awar qara wani aure,ke daya sumayya kin isheni,kuma babu wanda ya isa ya sani dole tunda ni zan zauna da ita”. ‘
Da sauri ta daga kanta daga qirjinsa tana dubansa tana kada kanta.
Ko bajima ko ba dade dole ya mukhtar sai ka qara aure,koda baka da muradi ‘yan uwanka zasu tursasa ka,tunda na kasa samar musu da abinda suke da buqata,na kasa haihuwa ….. Ta qarasa maganar kuka na sake qwace mata.
Da sauri ya sanya hannunshi ya rufe bakinta.
“Subhanallah,sumayya!,ina ilimin addininki ya tafi?,Allah kadai ke bada haihuwa kin sani na sani kowa ma ya sani saidai kuwa ya take saninsa,to saboda haka babu wani sake auren da zanyi,mu barwa Allah lamuranshi har zuwa lokacin da yaga damar bamu”. Ta lura da gaske mukhtar yake ba zaya karbi auren da aka bashi ba,wanda hakan dai dai yake ya debo baqin fenti ya yaba mata a idanun ‘yan uwanshi,a yanzun ma tana rakawa ne kawai da yanayin dangantaka da alaqarsu,ba zata iya tuna yaushe rabon da taga wani da yajibanceshi a gidansu da zummar ziyara ba,kawaici kara da ne kawai yasa bata dauki lamarin a bakin komai ba,ta riga ta sani ta kuma yi imani da shi shine dukkan tsanani yana tare da sauqi. Ji take a jikinta wannan ce kadai dama ta qarshe a gareta da zata dawo da kyakkyawar alaqar da ada can baya take tsakaninsu
” ya mukhtar”ta kira sunansa,bata tsumayijin amsarsa ba ta dora “Don Allah da annabinsa kada ka yimin haka,kada kace ba zaka karbi auren nan ba”
“Sumayya,bana so kuma bazan karba ba,bana da buqatar qarin aure a yanzu haka,domin babu abinda na nema na rasa ga mata ta” ya fadi yana dubanta kansa tsaye,rasa me zata ce masa tayi saboda yadda taga ya tunzura kamar ta sokeshi da allura.
Qarar wayarsa ce ta sanyashi mai da idanunsa kan wayar,har ta qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba,tana katsewa wani kiran ya sake shigowa,sai da ta kusa katsewa sannan ya daga
“Hello” aka fada daga can bangaren,ko bata ga sunan mai kiran ba tasan yaya yahanasu ce,tana jiyo muryarta ta tashi kasancewar tana jikinsa
“Assalamu alaikum”mukhtar ya fada ” sai yanzu kaga damar daga kiran nawa hamshaqi?”ta fada cikin fada ” ‘ah ha haka bane….” Ta katseshi da sauri ta hanyarfadin Ba wannan nake so naji daga gareka,munyi maganar yarinyar nan fa’iza,naji shiru baka ce komai ba” ransa ya sake baci fiye da dazu,har yanayin fuskarsa ya sake munana fiye da dazun. “Yaaya,kiyi haquri,inaga gaskiya gwara kawai abar maganar nan,kada in zama silar bata zumuncinku keda qawarki,domin a gaskiya bani da sha’awar qara aure a yanzu haka,mata ta babu abinda na nema daga gareta na rasa”.
” iyeeee,ni muntari kake gayawa haka,kai kuwa ka rasa komai daga matarka,shekararku nawa tare,ko dan yatsa ta taba haifa maka?,hala ma haka sumayyan tace ka fadamin kenan?”.
“Babu ruwanta yaya,hasalima bata san da zancan ba banda yanzu,nine kawai bani da ra’ayi”.
” muntari ka bini a hankali,idan nayi maka baki fa sai ya kamaka wallahi kai ka sani,aure kuma babu fashi wallahil azim,mu zuba ni da kai da ita kanta qaramar alhakin sumayyar muga wanda zai kai qasa,banza shashasha kawai solobiyo,yarinyar da a haihuwar tumaki ka haifeta zaka tsaya tana juyaka kana tsoronta”qit ta kashe wayar daga fadin hakan. Tuni sumayyan tayi nisa a duniyar kuka,so tayi ma ya saketa daga rikon ta zauna qasa ko ta kwanta ko zata fijin dadin yin kukanta son ranta amma yaqi sakin nata.
Cikin jarumta ta hadiye kukan nata ta dubeshi “Ya mukhtar,wallahi kaji nima na rantse qarin aure gareka babu fashi matuqar kana
qaunata da gaskiya kamar yadda ka fada,wannan kawai ya isheka ishara ka gane kashin kaji kake shirin sake yabamin bayan wanda na goga a baya,saboda haka ya zama dole ka yiwa yaayaa biyayya tunda mazaunin mahaifiya take a gareka” tana gama fadar haka ta miqe dagajikinsa ta shige dakin gadonta. Cikin kwanakin gaba daya ta daina yi da shi,ta tsame hannu daga sabgarsa ba wai don haka taso ba,tayi amanna auren da zaiyi ne kadai zai sama mata salama cikin rayuwar aurenta,ta tabbata ba zasu barta ba koba dade ko bajima tunda bata haihu ba.
Kwanaki uku kenan zaman babu dadi,saidai ta tara yaranta suyita sabgarsu amma ba ruwanta da shi. 
Ranar cikon ta hudun bayan ya dawo daga kasuwa,ya tadda kayan abincinsa ta jera kamar yadda ta saba,tayi shigewarta uwardakanta babu ita ba alamarta,toilet ya shiga yayi wanka duka tana jinsa bata ko motsa ba balle ta fito,ya gama ya kintsa cikin jallabiya,bai k0 kalli abincin ba ya shiga uwar dakan ta,nan ya cimmata saman gado zaunejingine da fuskar gadon,hannunta dauke da qaramin littafin alma’asuraat,ba taka  bace ‘yargado ce,domin gidansu gidan malamai ne akwai ilimin addini tsantsa wanda hakan ya sanya yara matan gidan basa karatun boko sam sam. 
Bata dubeshi ba har ya hauro gadon ya sanya hannu ya karbe littafin ya ajjiye gefe 
guda,ganin tana shirin yi masa bore ya sanyashi saka qarfinsa ya riqeta gam,cikin salo ya soma rarrashinta da neman sulhu daga gareta,cike da tuburewa ta dubeshi 
“Karbar auren nan ne kadai zaya samo maka kaina yaa mukhatar,idan ba haka ba zaka iya tafiyarka muci gaba da zama a haka,ya fiye min akan danginka su dinga ganin na mallakeka,kullum ban da kwanciyar hankali ko nutsuwa a cikinsu“ ta qarashe maganar zuciyarta na sake yin rauni,dama can a raunane take,dakiya da haquri yasa take iya sabgoginta kamar bata da damuwa,tun asali mutumce mai zurfin ciki,bugu da qaari zamanta da mukhtar babu wani abun turda yake mata don haka bata iya fadar matsala ko kai qara ba. ‘ Ya kusan kwashe minti talatin cikin nazari da dogon tunani,harta farajan abun rufa zata yi kwanciyarta tana tsammanin yana kan batunsa,ya waiwaya cikin sanyin jiki ya dubeta “Sumayya,ina sonki kin riga da kin sani,babu kuma abinda na nema na rasa daga garekin,ban dauki rashin haibuwarki a wata matsala ba,saboda na riga da na sani cewa bawa bai isa ya tsarama kansa ‘KUNDIN QADDARARSA“ ba,tunda kina gani shine buqatarki kuma shine kwanciyar hakalinki na amince”. 
Duk da hakan take buqata saboda tasan shine samun salamarta daga hannunsu yaa yahanasu amma sai da wata ‘yar banzar faduwar gaba ta ziyarceta,ta hadiye wani abu sannan tace 
” shikenan,amma ya kamata gobe kafin ka dawo gida kaje ka sanar da yaayaa yahanasu amincewarka,so nake ta daina zargi ko jin haushina“kallonta ya waiwaya yayi,saboda a yadda tayi maganar shi zai nuna maka akwai raguwar zallar quruciya a tattare da ita,bai son zuwan saboda haka ya kada kai yace “Bazan je ba saidai idan zaki shirya muje tare”. 
Ido ta dan zaro don har ga Allah batasan ya haduwarsu zata kasance da ita ba,amma sai dabara ta fado mata,kasancewar babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan yaya yahanasun bazai wuce naira talatin ba kudin mota 
” eh zani,amma saidai ka ajjiiyeni a gida,idan ka dawo kazo ka daukeni mu tafi”baice komai ba ya tire bargon ya shige ciki tare da janyota jikinsa,da sauri ta dubeshi “Abinci fa kaci ne?” Kai ya girgiza mata “Na qoshi” 
“Amma yaa mukhtar bai ……. “Shshshshsh” yace da ita sai tayi shirun tare da komawa ta lafe ajikinsa,ta sani tunda yace bzaici din ba bazai ci ba,ita kuma bata saba musu da shi ba saboda girman da yake da shi a idanunta. ‘ 
Cikin dare ta kasa barci,itadai bata san kishi ba tunda bata taba soyayya ba saboda shekarunta sha biyu a sanda aka aurar da ita,tadai auri yaya mukhatar,kuma tanaji a zuciyarta tana sonsa bata so wani abu ya rabeshi,amma tana jin babu dadi duk sanda ta tuna zai kawo wata gidan ta zauna tare da su,ya dinga kulata kamaryadda yake kulata,da tunanin yaqi qare mata sai ta sauko daga saman gadon,ta sadada ta fita ta daura alwala ta kabbara sallah. 
Kusan wannan tarbiyyar gidansu ce tun kafin tayi aure,mamarsu tasha gaya musu duk sanda suka kasa barci da kwanciyar banza suyita zaman tunani gwara suyi salla,zasu samu lada kuma daga bisani baccin yazo,a lokacin dariya sumayya take qyalqyalewa da shi saboda tsantsar quruciya,takan ce “Nikuwa mama mai zai hanani bacci?,bacci fa dadi ne da shi wallahi mama,bakiga da qyar nake iya tashi nayi sallar asuba ba,wataran ma sai kin sanya tsumagiya kin dakeni?” Murmushi kawai uwar takeyi kana tace “Sumayya kenan quruciya mai dadi ko” sai ta sake yin dariya tace 
“Hmmm,mama kenan,nikam babu abinda zai hanani bacci na,ga katifata mai laushi,ga iskar fanka”. 
Washegari tare suka tashi,shi ya dinga taimakata da ayyukan gidan kamaryadda suka saba yi wadansu lokuta,sunayi yana tsokanarta saboda ya fuskanci tamkar bata da walwala,hatta sallarjiya a idanunsa tayi kasancewar shima bai samu isasshen bacci ba,sai goma ya f’lta yana gaya mata ta shirya bayan sallar magariba idan ya dawo zasu fita. Qarfe shida ta kammala girkinta ta tsaftace gidan,ta hada kan yaranta ta zuba musu abinci cikin kwano daya,sannan ta kwashe na mai gidan ta kai falo tajera sannan ta shiga wanka tana gaya musu saura ta jiyo su suna fada,duk wanda yayi fada ba ruwanta da shi. 
Tsaf ta shirya cikin wami swiss lace mai matsakaicin kudi cikin kayan sallarta yake,sanyawarta daya wannan ne na biyu,mukhtar akwai qoqari da zuciyar yiwa iyali,sosai yayi mata kyau,ya sake fidda zallar quruciyarta,tana cikin fesa turare ta jiyo yaran na yi masa sannu da zuwa,bai shigo yau da baburdin nashi ba saboda zasu sake fita. 
Ta fito sanda yake raba musu alewa suna karba suna godiya kana suka yi mata sallama suka fice,haka ta koya musu,da ya dawo ko bata fada ba zasuyi mata sai gobe su tafl saidai 
idan ita ta tsaidasu,idanunsa a kanta ya bude mata hannayensa ta taka a hankali cikin kunya ta shige ciki ya kulleta gam cikin qirjinsa yana fadin 
” kinyi kyau my sumy ta”siririyar dariya ta saki cike da jin dadin yadda yake yaba kwalliyarta. 
Wanka ya shiga yayi a gurguje saboda qaratowar lokacin sallah magariba,y hada da alwalarsa ya fice,bayan ya dawo ya shirya cikin shadda ruwan bula mai turuwa (dark blue)wanda yayi shige da lace din jikinta,dariya ta dinga ganin yadda yake waqar(munyi anko da anko)irin ta yara. 
Gidan yaya yahanasu taga sun nufa,bugawa qirjinta ya dinga yi,bata so ta masa magana yaga kamar tana qin ‘yan uwansa,tunda duk tsiya naka naka ne,sai da ya faka baburdinsa qofar gidan sannan yace da ita 
“ldan mun gama da nan gidan mama zamuje ki gaidasu” hakan ne ya dan sake sa mata nutsuwa,”to”kawai tace da shi. 
Yana gaba tana biye da shi kamar wadda za’a kama,a tsakar gida suka ci karo da yaron yaya yahanasu wanda bazai wuce shekara goma sha uku ba,ya gaida mukhtar ya amsa yana ce masa 
“Jeka qofar gida ka kulamin da machine dina kafin na fito” “To kawu” ya fada yana ajjiye modar hannunsa saman randa ya fice. 
Suna shirin shiga rumfarta tana daga labulen dakin “Au sai yau kaga damar zuwa kenan …… shashashan yaro ana maka gata kana noqewa” ta fada tana sakin labulen tajuya zuwa ciki. 
Bata lura tare suke ba sai da suka shiga ciki suka zauna,sumayya ta gaisheta ta amsa sama sama,ganin idonta sam bai hana yaya yahanasu yin duk maganganunta ba,ita dai kam kanta ta sunkuyar,daga bisani ta miqe ta basu guri jin musu nason barkewa tsakanin mukhtar da yaya yahanasu kan lissafin abinda suke da buqatar ya bada,kama daga kudin aure kudin zance lefe har zuwa sadaki,yace zaya bada kudin aure da na sadaki amma shikam bazaya iya yin wani lefe ba,kasuwa babu ciniki,nan ta barsu batasan yanda suka kaya ba yadai fito yace ta tashi su tafi 
K0 sallamar da take wa yaya yahanasun bata tanka mata ba har suke wuce,suna kan hanya 
babu wanda yace da dan uwansa komai har suka qarasa gidansu. 
Ciki ya shiga suka gaisa da maman nata kasancewar abba malam mahaifinsu kamar yadda suke ce masa baya nan,’yan qannanta duk suna tsakar gida mukhtar ya raba misu biscuite kamar yadda ya saba,ya miqe zai fice yana cewa zai zaga bayansu gun wani abokinsa idan ya dawo zai kirata su wuce tace tom. 
Gaisawa sosai sukayi da mamanta ta tambayi lafiyana data gidanta ta amsa mata da komai lafiya. 
Shiru ne ya biyo baya,tunanin abinda ya faru dazun gidan yaya yahanasu yayi nasarar wafce tunaninta ba tare da ta shirya ba,haka maman ta tadda ta,ta ajjiye kwanon dambun dataje debo mata “Lafiya dai ko sumayya” murmushin yaqe tayi ta janyo kwanon dambun tana budewa sannan tace “Mama aure yaya mukhtar zai qara” maganarta dan taba maman,tsakanin da da mahaifi tausayinta ta dingaji yana ratsata,babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da haryau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,ga yarinyar tata 
gwanar haquri da shegen zurfin ciki ce,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka 
zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta. ‘ Murmushi maman tayi sannan tace 
“Babu komai,ai namiji mijin mace hudu ne,Allah ne ya halasta masa,abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,sumayya kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta sumayya ni mahaifiyarki ban yafe miki ba”. ‘ 
Kai ta gyada” in sha Allahu mama zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba”a hankali maman ta dinga hilatarta tana kwantar mata da hankali har ta kusa cinye dambun baki daya. 


About Ismail

Check Also

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30 Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *