[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 31 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA


CHAPTER 31

Karkarwa jikinta keyi, yayin da take dukkan gabbanta tamkar ba a akmjlkinta suke ba, tsananin zazzabi dake cizonta. Tana cikin wannan halin Dije ta shigo. Ganin Hafsa da tayi kwance ya bata gaggawar isa gare ta. “Ranki shi dade jikin ne haryanzu?”
Kai Hafsa tajinjma tana kwararan hawaye.
Aunty me zai fada a isar da sakon ga maimartaba tun da dai haryanzu yeriman bai dau wani mataki a kai ba?” Hafsa ta dakatar da ita.
“Bana so zancen yaje wa maimartaba kuma a karshe Yerima yaga laifina a kan na kai kararshi wurin mahaifinshi. Don haka zan ci gaba da dawainiyar ciwon nan harin samu sauki.”
Dije ta share kwallanta. “Ranki shi dade akwai kudi a hannuna, ni zanje asibiti na samo miki
maganin zazzabi. Babu yadda za a yi ki zauna da ciwo.”
Hafsa ta rikewa Dije hannu. “Ki barshi…” Bata kai aya a zancen nata ba amai yayo mata gaba. Baki daya a jikin Dlje tayi shi. Ga tsananin galabaita da tayi. kasantuwar babu komai a cikinta. Haka ta rinka yunkurin amai tamkarza ta harar da kayan akinta. A wannan halin sukaji kamshin turaren Jiddah. Cikin takunta na Kasaita ta isa inda suke cike da
mamaki tana kallon Hafsa dake ta yunkurin amai. “Amai?“ Ta ambata a fili hannunta bisa haba alamun mamaki. “Ke! Tun yaushe ne take wannan aman? Dama bata da lafiya ne? Meya same ta?”
Duk ajere Jidda ta saka wannan tambayoyin tana kallon Dije. Ba wai damuwa tayi da ciwon na Hafsa ba. Kawai al’ajabin abun ne take yi, harma ta rasa abun cewa, baki daya kanta a daure yake.
“Uhmm… Ni ma dai ban sani ba. A haka nazo na same ta.” Dije ta bata amsa cikin rawar murya. Saboda tana bala ‘in tsoron Jiddah. Ta san halinta bata da wasa in dai wurin karta rashin mutunci ne.
Buuuuuu! Jidda ta fice daga dakin ba tare data sake cewa k0 uffan ba. Kai tsaye dakinta ta dosa. Ta rafka uban tagumi tanajin sintirin hawaye a bisa kumatunta. Allah dai yasa kar zarginta ya tabbata. Matukar ciki ne ajikin Hafsa kashinta ya bushe. Ina! Ba ma zata taba sabuwa ba, bindiga a ruwa. .
Da gaggawa ta dauki wayarta ta Iatso kiran mahaifiyarta. Har ta tsinke ba a dauka ba sannan aka kira ta. Da kuka ta dauki wayar. “Momma wallahi akwai matsala. Akwai babbar damuwa.”
A kidime mahaifiyar tata ke tambayarta abinda ya faru Clkin kukanta tace “Momma bisa ga dukkan alamu abokiyar zaman nan nawa juna biyu ne gare ta. Ya zanyi? Taya za ai ace ni dana shekara biyar tare da Yerima Bukar ban samu Clki ba sai wacce tazo watanni uku ko hudu da suka gabata?”
Cikin mamaki Momma tace mata “Ke ya aka yi kika tabbatarda tana da cikin? Hasashe ko dai kina da tabbaci ne?”
Gyada kai Jiddah tayi. “Momma alamu ne suka nuna hakan. Duk da ban san mai ciki ba
amma yau na gane a warin Hafsa. Tabbas ciki ne da ita.” 
“To naji, ya isa ki daina kukan haka nan. Ba dai halhuwa ce ba kya so tayi  ba to Ina mai tabbatar miki da in dai harba ki harhu ba Ita ma kishiyarki ba zata taba haihuwa ba har ta mutu. Alkawari ne na miki.” 
Duk da haka dai hankalin Jiddah bai kwanta ba. Clkin kuka tace “Momma ki tabbata kin cika min wannan alkawarin. Wallahi idan har Hafsa ta haihu ba zan taba yafe miki ba.” Ta kai karshen maganar hade da yanke wayar. Babu irin kiran da Sarauniya Maimaunatu bata yiwa ‘yarta Jiddah ba amma taki dauka. Ta san halin yarta sarai. Raini na gidan duniya tayi mata shi. Ita ce ‘yar autarta a cikin yara hudu data haifa. Sauran duka maza ne, sai ita 
Jiddah. Ta dauki soyayya ta gidan duniya ta dora mata. Hakan yasa ta tashi fitsararra, har uwar tata ma bata raga mawa. ” 
Cikin kwantar da murya Zabbau ta ce, “Ranki shi dade, hala ba kiji zancen na Hausawa ba? Abin da suka ce Aure yakin ‘yanmata. Tabbas kuma hakan ne. shine zai sa ka haifi ‘yarka da cikinka, ka raini abarka har ta girma, amma kwatsan sai wani yazo ya raba ka da ita. Tabbas babu dadi. Amma hakuri ne kadai magani. Domin kuwa wannan aure shi ne daraja
da mutuncinsu.” Har ta kai aya Kursiyya bata ce mata ko uffan ba. Sai dai bata cire tagumin da ta rafka ba. 
“Ranki shi dade, yau kimanin watanni uku da mako biyu ke nan da Hafsa ta shiga lalle, amma haryanzu kin kasa daina tunaninta. Na sani akwaizafi, amma ki daure. Da haka zaki saba. Dukkan iyaye sunji irin wannan radadin yayin rabuwa da ya’yansu. ” 
Sai a sannan Kursiyya ta murza idanuwanta. Tace, “Zabbau. Haka kawai na kasa samun kwanciyar hankali a rayuwar auren Hafsa. Babu wanda ya fada min, sai dai kawai jlkina yana ba ni komai zai iya faruwa. Saboda ba wanda Hafsa keso bane aka aura mata. Abun haushi da takaici ma wai ashe mai mata ne. Gashi tun tale tale ban koya wa Hafsa yadda zata kwatar wa kanta fansa ba. Komai ni nake daukan mata, nake shigan mata. Yau gashi naga illar hakan. Ya zata kare zama da kishiya?” 
Zabbau ta muskuda hade da dan matsowa dafda Kursiyya. Tayi kasa kasa da murya cikin salon gulma da munafurci. “Ranki shi dade, me zai hana mu kai wa boka Fartsi ziyara.’ Dama kin ga munjima ba muje ba. Idan munje saiya bincika mana halin da Gimbiya Hafsa take ciki. ldan ma akwai wata matsala sai ya daidaita ta. Koya kika gani?” 
Murmushin gefen baki Kursiyya tayi. Saima yanzu abun yazo mata. Dacan bata taba kawo ma ranta zuwa wurin boka Fartsi ba, saiyanzu da Zabbau ta bata shawarar. 
“Kina da kyauta mai tsoka Zabbau. Tabbas kin cancanci kyautar dan maraki da turame bakwai. Kina fita ki turo mini Firdausi. Daga nan kiyi shirin tafiya kafin azahar.” 
Takaitacayar guda Zabbau ta saki. Tana mai tsananin jin dadi kyautar da KurSIyya ta alkawarta yi mata. Mikewa tayi ta fita. Sai data fara turo Firdausi sannan ta wuce can bangarensu, ta nufi nata dakin murna fal a ranta. 
Wuraren shabiyu na rana Zabbau ta shirya tayo dakin Kursiyya. Ta same ta ita ma din ta shirya, tsananin kagara har mayafi ta yafa Zabbau kawai take zamanjira. Sai da ta sauke 
ajiyar zuciya najin dadi sannan ta mike. Dama ta isar da sakonta ga mai martaba, kai tsaye mota kawai suka nufa hade da barin masarautar. 
A gaban boka Fartsi suka bayyana. Ya shafi gashin gemensa sannan ya dubi Kwsiyya. “Me yasa akai yi auren ba tare da an shawance ni ba?” 
Cikin rawar murya ta dukar da kanta kasa tace, “Bada saninmu ba aka yi Boka Fartsi. Mu din ma bamu san komai ba har sai da aka riga da aka daura auren. Ba da shi muka so ba. ” Boka Fansi ya sauke ajiyar zuciya. “Yarinyar tana cikin damuwa. Daga mijinta da kuma abokiyar zamanta.” ldanuwa Kursiyya ta fiddo waje hade da daga kai ta kalle shi, gabanta na tsananta duka. 
Matsalar taje inda ta hadu da gabanta. Kafin komai, zanso ki fara zuwa kiyo bincike kiji wace ce Sarauniya Maimounatu? Kiji komaigame da ita sannan ki dawo inda nake. Na baki kwana biyu kafin ki dawo.”
Ba haka taso ba. Taso ace kai tsaye kawaiya magance mata matsakar ‘yarta, shine babban abin daya dame ta ba wai sanin wata mata ba. don babu abinda zata karu da shi. Haka ta mikejiki sabule, Zabbau ma ta mike. 
“Kar ki dauki hakan a matsayin wasa Kursiyya. Ki tabbata kin yi binCIken nan sannan ki dawo. Ina nufin komai ki binciko a kanta.” 
Ta rasa gane madosar zancen nashi. Bata san amfanin aikin da ya saka taba. Wannan shi ne karon farko da boka Fansi ya taba yi mata irin haka. Me yasa? Me ya alakanta hakan da damuwar Hafsa? Shin wace irin mata ce wannan? Bata da amsoshin kafvtambayoyin da take wa zuciyarta. Hakan yasa ta fara ajje takunta, Zabbau na mara mata baya har suka fice daga gidan. 
Tun da suka bargidan babu wacce tace wa wata ci kanki. Sai dai Zabbau ta karanci yadda yanayin Kursiyya ya sauya a Iokaci kadan. Duk waccan damuwar ta kewar Hafsa ba ta kai ko da rabin wannan data shiga a yanzu ba. Tana son yi mata magana amma tana tsoro. Hakan yasa ta kama bakinta tayi shim, har suka isa gida. 
“Zabbau, ki same ni a daki bayan minti talatin.” Kai kawai Zabbau tajinjina hade da kama hanyar bangarensu. 
Kursiyya ta fada a bisa gadonta. Tama rasa abm da za tayi ita kam. Wani irin daci da radadi takeji zuciyarta na mata. Da kyar ta iya samu tayi wanka, babu batun sallah kawai ta koma ta kwanta hade da rufe idanuwanta. Ba wai barci takeji ba, sai dai hakan ne kawaizai sata dan samu sassauci. Tana cikin haka taji isowar Zabbau. Kanta ta dago ta kalle ta sannan ta mike zaune. 
“Ranki shi dade ga abincinki can an ajje miki, ba kici komai ba tun karin safe. Ki daure ko kayan marmarin ne ki sha.” 
“Ba najin komaizai iya shiga bakina a daidai wannan lokacin Zabbau. A gabanki baka Fartsi ya fada mana halin da ‘yarlelena take ciki. A gabanki ya kasa magance mana komai sai ma wani aiki mara amfani daya sakamu. Nifa ji nake tamkar ma kar inyi.” Zabbau tayi saurin tarar numfashinta. “Ranki shi dade daurewa za kiyi. Inaji a jIkina a nan warakar take. Tun da haryace kiyi bincike a kanta, na tabbata akwai amfanin yin hakan. Daurewa za a yi. ” 
Kursiyya ta gyada kanta. “To ta ina zan fara? Wama nasan zan tambaya? Ni dai kam ban san taba. Ban ko tabajin sunanta ba saiyau din nan.” 
Shiru jim… zabbau tayi kafin ta murmusa. “Akwai shawara ranki shi dade” A kagare Kursiyya ta kalli Zabbau hade da fadin, “Ke nake sauraron Zabbena.” Dariya Zabbau ta kyalkyace da ita. “Ranki shi dade yau kuma canza min suna ake yi?” Kursiyya tace, “Ke dalIa can sunan kauna ne. Tsananin sonki da nake ne yasa sunan kawai ya fado min. Yanzu dai fada min, mece ce shawarar takl?” “Na tabbata mai martaba ba zai rasa saninta ba. Abinda za kiyi shi ne, kawai ki tinkare shi da maganar. Ki tambaye shi wace ce Sarauniya Maimounatu? Kuma meya sanigame da ita?” Shirujim, Kursiyya tayi, kafin tace, “Ina yawanjin sunayen sarakuna a bakin maimartaba, amma k0 da wasa ban tabajin irin wannan sunan a bakinshi ba. Bana tunanin ma ya santa.” 
“Ehh to, kuma fa haka ne. Bari kafin safe nayi alkwari zan sama miki mafita ranki shi dade, wacce za kiji dadinta sosai. ” 
Fuska Kursiyya ta bata, don ita kam a yanzu taso ace sun sama mafita. Sanin cewa Zabbau nada zurfin tunaniya ysa ta barinta harzuwa gaben. 
Zabbau na komawa daki ta hau tunane tunanen yadda za suyi. A karshe ta yanke shawarar ta kira yar uwarta dake Birnin Gabas a wata masarautar can ta daban, ko ta tabajin labarin Sarauniya Maimounatu. 
Tana Ialubo wayarta ta latsa kiran Hashiya. Sai dai taji ana surutai babu kudi a cikin wayar. Clke da takaici ta bubbuga diyarta Indo da ke barci. Budurwa ce ‘yar kimanin shekara goma sha shida. Ta tashi tana mitsitssikar ido cike da takaicin tashinta barci da Zabbau tayi. “To bakar almura fitsararra! Niba iskanci na tashe ki kimin ba, rancen kudiza kiyo mini a layi, ina son yin waya mai matukar muhimmanci.” Tsoki lndo tayi hade da karbar wayar, ta ranto naira dari sannan ta mika wa Zabbau. 
Bugu biyu Hashiya ta dauka, cike da rakadi tace, “Zabbau gandun zunubi. Ko wacce yaja dake ya kwana kiyama. Yau kuma dame kike tafe?” 
Daure fuska Zabbau tayi, “Hashe bana son shegantaka. Kinfi kowa sanin na tsani kirarin nan .” Naji to. Ya gida ya iyali?” Hashiya ta fada cikin raha. ’ 
Zabbau ta canza muryana zuwa seriousness. “Tambayarki na kira in yi don Allah Hashe. Ki fada mini idan kin sani. Wata Sarauniya Maimounatu? Kin santa a wanne yanki take?” 
Ido Hashe ta zaro cike da al‘ajabi. “Zabbau! Me kike son sani a kanta? Mema ya dame ki da zancenta?” 
Zabbau ta sauke ajiyarzuciya. Alamun dai Hashiya nada masaniya ko yaya ne a kanta ke nan. “Uwargijiyata ce ta saka na mata bincike a kanta. Ke dai kawai ki fada mini idan kin sani.” 
Dariya Hashiya tayi tace, ‘ni dama nasan wani kaya sai amale. Idan kun saba yi kuna cin riba a nan dai baza kuci ba. Gwara ma karku jewa kanku zuwaga hallaka.” 
Kanta ta dafe Zabbau. “Kayya! Nifa ba wannan nake sonji ba. Hashe. Kawai ki bani amsar tambayata idan kin sani.” 
Hashiya ta tabe baki. “Kadan na sani ba sosai ba. Sai dai akwai wata mata da muke tare da Ita a nan wacce ta san ciki da bai na Sarauniya Maimounatu. Bariyanzun nan na kira ta na hadu ku ki sha Iabari. ” 
Kafin Hashiya ta kira Zabbau, Zabbau ta yigaggawar tafiya bangaren Kursiyya. Ta same ta tana barci. Sosai ta san yadda Kursiyya ta kijinin tana barci a tashe ta. Hakan yasa ta fara 
tunanin kota tafi ne. Sai kuma ta tuna da yadda ta matsu da ta samu wani labari a kan sarauniyar. 
A hankali ta hau bubbuga ta tana ambatar sunanta. Kursiyya sai gyarajuyi da tayi. Ta sake buga ta, ta gaggauta dago kanta da zummaryin masifa ga koma waye ya tada ta daga barcin data dade tanajuyi bai dauke ta ba. A daidai Iokacin data samu ya dauke ta kuma a tashe ta. “Zabbau! Ina ga duk gidan nan kinfi kowa sanin na tsani a tashe ni idan ina barci k0?” Clkin rawar murya Zabbau tace “Kiyi hakuri ranki shi dade. Alkhairi ne tafe dani din.” 
Saurin tashi zaune Kursiyya tayi hade da kasa kunnuwanta tana sonjin wani labari daga bakin Zabbau. 
Kafin Zabbau tace komai wayarta ta dauki kara. Murmushi ta saki hade da latsawa, tace, “Ranki shi dade, bayan fitata daga nan na kira ‘yar uwata Hasiya dake Birnin Gabas. Nake tambayarta kota san wani abu game da Sarauniya Maimounatu?” 
Ta zayyane ma Kursiyga tsafyadda suka yi a waya. Sannan a karshe tace, “Yanzu kiran nan da ya shigo mini Ita ce. Bari in kira sai na kunna kara yadda dukza mu iyaji.” 
Ta Iatsa kiran Hashiya. Da sallama Hashe ta dauka. Zabbau bata k0 tsaya amsa sallamar ba tace “Ina matar?””Gata nan. Sunanta Binta.” “Binta ana Iafiya? Ya iyali? Hashe ta miki bayanin komai ai k0?” Binta tace, “Ehh tabbas tayi mini bayanin komai, kuma yanzun nan zan sanar daku duk abin da na sani game da Sarauniya Maimounatu. 
Saraumya Maimounatu ’yaryankin Bani Hashim ne. Ta taso cikin wata irin rayuwa wacce babu wanda zaice ga mahaiyarta. Kowa daiya ganta a gaban Sarki Jaheed Hashim, a matsayin diyarsa ta cikinsa. Sai dai bai fito yace ga mahaifiyarta ba, bayan kuma kowa ya san bai da mata, matarshi ta rasu tun yana saurayi har a lokacin da ya kawo Malmounatu a matsayin diyarsa. 
Kowa yana shakkun tambayarsa inda ya same ta, saboda tsananin tsoronshi da akeyi. Sarki Jaheed Hashim ya cigaba da rainon Maimounatu da kanshi, ba tare da taimakon ‘yar raino ko kuma wata ‘yar aiki ba. Hakan yasa yarinyar ta tashi da wata irin gurguwar rayuwa, ta kin mutane, a takaice ma take tsananin tsoron shiga mutane. 
A lokacin da Maimounatu ta cika shekara goma cif Sarki ya dauke ta daga gidanshi, ya kai ta wani wuri wanda haryau hargobe babu wani malamin tarihi k0 masani da zaice ga inda Sarki Jaheedu ya kai Maimounaru, saidai mafi rinjaye ana zargin ya kai ta wani boyayyen 
daji ne, inda ta cigaba da rayuwa daga ita sai namun daji. 
An yi hasashen Maimounatu tayi rayuwa tare da namun daji ne saboda haryau maganar nan da nake miki, komai nata irin na dabbabin dawa takeyi. 
Haryau hargobe tana ziyarar inda tayi rayuwa, a wasu Iokutan ma har takanyi kwanaki da suka kaigoma a can, koma fiye. 
Bari in dan dawo baya. A lokacin da Sarki Jaheed ya mayar da Maimounatu can, mutane sun so su tambaye shi inda ya kai ta, amma aka kasa. Har sai lokacin daya kusa mutuwa, wato ciwon ajali ya kama shi. Da shi da wani babban amimnshi mai suna Sabi’u suka tafi inda ya kai Maimounatu ya dauko ta. Suna Isowa gida Sabi’u ya rasul Hakan ya tabbatar wa al’ummar wannan yankin cewa duk wanda yaje inda Maimounatu tayi rayuwa to shima saiya bakunci lahira. 
A gaban dukkanin mutane Sarki Jaheed ya nada sarautarshi ga Malmounatu, wacce a lokacin zata kai shekaru goma sha hudu. Ya tsorata mutane sosai game da duk wanda yaso daukar hakkinta. Sannan ya bada aurenta ga waniyardajjen hadiminsa. A take aka daura auren. 
Bayan auren Maimounatu da kwana uku kacal Sarki Jaheedu ya amsa kiran mahaliccinshi. 
Abun mamaki, k0 gezau Maimounatu bata yiba. Tamkar ma bata damu da mutuwar ba. 
Sai data aka shekara sha bakwai sannan ta hau karagar mulki. Ta kuma tare da mujinta mai suna Sahabi. Inda ta cigaba da mulki mai cike da zalunci. Duk wanda zaiyi laifi da kanta take hukunta shi. ldan tana zagayen gari wani yayi gigin fitowa ranarya bani. Don sai ya kwana a sijin, watakila ma daga nan ya zama ma,aikaci a masarautan 
Gimbiya Maimounatu na da manya-manyan asirrai, wanda kowa ke zargin tafiyar nan da mahaifinta ya yida ita a can ta samo su. Komai nata ba irin na mutane bane‘ lta ba dabba ba, sannan ita ba aljanah ba. Babu wani abu daya da take yi irin na mutane. Halittarta kadai Ce irin tamu. 
ldan Sarauniya Maimounatu ta daga yatsarta ta nuna ki dashi, rayuwarki ta kare. A take zaki fadi ki mutu. Idan kuwa ta tsura miki idamuwa tsafza ki iya makancewa. Uwa uba ace ta daga muryarta gare ki, zaki iya haukacewa ko kuma wata mummunar cuta ta same ki. A takaice dai karki bari ranta ya baci a kanki, shi ke nan sai a zauna lafiya. 
Da haka da haka ta hayayyafa. Ta haifi maza uku kafin nan ta samu mace, Gimbiya Jiddah. 
Ban san komai bayan ta hayayyafa ba, saboda daga nan nima na baro yankin Bani Hashim, na dawo Birnin Gabas nayi aure a nan. 
Wallahi ba komai na fada muku ba a kanta. Ba komai ba na sani. Domin kuwa kaidinta ya wuce duk yadda zan misalta muku. Sarauniya Maimounatu ta wuce gaban misali. Tun da nake a rayuwata ban tabaji k0 ganin mace irinta ba. Ta fi karfin kowa a duk duniyar ma baki daya. “Ta kai aya a daidai lokacin da kudin wayar Zabbau suka kare. Hannu Kursiyya ta dora aka tana murzar gashinta. Tama rasa abinda zatace. Da gaskiyar Boka Fartsi, ashe shiyasa ya tsorata. “To ranki shi dade, kinji dai ko wace ce Sarauniya Maimounatu a takaice…” 
Kursiyya ta daka mata tsawa. “Daalla can naji Malama, sai kiyi min shiru. Ki kuna fice min daga daki tun ban sauke fushina a kanki ba.” Sum-sum-sum Zabbau ta mike. “Allah ya hucivzuciyarki ranki shi dade. Bani na kar zomon ba…” 
Ta fice daga dakin ta bar Kursiyya na tajerangwama. Sai kai-kawo take yi daga wannan 
bango zuwa wannn bango. Tana tunanin mafita

Tofa wato gaba da gabanta kenan 
Koya zata kaya muje dai muji

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]