[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE


CHAPTER 2
Tafsir din Marigayi Sheik Auwal Albani ke tashi a speaker din motar, yana magana akan mutane da suka dauki akidar yahudu da nasara suka rataya akansu babu sassauci. Sannan kuma idan sun bude baki zasuyi turanci sai kaji tausayin su. Wa’azi ne mai shigajiki kuma ga barkwanci, a hankali Haske tadan sakejikinta tana darawa sama sama.
Da suka isa Havilla sai yayi parking motar sa, saida ya gyara zaman rigarsa sannan ya dauko tabaran sa yar yayee ya daura akan fuskan sa Da murmushi ya kalle Haske sai yace, “Muje ko Madam” a tare duka suka fita suka dunguma shiga wajen, abinka da yamma rana ya sauka duk anzo shan iska. Hankalin mutane da dama a wajen ya koma kansu, sunyi ne iya yi. Yadda Bilal ke tafiya cikin izza kasan wani ne wanda kejuya naira.
lta kam Haske ta harde girar sama alamar wannan gayen tane yan mata suje su nema nasu. Kamaryadda rana keda haske ya haskaka waje to haka itama takeda Haske. Duk inda ta shiga saita haska wajen, tanada fari mai dauke ido da fata mai santsi lub lub. Farar mace alkyabbar mata,faran mace sha kallo. Faran mace zinariya, faran mace HASKEN L Faran mace bakya laifi, Faran mace wata mai tsorata taurari. Faran mace mai sanyaya zuciyar mai kallonta. Full option, steering mota san kowa kin wanda ya rasa afuwan ba cin fuska wajen bakake, kuma naku kirarin na zuwa) a Gaba
Sun shiga sunyi oda aka kawo masu, ita Haske Vanilla take so, Laila kuma chocolate shikam Bilal yana shan Smoothie din apple. Bayan sun batar da mintuna kusan arba’in sai suka wuce, bai maida su gida ba illa wucewa gaba kadan Kanti Plus Stores. Shi ya shiga inda ya shiga siyayya kala kala, daga su tarkacen kayan zaki sai su maltina da biscuits. Haka halinsa yake, shi a cewarsa kudi na maganin komai. ldan Kanada kudi ka huta, idan kasha
wuya to bakada ko sisi kenan.
Laila kam kamarzata ara baki dan murna, taji dadi ainun. A duniya tana bala’in san wannan ranar, wai ace Haske Da Bilal sun samu sabani, zai rinka masu dawainiya kenan. Juma’a mai kyau tunda daga Laraba ake ganewa kuma tabbas yau Laraba ne. Taso tace ya siya masu Always da Roll on amma kuma saita fasa kafin Haske tace an kawo masu raini. lta bata ga aibun abin ba kwata kwata.
Daga nan ya mayar dasu gida watau Gidansu Laila dake Unguwan Shanu Layin Tambuwal. Laila ce ta fita domin ta kira su Baraka kannenta su kwashe kayan. Koda suka zo saida ta gargade su akan kar su kuskura su kai dakin Baaba watau mamanta. Bayan tafiyar ta babu wanda yayi magana. Mintuna 15 ya wuce babu abinda sukace. Shi keta danna |Pad dinsa yana dube dube na rashin dalili. Daga bisani ya karkato ya kalle ta.
“Madam fushin ne” yace cikin izgili. Kakalo murmushi tayi tareda fari da ido, “Fushi name kuma? Ni banida riko malam” salta daga girarta sama. Shima murmushi yayi sai yayi narai narai da murya. “Amma baby kinsan ke ce silar komai, bakya min abinda nakeso kuma ga stress din aiki sai nayi losing control nayi maki hauka, ki rinka tausayi na mana”
Batace komai ba, kuma batada niyyar tankawa, asali ma wasa da yatsan ta takeyi kamar bata jiba. Ajiyar zuciya yayi sai yace, “Koda yake ba excuse bane da zaisa nayi maki dibban albarka” ba hankali ta kalle shi sai tayi murmushi, a ranta kuma tace gwara ka sani.
Gyara zama tayi ta kalle shi, kana kallonta kasan babu wasa a tareda ita, “Meyasa idan kamin miss call daya baka sakewa?“ sam maganar bai gamshe shiba kuma kana ganin yadda yayi kasan bazai canza wannan mugun dabi’a ba. “But Sweet kinsan haka akida na yake, kowaye duk duniya na kira bai dauka ba bazan sake kira ba, kada ki fara min wannan rigima” yace fuskar sa a daure
“Kana nufin ban kai ba kenan? Wai tun yaushe muke tare fisabilillahi amma saboda
girman kanka muyita samun sabani. Ni ce zan zama iyalinka fa?A haka zamu rinka abu. Kullum kayita cewa baka ma mace kaza haka ma mace kaza akan mene? Mata basuda daraja a wajen ka kenan? ” mts taja tsaki sai tayi kwafa tareda Kauda kanta. Bai amsa ba saboda ba karya tayi ba. Mata basuda wani amfani wajensa bayan ya biya bukatarsa. Amma Haske tana bala’in kure hakurin sa, yadda takeyi kuma yana binta har mamaki yakeyi. Kowa yasan shi a Kaduna yasan halinsa, shine BADMAN BILAL. Sunar kawai ya isa ya fayyace maka waye shi.
Ba yaro bane, saboda dan 33yrs yafi karfin ace mesa yaro. Amma yana kamada dan 27yrs koma 25yrs. Bayada mako, akwai kashe kudi ma yan mata yasa yayi farinjini sosai. Binsa ake kamar kiyashi amma tunda ya fara soyayya da Haske wata shida daya shude yayi sanyi kamar ba Bad ba. Yanada hayaniya, yanada surutu. Yanada nuna cewa ya mallake wani dukiya ko makamancin haka, abubuwa da dama na alfahari wanda masu kumbar susa sukeyi duk yanayi kamar polo da badminton. Business din gidansu shine canjin dollars ko pounds ko makamancin haka, to yanzu shine ke running business din saboda shine babba.
Yaro da kudi abokin tafl’yar manya. Saidai yanada bala’in fada da masifa, abu kadan ya watse ka uwaka ubanka kamar rainon titi. Ga kuma tsabaragen girman kai, baya daukar darasi k0 nadama musamman idan mace ta nuna mashi rashin gaskiyar sa. Acewarsa mace bata kaiba saboda tana karkashin namiji ne. Sai dai kuma idan yana yayin ki to he is very romantic ya iya watsa kalamai mai ratsajiki yadda ya dace, ga kuma tattali da madaran soyayya. wannan kenan!
“Wai meyasa bakyada hakuri ne, tunda kinsan haka Allah yayini ki kyaleni mana. Halittar Allah zaki canza?” yace cikin masifa. Kallon ikon Allah tayi, bawai dama ba yana bata hakuri bane saboda yaso, a’a saboda kawai su cigaba da soyayya ne. Tattara jakarta tayi saita sakar masa murmushi,“ bari na shiga na gaji please ”
Saida ta bude murfin motar kana tace,” Zamuyi waya anjima, nagode” tasa kafa daya a waje sai yayi wuf ya riko mata hannu. Narai narai yayi da sexy eyes dinsa mai kalan barci, a hankali ya soma magana da bedroom voice dinsa, “Baby am sorry, like for real” kallonta yakeyi wanda ya dagula mata lissafi, a hankali taso zame hanunta amma yaki saki.
“Kalli cikin idona” ya umurce ta. Ta daga ido ta kalle sa amma ko seconds 3 bata yi ba ta sauke, bazata iya ba.
Wani sansa ke kwarara a jikinta kamar garwashin wuta. Tabbas yasan weakness dinta, kuma shine. Yasan cewa bazata iya fushi dashi ba. Karya zatayi ma kanta da zuciyar ta idan tace haka. Abu daya zuciyar ta yakeso kuma bai wuce ta samo Bilal a matsayin miji ba. Idan ba haka ba zuciyar ta zai mata barazanar fashewa. Tasan tayi sakaci data bari ya mamaye ko’ina najikinta, duk wani gabbanta yana amsa sunar Badman Bilal. Saidai kam soyayyar Bilal banda wahala da tashin hankali baya kawo mata komai, baya respecting dinta balle abinda tace. Kawai idan yaga tana barazanar rabuwa dashi saiya rude. Wannan shine mijin jaraba yaki rabuwa da ita kuma yaki faranta mata rai. Amma kuma ba laifin ta bane, so ne yaja mam haka, you don’t choose who you love, haka kurum wani a hanya bazai dagula mata lissafi ba. Dama to fall in love is to be vn. “please ka sake min yatsu na hakura” tace cikin tsoro
“ki kalleni nace” babu yanda zatayi haka ta kalle shi wanda ya bita da murmushi. Sannan saiya sake mata hannu. Da sauri tabarwajen tareda rufe masa kofa. “Haske sarkin tsoro” ya ayyana a ranshi.
Dakin zaure nanne dakin da aka ware masu domin su zauna. dukda suna yara mata bai canza komai ba tunda iyayen Laila basuda wadata kuma ma haya sukeyi a gidan. Haka ta murda hannun kofa kana ta yaye labule saita shiga ciki. Ta tarar da Laila an bude 
shortbread da maltina ana basga. 
Bata ce mata komai ba illa murmushi ta sakar mata tareda daga majuna gira. A duniya tana bala’in san Laila, tafi karfin Kawa a wajenta ta koma yar uwa, komai nata na Laila ne ko ajikin ta. Sam bata kishin ta balle kyashin mata wani alheri. ajiyejakar hannunta akan gado tayi saita fito da wayanta. Kai tsaye wajen extension box ta wuce ta saka charging sannan ta rage kayan jikinta, hijabi tasa ta wuce cikin gida. A kitchen taga Baaba mahaifiyar Laila tana tankade. 
“Ina wuni Baaba mun sameku lafiya?“ Haske tace. Da fara’a Baaba ta dago kana ta share zufa da habban zaninta. “Lau lau, yan mata adon gari” “Kawo na tayaki” Haske ta fada tareda da karba. 
Anan ta tankade garin tas sai tayi talge ta saka a ruwan dake tafasa akan murhu. Baaba ta riga ta gama miyan kuka wanda yasha man shanu da kifi ‘mushen Iagas‘ 
Dukda baci zatayi ba amma, saida ta tuka masu tas tasa a wani cooler kana ta sungumi buta taje bayi ta kama ruwa. Daga nan tayi alwala ta koma daki. Isarta keda wuya taga Laila bakin kofa da alamu itama zata shiga cikin gidan kenan. 
Sunyi sallah magrib suna lazimi da duba waya a tsakani har aka kira isha. Bayan nan saiga wayar Laila ya soma ruri. Murmushi tayi cikin azama ta kara a kunne “Rabin raina” ta fada chan cikin makoshinta. Samun waje tayi akan katifar su ta zauna tareda nade kafa domin taji dadin wayan. 
Daga dayan bangaren shikuma ya soma magana, “Na’am rabin raina kokuma nace ran baki daya, wallahi tun dazu matar nan ta isheni dajaraba yasa na kasa kiran ki” ya fada cikin takaici. lta kam Laila bushewa da dariya tayi na mugunta saita soma magana cikin kissa. “Tun yaushe nace ka saketa kaki, Allah ya kara ni ina ruwana” 
“Haba rabin raina ba haka bane, ki rinkajin ‘tausayi na mana.Wallahi saboda ta haifan min yara uku yasa nake zaune da ita. Nayi bala’in tsananta kwata kwata bata burgeni, gashi tayi uban kiba. Kinsan har dariya abokai na keyi wai matana kamar yayata” haka dama yake, kullum zai kira Laila yayita aibanta matarsa gabanta, itakam daga zuga shi sai dariya, su zauna suyita kwashe mata albarka. Kullum hira su baya wuce kaza kaza da matarsa tayi mashi. 
Kwafa Laila tayi saboda bataga dalilin dayake zaune da ita ba tunda ya tsaneta. Sannan kuma tana ganin laifin matar, saboda da ita ce suka cika fada da miji wallahi zata bar auren tunda ba’a dole. Yanzu jira takeyi ya tura magabatansa ayi aurensu, saita nuna ma matarsa cewa bata iya rike miji ba. .
Laila ta gama wayanta da Saurayinta Saifullahi cike da annashuwa. Ta fara gajiya da nokewan dayake yi. Kullum tayi hakuri yau zai tura wajen iyayenta. Abin ya soma damunta. Shikam Chemist ya wuce domin ya siyan ma yarinyar sa magani. Sadiya yar wata bakwai 
batada lafia Shine zaije ya siyan mata Coflin wanda mura ke damunta. Koda ya siya saiya hada da biredi bugun Kato dasu maradan three crown na gwangwani. Sai lemu da ayaba tareda dabino domin yakai gida. Matarsa Sameera tana zaune a falo rungume da Sadiya tanajijiga ta. Sannan kuma tana yi tana gage mata majinan dake kwararo mata. Sallama yayi saiya yaye labule kana ya shiga. Fuskan ta babu yabo babu fallasa ta amsa mashi. “Munata jiranka tun dazu jikinta sai zafi yakeyi” tace mashi. 
Bai ko kalleta ba ya amsa, “Mai chemist ne baya nan saida naje bus stop” ya zabga karya wanda babu inda yaje waya yake da Laila. 
Da kanshi ya tsiyaya ma Sadiya maganin ya bata, sannan ya bare mata ayaba ta soma ci. Abinka da yarinta saita mance tana ciwo sai basga takeyi. Shi kam bayi ya wuce wanda ya raba tsakanin dakinsa da dakin Sameera. Tunani yake fal yanda zai bullo da maganar aurensa da Laila. 
Idan yace Sameera tana masa wani mugun abu toh wallahi ya zalunce ta, tanada bala’in tsabta ga sanin ya kamata. Ko kudin cefane bai kaiba zata cika da kudinta domin abinci ya kara armashi. Kawai dai shi yaso aure ne. Gashi tana bala’in girmama dangin sa duk wani sha‘ani saita bada gudummawa. Suna bala’in Santa kuma yasan bazasu mara mashi baya ba. Tunani ya fado mashi yaje kauye wajen kanin mahaifmsa ya mashi siyasa da kudi sannan sai ya wakilce shi, balle dama babansa ya rasu. Wannan kenan! 
~~~~~~~~~~~~~~~~ ~~~~~ 
Yanzu dai labarin ya fara bayyana. Haske, Laila, Bilal, Saif da Sameera kowa halinsa ya fara bayyana. Toh ya zasu kasance, a cikin wannan labari. Sannu a hankali ku biyoni dominji. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]