FARHA CHAPTER 20

FARHA 
CHAPTER 20

Haka sukaci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin so da tattalin farin cikin junansu satinsu daya a Kaduna suka nufi Bauchi tana lafe ajikinsa har suka isa motar ta shiga gdan sarautar ta dago kanta daga jikinsa duk da an sakewa gidan fasali da tsari sosai amma bata kasa ganeshi ba ganinshi take kamarjiya ta barshi, sunayin parking aka bude musu qofofin shine ya fara fita sannan ita nan danan ido ya dawo kansu gdan ya rude da ihun murna tare da kabbara bayin mata sunata rugowa suna rungumeta itama ta saki jiki dasu tana hawaye suna rungumejuna saida komai ya lafa sannan suka nufi part din surukartata a hanya suka hadu da ita dajikanta sarki ta tafi da gudu ta rungume uwar mijin nata sai kukan da taketa qoqarin hadiye wa ya kwace mata itama Hajiyan kuka tasa tace “Farha ashe kina raye a duniya ashe da rabon zaku qara ganawa da Hafeez munyi kewanki tsayin shekaru Farha ashe kinanan keda jikalle na” 
Itama kukan takeyi ta janye jikinta suka shiga ciki suka zauna sunata jajantawa juna Sarki ne ya dubi Momynsa da kakar tasa yayi dariya yace “wlh Dad nake hangowa sanda ya laluba yaji ba Mom….” daquwa Farha ta watsa masa shikuma King Hafeez ya zuba masa dundu a baya ya kwallah qara yace “wayyoh Hajiya kina kallonsu zasu sheqeni” murmushi tayi da riqo hanunsa ya dawo kusada ita tace “aiba qarya yayi ba ya kake sanda suka bata din ai kaima zaucewa kayi kaidin badan qarfin addu’a ba da tuni ka shiririce” murmushi yayi daidai lkcn Hajiya Kilishi ta shigo itama ta nuna murnarta da farin cikin ta sosai aka rinqajere musu abinci kamar hauka da abinsha sukaci sukasha duk iyalan gdan Mai martaba sarki Hambali sun hallara harda Asiya da Nadiya da Umaimah harda Prince Hasheem da baima taba ganin Farhan ba ranaryini akayi ana shagali a gdan sarautar sai dare sosai King Hafeez ya dauke matarsa suka wucce part dinsu shi kansa part din an fashe shi an sake masa gini yanzu part daya ne qaton gaske saika shiga ciki ne zaka gane yanda tsarin gdan yake bangaren Farha parlour uku ne da dakuna uku kawanne an zuba furnitures yan gaske sai bangarensa me parlour biyu da daki daya sai wani daki wanda shima idan ka shigeshi parlour ne babba da aka qawatashi da kayan alatu sai daki biyu a ciki kai gdan ya tsaru sosai bangarenta ya rakata wanda ya cikashi da manyan pics dinsu tun na auransu suna shiga ya fara kiciniyarcire mata kayanta yace “ya kamata muyi wanka mu kwanta ko?” 
Daga masa kai tayi suka shiga bathroom din sukayi wanka suka shirya tare suka kwanta, haka kwanaki sukayita shudewa sarki ya tafi Rasha karatunsa inda King Hafeez ya hana farha aikin asibiti babban asibitinsa dake Kaduna ya mallaka mata yace duk abinda zaike shigowa aljihunta zaike shiga hakanan ta haqurada aikin ta zauna zaman ci gashi tunda haka ya zaba mata. 
Wata daya wata biyu wata uku har suka doshi shekara babu wani bayani tun abin bai fara damun King Hafeez ba harya fara damuwa duk lkcn da yaji tace tana period saiya kulle kansa a daki yayita kuka yana roqon Allah ya qara musu da k0 dayane me albarka harma ya saduda ya mayarda hankalinsa kan tilon dannasu da yake tunanin qila shi kadaine rabonsu. 
A cikin shekararsu ta biyu ne Allah ya azurtasu da samun qaruwa ita kanta batasan dashi ba kawai dai baccinta ya qaru saita yini tana bacci batare data gaji ba sannan takanji kwadayin wasu abubuwa da abaya basu dameta ba, yau litinin ce da wurita tashi ta hada musu break kasancewar tun dare ya fada mata yanason zuwa Abuja akan aikin wani sabon asibitin da yake ginawa batayi break din ba saboda cikinta da yake danyi mata ciwo tana kwance saman gado tana kallonsa ya gama shirinsa ya dauki laptop dinsa da wayoyinsa ya matso kusa da ita ya shafa fuskarta yace “zan tafi Queen” lumshe idonta tayi ta budesu a kansa tace “Allah ya kiyaye hanya ya tsare min kai” amsawa yayi da amin yace “yau bazan 
samu rakiyar bane” hanunsa ta ruqo tace “kayi hqr Allah yau kasala nakeji” murmushi yayi yace “dama ai kin dade da zama kasalalliya a ko inama ni wannan baccinya fara yin yawa da rana a yini anayi da darenma kuma dana nemi haqqina a kama yimin rakin bacci akeji” Yana wannan mitar ya fita ita kuma ta koma ta kwanta bacci me dadi ya dauketa tayi kusan awa biyu tana baccin taji zuciyarta da mararta na wata irin hautsinawa da sauri ta tashi zaune amma daqyarta iya durowa daga gadon amai ya qwace mata gashi bataci komai ba sai ruwan tea saboda hakanne ta jigata sosai ga ciwon marar da ya addabeta kwanciya tayi a qasa gefen aman tanata murgususun ciwo har qarfinta ya ida qarewa sai yamma liqis Jakadiyya ta shigo itama saboda King Hafeez ya kira yace taje ta duba ne ta gano masa lfyrta shiru yana Kiran wayarta taqi dagawa, part dinta ta fara shiga bata ganta ba saboda haka ta nufi part dinsa tana kiran “ranki shi dade uwar gijiyata Mai martaba yanata Kiran…” mgnr ce ta maqale saboda yanayin data risketa cikin amai ido a juye kamar matacciya, salati tayi tare da nufarta da sauri tana kiran sunanta amma babu alamun zata amsa hakanne yasata fita da gudu ta nufl cikin gdan a gigice ta fadawa Hajiya Fulani cikin tashin hankali suka rankayo harda Kilishi suna zuwa suka gyarata ruwan da suka sanya mata a jikinta ne yasata farfadowa amma da ganinta kasan a jigace take Hajiya ce ta dauki wayarta ta kira King Hafeez din bugu biyu ya daga yace. 
“He..,hello Queen ya akayi ne ina kikasa wayar…” katseshi Hajiya tayi tace ka turo mana likita cikin ma’aikatan ka akwai matsala Farha batada lfy” tana fada masa ya hau salati tare da cewa “qlau fah muka rabu Hajiya ciwon har yakai wanda bazata iya daga wayata ba?” katseshi Hajiya tayi da cewa “muma yanzu muka shigo akwai alamun ta jigata…” katseta yayi da cewa “ok ganinan Nima bari na kira Patrick yazo ya dubata” yana fadin haka ya kashe wayar ya miqe ya fita daga asibitin a hanya ya kira likitan ya bashi umarnin yaje ya duba matarsa. 
Cikin abinda bai wucce 15 minutes ba Dr Patrick ya iso ya shiga cikin gdan a wani weell chair aka turata zuwa clinic din dake part din aka kwantar da ita a gadon ya daura mata drip kafin ya fara dubata yanayinta kawai ya gani yasan matsalar ta amma saboda gudun kokwanto saida ya debi jininta ya gwada yayi murmushi tare da saita na’urar scenning a cikinta ya fara dubawa nan ma dai sakamakon dayane ya dago yayi murmushi yace “ Allah ya raya Hajiya’s Madam nada cigar baby wata uku” kabbara suka dauka tare da godiya ga Allah magunguna ya rubuta mata sannan ya kuma kallon Hajiya yace “a kula da cin abincin ta sosai baby yanason abinci saboda ya samu Energy sosai” amsa masa sukayi tare dayi masa gdy ya fita da takardar bai jima ba ya dawo da magungunan dayake abune na masu abun a parmercy dinsa aka debo shigowar Dr Patrick tayi daidai da shigowar motar da taje airport ta dauko kin Hafeez a qofar part din sukayi kacibis da Patrick yayi murmushi yace “Congrats Sir madam tanada sabon baby almost 3 mouth a gurin ya zube yayi wata doguwar sujjada Patrick ya saki baki yana kallonsa ganin bai dagoba ne yasashi sanya hanu ya dagoshi fadawa yayi jikin Patrick yace “Allah na gde maka ashe bayan Sarki zan sake haihuwa wayyoh Allah na Patrick na gde kaine mutum na biyu da kayimin wannan kyakkyawan albishirdin dole ka karbi kyauta me kyau yanzu Ina Queen din take?” a 
Kama hanunsa yayi suka shiga dakin ya zame hanunsa ya qarasa kanta ya tsugunna yana kallonta yau daya duk ta rame ta dashe ta qara wani sabon haske ajiyar zuciya yayi ya sanya hanunsa ya shafa cikinta tare dakai bakinsa yayi kissing bayan ya dage rigarta a hankali yakai har zuwa bakinta ya fara tsotsa kamar alawa kunya ce tasa su Hajiya ficewa daga dakin saboda ta lura idonsa rufewa yakeyi idan yana tare da Farha jin dumin lips dinsa a saman natane yasata tura hannunta cikin sumarsa da take kwance luf kamar ta balarabe bude idonta tayi a hankah ta zubashi a cikin nasa yayi murmushi yace “kiyimin murna nayi namijin qoqarin sake ajiye qwaina a mahaifarki daqyar, Sarki zai sami qani ko 
Kanwa

Hmm

About Ismail

Check Also

FARHA CHAPTER 18

FARHA CHAPTER 18 Tureshi takeyi da dukkan qarfinta tana kiran sunansa tana kuka tanayi masa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *