[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE

CHAPTER 5


Wacece Haske?

Hafsat da Hadiza tagwaye ne daga cikin yara goma na Alhaji Abideen. Komai nasu iri daya daga halitta zuwa yadda suke saka tufafi Mahaifiyar Alhaji Abideen asalin yar garin Misra ce kuma tanada jini mai karfi wanda yasa kusan duka zuri’arta akwai bala’in hasken fata ir’m na larabawa.
Dukda ana samun sabani tsakanin harshe da hakora amma su Hafsat basu fiye fada ba suyita tashin hankali kamar yadda sauran tagwaye suke, koda sunyi sai dai na kuruciya. Kansu a hade yake sai dai su taru suyi maka taron dangi suyi maka tas. Kuma basa bambanta kansu, koda Hafsat kace ko Hadiza wanda ke wajen zai amsa maka babu kyashi.
Sanda Hafsat takai shekara goma sha bakwai wani Zailani yaron abokin Alhaji Abideen ya ganta kuma ya yaba da halinta. A cikin tagwayen tafi saukin kai, sai dai kuma baka gane haka saika hadasu biyu a waje guda. Yadda zatayi faram faram dakai ya bambanta da yadda Hadiza zatayi. Sannan kuma Hadiza tafi san gayu, itace ma ta dauki
ragamar zaban masu tufafi da daura masu kallabi idan ta kama.
Lokacin Zailani na shekara 22 da haihuwa ya gama karatun sa na Chemistry kuma ya samu aiki a Abuja Water board. Su kuma su Hafsat ana FCE, soyayya ya kullu tsakanin su mai dadi da tsabta. Sai dai kuma a lokacin hankalin Hafsat ya rabu kashi biyu ne. Ga karatu ga Zailani, lokacin da zata samu suyi hira da Hadiza bai da wani yawa. Balle dama Hadiza tafi miskilanci batada saurin sabo da mutane yasa ma ko kawar kirki batada shi.
Duk wani kawa to fah na Hafsat ne, abin yana bala’in damunta yadda Hafsat tayi watsi da ita. Kuma duk samarin dake zuwa wajenta sam basuyi mata ba. Babu wanda yakai Zailani k0 rabin sa. Tun bata lura ba har karamin kishi ya soma shiganta idan suna tare yazo. Ta rinka fizge flzge tana cijewa, wata sa’in tayi karyan ciwo har saiya tafi. Amma duk abinda ta keyi bai rage ko digon soyayyar suba. In fact abu sai gaba yakeyi har iyaye sun saka baki gadan gadan. An saka bikin Hafsat bayan ta gama FCE.
Anyi tunanin idan aka tsaida lokaci mai tsawo Hadiza zata samu itama wanda takeso ayi biki amma har suka gama babu wani labarin kirki. Haka akayi auren Hafsat da Angonta Zailani inda aka kaita gidanta na Garki. Sannan kuma aka samo mata koyarwa a Government College a wajen inda take koyar da Social Studies.
Shekara ya zagayo har Hafsat ta haifa yarta mai suna Shamsiyya. Yarinya fara sol kamar HASKEN LANTARKI. gatada dan girma sai san barka. Rashin auren Hadiza ya soma daminsu cikin dangi har ta koma makaranta Direct Entry. Akai akai takanje gidansu Hafsat idan anyi hutu, wanda daga ita har Zailani basa binta da komai sai kyautatawa. Haka zata koma dasu provisions kala kala da suturu ga kuma Hafsat duk wata saita tura mata kudin kashewa. 
Kwana ya soma kaiwa shekaru, Hadiza babu wani labarin kirki wajenta. Ita ma Hafsa ta koma NTI domin ta karasa karatun ta na fannin malunta. Haka har Shamsiyya tayi girma tayi wayo sosai, ta tashi cikin kulawa wajen iyaye da kakanni. Balle ma Dangin mahaifinta asalin yan Paki ne a Zaria. Suma suna bala’in ji da ita kamar su lashe. Duk hutu a zaria 
takeyi ta raba kwana gidajen yan uwa. Gata batada matsala sam babu kiwiya. Akwaita da fara’a da san wasa. Ana haka ne sai Hafsat ta sake samun juna biyu. Farin cikin wajen yan uwa ba kadan ba, amma banda Hadiza. Bawai bakin ciki take mata ba. Kawai tsoro ta soma yi lokaci yanata taflya amma ita shiru. 
Wannan Karon cikin Hafsat ya bata wuya matuka tuni an mayar da Shamsiyya Zaria da zama, sai aka ce ma Hadiza ta koma gidansu domin ta taimaka mata da wasu aiki sabida 
kusan kullum sai an kara mata ruwa. K0 periods dinta na makaranta sai da aka rage mata wata sa’in kuma Hadiza taje maimakon ta. Tunda bawai amfani da Hassana k0 Hussaina 
suke ba balle a gane yan biyu ne. Haka zaman su ya kasance cikin aminci baka tabajin kansu dama basu saba ba. Koda watan haihuwar yazo tare sukayi ta siyayya wanda dama Hadiza tafl gayu ita ta zaba komai na yan gayu. Satin haihuwa Hafsa ta ji alama amma batace komai ba. Takan tashi da ciwon baya kala kala musamman da safe koda maraice. Gashi kuma kafarta ya kumbura yayi sukutum kamar doyan Benue. Bata gayama mijinta balle yar uwanta dama ance Expected Delivery Date(EDD) ana yinsa 2 weeks before or after bayan wanda likita yace. Ranar Juma’a sunata kwalema ana gyara kitchen aka wanke duk kwanonin da aka shekara ba’a taba ba. Bayan nan sai Hafsa ta koma daki ta kishingida sai Hadiza zata dafa masu abincin rana. 
Ita Shamsiyya tana chan Paki batasan abinda ake ciki ba. Balle dama Ammi dinta na mata gizo saita rinka ganinta sau biyu. Hafsa bata dade da kwanciya ba taji ruwa yana binta ta kasan jikinta. Nan ta kokarta ta tashi kafin ya gama jika gadon. Tsautsayi ya riga fata sai ya 
zuba akan tiles aikam santsi yaja ta. Nan ta zame tareda fadi rubda ciki. “ 
Hadiza karar ihunta tajiyo mai rikitarwa. Nan ta artayo taga yar uwanta malalejini ya fara tsinke mata. Kukan kura tayi tabi titi a sittin domin a kawo mata agaji. Aikam ta samo na annabi inda aka shigo aka kamata aka tafi da ita. Kuma lokacin babu wayar handset sai telephone wanda ba kowane gida keda shiba wajen 905 ake magana. 
Koda aka kai ta asibiti ta zubar dajini bila adadi, tiyata aka shigar da ita inda aka ciro yaro babu rai sabida yanda ta fadi kansa. lta kamjini yaki tsaya mata saida ma Hadiza ta bata Leda daya amma a banza. Zailani yayi kuka kamar ranshi zai fita. Saboda yana matukarji da ita kuma bayaso ya rasata. 
Haka yayi zaman dirshan yanata rizgan kuka babu abinda ya shalle shi da masu kallon sa. Ita ma Hadiza kukan takeyi saboda Hafsa mutum ce mai shiga rai balle uwa uba mahaifan su daya. A takaice bayan la’asar dab da magrib tace ga garin ku saboda nan ta koma gidanta na gaskiya wanda kowane dan Adam yake zaman jiran zuwa. 
Tashin hankalin Zailani saida ya karu saboda nan take ya zube sumamme. Gashi mutanen Zaria basu san da zance ba gari na rashin waya. Cikin haka ne wani za shi Zaria a daren cikin asibiti shine Hadiza ta roke arziki yaje gidansu ya sanar. Koda Zailani ya farka yayita sumbatu yana fisge fisge kamar tababbe. Saida aka bashi gado aka kwantar dashi 
tareda alluran barci. 
Kamar yadda Hadiza taga rana haka taga dare, tana zaune gefen Zailani zugudum abin duniya yayi mata cinkoso. Kwata kwata ranar bataci abinci ba, sallah kam tanayi tana tunane tunane daban daban hankalinta bayajikinta. Kashe gari da asuba yan Zaria suka dauki sammako suka nufa Abuja. Ko kafin goman safe suna chan, a lokacin Zailani ya farka. Banda hawaye baya komai. Hadiza ta samu taci abinci sanadiyar yar shegiya dake dawainiya da ita ga kuma cikinta yana neman hadewa da bayan ta. Da suka koma gida mutane makil sai suka sake barkewa da kuka. Tabbas ba mafarki bane Hafsa ta rasu. Anyi mata wanka an mata sutura. Yan uwa sukazo suna mata addu’a tareda fatan dacewa a lahira balle kuma ta rasu ranar Juma’a 
Da aka kaita gidanta na gaskiya kashe gari aka tattara karbar gaisuwa Chan zuwa Zaria inda duka yan uwa suke na uwa da na uba. Duk abinda akeyi Shamsiyya bata san abinda ake ciki ba. ldan ta bida uwarta gurun Hadiza take rashewa abinta. Bayan anyi sadakan bakwai sai aka yanke shawara akan a hada auren Hadiza da Zailani balle ma duk duniya babu wanda zai rike Shamsiyya fiye da ita. Aikam yaji dadin abin saboda duk wani so dayake ma Hafsa ya karkata zuwa ga Shamsiyya. Duk abinda takeso shi yakeso. Sannan kuma aka gargade dangi akan yadda Shamsiyya bata ganewa saboda kuruciya a barshi a hakan cewa Hadiza itace Ammin ta na asali. A cikin wata daya aka daura auren su inda lefe kawai ya sake. Sannan kuma duk wani gado na Hafsa daga kayan daki harna sakawa aka barma Hadiza. Tarewa kawai zatayi a gidan aurenta. 
Maman Zailani ta bukaci a bata rainon Shamsiyya idan Hadiza tayi haihuwa na farko saita koma wajen sa duk su zauna. Bazai kyautu ace tana amarya tana raino ba. Zailani bai ji dadi ba amma yasan yau da gobe duk daya ne wajen Allah, wannan kenan! ‘ 
Bayan kusan shekara uku… 
Hadiza bata samu ciki da wuri ba saida ta kusan shekara, bayan nan ta samu ciki inda ta haifa yarta fara itama mai suna Fijr. Shamsiyya takanzo masu hutu amma baya wuce na sati daya. Ko sau daya Hadiza bata taba nuna ma Shamsiyya wani bambanci ba. Kamar ita ta haifeta takeji. Abin kam ya kara mata daraja a idon Zailani da kuma sauran dangi. Saboda ta nuna hankali da sanin ya kamata. 
Ana haka ne sai takarda na transfer ya fito inda zai dawo Kaduna da aiki. Abin bai masa dadi ba wai daga Abuja ka dawo Kaduna. Amma saiya fawwala ma Allah komai tunda shine yasan gaskiya. Lokacin Fijr ta soma rarrafe kuma tadan girma sai Zailani yace ya kamata a bashi Shamsiyya saboda gaskiya yana bala‘in kewarta. Haka kam akayi ta dawo zama dashi sabon gidansu dake Malali Low cost. Sam makwabta basu san cewa ba Hadiza bace matarsa ta farko balle yadda take kamada Shamsiyya kamar an tsaga kara an fito da ita. 
Kaduna Capital School aka sakata Saboda kyansa a lokacin balle su private bawai sun yawaita bane kuma anan ne ta hadu da Laila. lta kuma Hadiza aka samo mata teaching a FGC inda take koyar da Economics. Rayuwar su gwanin ban sha‘awa gidan Alhaji Zailani wanda bana yaje Makka sauke farali da matarsa Malama Hadiza da yaransa biyu Shamsiyya da Fijr. Suna kokarin su kyautata ma yaransu iya gwargwado tareda iyayen su dake Zaria. Sai dai Fijr irin yaran nanne da tun suna yara suke keta da bala’in mugunta. ldan Shamsiyya ta dauketa tayita mintsilin ta tana kokarin shaketa ko kwakula mata ido. ldan ta daka mata tsawa sai tayi ihu kamar ana kashe ta. Haka Ammi zata zo tayita bugun Shamsiyya. 
Sam abin baya ma Zailani dadi, amma kuma idan ance ta ci zalin kanwarta bazai dauka wannan ba. Haka taketa kuka tana karyata wa ace ta koya karya inda zaa mata sabon dukan dole domin wuya ta yarda itace tayi mintsilin. 
Wata rana bayan Ammi tayi dukan da kanta take gasa mata jiki da ruwan zafi. Abinka da farar yarinya jikinta yayi luhu luhu. Bafa Shamsiyya takema wannan iya shege ba har ita Hadiza wahala yasa ta yaye ta. ldan tana shan nono zata damtse hakorar ta dan mugunta. 
Sannan idan bako yazo yana wasa da ita saita kaura mashi mari. Cikin borin kunya Hadiza . . ‘ . . 
zata ce ai batada wayo yarinya ce. Masu hakuri su yi shiru, marasa shi suyita mita akan rashin tsawata mata. Kara tun yana danye ake takwara shi idan ya tsufa zai karye ne. Shamsiyya ta tsorata da yarinyar ainun sai dai idan an bata rainon dole. Wanda shima da duka zasu wanye. A kwana a tashi har Ammi tanada shigar ciki na wata biyu, ita kuma Fijr an shiga nursery a lokacin tana shekara uku. lta kuma Shamsiyya tana primary 2 Tsakanin su shekara hudu ne bambanci. Kullum banda kiran ruwa Fijr bata komai. Ita ce dambace cikin yara gata kakkarfa saidai batada tsawo. Ta chaka ma wani pencil Kota kifar da abincin lunchbox din yara. Ita dai Allah yayita azzaluma tun tana kankanuwa. Ta buwayi kowa ta zama annoba, abin yana bala’in bama Hadiza takaici. Wai ace yar‘ta ke shedanci haka bana Hafsa ba. Wani abin ya soma raya mata kila Shamsiyya take koya mata wannan mugayen dabiu wanda ta tsinta a zaman ta datayi a dangin mijinta. 
Yanzu idan Fijr taso tsiya bayan an hada masu shayi na breakfast saita kabar ya zube a kasa. Nan take kuma zata tsandara ihu tana nuna Shamsiyya wacce ke gefe tayi narai narai da ido. Nanko zata bugu iya buguwa. Tun daga lokacin aka ma fara bama Shamsiyya sharginta tayi. Bata dai mata wani wawan duka gaban Zailani. Saboda abin ya soma damunsa sam ya fita harkan Fijr tinda ta maresa gaban abokan sa dayaje da ita majalisa. Nan ya soma inda inda aka ko watse shi akan rashin iya rike gidansa. 
ldan ya tashi siyan tsira zai bama Shamsiyya da uban yawa ita kuma Fijr zai tsakura mata.. Anan Hadiza zatayi ta korafi wanda ko ajikinsa. Nan zatayi masa diban albarka akan yana nuna bambanci saboda yafi san Shamsiyya tunda Hafsa ta haife ta. Abu kamar wasa Hadiza ta shiga filin yaki da Shamsiyya yayin data soma gallaza mata azaba kala kala. Yanzu batada wata abokiyar hamayya face Shamsiyya saboda yanzu kishi da ita takeyi ainun, duk zaton ta har yanzu Zailani bai mance da Hafsa ba duk da rasuwar ta bayan gata a gabansa a raye. Wannan kenan! 
Abu kamar wasa karamin magana ya zama babba, Ammi ta hana Shamsiyya shiga cikin bedroom dinta saidai takwana daki wanda ta ware mata. Shima dakin anan suke ajiye shargi dasu tsummo kara. Labta mata sharri tayi wai fitsarin kwance ya dawo sabida haka ba dakinta ba. Bala’i suka yi wanda har tayi yaji ta koma Zaria ga kuma tsohon ciki tulele. 
Nan akace yayi mata gado yasa mata labule da kuma ledan kasa. Sannan ya siya manyan basket biyu inda zasu rinka saka shargi ba kasa ba kaca kaca. Abin bai mata dadi ba amma kuma babu yanda zatayi. 
A satin da Hadiza ta haifa danta mai suna Imran yazo daidai da sallamar Zailani daga aiki. Tashin hankali ya shiga sosai amma yayi dangana. ‘ Nan ya shiga fafutuka neman aiki amma abin yaci tura, kullum yana cikin printing CV saidai shiru kakeji wai Mallam yaci shirwa. Gashi dan kudin daya tara ya soma karewa. Kan kace wani abu haryayi wata biyar babu aikin yi. Sannu a hankali Hadiza ita ta soma dauke masu duk wani dawainiya musamman na yaranta najini. Yanzu kam ta bala’in raina Zailani. Zagin sa takeyi uwarka ubanka musamman idan ya hanata kilan Shamsiyya. Su biyu zata zage  ta watse. Kuma idan taga dama su biyu zata hana abinci ranar. 
Wulakanci daban na yau na gobe daban, aiki kuma babu alamar samun sa. Fankama take yi da wani mugun jiji da kai yanzu. Aikam kudin makaranta datake biyan ma Shamsiyya tayi alwashin saita more kudinta. Duk makwabta aka shiga zundenta amma bai dadata da kasa 
ba. Zata labta Shamsiyya duka kamar Allah ya aiko ta ta kashe ta. Ita kuma Fijr yanzu banda kuka cikin dare bata komai, haka zatayi ta tsandara ihu na rashin dalili. Idan Ammi ta gaji ta kaita dakin Shamsiyya dole tayita rarrashi. Sam Fijr batada tausayi ko kadan. Haka zatayi ta fizgo gashin Shamsiyya kuma babu halin kwaba kafin ta labta mata sharri. Yarinyar al‘mura ce ga karya kamar kudin duba sannan kowane kalma da wallahi take binsa. Abin yasa Shamsiyya bata san yara kwata kwata sabida idan haka suke gwara kayi zama kai kadai. Koda a waje taga yaro nesa nesa takeyi dashi bata dauka sai dai idan ya kama. Duk da kaninta Imran ba haka yake ba amma mugun halin Fijr ya buwaye ta. 
Shamsiyya batajin dadin yadda Ammi kema Daddy dinta amma babu halin magana. Ta lura saboda bayada kudin siyan masu kayan dadi ne yasa take masu haka. Sai dai bata ce uffan ba balle tayi magana. Duk ta bushe ta rame tayi fari fat kamar fatalwa. A kwana a tashi har Alhaji Zailani Abubakar yayi shekara shida babu aikin yi. Buge buge yake yi irin na kanzagin yan siyasa yaje yana dan mara masu baya. Wata rana idan yayi wuta ya tashi da 2k. Amma dai kasuwar shi bai wuce na dari biyar ba. Sannan zai samu kuma yaci yayi nat kuma ya kulle ma Shamsiyya a leda.A lokacin Hadiza harta haifa yarta na uku mai suna Baraka. 
Haske ta soma zama budurwa tinda yanzu tana karamar sakandare. Batada jiki ko kadan amma kuma surarta na ‘ya mace ya bunkasa. Anan aka fara kiranta da suna Haske, gashi kuma kusan duka yan layinsu school dinsu daya har yan layi abinda suke ce mata kenan. Har sunarta na asali ya soma bacewa dan Abbanta abokin rahan ta Shima Haske yake ce mata. Laila kam tafi su jiki da balaga cikin jerinsu su da bala’in wuri tun tana firamare kamar yar sakandare. Har samari ta somayi tana fita tadi. Ita kam Fijr yanzu sunarta ya zama “Fijr annoba” kullum iyaye na hanyar kawo kararta wajen Hadiza. Ga masu sana’a suma suna yawan kuka da ita. Idan an tashi daga islamiya taje siyan su goruba, awara, shashaka, gullisuwa ko kalallaba idan yan kanta sun motsa saita shure da kafarta. Gata dama tun fill azal kakkarfa ce balle yanzu tayi mugun kiba kamaryar 15yrs. Ta fuska ne zaka gane yarinta ammajiki kam na manya ne duk tafi  Anan ne aka ma Hadiza shawara ta kaita boarding school koba komai ayi discipline dinta. Nan Hadiza ta yanke zata kaita FGC Kazaure. 
Wata Lahadi haka tsautsayi ya gifta ma Haske, da azahar bayan ta dawo daga kasuwan Sati a kafa inda Ammi ta aiketa cefane. Ammi na zaune akan computer desktop fari mai zungureren baya irin na lokacin. Fijr kam tana kallon Binta and Friends ta hakince kan kujera kuma tana cin goody goody tareda milk candy. Daddy tun asuba ya fice babu wanda ya san inda yaje. Kwana biyu asubanci yakeyi. 
Gidan kaca kaca ba kamaryadda ta barsa ba. Zuwa tayi gaban Fijrta tsaya, “Meye haka bazaki kwashe ledan kayan nan ba kamar baki gani” ko kula Haske batayi ba saida ta sake magana. “Ke badake nake yi ba?” Muryan Ammi sukaji, “Ke Shamsiyya bazaki je ki daura mana sanwa ba kin tsaya zakiyi jaraba? Balle yarinya da gidan ubanta” 
Haka Haske tajajiki a hankali tana tafiya tareda magana ciki ciki, “Nima ai gidan ubana ne” ashe Hadiza tajita aikam nan taji ‘fuuu an figeta. Ba’ayi wata wata ba aka sharara mata mari, kafin ta ankara aka kara mata sai kuma aka tokareta. Nan ta fadi kasa tana rike ciki. 
“Dan kutumar ubanki ko Zailani bai isa balle ke karamar alhaki. Saina tattake ki na taka banza muga karshen rashin kunya” huci takeyi tana nuna Haske wanda banda kuka bata 
komai. “sauri kije ki mana abinci ko ki yaba ma aya zakinta” da kyar ta mike tana numfashi sama sama tareda dafa ciki harta kai kitchen. Nan ta soma wanke wanke wanda dama batayi ba saboda zata kasuwa. Kwanoni da uban yawa ga tukwane wajen 7 kamar ana biki. 
“Dan ubanki baki wanke kayan cikin ba sai ya soma wari?” taji muryan Ammi daga bayanta. Gabanta ne yayi mummuna faduwa saboda ta san abinda zai biyo baya. Idan ana sabo da wahala ita kam tayi. Dundu Ammi ta soma kai mata a baya. 
Garin kokarin kaucewa ta dan tabajikin Ammi. Nan kam ta soma rapka salati wai ‘ta girma zata fara rama dukanta. Muciya ta dauko ta soma auna mata tana ihu amma babu abinda ya shalle ta. Banda ashar bata binta da komai. Fijr ko gezau balle Haske tayi mata magana dazu, haka ta kunna DVD tasa wakar Yahooze tanabi. Imran ne yazo yana kallo yanata kuka. 
Shamsiyya ta samu ta gudu ta koma daki amma kafin ta rufe karfin Ammi yafi nata. Nan ta cigaba da kai mata duka tana zagi. “Shegiya tsinanna, dan ubanki duk abinda nake maki na kyautatawa shine zaki min rashin kunya. Da wata muguwar ne ubanki na rasa aiki zan koreku ku biyu amma nayi ta hakuri daku. Sannan kudin makaranta bana fasa biyan maki“ nan ta kaureta da wani mari wandajini ya soma fito mata ta hanci. 
“Ammi dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan kara ba, ki yafe min“ tace cikin kuka. Ammi sakinta tayi tabi kayanta. Nan ta soma kwasa tana fitar dasu waje. “Yau sai kin bar gidan nan. Kuma wannan kayan konawa zanyi tas” haka ko akayi bayan ta fitar da komai ta kyasta mashi ashana tareda watsa kalanzir. 
Kana ta rufo kofa tabar shamsiyya a wajen. Malale gefen river Kaduna ne kuma wanda yasan wajen yasan akwai bala’in sanyi. Haka tayita zaman jira Daddy ya dawo ko ta samu ta shiga cikin gidan. Bashi ya dawo ba sai 11pm. Lokacin Haske ta rakube a baranda bazaka masan tana wajen ba tana barci. Sam bai san bata cikin gidan ba. Su Fijr da Ammi anata kallon Ultimate search. Ko abinci baici ba yaje ya kwanta. Allah Allah yake gari ya waye yayi ma Haske Albishir ya samu aiki a Hajj Commission. Shine Chairman na Kaduna State. Wannan kenan! 


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]