[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE

CHAPTER 8
Ammi Hadiza kallon Haske take yi mamaki fal fuskanta. Kallon sama da kasa ta rinka bin ta dashi wanda ita kuwa duk ta tsargu. A sanyaye ta shiga cikin falon saita je dab da wani kujera ta durkusa. “Ina wuni Ammi, na sameku lafiya?” Ammi taso ta share sai kuma ta
tuna abinda Daddy yace wanda dolenta ta amsa. “Lafia lau Shamsiyya” ‘ Anan Haske ta zauna a wajen Inda Ammi haryanzu bata bar kallon taba. Mamaki take yadda Haske tayi kyau tayi kashar kashar fatan ta yayi santsi. Gashi ta saka leshi ubansu wanda ba ita ta siyan mata ba. Tunani kala kala ya fara rikito mata, “Kodai ta soma gantali ne?” wani zuciyar ya raya mata. Sai kuma wani yace, “Kila dai tayi aure ne saboda wannan
kyau baya kamada na gantali ‘
Suna zaune haka babu wanda ya sake magana saiga Daddy ya fito daga dakinsa. Ya kara manyanta kuma furfura yayi dan yawa wajen gemunsa. Sake durkusawa tayi domin ta gaida shi, “Daddy ina wuni da fara’a ya amsa mata gaisuwa kamar babu abinda ya faru. Bayan wasu dakikai sai ya soma magana, “ya Kike shamsiyya ya aiki?”
“Alhamdulillahi”
Suna cikin haka sai ga sallama, Hajia Binta ce kanwar su Hadiza ta shigo da wasu daga cikin yaranta Maimuna da Amina duk basufi 13 and 10 years ba. Mikewa Haske tayi taje wajenta. ltama Hajia Binta ta bude hannu alamarzata fungume ta. Basu ce komai ba Ita da Hajia Binta har kusan dakika 30. Zaune take a US inda take aure kuma yanzu sun dawo nigeria da zama wata shida da suka shude. Tunda ta dawo take neman labarin Haske amma karya daban daban ake shirga mata. Daga bisani Ammi tace tana Uganda tana masters.
Sam abin Bai shige ta, sai tace toh a bata number din Haske. Anan idon Hadiza ya fito wai Haske batada waya sai dai idan ta kirasu zata isar da sakon gaisuwa Anan dai tabar zancen tasan komin nisan jifa kasa zai fado Bayan wannan da watanni Fijr ta nema kudi wajen Ammi 250k wai tanaso ta some business. Abin karya ne Isi wanda taki rabuwa dashi har yau yake bukatar kudi. Yayi mata alkawan idan ta bashi zan daina dukanta kuma kila yayi tunanin aurenta. Abin yayi mata dadi sosai saboda batada wani buri data aure shi. Yanzu ta cire ciki biyar bayan wanda aka kore Haske sanadiyar ta. Likita yayi mata sheda akan idan ta sake cirewa ba cikin ba har ranta zata rasa. ‘
Ba wannan Karon bane farkon karban kudi wajen Ammi, akwai sanda ta fara business tiryen tiryen na jaka da takalmi Isi ya kwashe kudin ya cinye. Sannan tayi na atamfa Shima haka yake dauka yakai kasuwa a kudin kadan ya cinye. Abinda yasa Ammi ke bata kudi saboda taga karatu yaki ci. Saita tursasa Daddy akan dole a neman mata tudun dafawa. A haka Ammi tana binta 470k bacin wanda ta bata kyauta.Bayan Ammi ta hana Fijr kudi saita zura takalma ta wuce Jabi road inda gidan Mommy Binta yake. Bayan sun gaisa saita ce “Mommy business nazo maki dashi, zan baki labari mai dadi amma sai kin bani kudi“ mamaki Mommy tayi saboda wani irin labari ne haka dake bukatar kudinta. Duk tsammani tana tunanin zancen 10k k0 20k ne abin ashe ba haka bane. ‘ 
Mikewa tayi tajejakarta ta kirga 15k yan dubu ta bata. Wani dariya Fijr tayi tana rangaji dakai. “Mom my 250k zaki bani kona rike labari na” 
Kallon Fljr tayi tana nazarinta, ko sanda take US idan tazo Naija basa wani dasawa da Fajr. Ance batada kunya yasa ta kiyaye ta. Sun fl shiri da Haske sosai. Yanzu meyasa zata bama 
Fijr kudi? Mema zatayl da kudi mai uban yawa haka? Ko dai ta soma shan kwaya ne?  “Me zakiyi da kudl haka?” “Nldai mommy babu ruwanki dani” tace tana tura baki tareda nuna hannu. “Labarin Haske zan baki ….. Ina nufin inda Shamsiyya take? Zaki bani kudin koko?” tace Cikin rashin kunya. Murmushi Mom my tayi mai ban takaici sai tace, “Kinada Account ne?” Warr idon Fajr
yayi saita budejakarta da hanzari. Account number din Isi ta bata. Nan ta soma komai na transfer inda ya nuna lsiyaku Mohammad Access bank saura password abu ya tafi sai 
Mommy ta dakata. “lnajinki saikin gama na tura” 
Anan Fajir ta labarta mata komai yadda aka koreta daga gidan cikin wulakanci da yadda ba’a sake neman taba. Komai bata rage ba harta yadda ta finCIke ta waje tanayi tana dariya. Hawaye fal idon Mommy, tasan sharri Hadiza tayi ma Haske saboda ba yarta bane. Lokacin Maman su na da rai an hadu duka, taga yadda Hadiza kema Haske har tayi magana. Sai mamansu tace babu komai kawai idanta ke ganin mata gaibu amma Hadiza tana mata rikon amana. Tura mata kudin tayi sai tace ta gode. ’ “Mommy idan zaki bani 50k zan baki labarin irin cin mutunci da muke ma Haske” ta fada da murna. Jikin Mommy duk yayi la’asar, dakyar tace, “Kinga 15k dincan shi kadai gareni. ldan kinaso ki soma magana kokuma ki tafi tunda ke bakya abu dan Allah” Nan Fijrta dauki kudin yafi babu, tabbas Magana jari ce. Gashi yau ya janyo mata arziki. Tas tayita zuba zance, abin ya soma isar Mommy tace ya isa. Abinda ta gane shine Haske bataji dadin zama da Hadiza ba. 
Bayan nan Hajia Binta bata zarce ko’ina ba sai gidan su Daddy Zailani akan ya kori Haske. Nan fah aka shiga family meeting kala kala akan zancen  Fijr ne wanda ba’a tambaya ba ‘a zauna ta sake labarta masu yadda Haske tayi ciki da yadda suka koreta kuma suka ce kartaje wajen yan uwa. Salati kawai kowa keyi anatajimami. Ruwa baya 
tsami banza haka kurum Haske bazata Masters babu sallama da dangi ba. Ba irin idon da Ammi bata mata ba amma taki shiru. Daga nan sai ta soma basu Iabarin rayuwar Haske tareda Ammi. Tunda Ammi na hanata kudin da zata bama lsi ya aureta ta saka kafarwando daya da ita. Babu rufin asiri ko kadan. Kunya yayi dawainiya da Hadiza ba kadan ba. Taci amanar zumunci wanda babban wanta wanda shine uba gareta iyaye sun rasu yayi mata Allah ya isa. Daga nan aka sallami Fijr wanda ta samu kusan 10k kuma tayi alkawari idan ana bata kudi bakin ta bazai rinka shiru ba. Wannan kenan! 
Falon yayi tsit daga Haske, Ammi, Daddy da Hajia Binta. Kowa da abinda yake ransa. Shi Daddy ba alan musuru bane. ldan Ammi tace Haske nada ciki to tabbas tanada shi tunda bazata yi mata kazafi ba. Ammi haushi ke damunta, mahaifiyar Daddy tace koda cikin duniya Haske ta dauka bai kamata ya koreta ba. Karamin su kuma babban su saboda Hajia Binta ta soma magana. “A ina kike zama?“ 
Anan ta labarta masu yadda ta koma zaman gidansu Laila, har,aka turata bautan kasa Abia amma ta dawo Kaduna sannan kuma wata 4 kenan tana aiki a Barau Dikko. Ammi ta sake kanne fuska ranta yayi mugun baci. Ta lura duk abinda take nufan Haske dashi baya samunta. Harare harare ta rinka watsa mata wanda ita kuma sunkuyar dakai kasa tayi. 
“Alhamdulillah” Daddy da Mommy suka ce. Shima yaji dadin yadda bata tagayyara ba. “Hadiza akwai abinda Shamsiyya tayi maki ne?” Mommy tace 
“Ni babu abinda tayi min” Ammi ta amsa a miskilce. “A‘a ina nufinda chan tun ba yau ba?” 
“Nifa nace bata min komai ba” “Hafsat fah?” 
Anan Daddy ya zaro ido yana kokarin magana, “Dan Allah abar maganar haka” Haske ita 
dai tana sauraro bata wani fahimce komai ba 
“To meyasa kike ma Shamsiyya haka, tana yarki amma kamar ba yarki ba???? ldan tayi maki wani abu wanda bai dace ba ki fada min yanzu na dauko belt nayi mata duka kamar ganga a wuce gurin” Mommy ta sake fadi 
Wannan Karon abin dariya yabama Ammi, ita batasan munafunci. Kowa yasan abinda Haske tayi amma ana so a nuna kamar ba’a gani, ya za’ayi ya dauki duk sonda yake ma Hafsa ya daura mata. ldan tayi magana dan munafunci yace ai saboda batada uwa ne. Ai taga zaman da yayi da Hafsat ya bambanta da nasu. “Binta nifa babu abinda Shamsiyya tayi min” “Kawai kin tsane tane?” Ammi bata amsa ba saboda tsanar data kema Haske yafi hasken rana bayyana. Mommy ta kalle Daddy tace yanzu yaushe Shamsiyya zata dawo nan. Zaro ido Ammi tayi tana dafa kirji, “Zata dawo ina?“ Kallonta Daddy yayi yace, “nan gidan mana tunda ba kanta farau ciki ba” “Wallahi banida Ciki kuma ban taba dauka ba” Haske tace cikin kuka. Murmushi kawai Mommy tayi, tasan hakan saboda yaushe Hadiza zata bar Haske ta huta balle ta samu damar gantali. 
“ldan babu damuwa saina dauke ta, dama nafisan hakan. Dani da Hadiza duk daya ne kuma kowa zai iya rike Shamsiyya” ita hausa tayi tana nufin daga ita har Hadiza babu uwa ga Shamsiyya, kowa ya gane hakan banda Haske. 
“Mommy idan babu damuwa wallahi gidansu Lalla ma yayi, rikeni suke babu bambanci da Laila” 
“Kash Shamsiyya ban sanki da gardama ba, karki damu zan maki riko mai kyau. Wallahi dana sani da tuntuni nike rike dake Yara rahama ne, bakasan wanda zai jlkan ka ba” 
Yanzu Ammi ta sake fuska sosai saboda Haske ta bar gidan dindindin. Anan akayi dan hira 
kadan har Mommy tabama Ammi 10k na Fijr. Dama ita ta samo number din Haske. 
A kwana a tashi har bikin Laila saura sati daya. Haske ta roki Mommy alfarma ta koma gidansu Lalla da zama sai bayan biki ta dawo. Mommy ta aminta da haka saboda su Laila sunyi mata halarci. Yaranta shida da Haske yanzu bakwai duk gabanta. Koda Haske zata bar gidansu Laila ita bata wani damu ba ko kewarta. lta yanzu batada abinda tasa a gaba face bikin ta. Su Laila kuma sana’a babu laifi akwai kasuwa. Bata fita aiki kamar yadda Saifya bukata. ldan zata fita gantali sai dai tayi karyan zata kasuwa daga nan ta biya hotel inda Wasco ke mata hanya. Yanzu da kyarta samu 180k inda saida tayi ma Wasco karamin zanga zanga kafin ta samo mata na karshen nan wanda ya bata 50k. Duk sauran yan 20k 30k ne. 
Bilal ya bama Lalla Plasma TV Samsung babba sai 50k. Abin yayi mata dadi sosai. Duk yadda taso tayi events abin ya faskara saboda gonar babanta daya aka samu siyarwa. Ba’a gama kayan daki ba balle wani shagali. Ta siya komai dai yanzu na amfani amma Banda Fridge. Anan Salf yace karta damu yanada fridge gidansa zai kwace yakai dakinta. Ta sake ganin mutuncin Saif saboda ya nuna yana kaunarta. Yan kawo lefe sukazo dashi. Akwati hudu da kit. Duk kayan kananan zannuwa ne guda ashirin. Super kwara daya tal sai Swiss biyu. Ko kayan kwalliya banda su Dark and Love|y babu wani abin kirki. Ko alfarman Classic bata samu ba. Mai kam banda vasellne masu uban yawa sai carotene. Babu towel, nail cutter, face mask, silipas dadai sauran abubuwa masu kara ma lefe armashi. Ran Laila idan yayi dubu toh ya baci saboda duk ta muzuma. Harda munafikin souvenir’s ‘akayi na ‘Welcome to the tarban Iefe of Laila Moham mad’ taji kunya ainun saboda saida 
Baaba da Haske suka hanata tara jama’a komai sirri yafi. lta batajin kira sabida list tayi ma Saif kuma ya tabbatar mata da ya siya komai. 
Anan ta kira shi ta soma korafl inda ya soma ranstewa ya siya komai. Amma a dakin Sameera ya ajiye. Kila ta faki idonsa ta canza komai kuma shi bai sake dubawa ba. Ya daukin mata alwashin saiya zane Sameera yau babu haufl. Kuma ana auren su zasu kasuwa ta siya abinda takeso. Hankalin ta yadan kwanta kuma tajaddada mashi kada ya mance ya farfasa ma Sameera jiki. Kuma ta rantse idan ta shiga gidan saita bigeta saboda ita rainin wayo ne bataso. Bilal yanzu abin duniya yayi masa cinkoso, yanzu ya yanke shawara akan yakai Haske gidansu wannan satin komai ma saiya faru. Abinda ya sani shine bayan yayi tasting dinta idan yaji dadi toh zai aureta. Kuma koda da karfl yayi mata koda fyade ne toh idan taji aure bazata guje shi ba. Dama burin yan mata bai wuce suyi aure ta kowane hali ba. Mata sukaje wajen boka balle ita zata same shi a bagas! 
Idan kuma baiji dadinta ba dole tasan nayi, tayi hak’uri saboda shi ba zai zauna da tasteless mace a gidan saba. Nan ya soma tunanin yadda zaibi ya shawo kanta akan ta yarda ta bishi suje wani wajen. Tunda yake da ita bata yarda suyi yawo babu Laila. At all taki yarda su kebe su kadai. Saidai cikin mota kofa a bude kofar gidansu Laila. 
Shawara ya fado masa akan yabi ta hanyar Laila ta samo mashi mafita. Anan ya dauki waya ya kira ta, “Amaryar Saif” Badman Bilal angon Haske” ‘ “Ya kike ya shirin biki?” “Lafiya lau munata yi” 
“Komai yayi daidai ko akwai wani matsala da zan iya taimakawa” anan tace gwara ta fada mashi tunda dai shiya tambaya. Dama tanaso ta kira yan kidan kwarya sai ayi mini shagali ranaryinin biki. Nan ta gaya mashi harda souvenir take so a karo. 
“Abu mai sauki ne, karki damu. Kawai abu nakeso ki taimaka min wajen Haske” “Kome kake so zanyi maka” Nan ya labarta mata yadda yakeso ya kebe da Haske amma taki yarda kullum tana zillewa. Da farko Laila taso taki amincewa amma sai yace harda DJ zai dauko mata ranar biki. Murna tayi sosai bazata wani kunyata a bikin ba. Nan tayi masa alkawari ranar Haske zata zama nashi. 
Ana sauran kwana biyu biki, su Laila sai ranarta soma dilke, daganan ta wuce saloon inda akayi masu gyaran gashi dana farce. Haske ta biya duka kudin a wani katon shago ne gefen 9-11. A saloon din Saif yazo karbar Wayan Laila zai gyara mata screen wanda ya farfashe. Tana feleke taje wajen sa tana yauki. “My Destiny” tace tareda fari idanu. Murmushi ya sakar mata saboda shi duk ya kosa a kawo mashi yar shilar sa. 
Mangal plaza yakai inda akayi gyaran aka bashi. bai samu damar mayar mata ba saboda hidimar biki. Har yau ba’ayi wiring wuta ba. Kuma za’a saka fanka a falo kawai. To dayake Laila ta cire Sim dinta sabida tsaro. Saiya saka sim dinsa ciki ya kunna. Abinka da whatsapp ba ruwansa da number dinda ka bude. Shi dai yana ganin data zai soma aiki. Nan ya shiga bada niyyarwani abu ba, chat dinsu yakeso ya gani da ita. Sai yaga wani chat da Khadlja, ya ganeta saboda Laila na yawan cewa zata gidansu kwanan nan. Sallama akayi tareda gaisuwa. Bayan nan sai tace ‘Kinga kin kusa aure ya kamata ki daina halin ki’ 
Salf ya amsa mata da ‘wani hali kenan?’ 
“Bansan wulakanci Malama kinsan abinda nake fadi” “Allah ban sani ba” 
“Munyi chatting da Wasco dazun ta fada min komai tunda babu boye boye cikin mu” “Wasco din? Toh me tace maki naji ko gaskiya ne?” 
“Nldai kawai banaso kina bin maza hotel sabida kudi, haba kin kusa aure kuma kojiya 
saida kikaje.‘ “Dan Allah Khadlja ki rufa min asiri, wallahi bazan kara ba” “ni bance zan gayama kowa ba, kawai ki dena ne kafin mijinki ya gane” “Karki damu in sha Allah bazan kara ba” 
Anan suka gama chat din, tuni Saif ya soma zufa. Gashi da bala‘in zuciya nan ya soma numfashi sama sama. “Dama Laila yar hannu ce?“ ya tambaya kansa. Wani shawara ya fado masa akan ya janye auren. Sai kuma yayi tunanin idan yayi haka ai ta cuce shi. Gwara tazo ta yabama aya zakinta. Zai zame mata kamar motaryan sanda, shiga ba biya fita da Allah ya isa. 
Kashegari kamar babu komai ya kira Haske domin su gaisa da Laila. Haka ya sakejiki da ita sai zuba mashi shagwaba takeyi. Nan take ayyana masa ta kosa akaita. Shima yace kamar ya janyo agogo ne. Da safe kafin ya tafi aiki ya biya ya bata Wayan. Sannan ya milka mata 10k na mai lalle wanda zasuyi anjima. Kowa da abinda ke ransa, shi ya kosa a kawota yaci ubanta. Ita kuma ta kosa ta nuna ma Sameera bata iya zaman miji ba. Ranar akayi kunshi da kuma kitso. Da duk abin tanada yalwataccen gashi. Sannan kuma a ranar dangin mahaifiyarta yan Hadeja suka sakata a lalle akayi mata kamu tareda dangin Saif wanda sukaje. ‘ 
Kashe gari ranar daurin aure, Baaba tafi kowa murna Laila zata tafi batajanyo abin kunya ba. Haske kam ko’ina ta wuce murmushi take. lta ce ta dauki nauyin shige da fice kuma ta tabbatar komai ya kankama. Wajen karfe daya aka daura auren Laila Mohammad da Saifullahi Abubakar a sadaki dubu hamsin. Daga nan Laila tasa wani shadda wanda yasha aiki yan Senegal, Wasco ce ta bata gudunmawa. Kamaryadda Bad yayi alkawari ya cika saboda ga masu kidan kwarya sun zo. ltace ta soma takawa sannu a hankali cikin filin tanayi tana dariya. Kowa mamaki yake kamar ba amarya ba. Daga baya sauran kawayenta suka shiga suma. Haske Itama ta dan taka kadan saita koma wajen baki. Data tambaya Laila ina ta samo kudi haka sai tace Saif ya dauki nauyi. Tayi mata murna sosai saboda yadda ya nuna zai rike Laila tsakanin sa da Allah. Yan ofishin su Laila sunzo bus guda tareda da kyaututuka. Shima Haisam yazo ya bata Wall clock mai kyan gaske. Duk dibar albarkan datake masa bai hana shi zuwa ba. Dama shi baida damuwa. Abin duniya baya damunsa. 
Sai Laila taje ta canza zuwa iro and buba na Swiss din da aka saka a lefe. Haka tayita rawa saida wata yar babanta tayi mata magana akan taje tayi sallah. Azahar da la’asarta hada a lokacin. A Iokacin mommyn Haske tazo saboda itama tana biki na wajen dangin mijinta, anan ta bama Baaba 10k saita wuce yan kawo tuwan biko sunzo da katan cooler din shinkafa da naman kaza. Dab da magrib sai akace Laila taje tayi wanka tafiya yazo. Anan ne tasa super din da akayi mata. 
Baaba tayi mata nasiha akan hakuri da rike sirrin miji. Kowa da nashi matsalar a aure kawai daurewa ne. Shima Baba yayi mata da sauran yan uwa. Ita banda kuka babu abinda 
takeyi. Haske ma haka sunata kuka kowa yanata tausaya masu. 
Bayan an kaita gidanta wajen 9 na dare, Bilal ne ya kira Lalla akan ta cika masa alkawari. “Haske dan Allah ina so kuje da Bilal zai karbar min wallpaper dayayi min alkawari” “Cikin daren nan? Ki bari gobe mana” 
‘Dan Allah ki tashi mana, gobe aiki zai mana yawa’ Haske shiru tayi Sam jikinta baya bata ba, amma kuma tunda tareda Bilal ne  tasan bazai cuce taba. In fact Laila bazata turata ga halaka ba. Wannan kenan! 

An daura auren Laila da Destiny dinta. Wanene zai daku ita ko Sameera? Ya Haske da Bilal zasu kasance‘shin Fijr zata samu tayi auren? 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]