[Advertisements⬇️]

FARHA CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

FARHA 

CHAPTER 12
Matsowa Momy tayi ta shafa kanta tana zubar da kwallah tace “danki ne baiwar Allah ki godewa Allah daya saukeki lfy Allah ya raya manashi yayi masa albarka yanzu inane yake miki ciwo?‘ 
Dago idonta tayi ta kalleta har yanzu ruwa ne yake zuba a idonta ta kada kai alamar babu komai ajiyar numfashi sukayi Daddy yace ” alhmdllh tunda babu abinda yake miki ciwo Momy bata abinci taci saita bamu labarinta saboda mu samu ku mayar da ita inda ta fito” kallonsa takeyi kamar wadda ta warke daga ciwon makanta har Momy ta zubo mata abincin ta hado mata tea me kauri Maryam ta karba ta zauna a kusa da ita ta rinqa bata tanasha saida ta shanye tea din tsaf sannan taci faten doyar kadan tace ta qoshi. 
Kyaleta Maryam din tayi ta kalleta tace “ya sunanki Aunty?” dago idonta tayi cikin hawaye tace “nidai kamar sunana Farhanah amma bani da tabbas akai?” Kallon Momy Maryam tayi ta share hawayen daya zubo mata ‘tace “anya Momy ba daga Sarcartry ta gudo ba kinji fah sunanta ma bata bambamcewa” girgiza mata kai tayi tace “bari kawai auta lamarinta akwai daure kai kinga fah sarqar wuyanta itace irin wacce muka gani lkcn da mukaje Dubai akace 5 million na fasa siya Maryam wannan ba matar qaramin mutum bace dole akwai wani boyayyen abu ba fitowar lfy bace tashi ki hada mana kaya mu tafi gida mayi mgnr acan” Miqewa Maryam tayi ta shiga diban kayan tana fita dasu har ta kwashe komai ta karbi babyn ta fita ita kuma Momy ta kama Farha suka fita a hankali har suka isa inda motar take suka shiga suka nufi gda suna zuwa Momy ta kaita dakinta ta dora ruwan wanka a gas sannan suka shiga gyara mata wani daki wanda yake komai akwai a ciki ba wani babba bane sosai gadone by six sai wadroop ta bango qarama sai tv plasma da qaramin fridge. Momy ce ta shigo tace ‘taso yata na gasa miki jikinki kinji haihuwar fari sai an kula sosai’ batayi mata musu ba ta tashi tabita toilet din dake wajan gidan babbane sosai tasata ta cire komai najikinta sai pant kawai ta zaunar da ita saman kujera ta fara gasa mata jikin da ruwan zafin towel ne babba take mammatsa mata tun tanajin zafin ruwan har ta daina bayan ta game mata ta zuba mata wani ruwan tace ta shiga ciki a shigarne sukayi artabu da qyata zauna a ciki damma ta hadu da Momyn qaqqarfar gaske da bazata shiga BaSai yamma liqis King Hafeez ya dawo gda kasancewar fitace ta gaggawa sukayi da governor zuwa wata ziyarar aiki tun a gurin yaji gabansa ya tsananta faduwa yana zuwa gdan bangaren Farha ya nufa harda gudu gudunsa yake hadawa ya shiga ya tambayi baiwar dake mata aikin ciki Ina take sunkuyawa tayi tace “wai dama ba tare kuka fita ba ranka ya dade tunda ta karya ban sake ganinta ba tun dazu jiran fitowarta nakeyi” bai jira qarasa maganarta ba ya nufi daya parlourn yana qwala mata Kira “Queen! Queen” Kina inane gani na dawo fito kiji jarabawarki ta fito tayi kyau sosai ina tayaki farin ciki dole nayi gifting nak ….. daukewa numfashinsa yayi lkcn daya bude dakin yaga kayanta kaca kaca’ tare da akwatunanta duk a wargatse, shiga yayi da sauri yana dube dube‘ yana cewa “fito mana matata banason wannan wasan don Allah fito na tayaki gyara kayan nasan duk shirin haihuwa akeyi babyna ya kusa zuwa duniya” zama yayi yana kulle akwatinan yana maidasu inda suke saida ya gama tsaf sannan ya nufi toilet a bushe ya tarar da bathroom din babu alamun an shigeshi nan kusa. 
A gigice ya fita ya nufi part din Amnah yana kwala mata Kira “Amnah ke Amnah ina Queen ne ina tace miki ta tafi fadamin’ yana mgnr yana banka qofar, a zaune ya ganta tana taunar Chingum shaqota yayi kamarzai kasheta cikin qufula yace “Kinajina ina tambayar ki ina 
Queen take ne?” Yatsina fuska tayi tace “bansani ba ajiya ka bani ita kome da zakazo kanamin ihun ina wata banzar matarka’ 
Sakinta yayi a fusace ya juya ya fice ya nufi cikin gdan duk wanda yaga yanda yake tafe a haukace saiya ratse ya bawa manya guri” bangaran Hajiya Kilishi ya shiga ya fara doka mata kira ta fito a tsorace tace “lfy Sarki?‘ dubanta yayi yace “ina Queen Hajiya?“ Girgiza kai tayi tace ‘rabonta danan kwana uk…‘ Juyawa yayi ya shiga part din Hajiya Fulani a parlour ya tarar da ita a zaune yana shiga ya zube yana haki yace “Haj… Hajiya ina Queen? Queen Farha nake nufi” dubanshi tayi da rashin fahimta tace “a,a ba kai kacemin ka hanata fita ba saboda tayi nauyi ina zata tana sashinta” kallon Hajiyan yayi yanason gasgata abinda take fada miqewa yayi yana layi yace “bate sashinta alamu sun nunamin bata cikin gdannan saboda na tuna dana gyara akwatunanta ashirin da uku na gani babu daya a ciki amma Ina zata Hajiya? Ina ta tafi”: bata fadamin ba? Inane da haryau yasa Queen ta fita babu izini na?‘ Yana mgn yana tafiya harya fita harya wucce bangaren Sogiji ya dawo ya shiga Amnah ce da Hajiya Sogijin da Umaima suna zaune sunata dariya kallonsu kawai yayi ya kira Umaima a tsorace ta tashi tajejanta yayi har waje sannan ya zube a gabanta ya ruqo hanunta yace ‘Umaimah ina kikaga Queen ta shiga duk na duba ko Ina banganta ba“ zaro ido waje tayi tace ‘wlh Yaya bana gda amma dazu na dawo daga makaranta naga motar ta fita daga gdannan nayi tunanin kaine a ciki?” fuzge hanunsa yayi yace “kika barta ta fita Umaima meyasa kika barta bafa ta taba fita da mota ita kadai ba” da gudu yabar gurin ya qarasa qofofin kamar zautacce ya rinqa tambayar sarakunan qofar ko sunga Queen? Amsar dayace data Umaima basuganta ba amma sunga motarta ta fita dazu, ‘ 
Tsayawa yayi sakatoto har Umaima tazo ta iskeshi a gurin tace “kaje gdansu mana Yaya kocan ta tafi” juyawa yayi da sauri ya dauki mota ya fice da mugun gudu ikon Allah ne kawai ya kaishi Hayin daudu lfy amma ba nutsuwarsa ba yana zuwa ya tarar da Baffa a qofar gdan yana alwalar sallar magaruba baiko ganshi ba ya danna kai gdan yana Kiran sunanta fitowa su Mama sukayi daidai lkcn da Baffa ya shigo ya qarasa kusa dashi yace ‘batazo nan ba Mai martaba Ify?” ruqo Baffa yayi yace “batazo bafa kace Baffa aa tazo wlh a fitomin da matata kawai” daqyar Baffa ya shawo kansa ya yarda batazoba gaba daya ya canza kala cikin mota ya koma ya zauna ya kifa kansa yana ambaton ‘Innanillahi wa innah ilaihirraji’un’qarasowa Baffa yayi shima cikin tashin hankali yace “meya faru ne Hafeez ina Farhanan tace maka zata?” dago idanunsa yayi da suke tsiyayar da hawaye yace “wlh lafiya muka rabu da ita batacemin zata ko inaba Baffa ka taimakeni kace ta dawo wlh babu wata rayuwa da zata saura gareni idan babu ita Baffa cikin jikinta ya kusa fitowa duniya kada taje inda zasu cutu…‘ Dafa kafadarsa yayi yace “kayi hqr kasan halin yayan yau muje gdan yan uwanta ko taje can” key yayiwa motar suka nufl gdan Rahmah suna zuwa tace “ita rabonta da Farha tun ranar bikinsu itama Rahina haka tace gidan Binta ne sukayi sa,a suka tarar da mijinta yace yaga wuccewar motarta ta jikin shagonsa kuma da alamun tasha ta shiga fita sukayi harda Shafi’u mijin Binta suka nufi tashar wannan karon harda jami’an tsarojiniyar gidan sarautar ne yasa kowa dake tashar shiga hankalinsa a waje yasa akayi parking ya fito kamar wani burgu ya shiga tashar yana dube’dube har ya isa inda yaga motarta suna zuwa gurin sojoji suka shiga harbin iska shikuma ya matsajikin motar tare da damqo dattijon me facin nan yace “ina me motar nan?” cikin rawar murya yace “Allah ya taimakeka tazo tun safe ta bani mukulli da takardar nan tace drive zaizo ya karba…’ fusgar takardar yayi ya bude ya soma karantawa kamar haka. 
Na tafi ni kaina bansan inda zani ba bansan meye ya fito dani ba kayi hqr wlh bansan ya rayuwata zata kasance idan babu kaiba inayi maka fatan alkhairi da fatan rungumar qaddarannu inda rabo wataran zamu hadu idan kuma babu kayimin addu’a nasan zan rigaka mutuwa domin akan siradinta nake duk da bansan wa nake rubutawa wasiqar ba amma inaji a jnkina makusanci nane,”‘ ‘”Kayi hqr! Kayi hqr!! Kayi hqr!!! Taka 

FARHANAH USMAN.”‘ 

Yana gama karanta abinda yake cikin takardar ya yankejiki ya fadi sumamme nandanan dogaran da sojojin suka kewayeshi aka daukeshi cak aka sanyashi a mota aka nufi babban asibitinsa dashi ana zuwa likitoci suka tashi a kansa domin ceto rayuwarsa bugun zuciyarsa ne ya tsaya cak daqyar aka samu ya fara dawowa wasu cikin jami’an tsaron suka fantsama garin Bauchi domin nemowa Sarkin su farin cikinsa wasu kuma suka tsaya a gurinsa aka kira rundunar tsaro ta qasa gaba daya aka sanar dasu batan matar Sarkin Bauchi tuni lbr ya cika gari‘ cewa matar Sarki amaryarsa ta bata da tsohon ciki kowa yaji lbrn sai jikinsa yayi sanyi saboda lamarin da daure kai ace mace ta bata a garin Bauchi harda tsohon ciki duk wani wanda yake gdan sarautar hankalinsa ya tashi hatta Umaima amma banda Amnah da Sogiji da sukejin kamaran yaye musu wani baqin cikin duniya ko rashin lfyr Sarki Hafeez bata wani damu Amnah ba qarshema cewa tayi idan ya gaji da zaman asibitin zai warke idan kuma yana ganin bazai hqr ba yabita inda ta tafi shida Farha dai sai a lahira. ‘ 
Kwanansa tara a asibiti baisan komai dake wakana ba a hakan Amnah da Hajiya Sogiji suka samu damaryin abinda sukeso ta debi kudi son ranta ta kaiwa boka shi kuma ya tabbatar mata da babu lbrn Farha da cikinta a duniya dodon tsafi ya tabbatar masa mota ta niqesu 
sun hade da kwalta, ranta yayi fes hankalinta ya kwanta ita da uwar goyonta suna tsula tsiyarsu son ransu. 
Ranar daya farfado yana bude idonsa tunaninsa yana dawowa kansa sunan Farha ya fara kira Hajiya dake kusa dashi ta riqo hanunsa tana share hawayen tausayin dan nata duk wani masoyinsu dole ya tausayawa Sarki Hafeez qiri’qiri ace matarka da danka su bata lfy yace “ina Farha Hajiya nasan yanzu ta haihu meta haifamin mace ko namiji?” Hajiya meyasa baki tahomin dasu ba naso ace ina farkawa ita na fara gani da dana bakeba Hajiya ki tashi kije ki tahomin da matata Hajiya Queen dita nakeson gani…’ 
Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tana hawaye Baffa ne ya shigo yace “Alhmdllh Mai martaba an tashi sannu kaji” jan qafarsa yayi ya qarasa gaban Baffa yace “Baffa kayiwa dana huduba k0?“ Queen tana gdanka k0?” Kada kuyimin sakaci da rayuwar iyalina sunada muhimmanci a gurina” shiru Baffa yayi tare dayin qasa da kansa shima yana share kwallah daidai lkcn Abokinsa Na’im ya shigo dakin yace “yawwa Na‘im kaine zaka fadamin gsky ina Queen take ta haihu ko nasan duk abinda ta haifa kama take dani don Allah jeka daukomin ita koda yakema kawai daukeni ka kaini inda take kaji” ya fada yana langwabar dakai so Na‘im yake ya aro nutsuwa yasawa kansa ta yanda zaiyiwa abokin nasa bayani amma ya kasa daqyar yayi qarfin halin kama hanunsa ya jashi ya cafe yace ‘babu inda zani fah ya ina tambayar ku lbm iyalina duk kunyimin shiru wlh idan Farha ta mutu saina kashe kaina saboda banga amfanin rayuwar da babu farin ciki a cikinta ba” kamashi Hajiya Fulani tayi ta zaunar dashi daqyar tace. tawakkali shine ya kamacemu Hafeez duk yanda zamuyi muga mun dawo maka da Farhanah cikin rayuwarka munyi abin yaci tura duk wata kafaryada labarai dake qasar nan an baza cigiyarta da hotonta amma kullum lbm dayane saboda haka ka rungumi qaddararka kaci gaba da addu’a” tunda ta fara mgnr yake kuka kamar qaramin yaro harta gama baice komai ba sai shatatar hawaye da idonsa yakeyi a hankali kuma a sanyaye yace “Allah kanaji kana gani Allah baka zalumci kuma baka yarda da zalumci ba Allah kasan wadanda suke da hanu a batan matata Allah ka bayyana minsu koda mahaifiyatace Allah ka tsaremin su idan suna raye idan kuma sun mutu Allah Nima ka gaggauta karbartawa rayuwar naje na tadda farin cikina’ Baffa ne ya rinqa tausarsa da bashi hqr amma duk da haka da yamma jikin nasa qara rikicewa yayi saida yayi sati biyu a haka shiba mara hankali ba shiba me hankali ba Hajiya Fulani ce taga dannata ya zauce hakan yasa tasa aka rinqayi masa roqon Allah tare da addu’ar Allah ya bayyana masa iyalansa Baffa shima yana iyakar qoqarinsa wajan ganin surukin nasa bai susuce ba to sun danyi nasara kadan tunda ya rage surutan da yakeyi saidai kullum bashi da zance saina Queen duk yanda kuke dashi indai ba hirar Queen Farhansa zakayi masaba to bazai saurareka ba hakan ba qaramin qara dagawa Amnah hankali yayi ba saboda kwata kwata‘ bashi da lkcnta duk wata alaqa ta aure ya yanketa da ita baya nemanta idan kuwa takai kanta to ranar wulaqanci ne zata shashi harta shayar da wani abubuwa duk sun rikirkice mata memakon ta samu yanda takeso saima qara shiga kunci da tayi tasha samunsa ya sanya hoton Farha a gaba ya zuba tagumi yanata kuka tare da Kiran sunanta ko bacci zaiyi da hotonta yake kwanciya idan kuwa tayi karambanin daukewa to ranar zatasha ruwan bala’i da tujatarsa ita yanzu kallon mara cikakken hankali ma takeyi masa saboda komai nasa ya zama daban dana mutane. 
A bangaren maijego Farha kuwa kulawa sosai take samu gun mutanen da Allah ya hadata dasu Alh Usman da Hajiya Hadiza sai yayansu biyu Nassir da Maryam Yaya Nasir yayi aure da matarsa Khadija itama mutuniyar kirki shekararsu biyu da aure k0 haihuwar fari batayi ba shiyasa jama’ar gdan suka dauki son duniya suka dorawa jaririn tare da tausayin rayuwarsa shida mahaifiyar sa. Kwanaki uku da haihuwar Daddy ya sameta har dakinta saida ya qarasa gadon jaririn ya daukoshi yana yi masa wasa yana dariya yace “wannan ragone bashi da aiki sai bacci a haka zaka zama jarumin kayy gsky soja zaka tafi” dariya Momy tayi tace “aa dai Alh kishine dai wannan saboda nayi sabon ango akemin ciki baqi” dariya sukayi dukkansu yace “farha duk yanda zamuyi dake munyi ki sanar damu daga yankin da kika fito kin kasa saboda haka zamuci gaba da addu’a Allah ya bayyana miki danginki ya dawo miki da tunanin ki yanzu yaron nan wanne suna kike ganin ya dace a sanya masa saboda cika sunnah kinga yau gashi har kwanansa uku” 
Ajiyar zuciya tayi ta share hawayenta tace “Daddy kayi masa huduba da duk sunan da kaga ya dace dashi wlh banida zabi” murmushi yayi yace “to na gde da wannan karramawa taki farha Allah yayi miki albarka na kirashi da Abdallah ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarsa yasa rayuwarsa ta zama abar koyi kuma abar kwatance ke kuma ki rubuta duk abinda kikasan kina buqata sai nabawa Momynku ta siyo miki” 
Gdy tayi ya miqe ya miqa mata Abdallah yace “bashi da aiki sai bacci sai ci gashinan ya tashi yana wawurar abinci wannan saboda kai zan share gona” 
Ranar suna Daddy raguna biyu ya yankawa Abdallah akai shagalin suna sosai Momy tacewa mutanenta qanwarta ce tazo daga Sokoto ta haihu aikuwa taga kara mutanen sun nuna mata halacci da gata itadai idan dadin yayi mata yawa kawai saidai ta fashe da kuka. Haka rayuwa taci gaba da garawa Farha ta saki jikinta sosai tana rayuwarta me dadi a inda Allah ya ajiyeta hoton mijinta dana mahaifinta kullum saita kallesu tayi kuka abin mamaki ta gane Baffanta amma ta kasa gane Sarki Hafeez saidai yanayi mata tsananin kama da danta Abdallah wannan dalilin yasa take yawan kallonsa idan tana kallon hotonsa sai tarinqa jin wani sanyi a ranta ta rasa meyasa. 
Abdallah wanda take Kira da Sarki yanata girmansa yaron kyakkyawa Mai shiga rai fari tas dashi kamar mahaifinsa komai nasa na babansa ne har jikinsa da tsayinsa, sunsha tambayar ta meyasa take cewa Abdallah Sarki saidai tayi murmushi kawai saboda ita kanta baza tace ga dalili ba kawai taji sunan yayi mata dadi ne watan danta biyar Daddy yaga zaman nata yayi tsayi yasa aka zana mata WAEC saboda ya lura tanada brain sosai duba da yanda take nunawa Maryam abubuwa da yawa a harkar karatun boko dana addini musamman bangaren Science jarabawa ko tayi kyau sosai Daddy ya biya musu suka zana Jamb itama Allah ya taimakesu tayi kyau aka fara nema musu Admission a AB.U Zaria cikin ikon Allah suka dace Farha ta samu abinda take buri karatun Science Daddy ya siya musu mota suka fara karatu ka’in da na’in babu wasa Maryam ta zama yar uwarta qawarta komai nasu tare kuma iri daya. 
Karatunsu ya fara nisa sosai kuma ana samun abinda akeso saboda Farha ita dama akwai kwashewa tanaja sosai duk Exams dinta daga Excellent sai Very good bata taba samun qasa da haka ba aikuwa lecturers sukayi mata cah nanfah tayi kicin kicin tace ita matar aure ce tun ana kawo Mata caffa a school din har aka daina aka kyaleta take abinda ya kawota a haka aketa tafe Sarki har yanada shekara uku lkcn suna level 300 shima aka sashi a school ta yayan masu dashi shima yaron yayo gado tun a pri nursery ya fara daukar fast class. 
Suna zanajarabawar end session na 300 level Aubty Hafsa matar Yaya Nasir ta haihu aikuwa Sarki ya tattara ya koma can da zama saboda shi akwai son yara shima Yaya Nasir yaji dadin hakan saboda yasan zasu samu damar yin karatu sosai shidai kam yaron na masa kama da wani Abokinsa da sukayi karatu a Rasha yana mamaki kamar hartayi yawa Prince Hafeez da dan qanwar tasa Sarki. 

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]