[Advertisements⬇️]

FARHA CHAPTER 17 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FARHA


CHAPTER 17Tana fadin haka ta miqe tabar gurin hankalin King Hafeez yayi mugun tashi ya zame qasa ya riqe qafafun Daddy yace “Daddy wlh da gaske nake itadin matata ce kayimin rai ka bani ita mu tafi wlh Dad rashin Farha a cikin rayuwata yakusa zama ajali na” murmushi yayi ya dafa kafadarsa yace “hqr zakayi Hafeez Farha da alamun har yanzu ba,a cikin hayyacinta take ba tunanin ta aka shafe mata wanda ya shafi rayuwarku ta baya kabani kwana biyu zanyi wani abu akai” girgiza masa kai yayi yace “kada kace haka Dad kabani ita wlh daganan zuwa safiya saita saita tunani ina da yaqinin idan nayi mata abu daya zai iya dawo da tunaninta gareni tunda dukduniya babu wanda ya taba yi mata shi saini kadai” Murmushi Dad yayi yace “kafiye gaggawa Hafeez badai kaganta ba? To ka kwamar da hankalinka bijahi rasulullahi nanda shekara daya sai munzo Bauchi suna dan daga ganinka akwai qoqari” shafa kansa yayi cike da kunya Mom da Maryam sukayi dariya shidai Nasir mutuwar zaune yayi yana saqe saqe a ransa yanzu shikenan yanaji yana gani Farha ta haramta gareshi? tambayar da yayiwa kansa kenan daidai lkcn da King Hafeez ha miqe ya kamo hanunsa suka fita suna fita Sarki ya rungume shi yana kuka shima kukan yakeyi yana bubbuga bayan dannasa bude baki yayi yace “Ina cikin farin cikin da tunda Mom na ta haifeni ban tabayi ba ashe Ina tare da mahaifina tsayin shekaru bansani ba ashe nima cikakken dan gatane kamar kowanne da Allah na gde maka daka azurtani da iyaye na qwarai…” rufe masa baki King Hafeez yayi da nasa yayi masa kiss me kyau sannan ya soma share masa hawayen yace “zo mu tafi yau a gurina zaka kwana tunda Mom dinka taqi yarda dani kada nayi maraici biyu kaji sweet Sweet Son” yana fadin haka suka shiga mota leqowa Sarki yayi yace uncle Nasir “kace dasu tsohon Dad na tafi yau a gurin Daddyn gaske zan kwana kuma kace da Mom na saita taho” duk da nauyin da Hafeez yakeji a qirjinsa saida ya murmusa haka yaja motar suka tafi suna tafe suna hira Sarki yanata zuba masa surutu da bashi lbrn zawarawan Mom dinsa da suketa zuwa take musu wulaqanci tana cewa ita matar aure ce harda lbrn irin badaqalar da sukayi da kawunshi Nasirwani kishine ya tasowa Hafeez da baisan yanada shibajikinsa har rawa yakeyi wai matarsa wasu qaratan
banza suke zuwa suna cewa suna sonta. Da wannan ‘tunanin suka shiga wani mall sukayo shopping suka wucce gda dama Sarki yasan dakinsa a gdan kai tsaye ya shiga yayi wanka ya canza kayansa zuwa wasu set na baqar singlet da bakin boxes yana fitowa parlourn ya tararda Dad dinsa shima yayi irin dressing dinsa ya zauna kusa dashi sukayiwajuna murmushi ya bude wata jaka ya rinqa fito da hotuna yana nunawa Sarki yanayi masa bayani wasu da yawa yasansu wasu kuma bai sansu ba saidai lbrnsu da yakeji a gurin Dad dinsa ajiyar zuciya yayi yace “amma Dad yaushe zakuyimin qani nima inason qani duk abokaina sunada qanne sai suyita yimin gori waini ni kadaine inna mutu banida meyimin addu’a” murmushi yayi ya shafa kansa yace “ka lallaba Mom dinka ta biyomu nan nikuma nayi maka alqawarin zan bata ajiyar qaninka bada jimawa ba kaji?” wani ihun murna yayi ya rungume mahaifin nasa yace “thanks Dad I love you so much” da haka suka gama kallon picks din suka tattare su King Hafeez ya dagashi cak ya kaisa dakinsa yayi masa addu’a ya kashe hasken shima ya kwanta a kusa dashi yaja musu bargo.
Washegari da wuri Baffa ya diro Kaduna aikuwa Sarki yayi murnar ganinsa da King Hafeez ya fada masa kakansa ne ya rungumeshi yanata kissing dinshi dariya sukayi Baffa yace “daga ganina kuma sai a karyani dan jikalle” dariya yayi yace “ai sonake na rama more kan da banyi ba tsayin shekaru” murmushi yayi tare da dauke hawayen tausayin yar tasa da jikansa King Hafeez ne yajasu har gdan Daddy tana kwance Momy ta shigo tace tazo tanada baqi tashi tayi ta dauki mayafinta ta yafa ta fita parlourn wani tsalle tayi ta dira gaban Baffanta ta fadajikinsa ta saki wani kuka ta matseshi sosai ajikinta tace “ba.. Baffa dama
kana raye ka manta dani Baffa laifin me nayi maka haka daka banzatar dani a duniya
kabarni baka tunanin sake ganina…” kukan da yaci qarfinta ne yasata yin shiru murna ce ta hana Baffa cewa komai sai Yaya Anas ne yayi qarfin halin matsawa kusa da ita ya janyeta daga jikin Baffansu ya hadata da nasa yana share mata hawayen a hankali cikin muryar kuka tace “Yaya Anass Ina su Mama da Ummah ina sauran yan uwana” zaro mgnrtakeyi batare da tasan ta inda take fitowa ba komai yanzu yake dawo mata na game da mahaifan nata da yan uwanta.
Daqyar suka saita nutsuwarsu suka zauna tana maqale da Baffa shikuma sai shafa bayanta yakeyi tausayinsu ya cika zuciyar mutanen gdan musamman Daddy Baffa ne yace “ya isa kukannan haka uwata ba kuka ya kamata kiyi ba gdy zamuyiwajalla wa azzah daya jefoki hanu na qwarai kika rayu cikin aminci keda danki Farha duk abinda Allah yayiwa bawa akwai hikima a cikinsa ki qara sujjada ki godewa ubangijinki dabai barki cikin mayuwacin hali ba ya azurtaki dayin ilimi mai zurfi sannan ya azurtaki da iyayen ruqo na qwarai wadannan bayin Allah sunfi gaban iyayen ruqo Farha iyayene na qwarai gashi kuma duk wadannan shekarun da kika dauka bakya tare damu mijinki yananan da soyayyar ki a zuciyarsa babu abinda ya canza halaccin Mai martaba ya maishemu dama maqotan mu Farha ina qarayi miki tuni da gdy ga Allah Allah ya fifita a rayuwa wanda ba haka maqiyanku sukaso ba so sukayi ki haukace ki rinqa bin bola bola kina tsince tsince koma ki mutu keda abinda ke cikinki” tunda ya fara mgnr take kuka me tsuma zuciya har ya gama ta dago tace “waye mijina Baffa?” matsowa King Hafeez yayi ya kamo hanunta yana share hawayen idonsa yace “nine mijinki Queen ki yarda wlh nine mijinki uban danki Abdallah” kafeshi tayi da sexy eyes dinta da suke zubar hawaye ta girgiza kai tace “inaso zuciyata ta gasqata ka amma ta kasa inasonka inajinka a cikinjinina amma na kasa yarda kaine uban dana Abdallah taya zan yarda dakai Hafeez?” komawa yayi ya zauna tare da dafe kansa, lamarin yabawa Baffa mamaki Daddy ne ya kawar masa da mamakin da cewa
“Tun farkon zuwanta gdannan na fahimci tunaninta na baya ya goge yanzu ne yake dawowa ka qara hqr Mai martaba a hankali tunaninta zai dawo kanka” nan ya kwashe yanda akayi ya tsinceta da abubuwan da suka faru tun daga lkcn kawo yanzu ya sanar dasu ya qara da cewa “wata ranace Ina farfajiyar gdan nan Ina Trenning kawai sai wata qatuwar kurciya ta fado gabana tana shure Shure bayan na gama na dauketa zansa ajazvin kawai sai naga wata laya a wuyanta a tsorace naja baya jikina yana rawa na dade a haka kafin nayi bismillah na dauketa na shiga cikin gidan ina Kiran me dakina ta fito nace mata maza ta juya ta dauko min Razer ko almakashi tajuya ta dauko ta zauna kusa dani tace “wannan fah Daddy?” Dagowa nayi nace “bansan komai ba nima yanzu zamu gani” daga haka naci gaba da yanke zaren da aka qullawa tsuntsuwar layar dashi na bude layar kawai sai naga wani irin rubutu abu daya na gane a ciki sunan Farhanah na dago na dubi me dakina nace “Momy wannan wani mugun abin akayiwa wani ko wata Allah shi kadai yasan waye qila yazo ko tazo garinnan Allah ne yasota da arzikinsa yasa aka daura sihirin a jikin tsuntsuwa me gajeran kwana” ranar yini mukayi cikin taajibin abin sai yamma liqis muka shirya muka fita kawai mukaga mace a qofar gdanmu da akwatuna kayanta har mun wucce mai dakina tace mu juya fita mukayi muka sameta zaune cikin azabar ciwo duk ta fita daga hayyacinta bamu bata lkc ba muka kaita asibiti saida ta kwana tana naquda sannan ta haifl danta namiji babu yanda bamuyi ta fada mana wani abu da zamu iya ganeyankin data fito ba amma ta kasa hakan yasa muka haqura mukaci gaba da riqeta kwana uku da haihuwarta na tambayeta sunan da za,ayi masa huduba dashi amma sai tace kawai ta bani zabi hakan yasa na kirashi da Abdallah ita kuma take kiransa da Sarki wannan shine taqaitaccen tarihin yanda akayi Hanah tazo hanunmu” Mamaki sosai sukayi da lamarin ubangiji itadai Farha bata iya cewa komai ba sai binsa da takeyi da ido shima kallonta yake ganin kallon yayi yawa tsakaninsu yasata miqewa da sauri ta shige dakinta ta fada saman gadon ta lumshe idonta ‘anajin zuciyarta na bugawa da sauri da sauri ji tayi an bude qofar an shigo an mayar an rufe bata bude idonta ba tunanin Momy ce duhun da taga ya mamaye dakin shine ya tabbatar mata ba Momy bace ta bude idonta da sauri sukayi ido hudu ya sakar mata tsadaddan murmushin sa ya fara takowa a hankali harya qaraso gabanta ya zauna kusa da ita ya ruqo hannunta yayi peaking nashi ya kwantar da kansa a qirjinta tayi saurin janyewa ya kuma kamota ya hadata da jikinsa ya sanya bakinsa saman wuyanta yana lasa kamar ya samu alewa kanta ne ya soma juyawa qwalwarta tana wani irin zafi tanajin kamar zata tarwatse riqe kansa tayi da sauri muryarta na rawa tace “Haa…feez ka bari don Allah banas…” bata qarasa ba taji harshensa cikin bakinta yana tsotsar Sweet lips dinta da harshenta da wani irin salo me narkar da zuciya shure Shure ta rinqa yi daqyar ta samu ya saketa yana mayar da numfashi ya miqe yace “Daddy yace ki shirya muje unguwa” miqewa tayi da sauri tace “ina zamu?” ajiyar zuciya yayi ya juya saida yaje bakin qofa yace “bansani ba nima kiyi sauri dare ya somayi” Yana fadin haka ya juya ya fice ta jima a zaune tana tunane tunane kafin tayi qarfin halin miqewa ta dauki after dress ta dora akan rigar bacci dakejikinta tayi rolling da dankwalin rigar ta dauki takalmi tasa ta dauki wayarta ta fito parlourn Daddy ne da Baffa sai King Hafeez din tana fitowa ya miqe yanayi mata wani irin kallo tsugunawa tayi tace “gani
Daddy”shafa kanta yayi yace “zakuje unguwa da mijinki ne” daga haka suka miqe sukabar Farha da King Hafeez su kadai a parlourn, matsowa yayi ya dagota ya kama hanunta suka fita itadai jikinta a sanyaye yake har suka shiga motar suka nufi wata babbar unguwajikin wani get taji ya doka horn security din ya bude suka shiga yayi parking ya bude ya fita itama ya bude mata ta fito ya kulle motar ya zagayo inda take ya ruqo hanunta yace
“Ina tayaki murnar dawowa rayuwar masoyinki a karo na biyu nima inayiwa kaina murnar dawowarfarin cikina gareni Queen ni din nan dai nine Sarki Hafeez dinki Farha duk yanda zanyi ki ganeni nayi kin kasa ganeni ni kuma nayi alqawarin saikin ganeni a yau dinnan” yana fadin haka ya dagata cakya nufi cikin gdan da ita qofar a bude take don haka kai tsaye dakinsa ya nufa da ita ya direta saman gadon ya koma ya rufe qofar ya dawo ya zuba mata ido yanayi mata kallon qurullah yana murmushi miqewa tayi a sanyaye tace “na roqeka kada ka bani matsala a rayuwata na yarda kaidin mijine gareni a wancan zamanin amma yanzu ni ba matarka bace kada kace zaka mu’amalance ni a matsayin matarauren…” yanda taga ya nufota ne yasata saurin durqushewa qasa binta yayi ya durqusa ya ruqo hanunta yayi baya da ita da ta kwanta flat 3 saman carpet din ya bita ya danne tare da dora lips dinsa saman nata lumshe idonta tayi tana tureshi….

Hmm masoya sun dawo

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]