[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE


CHAPTER 9
Sanye yake cikin Getzner mai kalar kwai, dinkin yasha aiki sosai sabida dashi yaje daurin aure dazu. Ya murza hula baka na tangaran a kansa. Agogon sa na Ralph Lauren ne manne a hannunsa na hagu. Ga kuma links masu dankarin kyau. Takalman Balmain half cover ke kafansa. Yana tafe cikin nishadi zashi Rigasa inda Laila take zaune, kamshin turaren sa na OUD da Yes Saint Laurent YSL ke tashi tareda sanyin AC da aka kunna. Badman Bilal yaro da kudi abokin tafiyar manya, mai dattawa biyu iya kudinka iya shagalinka. Kura da kallabin kitse, a ganka a kyale ka, yaron maye duk garinku ana tsoron ka.
Murna fal ransa zai gwangwaje kishinsa a wajen Haske. Gashi tayi gyaran gashi da dilke itama. Sannan tayi kunshi kyanta ya kara fitowa sai walkiya takeyi.
Yana tafe yana shan cool music wakar Whitney Houston saboda yau sama sama yakejin kansa. Koda ya isa gaban gidan yayima Haske text ya isa wajen. Ankon da sukayi karamar Holland yar 5k blue kejikin ta. Dayake batada jiki dinkin pencil gown tayi sai aka saka jela ta gefe. Blue gyale na R & S tasa mai stones saita fita waje. Yanayin tafiyan ta kalar yanga ne yasa tana tafiya zakaga tana rausaya. Daga cikin motarsa wanda tint ne ya hange ta. Lashe baki yayi tareda sosa gemun sa wanda yasha taza, shi kadai yasan me ke damunsa wani tafasa zuciyar sa ke masa. Da sallama ta shiga motar tana murmushi wanda dama yanayin tane. “HASKE” ya fada chan kasan makoshin sa tareda miri miri da idanu.
“Na’am Sweet muje ko” wani azabtacen santa ya sake dawainiya dashi. Muryanta kawai ya isa ya tada mashi lissafi. Ji yake kamar ya janyota ya soma lashe ta. bai tada motar ba saida ya rike mata hannu ya soma murzawa. Wani yar taji kawai ta kwace da sauri. “Sweet muje kar dare yayi” Dariyar mugunta yayi sai yace, “Baby sarkin tsoro, I won’t hurt you. Wallahi sanki kawai ke dawainiya dani” ltama murmushi tayi batace komai ba. Anan ya tada mota inda zashi gidansu dake Marafa. Tafe suke yana tuki tana kallon kwarewarsa. Ya iya murza steering mota abin gwanin ban sha’awa. Nan ta shagala ta koma duniyar tunanin sa. Tana tunanin itama wata rana za’a kaita dakinta kamar yadda aka kai Laila yau. Sun sha kwanar layin gidansu murna fal ransa, wai yau Haske ce zata wajen sa. Abin har mamaki yakeyi wai yana santa kuma bai taba kaita dakinsa ba. Ko first love dinsa Rumaisa da kanta ma take kai kanta gidansu. Mamakin Haske yake anya ita yar zamani ce kuwa? Ya za’ayi tace baza suyi wani mu’amala ba. Halan so take a kwace mata shi. Fatan sa kawai tayi dadi kamar tantabara yar shila.
Ya lura tanada bala’in hankali kuma zaiso ace matar sace, amma idan yajita salap dole ya hakura da ita. Suna isa kofar gidansu sai yayi horn. Mai gadi ne yazo da gudu ta wajen mazaunin driver. A hankali ya saukar da glass sai ya Kalle shi.
“Ya akayi ne?” ya tambaya fuska tamau babu annuri,duk cikin masu aikin gidan mai gadin ne kawai ya isa yayi mashi magana.
“Dama Yanzu Alhaji ya shigo shine yace a kiraka idan ka dawo” ya fada a ladabce
Gaban Bilal nan ya tsinke, yaga samu yaga rashi. A sittin yayi reverse saboda bai isa ya shiga da mace gidan idan Abbansa yana nan ba. Kowa kallon mutumin arziki yake masa, mai gadi ne kawai yasan sirrin sa. Duk abinda ake yi a idon Haske, bata ce uffan ba sai da taga sun soma komawa da baya.
“Sweet wallpa pers din fah?” 
“Gobe zan kawo” Tayi masa uzuri saboda taji ance babansa yana nan kuma bazai kyautu ace an gansu tare ba kafin ayi mata muguwar fassara. Wannan kenan! 
“Hello Destiny! Dama munata jiran snacks da kajin ne tun dazu!” Laila tace ta bangare daya. Shi kuma Saif shiru yayi daga farko, saida ta sake “Hello! Hello!!! Destiny kana jina kuwa?” “Eh rabin raina, me kike cewa ne?” “Abinci za’a kawo mana” 
“Toh ai tun dazu na aiko yaro da abinci daga Yahooza da Havilla, haryanzu bai iso ba kenan?”
“Okay Destiny muna jira dan Allah” daga nan ta kashe wayan. Nan ta sanar da kawayenta ga abinci ya kusan isowa daga Havilla. Saita kunna kida a home theater. Wakar ‘Legebge’ na Mr Real ta kunna. Saita soma babbaka rawa tana juyi. Daga kasa sai taje sama. Rawar Shaku Shaku da shoki taketa watsawa. 
Tanayi tana cewa haka zata rinka rashewa da angonta na kwana bakwai. Sai wata kawarta tace “jibi yadda kika watsake kamar bake ke kuka ba dazu” “Kukan lafiya, Wallahi ba abinda nayi. Ihu kawai nake yi cikin mayafi. Sai kace zanje inda ba’a sona” daga nan saita soma wani waka, “Ahayye mutane, nifa nace inaso. Da bance inaso ba da ba’a bani shi ba” tanayi tanajuyi. Kawayenta sai dariya suke duk sun kosa a kawo abinci su kwanta.
Shiru shiru babu abinci babu dalilinsa. Ta sake kiran Saif sai yaki dauka. Ranta yayi mugun baci saita zura mayafi. Wata ta tambaya ina zata shine tace zata wajen Sameera ne ta duba idan yana chan ne. Tasan tabbas ita ta boye mashi wayan. Anan aka ce kar tayi haka babu damuwa su zasu iya kwanciya haka.
Kawai dai kara suka mata amma cikinsu yanata kiran ciroma, gashi kamar zai hade da bayansu. Daga mai wakar yori yori sai bumper to bumper. Kowane ciki da nashi kukan. Haushi kam Laila taji saboda ta lura kawayenta zasu raina ta. Sai tayi ma Bilal Text idan ya gama da Haske kada ya maido da ita saiya hado masu da abinci. 
Ya kusan bakin ruwa yaga msg din, Tahir palace ya tsaya ya siyan masu meat pie da cake. Sai ya siya tsire masu uban yawa da drinks ya hado Haske dashi. Dawowan Abbansa ya kwafsa masa, kawai kallon fatan Haske yake yadda yake sheki gashi babu damarya mora. Sai dai abinda ya sani gobe ma rana ne. Idan yayi hak’uri zai samu.
Sallama tayi masa sannan ta bishi da addu’a mai tarin yawa. Shi karin kansa yaji dadin addu’an saboda bayan Umman sa babu mai masa addu’a haka kamar Haske.Ya kuma tausaya mata saboda ya lura da soyayyar sa kawai ta dukufa. Batada wanda ke santa tsakani da Allah, ba iyayen taba, ba Laila ba sannan kuma shi yana tareda ita saboda nashi manufar ne. Sai dai it’s a seMsh world kuma he is very semsh. Sai dai kam yau Haske ta tsallake rijiya da kafar baya. Wannan kenan! 
Haske ta shigo da kaya ninki ninki wanda Laila tayi murna dan yawan. Sannan kuma ta danji tausayin ta kadan a karo na farko. Dama abinda yasa take kawance da ita baifi saboda yadda kowa kesan mu’amala da ita ba saboda saukin kai da dadin sha’ani. Gashi samari na bala’in santa. Rabin samarin Laila wanda suka nema Haske ne suka rasa harta Saif. 
Yadda Haske ke koran samari duk daukanta zata hadata da Badman Bilal amma sai aka samu akasin haka. An gama shiga da kayan kenan za’a rufe kofa sai ga wata tazo da abinci a cooler. Nan ta ajiye masu ta koma ta kawo wani daga alamu na miya ne. Sannan sai tace Saif yace a kawo. 
Duk daukar Laila kajin ne akasa a cooler kar yayi sanyi. Abin yayi mata dadi saboda ya nuna yanada hangen nesa. Budewa tayi sai taga shinkafa fara, Dayan kuma miya ce tsululu an burga kifi. Idan kasa zai bude ta shiga data ji dadi saboda kunyar duniya Saif ya bata. Babu wanda yabi kan coolers din kowa abinda Haske takai aka ci. Daga nan akayi ta hira kala kala kamaryadda yan mata keyi. 
Kashe gari bayan sunyi sallah saiga Saif ya kirata. Anan tace dan Allah karya kunyatata da safen nan. Kamar ta sani saboda koko da kosai ya bada a girka masu. Wajen bakwai da rabi aka kawo. Haushi taji sosai ta soma masifa. Haske ne tayi ma Mommy text dan Allah a kawo masu abinci. Tunda take bata taba tambayar Bilal abu ba kuma bata tunani zata iya. Rokon saurayi yanajawo raini kuma bata san abin. 
Mommy tasa masu aikinta suka dafa doya sannan suka tsoma cikin kwai aka soya, sai kuma plantain da ruwan tea wanda yasha su na‘a na’a dasu citta. Abinda su Laila sukayi ma Haske yasa bata jin kyashin rama ma kura aniyarta.
Sameera tun safe ta tashi ta gyara gidanta tsab tayima yaranta wanka ta sanya masu kayan sallan su wanda ta dinka. Shadda ne light green wanda tayi masu anko. Abul khair yasha Cover shoe da hula dark green Sai Mubina da Sadiya hijab ne. Sannan ta soya masu kwai da dankalin turawa da shayi mai uban kauri suna sha. Saif shima babu kunya yace ta mika mashi kuwa ya hada yanayi yana zuba zance. lta kuma Sameera leshi tasa mai orange, purple da silver. Dinkin riga da skirt ne kuma ya karba jikinta dagwas. Gashi tanada diri mai kyau kamar coca-cola. Sannan akwaita da yawaltaccen gashi inda tayi parking dinsa na ponytail. Fuskanta hoda ta mitsika saita saka jam baki purple. Bakinta mai bala’in kyau ne ebony irin mai sheki. Gashi tana bala’in gyara shi da sabulun yan Ghana. 
Kyakkyawa ce ajin farko, fuskanta round ne sai hanci siriri. Sannan ga manyan idanu farare tas. Ko hakorin suma tar suke ga wushirya tsakanin su mai kyau. Akwaita da gashin gira mai yawa kuma a kwance sai gashin ido dogaye kamar ta saka. Babu yadda zaka ganta tajuya ido bai tafi da imamin ka ba. Salon maganarta daban yake cikin natsuwa da hikima. Bata rasa komai ba fannin halitta. Yadda tayi ado saida Saif yayita satar kallonta. Bakar mace tamkar fafare dubu. Bakar mace bakya kodewa, daki bari kenan, a hauki a zame ki hau mutum ki zauna daram. Bakar fata bugun Allah, babu a kasuwa balle a kwaikwaye ki, sanyi da natsuwa kike kamar al-fujr kafin gari yayi haske. Haka ya gama kallon ta wanda batabi ta kansa ba. Haushi takeji ainun tunda yasa harkan biki ya dena bada kudin cefane. Kuma idan ya dawo dole a zuba masa. 
Ashe abinda Sameera tayi yabama Saif haushi data hana shi dankali da kwai. Sai yaje kasuwa ya siya dankali da crate din kwai ya kaima Laila wanda zata rinka soya masu su biyu suyita ci hartagama satin amarcin ta. Kawayenta kuma dubu hudu ya bada kudin sallama, Laila ce ta cika 1k abin yayi armashi kamar haka ya bata. Anan suka sake gyara mata gidan tareda mata nasiha da addu’a. Sai suka tafi suka barta da halinta wanda zai 
kwace ta ba Hasken fata ba. Wannan kenan!
Yau aka kawo ma Ammi mai aikinta. Idan Fijr takejira za‘a bushe. Har yanzu haushinta takeyi sabodata hanata kudi. Gashi Baraka tana boarding babu mai tayata. Sannan gidan wakeke dole ta nema taimako. Anan taga kokarin Haske yadda take aikin babu mai taya‘ta. Duk yadda taso ta musa yarinyar nada hankali babu laifl ga kuma hakuri. Ta tabbata da Fijr ne da sunyi dake dake an bama hammata iska. 
Fijr ta sheka kwalliya tasa leggings wanda ya nuna surarta da top saita daura kimono akai. Fuska da uban make up kuma cikin ikon Allah ta ‘Iya wannan. Zata gidan Isi ne sai doki take kwana biyu bata gansa ba. 
A falo ta iske Daddy, yana waya da Haske inda ya bukaci tazo gida ta same shi idan ta samu hali. Fijr na daga gefe tanajiran sa. Bayan ya gama saita rinsina ta gaida shi. Ammi na wajen amma ko kallonta batayi ba. Daddy ya bata 1k tareda fatan alheri Dukda baisan inda zata ba. 
Bayan nan Ammi ta wuce kitchen dinta, yayi kal kal rabon daya samo kulawa haka tun 
Haske tana gidan. Anan ta karajaddada ma Lantana akan tsabta. Tana bala’in san taga 
wuri yana sheki kuma ba tasan nawa. Ammi tayi mata bayani akan duk wani aikin gidan 
zatayi sai girki Shima miya kawai zata bar mata. Amma wani tuwo, shinkafa ko doya duk ta dafa babu damuwa. Sai batun abincin Lantana, anan ta sheda mata cewa bazata rinka bata shayi ba. lta masu aiki basa shan shayi a gidan ta. 
Zata rinka dumama tuwo ko shinkafa ta rinka ci amma karta kuskura taganta da kofin shayi koda ruwan bunu ne. Sannan kuma bata lamunci taci abinci da nama ba. Ko nama dari ne karta saka. Sai ta dauko wasu kwanoni irin na almajirai da kofin karfe ta bama Lantana ta ajiye a matsayin nata. Karta sake taci a na gidan. Idan kuma aka rage abinci karta side mata kwano. 
Daga nan Ammi ta wuce inda Lantana ta jaddada mata cewa zata kiyaye komai. Sai ta wuce ta cigaba da aikin ta. Lantana ce mai aiki na biyar tun bayan tafiyar Haske. Banda danda ka haifa babu wanda zai dauka irin cin kashin da Ammi keyi. Tanada bala’i ga aiki kaca kaca babu hutu. Da an kawo mutum zai gudu, yanzu dai dillaliya tace idan ta bari Lantana ta tafi bazata sake business da ita ba.
Fijr ta isa gaban gidan Isi ta ganshi a garke da kwado ta waje. Abin ya bata mamaki saboda ba haka aka saba rufewa ba. Dama mai gidan yanada shago ta wajen gidan inda yake zama. 
Anan taje taji ba’asi sai yake sheda mata ai Isi ya kwashe kayansa ya tafl. Kuma jiya suka dawo daga Katsina wajen daurin aurensa. Kuma shi ya kama haya a Kano inda ya samu shago. Shiru tayi kamar bataji ba, kanta ne ya soma zugi yana charji, sai tace mashi ya nanata. Anan ya soma bayanin komai kafin ta mauje masa baki. Finciko shi tayi daga bayan kanta ta soma duka. 
Lallai ta cika annoba. Duka takeyi kamar Allah ya aikota ta kashe shi. Tanayi yi tana zagin ubansa tareda kiransa munafuki. Tareda shi akaci amanarta. Nan yayita bata hakuri amma Kota saurare shi. Yanayi yana tuna mata shine fa ke taimakon ta idan Isi yana kilarta. Saida taga ya rage ihu banda numfashi sama sama baya komai kafin ta barsa. Dukda yana namiji bai isa ya kara da ita ba saboda tanada girman jiki da tsawo da kiba. Balle kuma kanta yana motsawa dole ta kirbesa la’ada waje.
Koda yake tabbas idan tace yasan da zancen auren toh gaskiya ne. Sau da dama yakan 
shawarce Isi akan ya aureta amma yace ko gawarsa baxai‘ yi haka ba. Bai dauketa mai hankali ba kuma baxai yarda wani alaka banda na bariki ya hada su ba Anan ne yake sheda mashi cewa kudi yake nema ya samu wajenta yasa yake tarayya da ita. Yanzu haka yana jiran 250k ne wajenta inda zai kama haya wanda zai zauna da amaryan sa. 
Bayan tabar wajen tunani kawai takeyi. Tana ganin tanada shigar ciki wanda yasa duk ta matsu tayi aure. Yanzu kuma Isi ya gudu ya barta babu tudun dafawa. Gashi batada wani saurayi balle ta laka masa. In fact bayan Isi ta mance yaushe rabon da wani yace yana santa koda ta Facebook ne. Kuma ita tana bala’in tsoro ta cire tunda ance mata mutuwa zatayi straight. Tashin hankali ta shiga sosai, a yau ta soma ganin illar mugayen halinta. Wannan kenan! 
Kashegari Litinin kuma Haske zata wajen aiki. Yanzu kam ta saba da zuwa ita Kadai tunda Laila ta daina. Tayi kwalliya abinta ta chakare cikin Swiss material peach da ratsin purple. Bata daura kallabi ba saita saka gyale ta yana kamar na Iarabawa. Sai ta dauki wanijakarta wanda Bilal ya bata mai shape din Kiss. Afalo taga Mommy da iyalanta duk ana karin kumallo. Abin ban sha’awa sunayi suna raha. Ta rissina ta gaida Engr Muktar mijin Mommy tareda ita kanta Mommy baki daya. Abubakar wanda kansu daya Shima ta gaida shi. Sai sauran yaran, Maimuna, Amina da Ilham suka gaida ta. Yasmin kuma tana Ukraine tana karatu, shi kuma Al-amin yana high school a US finals dinsa yake. French toast suke ci da pancakes wanda an kawata plate din da strawberry da grapes. Abin yana mata daban idan tana zaune cikin su saboda bata saba ba. “ 
Agidansu sai dai taci a kitchen ko a daki, wani lokaci da Daddy Zailani ya matsa tana zaune amma harta gama ci Ammi tana watsa mata harara. Anan ta roke Daddy ya barta. Suna cikin cin abinci sai sukaji sallama. Bata daga ba amma tabbas tasan murya. “Oyoyo Ya Haisam” ilham tace saita ruga wajen. Da azama Haske ta kalle bakin kofa. Babu haufi Haisam ne Dr wanda suke aiki waje daya dashi. Amma kuma me yakeyi anan? Kuma meyasa suka ce masa Yaya? 
Karasawa wajen Dinning table yayi saiya rinsina ya gaida su Mommy kamar kowane da nagari. Daga nan ya bama Abubakar hannu suka tafa. Sai a lokacin yaga Haske. 
“Good lord! Me kike a gidan mu?” yace cikin barkwanci. Bata amsa shi ba kawaii murmushi takeyi. Mommy ce tace, “Ai ita ce Shamsiyya yar wajen Hafsa… I mean Hadiza kasan sunar yana confusing dina” sannan saita kalle Haske tace, “Wannan yaron sister dinsu Daddyn Abubakar…. Kunsanjuna ne?” 
Girgiza kai Haske tayi alamar eh kuma ta fahimta. Watau duk rashin mutunci da suke masa a ofis somehow dan uwanta ne. Duniya kenan! Anan ya zauna ya soma zabga shagwaba shi bazai tafi ba yaga pancake sai yaci. 
” Dan lele ina sakon nawa ka tsaya cin abinci?” 
Mika ma Maimuna key yayi taje mota ta dauko mata yama mance, sannan kuma su Maimuna suka ce shi zai kaisu school duguzum. 
“Ai wallahi kun hutarshe ni, kuma daga yau bazan sake kai ku makaranta ba, jibe su masu kan kwakwa, goruba,da giginya” Abubakar yace cikin haushi. Kowa yayi dariya banda yaran wanda suka tura baki. Dama haka suke ma Haisam wawa idan sun gashi basa bari ya huta. 
“Haske tashi muje na ajiye ki?” ya fada, dama shi kadai yake ce mata Haske cikin gidan bayan ya gani a IG dinta. Da sauri Haisam ya tare shi, “Man meye haka? Wajen aikin mu daya fah?” 
“Toh duk kun hutarshe ni” yace yana kada kafada. 
“yau Abubakar babu kasuwa duka yan matan sun guje ka, na me dey reign” Haisam yace wanda Abubakar dariya ya subuce mashi ya kai masa naushin wasa. Duk abinda akeyi Daddy Muktar da Mommy ana kallo ana dariya. Yadda family din ke wasa abin burgewa ne. 
Wrap din kilishi ne guda biyar, anan Mommy tabama su Haske da Haisam guda daya suci a ofis. Suma masu kan kwakwa da goruba daya sai mai kan giginya da Abubakar daya. Nan suka mata godia gabadaya. Haisam motansa makil da mata, zai ajiye su Maimuna da Amina a Zamani college. Ita kuma ilham yar firamare a Cavendish. 
Addu’a Mommy ta bisu dashi, shima Abubakar Dr ne yana aiki a Yusuf Dan Tsoho teaching hospital. Bayan nan sai Daddy shima ya fita aiki. shi ne shugaban firm dinsu a Nigeria wani construction company sun kware wajen gina gidaje, da, titi da makamancin haka. Gwamna mai ci yana gyara Kaduna kuma yayi hadaka dasu yanzu. Mommy kawai aka bari a gidan da mai aikinta Anty Umma. 
A mota bayan Haisam ya ajiye su saura Haske inda zasu karasa aiki tare. Ta mirror yake satan kallonta. Mamaki yakeyi ainun wai yau ita ce a motar sa kuma a matsayin yar uwansa. Idan suka hada ido sai su sakar ma juna murmushi. Baisan ta inda zai soma magana ba kuma duk ya kagu su soma hira. A hankali ya kawo zance wanda yana tsoron karta gwasale shi. Koda yake Laila ce sarkin abin. 
Yanzu mun zama yan uwa kenan?” “Uhmm I suppose” “Wonderful, wallahi bakiji dadin danakejiba” bata amsa ba illa murmushi wanda ke nuna lotsawa na dimples dinta. 
“Dama asalin sunarki Shamsiyya, akwai Wanda ya taba zuwa neman ki ban gene wa yake nufi ba?” “Eh, amma anfi sanina da Haske. Saboda fatana da kuma Shams literally rana ne kuma akwai Haske” 
“uhmm okay” duk zancen nan yanata tsoro karta gwasale shi. Amma saiya lura tanada bala’in saukin kai. Ga murmushi tana yi. Yanzu ya lura Laila ce batada hali kuma takeso ta bata ta. Koda yake tun yana musawa har ya yarda cewa Haske crush dinsa ne. Amma kuma bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane. Tafi karfin sa. Sau da dama yana ganin saurayin dake zuwa daukarta kuma ya bala’in haduwa.
“So… Yanzu kema yaushe zamu zo naki bikin kamar kawarki” yace yana kallonta kuma yana murmushi. Duk tsoron sa kada tace an saka mata rana. Babu abinda ke tsakanin sa da ita amma tabbas yau zai kasa barci. Basai ka fada ba amma yasan yana ruwa harda ocean. 
“Soon in sha Allah” wani zafi yaji a zuciyar sa amma sai ya daure. lta kuma kallon natsuwan sa take yadda yake tuki. Wannan babu haufi yafi Bila| iya murza steering. Babu mamaki akwai tuki cikin DNA dinsa. lta kadai take ta tunanin ta. 
Daga nan sun isa wajen aikin su. Anan taga ya rage glass ya gaida su Mallam Dauda a mutunce. lta ma ta gaida su suka wuce. Abin ya bala’in burgeta, tana san mutane masu saukin kai. K0 sau daya bata taba ganin Bilal ya gaida suba. Banda Laila babu wanda yake 
sake ma fuska koda su suka gaida shi. Bayan Haisam yayi parking mota sai suka fita. 
A lokacin ta sake kare masa kallo, Sanye yake cikin riga long sleeve baby pink Sai dogon wando na suit baka wanda ya zauna jikinsa. Sannan takalmin cover shoe yasa sai ya dauka brief case dinsa. Masu gardening da suka gama aikinsu suna hutawa ya gaida a mutunce. lnda yake tambaya ya iyalansu harda ma wani korafi akan kwana biyu baya ganinsa. Anan yayi bayani cewa bashida lafiya ne typhoid. Haisam yace dashi ya shiga ciki ya duba shi babu damuwa. 
Ita kam batama sansu ba a fuska, daya ne kawai zata iya ganewa. Kuma bata taba Iura dako sunzo ba ko basu zoba. Sai taji wani iri sosai. Tare suka jera dashi dogon corridor din zasu registry domin rubuta sunansu. Daga manyan Dr har kanana kamar Haisam sunata Mika masa hannu a gaisa. 
“Good morning Dr How are you doing?“ 
“Ina kwana Dr an tashi lafiya?” haka ake ta binsa dashi. lta kuma sai dai ayi mata sannu sannan abita da murmushi. Sosai ya burgeta matuka saboda saukin kansa. Wannan kenan! Shin Yanzu wani hanya Bilal zai bi domin ya cima burinsa? Ya Laila zata kasance? Ammi ya zataayi da cikin jikin Fiir? 
Toh yanzu ga Haske ga Haisam? 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]