[Advertisements⬇️]

FARHA CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FARHA
CHAPTER 19
Shafa fuskarta yaron yayi yace “momy meye yake damunki da har zaisa ki manta danki kwaya daya tak da kika mallaka a duniya?” lumshe idonta tayi ta cire hanunsa daga fuskarta tace “Mai martaba kai nake tambaya waye wannan? Meye alaqarmu dashi?” takaici ne da mamaki ya hana King Hafeez mgn ya matsa ya bude wadroop ya dauko jallabiya yasa ya koma ya kamo hanun Sarki yace “kyale Momynka batada da lfy Son” hawaye ya share yace “kanaji fah Dad wai bafa ta ganeni ba dama uwa na manta danta?”
Kamashi yayi suka fita yana lallashinsa mota suka nufa ya dauko musu break din da Momy tace a kawo musu suka dawo yanayi masa bayanin halin da Momynsa take ciki yayi ajiyar zuciya suka zauna a parlourn sunata hirarsu,jin shiru basu dawo ba yasata miqewa ta shiga bathroom tayo wanka daidai lkcn King Hafeez ya shigo ya miqa mata kayanta saida ya taimaka mata tasa kayan ya riqo hanunta tana lafe ajikinsa har suka shigo parlourn ya isarta har dinning din suka fara breakfast din gabadaya hankalinta yanakansu yanda suke hira kamar dama tare suke ita mamakin kamarsa da yaron takeyi saida suka gama sannan ta sake tambayar King Hafeez waye Abdallah murmushi yayi yace “shine albarkar auranmu Queen saboda Abdallah aka rabani dake tsayin 15 years aka barni da kukan zuciya dana fili saboda shine akayimana duk abinda ya faru damu a baya amma a yanzu ya zama tarihi Queen wannan shine amsar tambayar da kikayimin jiya da daddare shine abinda kika haifamin a cikin dakejikinki kinganshi dama ajiyan na fada miki shima ya kusan zama magidanci” Murmushi ta fara saki tana kallon Abdallah tana share hawaye tasowa yayi ya fada jikinta suka rungumejuna suna kuka me ban tausayi a hankali yace “yanzu kin tunani ko Mom Allah ya isanmu Mom duk sun juya miki tunaninki Mom bazan taba yafewa dukwanda yake da hanu a cutar min da iyayena ba sun sani kuka saboda rashin kasancewar ku tare har wasu ma cikin mutane suna cewa nidin shegene mara asali ashe Nima dane na sunnah me cikakken asali inasonku iyayena I love Mom and Dad” ya fada tare da rungume su suma dukkansu kukan sukeyi suna tausayin kansu sunajin ashe suma zasu kasance cikin wannan farin cikin, ranar haka suka yini nunawa junansu kulawa da tattalin juna cikin su ukun babu wanda yakeson dayansu ya motsa har gasa King Hafeez da Abdallah sukeyi wajan nuna mata kulawa shi Abdallah ya yarda Morn dinsa zazzabi takeyi shi kuma King Hafeez dake yasan shine yayi barnar pain relief kawai yake bata tare da wasu magunguna na kashe zugi.
Sai yamma Baffa da Daddy da sauranjama’ar gdan sukazo yanda suka tarar dasu saida sukaji kunya King Hafeez ne kawai a zaune Farha na kwance tana bacci ajikinsa Sarki ma yana kwance a daya bangaren yana ta zuba ma mahaifin nasa surutu, Maryam ce ta qarasa kusa da ita zata tasheta da sauri King Hafeez ya dakatar da ita yace “ki taimakeni kada ki tasheta daqyar na samu tayi bacci batada lfy” yanda ya marairaice yanama Maryam din mgn yasa dukka suka kwashe da dariya shima dariyar yayi hakanne yasata tashi ta bude idonta tana binsu da kallo Baffa kawai ta gane ta yunqura ta tashi zaune tace “sannunku da zuwa Baffa dama kananan ashe zakazo baka fadamin ba kuma harda baqi ma Yaya Anass sannu da zuwa” kallon kallo Momy da Dad da Maryam da Nasir suka farayima juna sukayi murmushi tare da hamdala Daddy yace“alhmdllh hakan ma anyi nasara Hafeez me kayi mata ta dawo daidai da wuri haka?” Murmushi yayi ya shafa kansa yace “Daddy kenan ai nida Farha ba,a shiga tsakaninmu yanzu matsa’lar da muke fama da ita kuma duk abinda ya faru 15 years dinnan baya ya goge a mind dinta bata iya tunawa dashi sai an tuna mata.
Ajiyar numfashi Baffa yayi yace “tunda wancan tunanin ya dawo shima zai dawo dama munzo ne muga ya kuka kwana kuma inason wuccewa Bauchi gobe idan Allah ya kaimu” yana fadar hakan ta miqe tanajan qafarta daqyar ta matsajikin Baffa tace “don Allah meye yake faruwa danine Baffa nifajina nake wata iri kamarwadda ta taba ciwon hauka” murmushi Baffa yayi ya zaunar da ita a kusa dashi ya shafa sumarta yace “ba daga ciwon hauka kika tashi ba Farhanah kawai dai kin samu gushewartunani ne na tsayin shekaru goma sha biyar to yanzu kuma shine tunaninki na baya ya dawo kuma duk abubuwan da suka faru a cikin 15 years dinnan sun goge a qwaqwalwar ki amma insha Allah zasu dawo” nan ya zauna ya rinqa yimata bayanin kowa a gurin da irin gudummawar da yabawa rayuwarta miqewa tayi ta rungume su Momy tana kuka me ban tausayi tana cewa “kuyi hqr wlh nasan na sanku amma ban tuna inda na sanku ba Saida Baffa ya fadamin na gode Momy na gde Daddy Allah yabar qauna” shafa kanta Momy tayi tace babu komai my daughter Allah ya tsare mana ku ya kiyayeku daga kaidin maqiyanku Allah ya dawwamar da wannan qaunar taku da soyayya Allah yasa nanda wasu yan watanni mu dawo suna”
Dagowa tayi suka hada ido ya daga mata gira tare da amshewa da “amin Momy insha Allah hakance ma zata faru Son ya gaji da zama shi kadai qani yakeso ko My Son?” daga masa kai yayi yace “yess Dad kuma twince nakeso ma” dariya sukayi ita kuma ta matsa kusa da Maryam suka rungumejuna suna kuka Maryam tana cewa “na dade lnajiran zuwan wannan ranar da zan ganki cikin gdan mijinki Sister Hanah” qasa tayi da muryarta tace “da alamun ma harAli yaga Ali k0?” Qasa Farha tayi da kanta tana dariya itama dariyartayi tace “dama tsoffin masoya kuma mayunwata irinku ai babu wanda zai ragawa wani na sani muje kiga wani abu” tana fadin haka suka juya suka nufi wata qofa da alamun kitchen ne suna shiga suka tarar da kuku yanata aikin girkinsa zubewa yayi a qasa yana kwasar gaisuwa tayi murmushi tace “akwai baqi a parlour kakai musu ruwa da abin tabawa” hada kayan yayi ya fita sukuma suka fara tattaunawa Maryam ta fito mata da wasu sirrika ta bata tace “suna da kyau da tsadar gaske tun lkcn da Yaya Nasir ya nuna yana sonki na siye wasu saboda ke so da mgnr ta shiririce ma nayita ajiyarsu lnajiran wannan ranar gata kuwa Allah ya kawota ki dage kiyi amfani dasu zakiji dadinsu sosai nasan saikin nema da kudinki don da ganin mijinki bazaiyi sauqi ba garama ki dage kam ya gano wata” ajiyar zuciya tayi tace “ai yanzun ma yanada wata matar akwai princess Amnah” Tsaki Maryam tayi tace “ke kina Ina sanda yabada lbrn rabuwarsu yanzu ke kadaice saboda haka ki shirya kulada mijinki ke daya ki zamajaruma wajan kula da duk abinda ya shaf’l rayuwarku Allah ya shige muku gaba” haka Maryam ta rinqa nuna mata abubuwan da yanda zatayi amfani dasu kafin suyi musu sallama su tafi Sarki ya dage kan shi dole sai yabi Baffa Bauchi dole suka qyaleshi yabisu akan Suma goben zasuzo suyi sallama da Baffa kuma idan sun huta zasu taho Bauchin suna tafiya ita ma ta miqe ta shige dakinta tayi wanka tasha magungunan ta tayi sallar magaruba da isha daidal lkcn ya shigo dakin ya tararta a kan sallaya tana azkar zama yayi a gefen gadon harta gama ta juyo ta kalleshi shima itan yake kallo sukayi murmushi a tare ta miqe ta cire hijab din jikinta ‘ta linke ta nufi jikin mudubi ta fara gyara gashinta bayan ta gama ta dauki turare ta shafa ajikinta ta raba ta gefensa ta kwanta ya hadiye yawun kwadayinsa ya kwanta a gefenta yajanyota jikinsa yana ajiyarzuciya yace “I Miss you My Heart long time Ina kewarki lna zubar da hawaye akan rashinki My Queen wlh bazan taba yafewa dukwanda yayi silar nisantani dake ba” Yana fadin hakan yana qara shigewajikinta janyewa tayi ta koma ta kwanta ya sake matsota yace “ I hope matata jaruma ce me qoqarin sanyani farin ciki da sallama min jikinta a duk sanda na buqaceta tana iyakar yinta wajan ganin ta gusar min da qishirwa ta Queen ke kanki kinsan nayi qoqari bayan batanki da shekara bakwai muka rabu da Amnah kuma ko sanda muna taren nayi samada shekara biyu bama mu’amalantarjuna in kika hada shekara tara da biyu zai baki kusan sha daya kenan kinga kuwa ai nayi qoqari a matsayi na namiji” yana fadin hakan yana matsawajikinta kuka tasa masa tace “nidai ka qyaleni Abban Sarki wlh bazan iya ba na gaji jiya Pls ka tausayamin don Allah” ajiyarzuciya yayi yajanyota yace “shikenan na hqr mu kwanta muyi bacci” da wannan bacci ya dauketa shikuma ya nata juyi da haka baccin ya daukeshi sai asub ta farka tana shirin sauka ya ruqota yace “ki daure kiyimin wani abu kafin muyi sallah” tureshi tayi tace “Allah ka cika matsala Mai martaba anfa shiga masallaci don Allah” miqewa yayi yace “is ok muyi sallah tukunna a bani breakfast” batace masa komai ba ta nufi bathroom wanka kawai tayi ta dauro alwala shima ya tashi ya shiga yayi sukayi sallah ta miqe da niyyar fita yasan nufinta saboda haka ya ruqo ta yace “hqr zakiyi dani fah Queen” turo baki gaba tayi ya dagata suka koma saman gadon daqyar ta qwaci kanta shima saida tasa masa kuka sannan ya qyaleta sukayi wanka suka fita dinning din sukayi breakfast sai sha daya suka nufl gdansu Momy lkcn Baffa ya shirya yana jiransu suna zuwa ya miqe sukayi sallama suka fita Sarki na daga mata hanu itama daga masa takeyi King Hafeez shine yakaisu airport ya juyo gdan ya dauketa suka tafi gdansu.


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]