[Advertisements⬇️]

FARHA CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FARHA


CHAPTER 16
Hajiya na mgn tana qara nufoni har nakai qarshen dakin sannan itama ta tsaya durqushewa nayi na daga hanuna sama ina roqon Hajiya nace “na roqekl don glrman Allah ki tsaya ki fahimceni Hajiya wlh tallahl cikin jlkin Amnah ba cikina bane bansan inda ta samoshi ba nidai iyakar sanina munfi shekara wani abu bai shiga tsakanin mu ba sai sati biyu da suka wucce cikin jikinta kuma ance wata biyu…” wani kyakkyawan jifa Hajiya takaimin da wani kofin glass tayi nasarar samuna a fuska take jini ya balle min nayi saurin dafe gurln a hasale ta kuma cewa “kadan ka fara gani Hafeez indai akan Amnah ne kuma ciki kamaryanda ka karbi wancen shegen tsunannan yaron naka na kwararo dole shima ka karbeshi domin mu shi mukasani shine Yariman Bauchi kallon banza kasake ya shiga tsakaninka da baiwar Allah Amnah a bakacm nono na da kasha Hafeez na yafeka duniya da lahira balle kuma baqar mgn shashasha kawai wanda baisan abinda yake masa CIWO ba nidai wlh nayi asarar haihuwa” juyawa tayi ta fice nikuma na bita da kallo hawaye nabin fuskata ina tambayar kama “anya kuwa wannan Hajiya tace iyakar sanina Hajiya ta me jin tausayi nace dason farin cikina amma yau komai ya canza har tana iqirarin yafeni akin yayanta akan abinda nasan iyakar gsky kenan”
lnanan cikin dakina har saida nayi kwanaki uku ban fita ba komai a ciki nakeyi hankalina yayi qololuwar tashi kukana ta zama biyu kukan rashin salihar matata da rashin halattaccen dana dana kwallafa raina da burina akansu sannan ga kukan wannan muguwar qaddarar data shigo rayuwata waini Hafeez nine matata ta sunna take dauke da cikin daba nawa ba kuma a cikin gdana kuma dole inaji ina gani aka liqamin shi babu yanda zanyi, miqewa nayi a fusace nace ina wlh bazai taba yuwuwa ba dole nadau mataki bazan iya zama baqin cikin Amnah ya kasheni ba, wanka na shiga na fito na shirya cikin qananan kaya na dauki wata qaramarjaka na shiga tattare duk wasu muhimman takardu na na karatuna dana kadarorina dake ciki da wajen qasarnan na zuba a Ciki na debe komai da nasan me amfani ne a gurina sannan na bude bangaren Farha na dauke mata gwala-gwalanta da takardun karatunta da hotunan bikinmu gaba daya da duk wani abu da nasan yanada amfani na
sake zubasu a wata jakar na fita nasa a cikin mota naja na fice daga gdan sarautar.
Kai tsaye nan Kaduna nan nufo saida na shigo Cikin garin na kama hotel sannan na kira Nasir na sanar dashi Ina cikin garin bai wani bata lkc ba sai gashi yazo tun daga nesa nake kallon ayar Allah shima yaron kafeni yayi da ido sakin hanun Nasir yayi ya nufoni da gudu ya riqe qafafuna duk nauyin da zuciyata tayi sai naji ya kau farin ciki ya mamayeta nasa hanu na dagoshi ina juyawa dashi yana ta dariya nima inayi dakatar da tawa dariyar nayi na zuba mishi ido inason tuno yanayin dariyarsa da tawa takemin kama, shima daina dariyar yayi ya kwantar da kansa a kafadata yana sauke ajiyar zuciya har muka shiga dakin da na kama muka zauna na kwantar da shi a cinyata nayi kissing nashi nace masa My Son yadai?” Dariya yayi ya sauka daga cinyata ya fara wasansa muna tattaunawa da Nasir amma hankalina yanakan Abdallah har muka gama Nasir yakai hannu zai daukeshi yaqi ya maqaleni da qyar mukayi masa wayo ya yarda suka tafl tundaga wannan lkcn nakejin so da qaunar Abdallah a cikin jinina kuma nakejinsa tamkar wata tsoka ta jikina har kawo wannan lkcn Daddy bayan barowata Bauchi abubuwa da dama sun faru wasu na san zasu
faru wasu kuma da wasa bantaba kawowa zasu faru ba.
Watana tara a nan cukin garin Kaduna a wannan Ikcn ne na gina asibitin Queen Farha consultancy hospltal inda na dauki manyan ma’aikata a kuma daidai wannan Ikcn ne naji yakamata na waiwayi gda naga wainar da ake toyawa shigar dare nayi cikin garin Bauchi saboda haka babu wanda yasan da zuwa na kai tsaye bangare na na nufa abin dana gani ya kada hanta ta da hanjina Amnah ce a cikin dakin kwance Itada qanin mahaifina Waziri Iliyasu gefenta ga jaririyar data halfa nan kwance a gadon juyawa kaina ya farayi daqyar na dafe bango nayi qarfin halin kunna light din da zata wadata dakin da haske zumbur suka miqe dukkansu tsirara babu komai a jIkinsu maimakon ganina yasa su razana aa saima daukan boxes dinsa da yayi ya saka ita kuma ta koma ta kwanta a gadon ya nufoni gadan gadan yana zuwa ya shaqoni yana huci yana fadin “meye ya shigo dakai turakata munafikin Allah ta‘ala meye ya kawoka dakin da nake kebewa da matana?” mamaki ne ya cikani nasa hanuna na cire hanunsa nace “matanka kake cewa k0 Iliyasu? Ashe Amnah ma matarka ce kenan? Kayi hqr bansan cewa mace tana auran namiji sama da daya ba daban
shigo muku a wannan Ikcn ba…”
Ban ida rufe bakina ba ya daga hanu zai marenl na rlqe hanunsa Ina girglza masa kal nace “gangancin da zakayi qwaya daya tak a rayuwarka shine fitar da hanunka ka taba jlkina nasamu lbrn komai da kakeyi a masarautar nan saboda bananan to ka sani kuma ka rubuta ka aJiye da sannu zaku girbe abinda kuke shukawa” Ina fada masa haka najuya na fice daga dakin na nufl part din Farha na bude na shiga dakin duk da qurar dake part dIn haka na fada saman gadon na kwanta inata juyi zuciyata na tafasa tanayimln wanI irin zafl dana rasa wanne irine ranarta ta qarshe da Farha ta rinqa dawomin a wannan dare nayi kukan daban tabayin irinsa ba da safe labari ya cika fada cewa Mai martaba ya dawo tun ina Ciki na rinqajiyo hayaniyar mutane daqyar na tashl nayi wanka na fita ina fita wasu manyan fadawa na suka nufoni suka dagani suna fadin “takawarka Ify dan waliyin Allah haqiqa munyi rashin adalin Sarki Allah yaja kwananka fada dama qasar Bauchi tayi kukan rashinka da fadawarta hanun azzaluman bayi tabbas bayan tafiyarka gasklya ta bayyana anyi yunwa halin kowa ya Fito kuma walqiya akayi me qarfl mukaga munafukai a rana Allah ya qara maka lfy Hajiya Mai babban daki kullum sai tayi kukan rashinka hakan har yana neman haifar mata da wani ciwon ka fara zuwa ta ganka kafin zaman fada” suna saukeni na keta tsakiyar mutanen na nufi bangaren Hajiya ina shiga ita kuma tana shirin fitowa da gudu ta nufoni ta rungume ni tana wani irin kuka dana kasa gane wanne irine na farin Cikine kona baqin ciki shafani take tana qara cusa kanta a qirjlna tana fadin “kaine kaine da gaske Hafeez kana raye basu kashemin kaiba Allah na gde maka daka tseratar min da yaronnan daga kaidin mugayen mutanen nan Hafeez ina ka shiga kamanta da tsohuwarka da jama’arka Allah babu abinda zancewa Shugaban malaman fada Mal Usman Giyyade mahaifin Farha sai gdy”
Tana mgnr tana shafa Qirjlna wasu hawayene masu zafl suka zubomln na durqushe a gabanta na saki kuka nace “kiyi hqr ki gafarce ni Hajiya wlh bazan iya jure baqin cikin ganin matata Amnah da cikin daba nawa ba shiyasa na yanke shawarar barln qasar Bauchi baki daya amma yanzu gani na dawo kiyi min umarni da duk abinda kike ganin shine daidai nayi alqawarin zanyi biyayya a gareki” itama durqushewa tayi ta kamo hannuwansa tace “so nake a yanzu basai anjima ba kayiwa Amnah saki uku kyawawa sannan kasa a koreta daga garin Bauchi Ita da Baffanku Waziri lliyasu wannan shine umarni na qarshe da nake fatan baka a rayuwata Hafeez” dama wannan ranar nake jira don haka yanke take na kira magatakardar fada nasa ya rubutawa Amnah saki uku tare da umartarsa yasa a hada mata kayanta itada Wazin lliyasu a fitar dasu daga qasar Bauchl gabadaya haka kuwa akayi cikin qanqanin lkc aka aiwatar da abinda na fada. ’
Dagowa nayi na kalli Hajiya nace“Hajiya saime kuma kikeson nayi mlki” murmushl tayi tace “nayi halhuwar albarka Hafeezu Allah yayi maka albarka ya dawo maka da farin Clkinka Hafeez Allah ya baka zuri’ar da zasu zama gatanka anan gaba Hafeez nayi nadama da danasanin abubuwan da nayi maka har sukaja kayi fushl dani ka tafi ka barni cikin tsaka mai wuya bayan tafiyarka nice nake kula da lamuran Amnah duk wani abu da za,a fadamin game da ita bana yarda nasha zuwa domin duba lfyr cikin da na qwallafa raina akai ina ganinshi kamar kai amma idan naje saina tarar da Ita da mata suna harkokinsu bantaba damuwa ba saboda an kashemin zuciya kai tafl ta tafi harta fara shigo da maza sau yafi goma ina zuwa ina tarar da in da WaZiri lliyasu suna ha’lntarka a lkcn ne na fara damuwa na klra uwarta Hajiya Sogiji nayi mata mgn alkuwa sai ta hauni da fada har tana cewa wai ai gara Amnah da qanin mahalfinka take harkarta kaikuma fah wa yasanma wannejinsun ka aJiye kake badalarka da ita har kayi mata Ciki ta halfa maka dan dakan dauka kacika duniya da hotunanka dashi kana fakewa da cewa wai tsananin kamace kawai bayan ga juninka nan yana gudana a jikin yaron, har cemin tayi kamar yanda kake da da a bayan fage to Itama Amnah da bakason ta samu salta samu kuma Allah ya dubeta ya bata dan baqin Ciki saldai ya mutu waI dani dakai din babu yanda zamuyi da ita, ban sake magana ba kawai saina duqufa addu’a da fatan Allah ya dawomin dakai kazo kaga yanda komai ya lalace a masarautar ka kwatsam bayan wani dan lkc sai Amnah ta fara naquda muna kalta asiblti ta haifo yarta mace me kama da Waziri Iliyasu hasken fatarne kawai na Amnah aikuwa magana ta rinqa zagawa a fada da wajenta cewa yafa ba taka bace ta Waznri iliyasu ce domin damacan tun kafin kabar qasar Bauchi shine kwartan Amnah tun zamanin Farha duk ranar da kake tare da Farha to ranar ita kuma tana tare da Waziri llIyasu wannan abu ya daki zuciyata data yan uwanka musamman Hasheem da Umaima shI Hasheem yana mamakin yanda abubuwan sukayi tsanani haka inda ita kuma Umaima take kuka tana
fadin ai duk abmda ya faru kitimurmurar mahalfiyarsu ce Hajiya Sogiji.
Bayan komai ya lafa mun zubawa sarautar Allah ido wata ranar juma’a data kama ana gobe sunan yar da Amnah ta hanfa muna zaune a parlour nida yayarka Hauwah da Hajiya Kilishi da Hasheem da sauran yan kawai saiga Umaima ta fada tana wani irin kuka tana cewa “ innanillahi wa innah ilaihir raji’un La’Ilaha illah anta subhanaka inni kuntu mlnazzalumln Hajiya sune wlh sune ashe sune sukayiwa Aunty Farha kurciya ta bata tabarYaya saboda kada ta halfi Yariman Bauchi ashe sune Hajiya sune suka shiga tsakaninki da Mai martaba suka sanya mlki tsanarsa dajin haushinsa sune suka sake kada Mai martaba duniya saboda su dafe dukiyarsa ta hanyar cikin jIkin yaya Amnah wanda bashida wata alaqa dashi ashe Waziri llIyasu shine uban yarinyar nan da yaya Amnah ta halfa wlh da gaske nakeyi Hajiya mun shiga ukunmu Hajiya tayi nisa a shirka ta bata Allah dama ba Hajiyan muce ta haifemu ba haqqin rai…” yarinyar tana fadin haka ta yankejiki ta fadi tana wani irin kuka mecin zuciya. 
Dukkanmu kanmu kullewa yayi da mamakin wannan al’aman daqyar Hasheem ya miqe yana kuka ya fita ya nufi bangaren mahalflyar tasu yana shiga ya rufe Amnah da duka kamar Allah ya alkoshi bayaji baya gani Hajiya Sogiji tayi yunqurin hanashi bisa tsautsayi ya bigeta ta fadi a sume mu da muke shigowa muka nufeta muka dagata aka fice da ita akabar Amnah kwance cikin jini muna zuwa aka shiga da ita emergency aka tabbatar mana da tasamu shanyewar barin jiki wlh Hafeez tundaga wannan lkcn gda ya dada rikicewa Amnah ta samu goyan bayan farkanta da yake iqirarin ka mutu yanzu shine Sarki suke tsula tsiyarsu son ransu babu mece musu donme, tunda Hajiya Sogiji ta kwanta ciwo Amnah bata taba zuwa ta dubata ba idanma akayi mata mgn sai tace ita bai shafeta ba yayanta sune dolenta ba Itaba haka akaci gaba da cakudawa har kawo yanzu da Allah ya dawomin dakai” hawaye na share me zafin gaske wannan wacce irin musiba ce me Farha tayi musu haka mena tare musu da suka rabani da farin Clkina?” Tabbas badan Hajiya tasa na saki Amnah ba dasai na kasheta har lahira kuma har yazu inada wannan burin a raina. 
Bayan Hajiya ta gama bani lbr ta qara riqe hannuna tace “ Hafeez Ina zaka samomln wannan yaron wlh kullum da qaunarsa nake kwana nake tashi ka karboshi mu rikeshi idan da halima ka yanta uwarsa ka aureta ku daina wannan qazamar rayuwar don Allah kaji” 
sunkuyar da kaina nayi qasa ina share hawayena nace “wlh Azeem Hajiya bansan mahaifiyar yaronnan ba ban taba ganin mahaifiyar Abdallah ba kiyi believing dina iyakar abinda na sani Abdallah maraya ne mahalfinsa ya mutu tun kafin a hanfeshi sannan dane ga qanwar Momy mahaifiyar abokina Nasir mutumin Kadunan nan da mukayi karatu dashi a Rasha iyakar abinda na sani kenan” sake kallona tayi tace “na yarda dakai Hafeez amma ikon Allah  wlh yaronnan kamar kai lkcn kana quruciyarka inasonshi Hafeez ka roqesu subamu shi don Allah” hawaye na sake daukewa a idona nace “zan gwada hakan nima jinsa nake a cikin jinina” tun daga wannan lkcn Hajiya ta dauki son duniya ta dorawa Abdallah duk maganarta bata wucce Abdallah wani lkcn ko banyi niyyar zuwa Kaduna ba zata sani a gaba tana roqona naje na gano mata alawar zuciyarta tasha sani na dauko matashi kusan duk zuwan da nakeyi na daukeshi Itace take sani idan zasu rabu kuwa da kuka suke rabuwa yanayi tanayi. 
Daddy lamarin sabanin da muka rinqa samu da Farha shine yafi komai bani mamaki tun farkon fara aikinta a asibitina nake son haduwa da ita amma tsayin shekara bakwai dinnan Allah bai taba gama fuskokinmu ba sai yau Dady indai Farha itace mahaifiyar Abdallah to shakka babu nine mahaifinsa wannan shine abinda zan iya fada muku a taqaice Ina fatan ku gasqatani nine mijin Farha da muguwar qaddarar mu ta nisanta mu da juna tsayin shekaru” miqewa Farha tayi zatabar gurin yayi saurin ruqo hanunta Daddy ya dubeta yaga yanayin kallon da takeyi masa ya nuna mata guri yace “zauna” komawa taYI ta zauna ya sake dubanta yace “na gamsu da maganganun Hafeez Farhanah kuma tabbas biri yayi kama da mutum dubada tsananin kamarsa da danki Abdallah amma bazan katsi hanzarinki ba ko kinada abln da zakice game da hakan” dagowa tayi ta kalli Daddy ta girglza kanta tace “nidai Iyakar saninan nasan inayi masa kallon sani amma bansan wata alaqa tsakanina dashi ba bansanshi a matsayin muji ba amma ‘tabbas jikina yana bani shidin makusanci nane”…. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]