WATA SHARI’A CHAPTER 4

WATA SHARI’A 


CHAPTER 4

A gajiye na koma gida, da hanzari Mama ta tarbeni ta karbar min jakata ta makaranta kamar yanda ta saba koda yaushe itace take karb’ar jakata idan na dawo daga School. 
“0yoyo Aunty Ummimah” shine abunda ya fito daga bakin Afrah cike da farin cikin ganina. 
Murmushi na miyar mata dashi, 
“Sannu Afrah, ‘yan JSCE, ya jarabawar? lnce dai tayi dad’i” 
“Tayi dadi sosai Aunty Ummimah, ashema babu wahala jarabawar haka nan ake sakamu jin tsoro”, 
“Ai dama na fada maku babu wahala, ina Amrah ne?” Na tambayeta saboda ban ganta ba. 
“Amrah na daki batada laflya, kinsanta ita kingin ciwo ce, kullum daga wannan ciwo sai wancan ciwo”. 
“Subhanallahi! Ina zuwa barin dubata” kai tsaye na shiga dakinmu. 
Sosai hankalina ya tashi saboda yanda na ganta sai rawar sanyi take, Kusa da ita na zauna har inajin gumin jikinta, 
“Sannu Amrah, ashe bakida Lafiya”. 
Muryarta na rawa da k’yarta iya furta “ehh Aunty”, 
“Ayyah sannu kinji? Kinsha magani kuwa?”, 
“Nasha paracetamol sauran wanda nayi amfani dashi last week da banida lafiya”. 
“Gaskiya ya kamata ace an kaiki asibiti Amrah, zama da ciwo bashi da wani amfani, bazai yiwu a ringa ciwo daban magani daban ba, kullum saidai ana dirka miki pain reliever, kar aje ciwo ya ringa cinki kuma ba’a san kalarshi ba”. 
Shiru Amrah xayi bata kuma cewa komai ba saidai kuma har yanzu jikinta bai daina rawa ba, idonta yayi jajur tsabar ciwo da yake cinta. 
Muna cikin hakane Mama ta shigo d’auke da School bag dita a hannunta, 
Bayan na karba nace “gaskiya Mama ya kamata akai yarinyar nan asibiti, kinga jarabawa sukeyi kar ciwo ya hanata zana jarabawarta kuma azo a samu matsala daga karshe, kinsan makarantun gwamnatin nan har korarta suna iya yi daga makarantar”, 
“Hakane Ummimah, amma kema kinsan halin da muke ciki, wurin aikin mahaifinki kusan wata biyu zuwa uku kenan basu samu albashi ba, harma an fara tunanin rufe company din za’ayi saboda karayar arziki daya samu mai company’n ya daina biyan ma’aikatansa albashi, kinga kuwa ina mukaga kudin da zamu kai Amrah asibiti?“. 
Ajiyar zuciya na sauke, tabbas maganar mama gaskiya ne, amma kuma ai baza’a bar yarinya ciwo ya ringa cinta ba, duk ta jarabawa ma mai sauki ce indai tanada lafiya. Ban kuma fad’ar komai ba kawai na fara cire Uniforms dina, saboda har an fara kiran sallar 
la’asar kuma bana son makara Islamiya. 
Bayan nayi sallah na shirya cikin uniforms din islamiyarmu, riga da hijabi milk colour, sai d’an kwali da wando coffee brown, 
Har na dauki jakata na hau kan karamin gadonmu na fuskanci Amrah da bacci ya d’auka yanzu, 
Cikin magagin bacci ta jawo hannuna ya shiga cikin nata, tam ta rikeni kamar da gangan 
tayi, hakan yasa na ki cire hannuna daga nata hannun har hud’u da rabi ta kusa munawa a haka dan bana son in cire hannuna kuma hakan yasa ta tashi daga bacci. 
Mama ce ta shigo ta samemu a haka, 
“Ki tashi ki tafi islamiya mana Ummimah, Afrah har ta gaji dajiranki tayi tafiyarta dan kinsanta ita tsoron bulala gareta”. 
“Mama bazan iya tafiya in bar Amrah a haka ba, na fasa zuwa kawai”, 
“To shikenan ai, kekam wannan soyayyar da take tsakaninki da yarinyar nan tayi yawa, zanga ranar da zaku rabu da junanku, ko kuma ranar da mutuwa ta dauki waninku tabbas zakusha wahala”. 
Wani irin hawaye naji yana bi min kumatu a lokacin da Mama ke wannan maganar, cike da tashin hankali nace “dan Allah mama kibar wannan maganar, muyi mata fatan Allah ya bata lafiya”. 
Da haka har dare yayi, bayan sallar isha Baba ya dawo daga masallaci, Lokacin kuma Amrah ta dan samu relief dan har ta fito palor amma dai duk da haka batada wata walwala. 
Bayan Baba ya gama cin abinci ne na masa maganar rashin lafiyar Amrah, “Baba dan Allah idan ka samu kudi ayi kok’ari ko chemist ne a kaita ayi mata awonjini dan a gane ciwonta“. 
“Hakane Ummimah, insha Allahu gobe zan tafl da ita wurin aikina, zan kaita wurin wani uban dakina wanda a karkashinshi nake aiki, zan gwada mishi ita insha Allahu indai ya ganta nasan zai tausaya mata, sai ya taimakemu da kudin da zan kaita asibitin saboda yana da matukar taausayi, ko kud’in dana baki jiya kika biya maku kudin islamiya na wata biyu da ake binku shine ya bani su “. 
“To shikenan Baba, Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya bata laflya” na fada cike da tausayin mahaifina, saboda nasan duk wata wahala da yakesha duk saboda mune, babban burinshi shine yaga ya sakamu cikin farin ciki, baya so ya gammu muna bukatar wani abu shi kuma bayada halin yi mana abun”. 
Ummimah ta fashe da kuka bayan tayi wannan maganar. 
Barrister Sultana ta kalleta sosai sannan tace “bazan hanaki kuka ba Ummimah, saboda 
bansan abunda aka miki ba, ban kuma san dalilin kukan ba, amma dan Allah ki daure kici 
gaba da yimin bayani ko zan samu bayanin da nazo nema a wurinku“. 
Bayan ta share kwallarta taci gaba da, 
“washe gari kuwa da sassafe baba ya tafida Amrah wurin aikinshi, duk da jarabawar da gareta a ranarda safe, 
Mun yanke shawara akan ni zanje in rubuta mata jarabawar saboda ba lallai bane a iya banbancemu, ba duk da kamar da Afrah da Amrah keyi amma nafi kamada Amrah, tsaf wanda bai sani ba zai iya cewa nice twin sister d’inta ba Afrah ba, musamman ma yanda na shaku da ita, duk wata shawara ko matsala da gareni ita nake sanarwa kafin kowa ya sani. 
Hakan kuwa ta kasance, ni na rubuta mata jarabawar kuma ba‘a ganeba har aka gama muka koma gida, 
Nikam nama manta da maganar Gentle, kwata kwata ban bi mama da maganar ba 
saboda nikam rashin lafiyar ‘yar uwata shine damuwata a halin yanzu. 
Da yamma likis Baba ya dawo, kallo daya za’a masa asan baya tare da walwala, da kyar Amrah ta iya sauka daga kan tsohon mashin din baba, 
A hankali take tafiya har suka shigo cikin daki, 
Da sauri na tashi na nufi inda take na rirriketa na zaunar da ita akan kujerar dana sauka, ni kuma na zauna kasa ina kallonta cike da tausayi, 
“Sannu Amrah,ya jikin naki?”, 
“Alhamdulillah” ta fada bayan ta kwanta ta dukunkune jikinta akan kujerar. 
“To Allah ya baki lafiya, sannu kinji? Na rubuta miki jarabawar yau kuma lafiya lau ba’a samu matsala ba”, 
Daga min kai kawai tayi ba tare data fadi komai ba,jikinta sai rawa yake, jijiyoyin kanta 
duk sun tashi, idonta sun k’ara girma sosai dama abunka ga mai manyan idanuwa. 
“Babansu ya ake ciki ne?” Mama ta fada tare da zama kusa dashi, saboda a yanayin data ganshi ciki tasan akwai matsala, amma ita a tunaninta ko kudin da zai kai Amrahn asibiti ne bai samu ba. 
“To lafiya lau zance“ ya fada bayan ya sunkuyar da kanshi kasa. 
Dajin haka gabana ya fadi, dan nasan tunda baba ya fad’i haka to akwai matsala. 
“Wanda nake fada maku zai taimakeni din ya taimaka mana,ya kaimu asibiti kuma asibitin ma ta kudi, ya biya kudin duk wasu test da akayi mata, 
Amma kuma bayan sakamakon ya Fito ne hankalina ya tashi, 
Saboda Amrah tana dauke da wata cuta a cikin kwakwalwarta wadda ake kira da “brain tumor,‘ likitan yamin bayani sosai akan cutar tare da illolinta. 
Yace min cutace wadda take uncontrolling na cell division na mutum, 
Cutar bata tsananta ba sosai a jikinta, dan haka yasa mukaga iya alamar hakan a tattare da ita, 
Idan tayi tsanani sosai tana saka mutum shan ruwa sosai babu control, ya gwada min wani bokiti plastic yace min zata iya shanye baki dayanshi ba tare da taji ya isheta ba, sannan kuma fitsari ma babu control zata ringa yinshi, komai dai zai koma mata babu control tamkar mahaukaci, sannan kuma yana hana haihuwa, yayi mamakin yanda cutar ta kama Amrah ‘yar shekara goma sha uku, saboda sai manyan mutane take kamawa, yace 
shi tunda yake ma bai tab’a ganin ta kama mai kananan shekaru kamarta ba. 
Amma da sauki tunda abun baikai haka ba, yace min hanya d’ayace wadda za’abi dan ganin cutar batai tsawo kamar haka ba, 
Saidai idan za’a fitar da ita kasar waje a fidda mata ita, idan aka fitar da ita kuma akwai wani magani wanda za’a dorata a kanshi, 
Duk bayan sati biyu maganin yake karewa, kuma an sameshi da sauki to dubu talatin da biyar idan ma an samu a kasar nan kenan saboda maganin Indiya ne ba’a cika kawoshi Nigeria ba, kati biyu ne a cikin wani kwali, duk sati daya ake shanye kati daya. 
Wannan maganin shi zata ringa sha har karshen rayuwarta saboda ko an cireshi idan ba’a shan maganin to cutar tana iya sake yin dashe a cikin kwakwalwarta, idan ba haka ba kuwa 
to komai zai iya samunta idan cutar ta tsananta ajikinta”. 
Tunda Baba ya fara wannan maganar nake kallonshi, 
Ji nake tamkara mafarki ne da nafi kowa farin ciki. 
“Yaa Salaam” Mama ta fada hannunta dafe a kirjinta. 
“Allah gamu gareka, Allah ka fitar damu daga wannan jarabawar” ta fashe da kuka mai 
cike da tsananin ban tausayi. 
Mutuwar zaune kawai nayi, kukan baizo min ba and i was totally speechless, 
Kara kallon Amrah nayi cike da tausayinta, 
Yarinya karama ‘yar shekara sha uku ce a cikin wannan hali, 
Sai a lokacin naji wani irin kuka maras control yazo min, 
Na dora hannuna bisa kai inata sharar kukana, Afrah ma kukan take, Mama kuwa dama tun sanda baba yake maganarta fara kuka. 
Shi kanshi Baban hawaye ke zarya a bisa kumatunshi, ya kasa ko rarrashinmu ma, 
Babban tashin hankalinshi bai wuce inda zai samu har miliyan biyu da rabin da za’ayiwa Amrah aiki ba, kuma ma idan ya samesu ina zai samu kudinda duk bayan sati biyu za’a 
ringa siyama Amrah magani?. 
lta kuwa Amrah baccinta take batama san abunda ake ciki ba, sai wannan zafin jikin wanda baya yin sauki, idan tasha pain reliever ne yake dan kwanciya na awa daya kuma sai ya dawo, ga yawan yin amai da takeyi, wani irin kuka na sake fashewa dashi had’e da rungumarta na makalkaleta har saida ta tashi daga bacci. 
Agigice ta farka cike da azabtuwar ciwo, ganin ina kuka yasata kara kankameni itama tana kukan, “Aunty Ummimah ki daina kuka ai naji sauki, tunda Baba ya saimin panadol nasha zazzabin ya sauka, ki kwantarda hankalinki, idan kuna kuka nima sai kisani in ringayi”. 
Wani kukan maras control ya sake Fito min da karfi, kenan Amrah bata san cutar da take tare da ita ba? Allah sarki baiwar Allah, Allah ya bata lafiya. Fatan da nayi mata a raina kenan bayan na saketa nace, 
“Barin kawo miki abinci nasan bakici komai ba”. 
Da hanzari Baba ya share hawayensa dan baya so mu fahimci cewa shima kukan yayi, 
“Ki duba booth din mashin d’ina akwai yoghurt na nan ki kawo mata, nasan zata Fl 
buk’atar abu mai ruwa ruwa”. 
Tashi nayi kuwa na nufi inda mashin din yake, 
Bayan na bude booth din na fiddo yoghurt kai tsaye na wuce palor, 
Budeshi nayi na juye a kOfi na fara bama Amrah, 
Saida tasha kamar rabin kofin sannan na sauke shi kasa, 
Kamar tana jirana kuwa sai amai ta fara kwarawa babu sassauci, saida ta harar da komai dake cikinta sannan cike da azabar ciwo ta koma ta kwanta, 
Hawaye naji sosai suna fita daga idona, 
Cikin natsuwa na dangwali ruwa a hanky na goge mata bakinta sannan na fara gyara jikina, 
Har a lokacin Mama da Afrah basu daina kuka ba, kowansu tana tausayin halinda muka 
tsinci kanmu a wannan yanayi. 
Bayan na gama gyaran wurin duka na koma kan kujerar na dora fuskar Amrah akan 
cinyata, baki daya zazzabi mai zafi ya taso mata, 
Kuka nake sosai amma maras kara, hawayena ne ya sauka bisa kumatun Amrah, 
Kokarin tashi zaune tayi amma ta kasa, 
Ganin haka yasa na tasar da ita zaunen ta fuskance ni, 
“Dan Allah ki daina kuka Aunty Ummimah, na fada miki naji sauki fa, yanzu ma aman da nayi ne yasa zazzab’in ya sake dawowa”. 
Goge hawayenta nayi tare dayi mata murmushin yake, itama murmushin tayi sannan ta koma ta kwanta a bisa cinyata, 
Mama da Afrah kuwa barin d’akin sukayi dan bass so ta fahimci kuka sukeyi. 
Bayan sati biyu. 
Zaune muke ina bama Amrah abinci a baki, 
Kwatsam naji sallamah da muryar mace babba sai kuma dayar muryar kamar ta budurwa, 
A lokacin Afrah ta tafi islamiya Baba kuma bai dawo daga wurin aiki ba, 
Mama kuma tana dakinta tana Fitar da kayan wanki. 
Amsa sallamar nayi tare da ajiye abincin a kasa, “Maraba daku, ku shigo daga ciki”. 
Babbar macen ta fara yin gaba sannan budurwan ta shigo, 
Murmushi na saki a lokacin danaga Gentle, itama murmushin ta miyar min dashi, 
Kamarsu daya ita da babbar matar hakan ya tabbatar min da mahaifiyarta ce, 
Sauke Amrah nayi daga bisajikina na gaishe da matar, 
“Ahh Salmah kune a gidan namu?, 
“Wallahi kuwa mune Aisha, na jiki kwana biyu bakizo School ba, shine naje har Principal’s Office ya duba min address dinki, 
Nayima Momy na bayaninki sai tace zata biyoni mu duba ko lafiya kike, shine fa kika 
gammu da yammacin nan”.
Murmushi na mata sannan nace “Amrah baki iya gaisuwa bane?”, 
Jiki babu kwari ta duka har kasa ta gaishesu, 
Bayan sun amsa ne Mama ta shigo saboda muryoyin da taji, 
Fuskarta dauke da fara’a suka gaisa da Momy, 
Nayi ma Mama bayaninsu da kuma dalilin zuwansu, 
Sannan kuma nayima su Gentle d’in bayanin rashin zuwana makaranta, 
Sun tausaya mana sosai sun kuma tausayawa Amrah, 
Sai yamma likis sannan Momy ta bama Amrah 10k cike da tausayi suka bar gidan. 
Sosai Momy ta yaba da kirkinsu, hakan yasa ta amince min da yin kawance da Gentle, koba komai tanada hankali, sannan kuma tanada kula itada mahaifiyarta. 
Tun daga wannan lokacin kusan kullum sai Gentle ta ziyarce mu, hakan ba karamin dadi yake min ba, Wannan kular da take mana ita ta siye min zuciya baki daya, naji Gentle ta kwanta min a rai. 
Saida mukayi wata daya a haka, lokacin har na gama rubutama Amrah jarabawa, hakan yasa na koma makarantata, ammafa rabin karatun da nakeyi hankalina yana gida, ina matukar tausayin ‘yar uwata, saboda yanzu ciwon k’ara yawaita kawai yake, kuma gashi babu k0 maganar ‘kudin aiki’ bare kudin magani, shi,isa a kullum na zauna banida aiki sai kuka. 
Wata rana cike da murna Baba ya dawo daga wurin aiki, kallo d’aya na masa na gano farin ciki a tattare dashi, 
Da sauri na karbi ledar hannunshi, 
“Balango ne na gani a hanya na siyowa maras lafiya, idan taci sai ta baku sauran”, Murmushi nayi na fara bata a baki, 
Bayan Mama ta shigo d’akin tayima Baba sannu da zuwa, 
“Nazo maku da albishir mai girma, amma fa sai kun bani goron albishir
Murmushi d’auke a fuskata nace “ka fada mana koma menene Baba, zan baka goro babba”. 
“Yanzu na dawo daga wurin likitan da yake duba Amrah, ya tabbatar min da cewa gwamnati ta kawo manya manyan likitoci daga India, wanda zasu duba narasa lafiya wanda suke dauke da ko wace irin cuta kuma kyauta bada ko sisi zasuyi wata uku 
sannan su koma kasarsu, Dan haka ya bani form daya na cike da sunan Amrah, nan da sati d’aya zasu fara aiki”. 
Hamdala muka saki mu duka dake dakin, harda Afrah da yanzu ta shigo ta tsinci zance, Amrah kam dama bata san ciwon da yake damunya ba, tayi zaton zasu dubata ne kawai akan yawan ciwon da takeyi. 
Shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da Gentle, ta kaiga bani boye mata ko wace irin damuwa ta haka itama bata boye min tata damuwar, 
Saidai a iya zamana da ita na fahimci sam ibada bata dameta ba, amma dai ina kokarin nunar mata da muhimmancin ibada, 
Saidai kuma a duk lokacin da zan mata maganar ibada sai ta bata rai, wani lokacin ma ba zata sake min magana ba har a tashi daga makarantar. 
Sam hakan baya sa indaina fad’a mata gaskiya. 
Yanzu kam mun dan samu kwanciyar hankali har sati ya zagawo, 
Baba da Mama da kansu suka kaita FMCK saboda acan ne za’a gudanar da taron likitocin. 
Likitici biyar suka hau kan Amrah, da manya manyan na’urori suke amfani wanda suke haska mata baki dayan kwalwarta, 
Sun tabbatar da brain tumor ce take dauke da ita, saidai kuma bata tsananta ba, 
Dan haka akwai wani gashi da za’a ringa kaita na tsawon wata uku, duk bayan sati za’a ringa gasa mata kwalwarta sannan kuma akwai wani ruwan allura da za’a ringa zuba mata a hanci shima dai duk satin ne, 
Sannan kuma sunma baba bayanin ba lallai bane idan akayi haka cutar ta rabu da ita har abada ba, amma kuma zata samu saukintana wasu shekaru. 
Duk da hakan Baba yaji dad’i yayi masu godiya sannan suka kama hanyar dawowa gida, Lokacin da Baba yaimana bayani ba karamin dadi mukaji ba, har da sadaka saida Baba yayi duk da shima mabukaci ne. 

Bayan shekara uku 


About Ismail

Check Also

WATA SHARI’A CHAPTER 20

WATA SHARI’A CHAPTER 20 ‘KOTU’ Kotu ta cika mak’il dan zan iya cewa duk zaman …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *