[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE


CHAPTER 7

Wata sa’in makashinka ka shine dan uwanka, gwara bare akan na kusa da kai. Saboda sau da dama ana samun matar uba mai mutunci da amana. Yadda zata rike yaran mijinta kamar nata.
Ammi Hadiza tana staff room dinsu suna zaune. Sai wata Itama Anty Hadiza tareda kawarta Fatima da Aisha suna zaune. Duk malamai ne anata hirar duniya. A cikin staffdin babu wanda yasan ba Ammi Hadiza ta haifa shamsiyya ba. Koda sunje gidanta sukaga yadda take mata kawai mamaki sukeyi wai dan cikin ka kake ma haka. Sai dai kuma kowa da irin nasa tarbiyan. Balle ma sunyi kama ba kace wa ba diyarta bane.
Anan suke ta tsegumin wata makwabciyar Hajia Fatima wanda ke gallazawa yaran yayarta. Wannan su hudu duguzum take cin uba. Aikam tasha tsinuwa wajen su. Nan suka yi ta magana yadda abin ya zama ruwan dare. Babu mutunci dan uwanka na mutuwa ka auri mijinsu saika soma kishi da yaran. Ko gezau Ammi bata yi ba. Kawai abinda ta sani shine basu san irin abinda take fuskanta ba. Gabadaya soyayyar Hafsa ya daura ma Shamsiyya ba itaba. Yasa ita kuma ta dauki alwashin saita rabasu kowa ma ya rasa.
Bayan ta tashi wajen karfe biyu, bata koma gida kai tsaye ba saida taje kasuwar sati ta siya su doya da dankali ta cika boot dinta. Koda ta isa Haske tana kwance babu lafia, bakonta na wata wata ne amma koda yaushe saiya kwantarda ita. Dakyartake komai danma ta samu Baraka tana kama mata wani aikin. Yarinyar tanada mutunci matuka ga girmama na gaba da ita. Duk yadda Ammi taso ta shiga tsakanin su da Haske abin ya Faskara. Shima Imran babu laifi ya zama zankadede saurayi yana fita ball duk unguwa an sanshi. Shine Daidai Fijr yake taka mata birki idan tana ma Haske diban albarka. “
Anisa ne dai akwai shagwaba, sai dai kana bata chocolate ka tafida imanin ta. Da Haske da Baraka suka kwashe kayan wanda dakyar take ma tafiya. Ammi kallon ta take ta gefen ido. “Kin kusan barin gidan nan” ta ayyana a ranta. Yam and Egg and liver sauce Haske ta masu na abincin dare. Bata wani ci ba saidai tsakura. Fijr sai bayan magrib take dawowa kafin Daddy ya dawo. Idan kuma baya gari saita kai wajen karfe 9 ko gezau.
Haka itama ta saka tana cikin ci sai tayi tsaki. Lokacin Haske ta fito zata kitchen domin ta ajiye kwanon. “Wannan wani irin doya ne an wani yanka gabza gabza kamar awakai zasu ci” tace da karfi wanda Haske zataji. Bata ko kula taba harta kai kitchen ta fito, har zata shiga daki sai taga bazata iya barin maganar ba.
“Fijr idan kinji haushi kije ki dafa da kanki, gwara ni na iya abinda awakai zasu ci kuma suyi alfahari” saita shige bata tsaya sauraron me zata ceba. Ba Ammi dake gefe ba, har Fijr abin ya bata mamaki. Idan kaga Haske tana magana to fah tana tare da Laila ko sauran yan ajinsu. Zaka tsinta abinda take cewa a wata cikin gidan.
Kashe gari Ammi bata wuce aiki ba saida ta tsaya bakin titi wajen masu bunburutun mai. Anan tayi ma Habu bayanin abinda take nema daga gareshi. Dubu biyu ta bashi tace idan ya cika mata aiki zata cika mashi sauran. Nan yayi godiya saboda ko ba’a cika mashi ba ya dade yana san Haske. Duk sanda ake wuyan mai shike kai masu ta black Market har gida yasa suka saba dashi sosai. Banda gaisuwa Haske bata yarda wani zancen ya hadasu ba. Da Ammi zata bi tashi bayan ya cika mata aiki ya tura iyayen sa domin ya auri Haske.
Wajen yamma lokacin Haske ta dan warware, har tayi ma Daddy dan wake ta ajiye saboda ya kira yana bukata. Tana zaune a dakin ta hankali kwance tana yanka farce saiga Ammi ta shiga dakin da fara‘arta. 
“Shamsiyya ana yankan farce ne?” tace tana murmushi Eh Ammi” sai tayi shiru tanajiran Ammi 
Abin ya masu bambarakwai saboda duk basu saba ba. Bayan gaisuwa babu abinda ke hadasu sai aike. Ammi bazata tuna randa ta tambaya Shamsiyya lafiyarta ba ko wani matsala idan tanada shi. Babu abinda ya shalle ta. “Yauwa kinaji koh? Dama gidan Hajia Zainab zaki je. Ina so ki kai mata abu” Babu komai a ran Haske ta mike tsaye ta soma shiri. Ammi na kallonta tana kara bakin ciki da irin suffar ta. Maganar da Haske tayi ya dawo da ita daga duniyar tunani wanda ta apka. 
Anan ta mika mata wani lace mai kyau wai ta kai mata. Yadda taga Haske a farfagiyar gidansu ta nufa hanyar Gate abin yayi mata bala’in dadi. lta kam Haske ganin magrib ya gabato ga kuma hadari ya hadu saida tabi kanta da addu’a. Nan tayi ayatul kursiyyu da amanar rasul, sannan tabi da ‘Bismillaahi, tawakkaltu ‘alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah. 
Hajia Zainab aminiyar Ammi Hadiza ce tun zuwansu garin, layin dasu Haske suka bari nan ne gidanta yake. dama chan batada wata abokiyar kirki yasa yanzu suka bala’in dinkewa. 
Habu yana nan murna fal ransa, yasan hanyar da Haske zata bi kuma yasan yadda zaiyi. Tareda wasu samari biyu yaje saboda su tayashi duba hanya. Yana kallo Haske taje gidan Hajia Zainab ta fito. Babu yadda batayi Haske ta jira yaranta su dawo da mota a ajiye taba amma tace gwara ta tafi. Gashi tafiyar da dan dama amma inda sabo ta saba shafa titi. Akwai lunguna kala kala da idan kabi zai kaita inda zaka cikin kankanin lokaci. Haske tana tafe fuskanta akwai walwala. Kawai wani tagani a gabanta ya rikito mata. “Innalillahi” tace a tsorace saita ja da baya. Sannan kuma taso ratsawa saiya capke mata hannu. ldonta ya fito saboda duk tsammanin ta sata za’ayi mata. Batada ko sisi a jikinta bata fita da purse ba. Wayace IPhone wanda Daddy ya siyan mata daga Makka. 
Haka ta mika masa IPhone 6s, “Dan Allah gashi karka illan tani” tace cikin sheshekar kuka. Murmushi yayi na keta saboda Ammi batace ya karba wayanta ba. Abu daya zai karba kuma shine budurcin ta. “Dan Allah nace ka karba, wallahi IPhone ne” ta sake maimaitawa. Dataga bashida niyyar kyale ta saita zura baya a guje. Anan tayi kicibis da saurayi daya yana dariya. Zata koma inda ta fito kuma ga Habu wanda bata gane Shiba da kuma wani suna dariya. 
Zobe sukayi mata, babu inda zata iya tafiya. “Tawa ta sameni” ta ayyana a fili. “Tukun nan dai” daya daga cikin su yace. Wrap din wiwi wajen shida Habu yasha, sannan dasu tramol da alabuko duk yayi ambaliya dasu jikinsa. Babu yadda zaiji tausayinta. Yana sane da abinda yakeyi sai dai kawai shedanci yaci karfin sa. Nan ya fizgo ta ya rungume kam. 
Sanyi yaji nata wanda ya ratsa shi itama banda bauri na kayan maye bata jin komai. Hawaye ya soma malala mata. Allah kadai ne gatan ta amma yau tasan ta kade. Nan ya rinka kokarin hade bakinsa da nata wanda ta samu ta yakuta da farce wanda bata gama yankewa ba. Abin yayi masa zafi saiya zuciya. Da hannu daya ya murde ta dama gashi murdarde yanacin karfejiki dukjijiya a mokade. 
Nan ya soma kokarin kwance mata skirt, tanayi tana shure shure amma a banza. Sukam masu tsaro sai dariya suke. Lungu shiru dama ba’a fiye bi ba sai dai idan kana nesa ne kana sauri. Dayaga tafa iya dambe sosai kamar Mike Tyson saiya umurce daya yazo ya kama mashi ita. Haka ya riketa ta baya shi ya samu kwance skirt din. Gabansa ne ya fadi dayaga tana al’ada. Aduniya ya tsana abin saboda ko yanmatan sharholiyar sa yagani zai kaurace masu harsu dena. 
Baya yayi kansa ya hau zafi, Sukam yan iska biyu suna mamakin meyasa ya tsaya. Haka 
yayi yunkuri zai cigaba amma ya kasa. Nan ya sharara mata mari kyawawa guda shida saiya wurgar da ita. “Muje kawai” yace masu suka barta. Da sauri ta mike ta gyara kayan jikinta kana ta koma kan titi kafin ayi part 2 da ita. Allah kawai take gode mawa saboda shiya kubutar da ita. 
Ammi Hadiza tana bakin gado tana shafa mai, yau wani dadi yake ratsa ta. Wayanta ya soma ruri da azama ta dauka. “Nagode sosai Habu nasan ka cika aiki” tace cikin murna. Yadda yaga tanayi kawai ya kasa gaya mata gaskiya “eh Hajia tura min kudina” 
“Karka damu gobe zan kawo maka har rumfar ka” daga nan sukayi sallama. Bayan nan da wajen 30mins Haske ta shiga gidan. Kana ganinta farau farau kamar kazar mayu duk ta susuce. Abin ya tabbatar ma Ammi matsalar ta yazo karshe. Gidan Zailani zai koma daga ita sai yaran cikin ta. Wannan kenan! 
A kwana a tashi har anyi mobilizing dinsu Haske inda sunje sunyi online registration nasu thumb print da cika green slip dinsu. Har Daddy ya bata kudi inda ta soma siyan su farin takalmi, wando da riga wanda zatayi amfani dasu idan anyi posting dinta. Wannan Karon Ammi duk motsin Haske yana Idonta. Kawai ranta ya bata tana dauke da juna biyu. An sake dawowa bakon Haske wanda yake zuwan mata da ciwo da kasala. Sannan dama yana zuwan mata da amai wata sa’in. Ammi taje wajen mai duba tace mata tabbas akwai mai ciki a gidan. Idan ba ita bane to fa Haske ne. Abin yayi mata armashi saita bata dubu saba’in na aikin da zatayi akan Zailani idan yaji labarin. Nan ta bata turaren wuta Wanda zata rinka amfani dashi idan ya turaru a kwakwalwar Zailani shikenan. Ran Lahadi Haske tana masu kosai da kunun tsamiya. Anisa yan rigima sun motsa bataga kayan wasanta ba. Nan tayita kuka mai takaici dole a duba mata bola kila yana wajen. Har chocolate Ammi ta bata amma taki shiru. Gashi suna zaune suna kallon Telemundo ne. Daddy na daga chan kurya wajen Bookshelf yana karatu abinsa kafin kalaci. Ita kuma Fijr ana danna waya ana yatsine. ‘ “Fijr kije ki duba mata mana” Ammi tace. Ko kallo batayi ba tace “Wallahi babu wanda ya isa ya tadani, ina kallon fada a wani group kuke so na bari…. Dankari” saita sake gyara kwanciya. Ita Anisa anata kuka har saida Daddy yayi magana. “Wai me yarinyar Chan keso ne?” 
“Wallahi bola takeso a raka ta gashi kuma Shamsiyya tana aiki” ”Aiba Shamsiyya ta haife taba, please kiji da yarki tana damuna” 
Haka Ammi ta tashi tareda dungure ma Anisa kai, “rufe min baki tunda na tashi” tace a dikilce. Suna wajen bolan ana bincike sai ga pregnancy test tube sun gani. Haba da sauri tayi wuf ta dauke to koma ciki, Anisa na magana akan basu gama ba ko ta kula ta. “Shamsiyya…. Shamsiyya ….. Dan ubanki kina ina?” tace da karfin tsiya. Ita kuma Haske tana dandana kosai, ashe akwai wanda bai niku ba saita tauna danyen wake. Nan ya tada mata zuciya taje sink tana kakarin amai. Abin yazo daidai Ammi tana shiga. “Wayyo jama’a Shamsiyya tayi cikin shege” ta sake fadi. Da sauri Daddy yabar inda yake domin yaje ya warware Ammi. Koda zasu rabu ne sai dai su yi. Ita kam Fijr gabanta ya fadi tabi sahunsa tana raba ido. 
“Hadiza ki fita a idona, wallahi zan saba maki” 
“Toh aiba karya nayi ba, gashi na kamata tana kakarin amai” 
“Ammi daga na tofar da abu shine ciki?” tace cikin kuka. Sharara mata mari tayi wanda ta dade batayi ba, “Zan bibbige ki yar iska, baga pregnancy stick dinki ba ko ance ban iya karatu bane“ saita nuna masu. 
“wallahi wallahi… Ba…. Wallahi ba nawa bane” tace dakyar wanda zufa ya soma karyo mata. Nan ta fashe da kuka wiwi mai tsuma rai. Saita durkusa kasa. Daddy idonsa ya cika fal da hawaye, “Da gaske ne shamsiyya’!” 
Kam ta amsa Fijr ta capke, “Ammi, Daddy… Wallahi karku yarda da bakin shamsiyya. Duk unguwa ansan halinta banda ku. Asalin gantali takeyi. Ko KASU ance tayi kaurin suna, dabin ofishin malamai ta samu ta gama… Duk kawaye na a kasu suka gaya min” Ammi taji dadin shedan nan wanda tayi ma Fijr alkawarin 10k anjima cikin ranta. 
“Innalillahi na shiga uku nijikar Aisha” Ammi tace tana kuka tana tafa hannu, “Wai Ace Shamsiyya yarinyar Alhaji Zailani tayi cikin shege, wai ace duk san dayake maki kika take. Bai hanaki shiga makwabta ba amma shine kike so ki hana shi” saita fashe da kuka itama. 
“Wallahi tallahi banida ciki… Wallahi wallahi wallahi” ta rinka fadi. Duk ta tsure tasusuce. Wai yau ita ce ake mata lakabi da ciki. Ita kuma Fijr abin yazo mata daidai. Gwara tayita zugawa saboda idan aka gane ita keda ciki zata ci kwal ubanta. 
Saurayin ta lsi wanda take tunanin aure ya dirka mata. Bama abinda yake bata haushi ba kenan face wai yayi mata duka tareda fatali da ita sanda ta gaya mashi. Haka ya bita titi yana duka saida yan unguwa suka ‘taimaka mata. Nan yayita kiranta karuwa yana tsine mata. Dadin abin ba unguwar sarki suke ba yasa babu wanda ya sani. 
Dama in dai duka ne ba yau ya saba mata ba, abu kadan yana faruwa zai mata lis ya kore ta, itace zatabi abokai su bashi hakuri. Dama yayi warning dinta karta kuskura ta dauki ciki ko tasha madaran mamaki. Shi baya san yara. Babu abinda bata mashi da su wanki, Shara, dafa abinci etc. Amma dukda haka yakusan kashe ta. Shi yaso ya zubar ne saboda naushi da hambari yafi auna mata. 
Yanzu haka ta tura labarin ta Instagram irin shafuna mai tattauna matsala akan yadda zata shayo kan lsi ya aureta. Daga masu tsine mata sai masu kiranta dabba. Dayawa sunce batada hankali wai saurayi tun a waje yana dukan ka balle idan ka shiga gidan. Ita kuma jinsu take saboda saita aure lsi. 
“Wallahi Daddy yasa bana shiri da Haske, kullum muna cikin fada. Zakaga kullum bama jituwa. Nasiha nake mata amma takiji. Sai tayitajin haushi na. Nasan asalin halin Haske. Sau nawa zata gantala gidan samari. Kune kawai kuke tunanin mutumiyar arziki ce” Fijr tace tana kukan munafunci. Dama Haske kila idan an koreta akwai wanda zai dauke ta. lta kam kakarta na Zaria sunyi watsi da ita sunce karta sake dawowa saboda batada kunya. 
Kuma cousins dinsu da dama basu santa,ba balle Ammi batada wani fara’a balle yan uwa suyita zuwa gidan. Sau nawa za,a zo daga Zaria ta hanasu abinci tun safe har yamma idan Daddy baya nan. Haka zasu zauna farfajiya suyita shan ruwan famfo. Da suka gaji suka dena zuwa. K0 sha’ani idan basuda kudi bata zuwa. Daddy ne kawai yake zuwa kusan sati biyu amma bamai zuwa nasa gidan. Bama yan uwan Daddy ba harta nata. Tun sanda iyayen ta suka rasu shekaru da dama ta yanke da sauran yan uwanta. Duk a ciki mijinta yafi kudi sai kwara daya wanda ta dareta ita a US tayi aure Hajia Binta. Kila Haske tanada wajen zuwa idan an koreta. Ita kam Fijr banda nan sai dai titi kowa gudunta yake. Dan kowa yayi 
shedan ita annoba ce. 
Kuka Shamsiyya takeyi amma banda zagi ba’a binta da komai daga Ammi har Fijr, shi dai Daddy yayi shiru bai ce komai ba. Gashi Imran baya gida balle yaji ta bakinta. 
“Yanzu abinda zaki saka min dashi kenan? Menene kike nema da kika rasa? Wani irin so kike nema Dana hanaki? Ko tausayi na bakya yi abinda zan shiga akan wannan abu? ldan aure kike so kinsan ni mai maki ne amma shine kike bi wannan hanyar” 
“Daddyn Fijr kawai dole tabar maka gidan kafin mutane suce kai mutumin banza ne” yayi shiru yana saurare sai kuma ya aminta da zancen. 
“Kibar min gidana Shamsiyya, karki kara dawowa. ldan kika kuskura kika je gidan wani amini na ko yan uwana Allah ya isa tsakani na dake. Ki rufawa kanki asiri tunda ban tsine maki tukun ba” 
“Aida ka karasa tsine mata tunda me yayi saura saita fada bariki da kyau” Ammi tace. 
“Dan Allah Daddy kar kayi haka, wallahi karya ne banida komai. Daddy ana so a rabamu kuma shine zaka yarda. Don’t you trust me. Nice Fah, Shamsiyya dinka… Dan Allah Daddy ka duba mana” tace tareda rike masa kafa. Da sauri Ammi ta fincike ta kafin takai ta bata mata wasa. Taga kamar abin bai gama kama shi ba. Duka ta somayi tana zaginta. “Alhaji barni da ita kawai ka koma daki, kafin ka fito ta tafi” Haka ko aka yi ya tafi. 
“Fijr muje mu kwashe mata kaya” sai suka dunguma suka tafi dakin. Nan suka kwashe komai suka rinka sawa a jaka. Har Fijr taje dakinta ta dauko Ghana must go domin a zuba wasu kayan. Komai tas suka kwashe kamar anyi shara. Ita Haske batasan abinda ake ciki ba. Tana durkushe a kitchen tana kuka tana tunani. “Allah ya isa idan kika je gidan wani nawa” abin ya rinka dawo mata. Saita yanke shawara zata wajen dangin Ammi tunda ita bata tsine mata ba. Fincika taji anyi mata anata figa. Tana turjewa amma Fijr tafi karfin tunanin ta. Asalin kakkarfa ce. Chabas ta janye ta sai wajen Gate. Su Baraka da Anisa suna daga gefe suna kuka. “Dan Allah Ammi kiyi hakuri ki kyale Anty” Baraka tace. Ko kulata babu Wanda yayi. Sun fitar da ita bakin titi sai ga masu kwasan bola irin yara da bare. Nan Ammi tace su dauke kayan suyi chan bus stop sai su dawo su karba kudin. Gashi ko mayafi batada. Allah yaso Abaya kejikinta da kallabi. 
Harsun soma tafiya Ammi ta aiko Fijr ta sheda mata idan taje wajen dangin ta Allah yasa kuma sai tayi mutuwar wulakanci. Haka ta tsaya sororo tana neman tudun dafawa. Wani gagarumin hadari ya soma haduwa ana yayyafi. Nanfa masu baro suka juye mata kayan suka taho a sittin sabida nauyi basa gudu da kyau gashi titi yayi empty babu kowa. Ruwa akeyi kamar da bakin kwarya wanda har tureta yake yi tana baya baya saboda babu auki, tana kuka tana neman agaji amma babu wajen zuwa. 
Haka ta soma Kokarin hada kayanta dadin abin babu gutsul gutsul. Ta faraja kenan ta zame ta fadi wanda har ciwo taji. Gashi tana al’ada jini sai zuba yakeyi yana bin ruwar jikinta. 
Sauri yakeyi sai aka fara ruwa wanda dole ya rage gudu, yana tafiya sai yaga wata tsomo tsomo cikin ruwa. A yanayin sa bai dame Shiba. Amma ganin yadda ta zame ta fadi yasa yadan tsaya. Reverse yayi ya koma wajenta. Da sauri ya fita sai yaje boot da gudu ya dauko lema makeke. Anan yaje ya tsaya saman kanta wanda sai a lokacin ta lura da shi. “Maimakon ki fake sai ki flto cikin ruwa?” yace cikin dari wanda har sanyi ya soma daminsa. Sandarewa tayi wanda yafi nada. Badman Bilal kenan. Yayi kaurin suna a lnstagram. ldan kanayi to fah saika ga hotonsa koda baka san sunan saba. Duk shafuna na Arewa suna yawaita sakawa. Yaro da kudi abokin tafiyar manya. 
“Ina zakije ne ?” yadda ya fada kasan ya soma jin Haushi. Da sauri tace Unguwar Shanu watau gidansu Laila ta ayyana a ranta. ldan itama ta koreta babu damuwa dan ubanta ma yayi balle wata kawa. Shiya tayata daukar kaya ya saka boot sannan bai damu da yadda duk ta jike zata jika masa mota ba. Besides motar ma tayi datti dole a wanke kafin ya sake hawa. Sannu a hankali tayi masa kwatance har suka isa gidan Laila wanda ya sake fitar mata da kayan. 
Abinda ya bata mamaki da Bad shine halinsa na ko’in kula. Kwata kwata ko kallonta bai sake ba. Bai kuma tambaya daga ina take, ko kuma sunarta.ba Sannan kuma bai karba lamba dinta ba kawai yayi tafiyar sa. Anan ne ta yarda duk yadda ake zuzuta girman kansa to abin yafI haka. 
A hankali ta shiga da kayan ciki, su suna daki ita keta shige da fice cikin gidan. Motsi suka ji yayi yawa sai Baaba ta leka tagani. Shamsiyya tagani duk ta fota hayacinta ga kaya ninki ninki. “Assalamu alaikum” Haske tace tareda shiga dakin. 
“Wa’alaikumus salamu” kowa ya amsa. Hawaye kawai takeyi. Kowa yasan meya faru. Yanzu batada muhalli. Anan ta labarta masu abinda ya faru yau kap bata rage komai ba har inda Bad ya kawo ta. Baba na kan kujera yanata tunani. Sai yayi ajiyarzuciya yace, “Komai mai wucewa ne Shamsiyya, dan adam ba abin wulakantar wa bane. Kome kuma ya faru dake daga Allah ne. Allah bazai bama bawa abinda bazai iya dauka ba. Kuma a Hakan akwai wanda kika fisujin dadin rayuwa. Kiyi hakuri da yadda taki kaddarar tazo maki” shiru yayi saiya cigaba. 
“Banida komai Shamsiyya, noma nake yi. Ko gidan nan haya nakeyi. Amma zan rike ki. Bakin da Allah ya tsaga bazai hana shi abinda zai ciba. Zan kama maku hayar dakin zaure tunda babu kowa. Kuyi hak’uri dashi keda Laila. Nasan banida kudi amma kuma zan rike ki tsakani da Allah. Zan kaunace ki tsakani da Allah. Bakasan wa zaiji kanka nan gaba ba. Kiyi addu’a ki gama da duniya lafiya. Duniyar kwara nawa ne, idan akayi hakuri wata rana za,a barta. Lahira ake nema. Akwai wanda iyayen su duk sun rasu kuma babu abinda suka rasa a duniya balle ke naki sune suka guje ki, karki damu komai lokaci ne sabida wata rana sai labari ” anan ya tsagaita. Haske, Gwaggo da Laila duk kuka sukeyi. Tunda daga ranar Haske ta koma zaman gidansu Laila kamar yar gida. 
Kashegari Haske ta shirya tsab domin taje gidansu. Duk addu‘a dinta bai wuce sun yafe mata ne. Koda taje bataga Fijr ba, lmran yana University lta kuma Baraka tana Boarding. Duk Anisa wanda take da 6 yrs ta labarta mata. A falo ta iske Ammi, zaune take cikin wani tsadenden lace mai furanni da kalar toka. Daurin ture Kaga tsiya tayi tana kallon Zeeworld. Sallama Haske tayi inda suka soma kallon kallo. Wannan kenan! 


To jama‘a munji labarin Haske da dalilin zamanta gidansu Laila. Yanzu zamu dawo labarin gadan gadan yadda zasu cigaba bayan haduwar su da Ammi. Shin Haske zata samu rayuwar aure mai kyau koko shima kamar na yarintar tane? Ya Laila zata kasance da shirin samun kudin biki? Ya rayuwar aurenta zai kasance da Saif? Meye labarin Bilal? Ku rinka hakuri dani sannun a hankali dukzan amsa maku duk wani tambayoyin ku. Nagode da kulawarku. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]