NAYI GUDUN GARA CHAPTER 42 THEND KARSHE

Advertisements

_____

NAYI GUDUN GARA

CHAPTER 42 THEND KARSHE

Wata biyu da haihuwar Twins custome suka saki kayansu ramadan. Fari Clki kamar me ramadan keji.
Cikin wata daya komai ya fara dawowa suka fara farfadowa. Gidan ramadan ya zamo gida na fahimtar juna da kwanciyar hankali ga matansa Dashi kansa. Ladifa twins basa bata wahala sosai! saboda an samo wata babbar mace mai kulawa dasu,
tana zaune a falon safna data tashi. Wanda a lokacin kuma yar uwan hajiyarta ta tafi.
Ramadan da ladifa soyayya suke sha kamar basu suka ajje su fuad da twins ba. Dan yanzu ramadan har so yake ya nunama ladifa kulawa, dan ya dada wanke kansa Akanta, bangaren laila ma suna zaune lafiya tana mai ladabi yanzu, kuma itama yana ji da ita yanzu, saboda tayi hankali tana yin abinda yake so tabar kuma wanda ba yaso, sai dai zafin zuciya da dan fada wannan kuma halayyar tane.
Ladifa na tsaye a falon ramadan tana fesheshi da air freshener . Tana sanye da doguwar riga yadin cotton mai kyalli Kalarja. Zip din rigar agaba aka yi shi, akai mai style saboda bawa twins abincinsu, hakan ya dada bawa dinkin wani style na daban. Kai baka ce ladifa ba ce
domin tayi kiba yanzu bacan ba hips nata ya dada fadi sosai haka kirjinta ya cika sosai! da yake nata ba masu girma bane to da sukai cikar sai sukai dede misali, dan cikar da tai daidai misali ne ita ba za a sanyata sahun masu kiba ba, kuma ba za a sanyata sawun sirara ba. Atsaka tsaki take, kai baka ce itace take shayarwa ba kuma ta haihu. Don jikinta me kyau ne an mata kitso yiri-yiri ya zubo kafadarta, sai kamshi take ya taka ya shiga dakin, kura mata ido yayi. Ta baya. Ya saki akiyar zuciya. Ya taka ya rungumeta jikinsa tsam hannuwansa dukkansu suna bisa jikinta yana kaikawo da shi wajen shafata, duk sunyi shiru domin yanayin na shigar Kowannensu.
A kunnenta ya rada mata yace “kin hadu, kina da sirrin da naso nai fatali dashi, wanda ban gano ba sai yanzu, babban kuwa shine kyawun hali da nagarta. Wanda shi ya haska min dukkanin wani sirri naki, wanda in mutum bashi da kyawun hali da nagarta komai kyawunsa ba zai tasiri ba. Baby gaki da kyan surar da Allah ya baki, kai ni na godewa rabbu. Wallahi l love you.” ‘
Numfashi tayi idonta Iumshe tana jin soyayyar mijinta na ratsajininta harzuwa jijiyarta. Sai ta sanya hannuwata ta rike hannusa, hakan yasa ya dan saketa ta juya ta fuskance shi ta ce “I love you too maigidana mijin laila.Akullum yaumin nakan godewa Allah da yajarabceni
dakai, yajarabceni da komai naka. naji dadi da mijina yaji dadin ganina a yanzu.‘ Iumshe ido yayi yace “mace ta gari ita ce a kullum mijinta ya kalleta ya kejin farincikin ciki, baby am so sorry da abubuwan daya faru baya.’ dan yatsina fuska tai tace ‘nifa nace ka daina yawan cewa nai hakuri komai lokacine fa.”
“Dole ne baby.” “Au ba zaka daina bako.” Sai yayi murmushi yace “sai an bani tukwici zan hakura.‘ Tace “tukwicin me?.’ Sai ya nuna lips dinsa, “anan na keso a bani.” “Wannan ai wasan amare ne.‘
“Au! keme cece?.”
“Ni ai uwargida ce.” “A bani na uwargidan.” Sai tai murmushi Sumarsa ta shafa ta kashe mai ido daya. Murmushi yayi ya Zauna tare dajanta ta zuwa kan cinyarsa ya shiga shakar kamshinta. Yace ‘oya help me inajira.“
Lumshe ido tai ta mai da bakinta kan nasa, nan suka rikice suka shiga duniyar masoya… Cikin yanayi mara musaltuwa da soyayyarjuna. Sun dade a yanayin. Wanda basa so koda kankanin wani abu ya katsesu.
Kwatsam! Wayar ladifa ta fara kara ta dauka, taga inna mariya ce mai kula da su twins tace mata hanan na ta kuka.Tace mata gata nan.
Yana kwance flat akan gadon yace “oh! Yanzu gudu zakiyi ki barni?.”
Lumshe ido tai ta dan saki murmushi tace ”na kula sai da na haifi twins ka koyi wata sabuwar soyayya bayan yanzu mun fara tsufa.“
Murmushi yayi yace ‘waya gaya miki soyayya na tsufa, sai dai masuyinta su tsufa, balle ke, kalleki fa har yanzu baki kai 25 ba ai kuwa yanzu aka soma. Kuma yara ba zasu hana ba.”
Sai tai mumushi tace ‘haka nake so nawan, yanzu dai na sallameka bari naje sallame su suma.” Ta fada tare fita ya bita da ido ya lumshe su.

BAYAN SHEKARA UKU

A cikin wannan shekarun nasarori da faduwa duk sun samu, farin-ciki da bakin ciki. Rayuwarsu suke cikin aminci da yardarjuna.
A bangaren sana‘a kuwa yanzu ladifa likkafa tai gaba dan yanzu tana kaiwa store ,store suna sarar curry powder din nan. Sannan a gefe daya tana sayar da atampopi da shadda su lece wanda har bude dealer take, wanda ramadan ya kuma kara musu jari sun habbaka business nasu.
Abangaren laila ma haka. Takalman da take saidawa da mayafai sun habaka wanda har abaya take sayarwa. Wanda Ga yaransu fuad da najwa duk an saka su a makaranta. da cewa su suna wajen hajiya. Sai dan shekara uku da aka sanya shi wata biyu baya. twins
ne kadai ba a sanya ba inda suke yan shekara biyu cif.
Duk kowacce da sana‘ar da take yi ta saiwa kanta mota, motar kuma da ramadan yaba su tafarko ake kai yara makamta. Sai kuma aduk lokacin nan ladifa ta koma makaranta. wanda har ta fidda rai sai gashi ramadan da kansa ya sayo mata jamb kuma Allah ya taimka taci ta samu gurbin karatu a jamia take zuwa abinta. Gashi a sa’ar da take yi takan taimakawa iyayenta. ‘Yan uwanta uwar mijinta da danginsa, da marasa k’arfi. Wanda hakan ke dada yalwata ta, domin duk abinda ka bayar shine rabonka.
Hadin kai kuwa ita da laila kamar ba kishiyoyiba. Wanda duk da jajircewar ladifa hakan ta wanzu, ita dai ladifa za ta iya cewa taga ribar hakuri, domin taga nasarori da dama, wanda sanadin biyayyarta da hakun’nta. Kau da kai, Ramadan ya zame mata jela, wanda babu boka ba malam ta mallake abinta. shi hakuri kamarjari ne idan ka zuba shi, komai dadewa ka kan dauki riba, idan kuwa kaga baka samu n’ba to hakurin naka bai yawa ba.
Ramadan ne zaune a farfajiyar bayan gidan da yamma. Ga laila agefensa tana yanka mai lemo da ayaba. gashinta yasha saloon, ta dan yafa siririn mayafi, fuskarnan radau, dan yanzu kwalliyar tata,ta koma ta masu aji sosai wanda suka san me suke. Kallonta yayi yace “oh maman najwa narka kiba kike ba ruwanki.” 
Murmushi tayi tace “ai haka hake so kiwonka ce ni.‘ 
Sai ya murmusa. Ta tura mai fruit din gabansa tace “wai ni kuwa yanzu ka daina son mata masu abubuwan ne,” ta fada tana kyalkyala dariya. kunu yasha yace ‘zaki fara ko.? Ke da kika ma yaudaren dasu.” 
Tace “Au na yaudareka koka like min kaga ‘yar duma duma.‘ 
Dariya yayi yace rabani da wannan zancen yanzu, ai k0 ganin mata nai ba ruwana, to me zan kalla bayan duk ina dasu agida.‘ Murmushin jin dadi tayi. Tace “kar dai a gane wata.”Sai yace “zancen kike so sai ta fasa dariya ta mike tana dariya ta ce mai zata shiga cikin dan duba girkinta. 
A kuma lokacin ladifa ta sauko daga samanta. Ta shiga dakin yara su twins da arif na  wasa. Inna mariya na kula da su. Ladifa tace duk abar kiriniya ku zauna ina karatun da mukai jiya oya a zo a fara ta fad’a da murmushi a saman fuskarta. Arif yace na tuna mami da yake 
yafi su twins wayo sai daya fara suma suka fara.. Suna rabbana atina fiddunya hasanatan…. Har karshe nan ladifa tace yawwa yarana saita fita. Tai wajen ramadan. 
Cikin nata salon kwalliyar mai kwantarwa arai na fitattun mata masu aji, ta zama irin wayayyu hadaddun matan nan na kalar gayu, wanda fatarsu ka kalla kasan suna jin dadi, ga kuma nutsuwa ta dada zama a dabi’arta. Da kuma ilmi. 
Karasawa tayi ramadan ya kalleta. Ya tike hannunta. Yace ”heart beat” ya fada yana kallonta, tai mai kyau sosai a ido, shi yanzu gani yake babu wacce takai ladifarsa haduwa da kyau ta ko’ina, wanda da bai fahimci qualitynta ba ba sai yanzu, gashi tayi kiba daidai misali, ita ba tai da yawa ba, kuma ba ramammiya ba, adai tsakiya take, kuma hakan sai ya kara mata kyau sosai. Dan a yanzu in tana tafiya kirjinta da hips nata na motsawa ya kanyi mamaki sosai yakance nayi gajen hakuri. Ajikinsa ta zauna tana yi mai barka da hutawa. Suna hira. 
Safna kuwa acikin shekara ukun nan ba irin taskun da bata gani ba, domin zaman zawarcin ya dameta, gashi dai tana samun mazan auren, amma wasu da gaske wasu da shashanci. Masu sonta da aure kuwa suna fara nema ake soke mata, akan ce me zakai da ita yarinyar da bata zaman aure, duk mijin data aura shanye shi suke su mallake shi ita da uwarta, ai uwarta ce ke hanata zaman aure. . 
Wannan dalilin ne ya sanya duk sai a hankali, gashi yanzu wasu daga cikin ‘yan matan gidan da sukewa dariya sunki auruwa, duk sunyi auren kuma suna zaunensu. Kullum cikin fada take da kannenta, hatta ita kanta maman wataran takan ce mata ta takurawa yaranta 
da duka, ta dame su tace tai aure mana, takance mama koma menene aike kika kashemun. Haka za suyi ta fadi in fada da ‘yar ba kunya. 
Haka dai take zaune dan kullum mafarkin komawa gidan ramadan take, ba irin wurin malaman da basuje ba, kan ramadan ya koma da ita amma abu ya faskara sai cin kudinta kawai da suke, dan tasan taji dadi agidan komai da take so tana samu lallai ta cuci kanta. Kayan kwalliya ma gagararta suke sai ta fara sana’a, annan take Samun na kashewa, a kullum sai tayi danasanin kaso auranta na farko dana biyu. 
Zaune suke suna dinner yaran kuma na wajen inna mariya suna wasa. Suna kuma kallon catoon. Laila da ladifa sunci kwalliya sosai, ramadan sai kallonsu yake yanajin dad’i aransa. Nan suka kalli ramadan dake tacin abinci dan yayi mai dadi ladifa tace ‘hmmmm kayi shiru angona.” 
Ya dago yace “nice food.” Laila ta ce a sanya mai waigi. Sukai dariya. 
Laila da tsokana tace “waini ya batun amarya ne, ya dago yace tana nan zuwa dan na gano wata fine baby.” 
Laila ta ajje cokali “wai da gaske kake?.” Yace kwarai.’ Ladifa tace “Allah yabada sa’a.‘ 
Ya kalleta yace “haka kika ce?.” 
Tace “tome zance, ta kanne mai ido daya da manyan idanuwanta.” Murmushi yayi kawai yaci gaba da cin abincinsa. 
Kallon laila yayi yace “oh habibty abarwannan fushin aina gaya muku ku kadai din nan kun isheni fa.da Nayi banji dadi ba. Kuyi min addu’ar karin arziki kawai da zama lafiya. Idan kuma kuna so ne sai na samo.“ 
Sai lokacin laila ta saki ajiyar zuciya tace wallahi na dauka da gaske kake.‘ Yace ‘maman kishi.‘ 
Hakan zaman na su yake kullum cikin kyauatatawa juna, ance harshe da hakori akan saba, to wataran suna taba kishin to kadanne, dan komai zaman Iafiyar kishiyoyi sai an gwada kishin nan wataran, idan ka ga fadan ramadan to akan yara ne ko basu kula dasu ba k0 sunyi wani abun. ‘ 
Ladifa ce ke kwalliya, bakinta yasha jambaki, sai tashin kamshi take, daga ita sai dogon wando mai lafewa a fata, da wata ‘yar riga iya saman gudunta sosai ya fito da shape dinta. Tayi tsamtsam! Da ita. Dan yau girkinta ne dan in dai girkinta ne a samanta take show dinta.Saboda kaucewa idan yaransu da kuma na kishiyarta dan samun zaman lafiya. 
Ta fito ta zauna a falonta ‘tana kallo. Dan lokacin karfe tara ne Dan yanzu ramadan na son tana mai irin shigar dan tana kyau sosai
Tun da ya shigo, ya kasa hak’uri, anan falon ya fara nuna mata wani irin salon soyayya mai riikitarwa.Dan ba karamin burgeshi tai ba. Wanda shaukinta ya debeshi. 
Sakinta yayi ya rungumeta yace “Kece farincikina wallahi, banki na dawwama ina tare dake ba. Allah ya bar mini ke ‘yar aljanna. Macce ta gari.” 
Murmushitai tace “ina godia mijina nagari Allah ya barmin kai kai da babies namu, har ma da wanda ke cikina a yanzu.” 
Murmushi sukaiwa juna.Yace “Allah yayi miki albarka duniya da lahira ya saukeki lafiya.” Tace “ameen”tare da kuma kankame shi. 


Alhamdulillah anan na kawo karshen wannan littafi mai suna nayi gudun gara mu hadu cikin wani sabon littafin naku har kullum

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 37

Advertisements _____ NAYI GUDUN GARA  CHAPTER 37 Lalla na shlga d’aklnta ta zauna ta shlga …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *