[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A CHAPTER 7
Bayan sati daya na farajin sauk’i, harzama na farayu sabanin da da ko zaman ma bana iyawa, 
Sosai Dr. Rafl’iq yake bani kulawa, komai shi yakeyi min, hatta da magani da kanshi yake siyamin ya bani ruwa insha, 
Kawayena Zarah da Rabiatu kuwa tamkar ‘yan uwana na jini, duk wani abu daya dace suna yiminshi, 
Abun haushi kuwa har yanzu Gentle batazo da dubani ba. 
Kwatsam ina zaune Rabiatu da Zarah na gefena, labari muke sosai suna bani dariya, hakan yasa hankalina yadan kwanta, a gidanmu kuwa har yanzu basu sani ba, saboda Dr. 
Raflq yace kar in fada masu abunda ya sameni harsai idan na koma gida dan kar in tayar masu da hankali. 
Securities ne suka shigo roon din har mutum hudu, bayansu kuwa wani babban mutum ne sanye da babbar riga, 
Bayan shigowarshi saiga wasu securities din guda hud’u a bayanshi. 
Cike da girmamawa muka gaishesu, Mutumin kawai ya amsa sallamar, tun bai rufe baki ba saiga wasu manyan mutanen sun 
shigo masu yawan gaske, har room dinma bai iya d’aukarsu ba wasunsu a bakin kofa suka tsaya. 
Hankalina ya tashi sosai ganin manya manyan lecturers dinmu ne, Kallo suka bini dashi baki daya kmn sukayi min ya jiki, 
Wancan mutumin wanda ya fara shigowa ya gyara zamansa a plastic chair dinda yake zaune yace 
“Aisha Abu bakar ko?” 
Cike da mamaki na d’aga kaina alamar ehh, 
“Good” ya fada tare da zaro wata ‘yartakarda daga aljihunshi na gaba. 
Dan rubutu yayi sannan ya mikata ga wani yace “PA a ajiye min wannan” sannan ya juyo gareni yace “Ya jikinki?” 
Alhamdulillah na furta Cike da alamartambaya. 
“Karki damu ba wata matsala bace kinji, sunana Khalil MA Khalil” ya furta tare da mikewa tsaye yabar d’akin, 
Securities dinshi ne suka mara masa baya sannan sauran malamn ma suka fita. 
“Ya Salam” na fada sabida jin sunanshi, Da fitarsu Zarah tayi ajiyar zuciya tace 
“VC nefa da kanshi yazo dubaki Ummimah, lallai kin ciri tuta, wata kila sun samu labarin abunda aka mikine sukazo dubaki”, Rabiatu tace 
“To a ina zasuji labarin? Ke VC fa, wa zai fada masa? Kiga gayyar da sukayi fa“. 
Nidai saurarensu kawai nake amma fa sam hankalina bai kwanta da zuwansu ba. 
Bayan kwana biyu aka gama exam aka rufe School baki d’aya, 
A ranar nima na nemi sallamah, saboda Zarah da Rabiatu bana son na shiga hakkinsu, 
sunce wai ba zasu tafi su barni ba. 
Babu yanda Dr. Rafiq bayyiba akan inyi hakuri in kara samun sauki amma kuma na nace sai ya sallameni, hakan yasa ya bani takardar sallamah tare da kudi masu yawa yace inyi kudin mota. 
Karfe hudu na rana na sauka Katsina, Akwatina naja tare da tsayar da mai napep nace ya kaini Saulawa, 
Babu bata lokaci kuwa muka isa gida. 
Cike da farin ciki Afrah ta tareni, jakata ta karba tare da kaita d’aki, “Afrah ina sauran ‘yan gidan ne?” Na tambayeta bayan ta zauna tana min saanu da zuwa. 
“Sun tafi sukai Amrah asibiti, booking zasuyi mata, kinsan ance wai nanda wata biyu ko 
uku indiyawan nan zasy dawo”. 
Harda tsalle nayi dan murna, hakan yasa na fama ciwona sabida har yanzu raunukana basu gama warkewa ba. 
Saurin dukewa nayi ina matse matse, Da tausayi Afrah tace min “Bakida lafiya ne Aunty?” 
Kai kawai na daga mata alamar ehh, “Ayyah! Sannu gashi kuma kun gaji, kiyi wanka kam nan na kawo miki abinci, nasan su 
Baba ma yanzu suna hanya saboda tun safe suka tafl”. 
Haka na tashi jiki babu kwari na nufi toilet, 
Har ga Allah naji dadin bayanin Afrah, 
Bayan nayi wanka najiyo muryar su Mama, 
Aikuwa da sauri na saka kayana na nufi parlor k0 mai ban shafa ba. 
Har kasa na gaishe dasu Baba, Sunji dadin ganina sosai Baba yace “Wannan zuwa na bazaka, baku fada mana zaki dawo ba ai”, “Ehh Baba, nafison nayi surprising nakune dama“, “Gashi kuwa kinyi ai hankalinki ya kwanta” mama ta fada tana kallona. Baba ya k’ara yimin bayanin komai, Naji dad’i sosai na matsa inda Amrah take, “Sannu kanwata, ya jikin naki?”, “Jiki da sauk’i Aunty Ummimah, ya karatu?”, “Alhamdulillah, Allah ya baki lafiya”. 
Bayan naci abinci nayi tunanin in fad’a masu abunda ya sameni amma kuma na fasa, Da zarar nayi kokarin fadi sai wata zuciyar ta haneni, Hakan yasa nayi shiru nabar maganar a cikina dukda cimin rai da takeyi. 
Idan ma zaune nake na tuno da wannan abu sai hankalina ya tashi, kuka sosai nakeyi ni 
kadai ba tare da kowa ya sani ba, Wata rana ina cikin yin kukan Mama ta shigo ta sameni a haka, Sallamah uku tayi amma duk bansan tayi ba, Karisowa ciki tayi ta ganni inata sharar kuka, Hankalinta tashe ta tsuguna kusa dani tace “Ummimah lafiya? Me sameki kike kuka?”. 
Zabura nayi tare da share hawaye ina fad’in “Babu komai mama”, 
“Kamarya babu komai? Babu komai shine kike kuka?” 
Gyara zama tayi sannan tace 
“Nasan babbar matsakarki itace ciwon ‘yar uwarki, dan Allah ki cire wannan damuwar, insha Allahu karshen cutarta ya kusa zuwa, saboda muna sa ran nanda wata uku indiyawan nan zasu dawo, kuma wannan karen ance zasu iya tafiya da marasa lafiya a kasarsu, kinga kuwa insha Allahu Amrah ta kusa rabuwa da cutana har abada”. 
Goge hawaye nayi nace “Shikenan Mama, Allah ya bata lafiya” na fada kamar da gaske abunda ya sakani kukan kenan. 
Murmushi tamin nima na miyar mata dana karfin hali, “Kizo Afrah ta gama girki, nasan kina jin yunwa”, Tashi nayi nabi bayan Mama har parlor. 
Satina biyu a gida Mama tamin maganar Gentle, gar saida gabana ya fadi data ambata min sunanta, “Naji Salmah shiru kema kuma bakije inda takeba, Allah yasa dai lafiya”, Gabana ya fadi na rasa abunda zan fada mata, sai daga baya nace “Ta fad’a min cewa ba’a garin nan zatayi hutu ba, wai Kaduna zata tafi” nama Mama k’arya, “Ahh to babu komai ai, Allah ya dawo da ita lafiya” “Ameen” na amsa mata dashi cikin raina kuwa wata irin kunar rai nakeji, saboda yanzu babu wadda na tsana a doron k’asa kamar Salmah”. 
Sannu sannu har hutunmu ya k’are na fara haramar yin registration, Da k’yar da wahala Baba ya samo min kudinda zanyi, Koda naje banki zan saka kudin abun mamaki da zarar an saka password dina baya buduwa, An gwada kusan so biyar amma portal d’ina yaki ya bud’u, Zarah na kira a waya na fad’a mata abunda ke faruwa, “Wannan ba matsaka bace, akwai sauran lokaci kuma kinsan akwai table payment, ki bari a koma School sannan kawai ki biya acan, kinsan dama bank payment din nan 
matsalace dashi”. “Hakane kawata, to nagode sosai”. 
Da haka na kashe wayata tare da ajiyeta k’asa. 
Sati daya daya zagayo na fara shirin komawa, 
Su Mama sunyi mamaki da sukaji nace masu ni kadai zan tafi, Sallamah nayi dasu na nufu tashar mota, 
Babu bata lokaci muka sauka cikin garin Jalingo. 
Wurin biyan kudin naje, Abun mamaki ki acan dinma babu sunana, Abu wasa wasa  har maganar taje sama, Anan ne aka tabbatar mun da anyi expeling d’ina from the University, saboda kamani da 
akayi da zubar da cikin shege, An samu takardar asibiti wadda ta tabbatar da hakan, sannan kuma likitan daya dubani 
da kanshi shi ya tabbatar da hakan. 
Takejikina ya dauki rawa, bakina ya kasa furta komai, kaina ya ringa jujjuya min, 
lummm na fadi kasa sumammiya. 
Tun daga nan ban k’ara sanin abunda yake faruwa ba, sai farkawa nayi na ganni kwance kan gadon asibiti, gefena Zarah da Rabiatu ne sunyi tagumi sunajiran tsammani. 
Kallo daya na masu suka bala’in bani tausayi, domin kuwa na kara tabbatarda sune kawayena na gaskiya wanda suke kaunata. 
Basu ankara da farkawata ba saidai shesshekar kukana sukaji, Da hanzari kuwa suka mike tsaye, Rabuatu ta furta “Alhamdulillah tunda kun tashi, sannu Aisha”, Kai kawai na daga mata ina hawaye sosai saboda kara tunowar da nayi wai yau nice aka kora daga makaranta, an cuceni kuma an hanani kuka. 
Zarah ta zaro dan kwalinta daga kanta dake cikin hijabi ta miko min 
“Bana son kina kukan nan Aisha, ya kamata ki dauki kaddara saboda ‘KOWA DA K’ADDARARSA,’ ba wai Allah baya sonki bane yayi miki hakan, kawai dan ‘JARRABTARKI KENAN’ kuma ina fatan zakiyi kokarin ki cinye wannan jarabawar, 
Wanda suka cuceki kuma ki barsu da Allah shi zai miki sakayya, kiyi fatan Allah yasa 
hakan shine mafl alkhairi a gareki, ungo wannan ki share hawaye” ta miko min dan kwalin nata. ‘ 
Karba nayi na fara share hawaye saidai kuma da zarar na share sai wani ya fito, Da kyar na iya furta “Babu komai kawayena, na yarda na kuma dauka cewa KADDARATA CE’ banida hanyar maganceta, na barwa Allah komai saboda shine zai saka min, dan Allah wacce asibiti nake?” Zarah tace “inda aka kawoki ne last time, munje School clinic anki karbarki sunce saboda wai ke yanzu ba student bace”. 
Saurin mikewa nayi dukda ciwonda duk gabobin jikina suke min, 
“Na gwammaci in mutu akan in zauna a asibitin nan, Zarah mesa kuka kawoni nan? Kunsan kuma irin sharrinda suka kullamin, suda kansu suka rubuta takardar karya cewa an zubarmin da ciki, basu fidda takardar gaskiya ta cewa fyade akamin ba” na kara fashewa da kuka bayan Rabiatu ta rungumeni a jikinta itama kukan take sosai tana kara jin tsanar Gentle a ranta, saboda tasan duk sharrintane da makircinta. 
Duk maganganunda mukeyi ashe a kunnen Dr. Rafiq ne, shigowa yayi jiki babu kwari ya nufo inda muke tsaye 
“Ka fita daga nan bana son ganinka, kai mugune kuma munafuki, ka munafurceni ka gwadamin kai mutumin kirkine ashe ba haka bane sai naga sabanin haka, ka fita kafin in fasa maka kai da kwalbarcan” na nuna kwalbar malt dasu Zarah suka kawo min. 
“Nasan zayyi wahala ki yarda dani, amma dan Allah inaso ki ajiye hankalinki ki saurari bayaninda zan miki” ya fada bayan ya kariso inda muke, “Ki koma ki zauna haryanzu jikinki bayyi kwari ba”. Cikin zafin rai na saki Rabiatu, a tsiwace nace “Bazan saurarekaba Dr. Saboda bakada abunda zaka fada min in yarda dakai, wallahi ka bani kunya, ka shirya karya kanaji kana gani bayan kuma ga gaskiya, to an koreni kun 
samu abunda kuke so san kuji dadinku da kyau kaida wanda suka sakaka” ina gama fadin haka najawo hijabina na saka, 
Hanyar fitana kama ina kallon yanda Dr. RafIq yayi shiru alamar yaso in saurareshi amma sam naki bashi damar yin magana saboda babu abunda zai fada min in yarda dashi. Bin bayana Zarah da Rabiatu sukayi, 
Purse dita Rabiatu ta bani tace 
“Anata kiranki daga gida, ban daukaba saboda bansan abunda zan fada masu ba, bana son tayar masu da hankali”. 
Karba nayi na zaro wayar daga ciki na danna kiran Baba, 
Bugu daya ya d’auka hankalinshi tashe yace 
“Aishatu ince dai lafiya kike, tun jiya nake kiranki inji ko kin sauka lafiya”, 
Gabana ya fadi sosai na kirkiro murmushi, 
“Na sauka lafiya Babana, wayar na jefa a cikin jakata can kasa, sai yanzu na ganota”, 
“To masha Allahu, dama sauka lafiyar ake fata ai, ina Salmah kun hadu ko?”, 
Har wayar da Baba ma ji nayi bana so, tsinke wayar nayi kawai naci gaba da kukana tare da kashe wayar baki d’aya. 
Bayan mun bar asibitin kai tsaye makaranta muka wuce, A bakin gate na tsaya su kuma suka shiga ciki domin su kwaso min kayayyakina, Ina nan tsaye saiga wata mota tayi parking a daidai bakin gate din kasantuwar ba’a barin mota mai tint shiga cikin harabar makaranta, Gentle ce ta fito sanye da irin skirt din nan baki mai barka doguwa daga gabanshi, sanye take da riga ’yar karama orange bakin hannu da kwalar rigar anyi ado da burberry bak’i, sai tadan yafa dan kwalin after dress karami, Babu wanda zaice ita bahaushiyace sai idan dama ya santa, Dariya hade da shewa ta dauka a lokacinda taga ina kallonsu, Cike da bacin rai na kawar da kaina daga garesu itada saurayinta. ‘ 
A cikin hakane su Zarah suka iso, kallo sukabi Gentle dashi Rabiatu ta watsa mata harara, 
Wata dariyar ta saka bayan sun matso inda muke ita da saurayin nata. 
“Tunda an koreki ai saiki tattara tsimmokaranki kibar makarantar saboda ba anan aka haifl uwarki da ubanki ba, sai a koma aci gaba da cin kanzo da tuwon dawa, 
Ai dama na fada miki nafi karfinki, wanda ya fikima nafi karfinsa, 
Talent University tamuce mu keda ita, saboda malaman cikinta namune kaf mun gama dasu, tun daga junior har senior lecturers din, ke har senate mun gama da ‘yan cikinta 
saboda damu suke damawa”. 
Daga hannu nayi na dauketa da kyakkyawan nari saboda maganganun da sukemin sun isa haka, 
Kanta ta dago ta kalleni cike da mamaki tace “Ni kika mara Ummimah?”, 
“An mareki din wacece ke da ba za’a marekiba? Ki sani yanzu ni ba daliba bace a makarantar nan, inada damarvyi miki komai ba tare da naji haufin wani abuba, idan kikaci gaba da fada min magana kuma in kara miki wani”. 
Saurayin natane ya daga hannu da nufin rama mata, Dakatar dashi tayi tareda fadin “Kyaleta Bash, nasan maganinta”, 
Tajuyo gareni “Ke kuma sai kinyi regreting din marina da kikayi, ba gida zakije ba? Ki tafi” tana gama 
fadin haka ta wuce cikun School abunta, shima saurayin nata yabi bayanta. “Karki damu kawata, babu abunda zaki gani a gida sai alkhairi, kar kiji komai ki rabu da 
ita Allah ya fisu” Zarah ta fad’a cikin sigar rarrashi. Hakuri sukaci gaba da bani har lokacinda keke napep tazo ta sauke wasu, tsayarmin da ita Rabiatu tayi, Da kuka muka rabu dasu, har mukabar wurin suna daga min hannu, Saida sukaga tafiyarmu sannan na hangesu sun shiga cikin makaranta. 
Wani sabon kukan ne naji yana saukomin, Mai napep din yace 
“Baiwar Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan, tunda na daukoki kike kuka kar wani ciwon ya kamaki”, 
“Karka damu bawan Allah, kaidai kayi aikinka” na fada cikin muryar kuka. 
Tashar mota ya kaini babu bata lokaci kuwa na samu motar Katsina, 
Mun jima bata cikaba kasantuwar yamma tayi babu matafiya sosai, 
Sai wurin karfe biyar sannan motarta tashi. 
Karfe tara da rabi na dare muka shiga Katsina, Nice banje gidaba sai kusan goma da rabi kasantuwar abun hawa da yake wahala idan 
dare yayi, A bakin gidanmu napep ta saukeni, Saidai kuma mutane dana gani makil kofar gidan, Duk wanda ya kalleni saiya gyad’a kai wasu suna hawaye. 


Shin ko me ya faru muje dai zuwa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]