[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A 
CHAPTER 3
Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun karfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki, 
Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka dauko Hafsa sannan suka wuce gida. 
A cikin motar Hafsa tace “Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kadai ba dan kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin Head Master’s Office, 
Na gaisheshi ya dafa kaina yace min “kece Hafsa ko?”, 
“Ehh nice Hafsat Umar Muhammad” na bashi amsa, 
Shine yace min wai dama sakone zai bani wurinku, 
“Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matukar muhimmanci, idan Allah ya baka damar taimako to kayi kokarin aikatashi tun kafln damar ta kufce maka” ya kuma ce min “karki manta ki fada masu wannan sakon”. 
Yana gama fadin haka English Teacher dinmu yazo harda bulala a hannunshi 
“Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!” Naji tsoro sosai Abbah dan nasan sai ya bani kashi idan na koma class, 
Abbah abun mamaki ashe wannan mutumin wanda ya bani sak”o wurinku ya iya turanci sosai, 
Aikuwa ya taimakeni ya fadawa Teachernmu cewa ba Hausa nakeyi ba turancine, harda cewa yayi wai yaji dadin yanda ya jini ina speaking kamar ba ‘yar Nigeria ba, kuma sako yake bani wurin parents dina, daga nan kuma sai ya tafi” ta gama basu labarin hankalinta kwance tana bude dash board dake side dinta. 
Juyowa Umar yayi ya kalleta taci gaba da wasanta, 
Bai tanka mata ba, haka Sultana ma batace mata komai ba, 
“Abbah da Momy kunyi shiru, nidai babu ruwana idan ya tambayeni nasan na fada maku sakonshi”. “ 
Shiru sukayi har suka isa gida, 
Bayan Umar ya shiga daki ne Sultana tajuyo ga Hafsa tace “mutumin da yayi miki maganar ya yake?”, 
“Momy nifa ban sanshi ba, kawai dai nasan ya iya turanci kuma yanada fara’ah” ta bata amsa. 
… 
Washe gari. Da sassafe Sultana ta tashi, ita dama haka tsarinta yake kullum ita ke rigar Umar tashi, sai data gama ayyukanta kaf ta bade gidan da kamshi sannan ta tasheshi yayi wanka, idan yayi wanka sai su karya tare lokacin itama ta shirya kuma ta gyara Hafsa da Haydar. 
Bayan sun zauna kalaci ne Sultana tace “Abbah yau kuwa ina son fita ko zuwa da yamma ne insha Allahu”. 
Gyaran murya yayi yace “dama kinga nima inason fita, ina zakuje ne sai mu fita tare?”. 
Ido ta ringa zarowa dan batasan kalar karyar da zata masa ba, 
“Gidan Hauwa nake son zuwa, kwana biyu bamu gaisa ba”, 
“Ehh kuma damajiya ta kirani ni nama manta, tace ince miki Zarah batada laflya saima yanzu na tuna wallahi, afuwan”. 
“Amma dai honey ka cika mantuwa da yawa, yanzu inda ace bance zanje ba kenan da bazaka fada min ba, saidai ta ringa kallona da abun ko? Ai babu dadi ace yarinya batada 
lafiya banje na ganota ba”, “Nidai kiyi min hakuri tunda gashi na fada miki, anjima din kinga sai mu tafi tare nima in dubata da jikin”. 
Damm! Gaban Sultana ya fadi sai raba idanuwa take saboda bata son ya bita, “A’a kafa san dama ba tare dakai nake zuwa gidan Hauwa ba, bana son inje ka azalzaleni sai na tashi mun tafi gida, ni kuma ina son in zauna muyi fira sosai barin yanzu mun dade bamu had’u ba”. 
“To naji uwarson fira, kije yau ni kuma gobe sai inje, kuma inji kince zaki bini yawon gobe in kurta miki rashin mutunci” cike da soyayya yakeyin maganar. 
“Ehh naji dai babu komai, nima kuma daga can sai mu wuce yawonmu ko Hafsa?” 
“Ehh Momy, harki kaini Royal Bakeries ki siya min shawarma da ice cream” Hafsa ta fada tana murmushi. 
“Karki damu ai yawo zamusha sosai cikin garin nan, harda inda wani baki taba zuwa bama sai munje ko?” “Ehh momy zanje, shi kuma Abbah sai mu barshi da Haydar ko?” 
Kwakkwabe baki Haydar yayi alamar zayyi kuka, “Ni bajakuje daniba ko? Appa kaji wai bajazu tafi dani loyal ba nima insha ayish kilim”, “Wooo Haydar bai iya magana ba, wai ayish kilim, yaro kazo in koya maka magana” Hafsa 
ta fada tana mishi gwalo. ‘ 
Kukane ya fito da karfi ya fasashi, yanayi yana kallon Umar dan yaji abunda zai fada, “A’a fa Hafsa, wallahi idan kikaci gaba da samin yaro kuka duka ma sai in hanaku Fitar, ni kuma gobe muyi tafiyarmu nida dana Haydar” Umar ya fada yana rarrashin Haydar din. 
“A’a fa wasa take masa, nidai ka barmu mu fita ai hardashi zamu tafi amma fa sai idan yayi shiru da kukan nan”, 
Saurin goge hawayen yayi yace “nayi shilu momy, jaki tafl dani?”, 
“Ehh zan tafi dakai yarona” sukayi murmushi su duka ukun. 
Ranar tunda wuri Sultana ta daura abincin rana, dambun cous cous da sauce din hanta ce tayi, cikin lokaci kadan kuwa ta gama komai ta saka a food flask, Dining suka zauna suka shari abincinsu, Umar harda santi ya ringayi. 
Ta sake yima Hafsa da Haydar wanka ta shiryasu sannan ta umurci Safiya ma data 
shirya su tafi tare. 
Karfe uku daidai suka fita, motarta kirar vibe ja suka shiga, Hafsa ce gaba sai Safiya da Haydar a baya, 
Basu wani d’auki lokaci a hanya ba suka isa gidan Hauwa kasantuwar babu nisa sosai unguwar. 
Sosai Hauwa tayi farin cikin ganinsu, Sunsha fira sosai kafin Sultana tace “zanje in dawo yanzu insha Allahu”, “Daga zuwa kuma? Ina zakije ne?“ Hauwa ta tambayeta, “Ehh zan dawo ai anan zan barsu Hafsa, Tudun wada zanje yanzu bazan dade ba ai”. “Momy kince fa zaki tafi damu musha ice cream, ya kuma zaki tafi ki barmu?”, “Ai yanzu zan dawo Hafsa, ga Zarah nan kuyi wasa kafin in dawo sai mu tafi royal din ku zabi duk abunda kuke so”, 
“Yauwa momy na sai kin dawo”, “0k sai na dawo, Safiyya ki kula da Haydar kin sanshi da barna da kuma yawo” Tana gama fadar haka ta dauki hand bag dinta ta nufi hanyar fita. 
Kai tsaye Tudun wada ta wuce, 
Wayar’ta fito daga cikin jaka ta sake duba text message na address dinda aka turo mata, 
A hankali ta ringa driving tana kara duba message din, 
Daidai gaban gidan da yake kallon masallacin kuwa tayi parking kamar yanda aka rubuta mata, Bayan ta rurrufe motar ta fito tana rike da jakarta. 
“Assalamu alaikum” Sultana ta fada bayan ta zare medical glasses dinta daga ido. 
Shiru taji ba’a amsa sallamar ba, hakan yasa ta sakeyin wata sallamar amma har yanzu shiru ne, 
Sallamah ta sakeyi a karo na uku sannan wata murya ta amsa sallamar. 
A hankali tayi taku hudu zuwa biyar ya sadata da cikin gidan. 
Dan karamin gidane ginin jar kasa, yana dauke da daki kwaya daya tal sai bandaki, daga can gefe kuma kitchen ne aka zagaye da langa langa, kasan kuwa dukjar kasa ne. 
“Marhabun, shigo daga ciki mana” matar ta fada tana kallon Sultana dukda bata wayeta ba. 
“to mama nagode” ta fada bayan ta shiga cikin dakinda matar ta nuna mata ta shiga. 
“Sannu da zuwa baiwar Allah” Matarta fada har yanzu tana kallon Sultana, 
“Yauwa sannu mama” ta tsuguna kasa tace “ina yini mama?”, 
“Lafiya kalau baiwar Allah, saidai kuma ban wayeki ba”, 
“Ehh gaskiya dama nasan ba zaki wayeni ba dan baki sanni ba” ta zaro ID card dinta, 
“Sunana Barrister Sultana Saddam Bakori” 
Dafe kirji matar tayi tace “na shiga uku! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah dai yasa lafiya ba wani abu mukayi ba”, 
Murmushi Sultana tayi tace “karki damu mama, lafiya lau ba wani abu kukayi ba, zuwana alkhairine insha Allahu”, 
“To ina fatan haka Sultana, Umaimah!” Ta kira sunan a hankali. 
Daga kan gado wata budurwa ‘yar kimanin shekara gona sha takwas ta sauko, A hankali take tafiya fuskarta bushe da hawaye. 
“Waike Umaimah haryaushe ne zaki hakura ki daina wannan kukan? Kukan banza tunda kinsan ba wani magani zayyi miki ba”, 
Saurin goge sabon hawayen daya fito mata tayi sannan tace “sannu baiwar Allah”. 
Cike da tausayi Sultana ke kallonta tare da fadin “yauwa Ummimah, ya gida?”, “Lafiya Sannu da zuwa, barin kawo miki ruwa” ta fada muryarta na rawa sosai alamar wani kukan take shirin tayi. “A’a ki barshi wallahi banajin kishi”, ” ‘a indai kinsan ba kyamarmu kike ba to kisha ruwanmu” Mamar ta fada cikin natsuwa. “Hmm! Me zaisa nayi kyamarku mama? Kuma fa mutane ne kamar ni, Wallahi kawai dai banajin kishin ne yanzu daga wani gida nake, amma dai Ummimah ki kawo min kadan zansha”. 
Tashi kuwa Ummima din tayi sai gata da kofin roba cike da ruwa, Mikawa Sultana tayi aikuwa tajishi da sanyi kamar daga fridge aka diboshi, Kadan tasha sannan ta ajiye kofin a kasa ta fuskanci mama da Ummimah. 
“Nasan baku sanni ba, kuma bakusan dalilin zuwana wurinku ba”, 
“Ehh kam hakane, ni a tunanina ma ko kinyi batar hanya ne, amma ke nake saurare sai kin fada zan tabbatar ko wurinmun kikazo” mama ta fada tana kallon Sultana, 
“Wurinku kam nazo mama, Kamar yanda na fada maku ni lawyer ce, nazo ne muyi wata magana idan har ba zaku damu ba”, “Ehh munajinki Sultana”, 
Ta bude baki zata fara maganar kenan wayarta ta dauki ruri, hakan yasa ta ta fasa yin 
maganar, fiddota tayi daga cikinjaka sannan tayi picking ta kara a kunnenta. 
“Hello honey” ta fada a hankali, “Na’am wifey, kina kusa da Hauwa ne? Ina son inyimata ya mai jiki“, Shiru Sultana tayi kafin tace “aikuwa na fita yanzu amma zan koma, saidai ko ka kira numbernta ko kuma idan na koma in kiraka sai in bsta”, “To babu damuwa, idan kin koma d’in sai ki kirani, saboda gaskiya babu tabbas din zan samu zuwa gobe gidan nata dan akwai hidimar data taso min goben“ “0k honey sai na koma din” ‘tayi hanging up na wayar. 
Juyowa tayi ga Ummimah da Mama tace “kuyi hakuri fa mama, maigidana ne ya kirani”, “Uhm babu komai Sultana, bari ki fara ji daga bakin Ummimah sannan nima in fad’a miki 
abunda na sani” mama ta fad’a cike da natsuwa. Ga Ummimah ta juya tace “ina saurarenki Ummimah”. 
“Asalin sunana Aisha Abubakar ne, amma Mamana da babana suna kirana da Ummimah kasantuwar sunan kakata wadda ta haifi babana aka saka min, nice babba a wurin iyayena sai kannena guda biyu ‘yan biyu ne Afrah da Amrah, shekara biyu ke tsakanina dasu tun daga nan kuma haihuwa ta daukewa mamana, dama wurin haihuwarsu Amrah tasha wahala sosai. 
Mahaifina nada rufin asirinshi daidai gwargwado, muna zaune a gidan haya a cikin unguwar Saulawa dake nan cikin garin Katsina, babana yana aiki a wata karamar 
ma’aikata a karkashin wani mutumi inda ya zama masinjanshi. 
Akwai shakuwa sosai tsakaninmu, mukan zauna a koda yaushe muyi raha tare da iyayenmu, 
Babana ya sakani a makarantar gwamnati saboda bashi da halin da zai kaimu makarantar kudi duk da yanada burin hakan, 
Na taso da bala’in son inyi zurfl a karatun boko ina son in karanci fannin education kodan in gyara rayuwar bokon zamani, hakan yasa nake miyar da hankalina a kowane term, tun yarintata ni nake daukar first position har na shiga secondary School, 
Bani da kawa ko daya ni kad’ai nake rayuwata daga ni sai kannena biyu wanda bana boye masu damuwata suma kuma basu boye min tasu damuwar, a raina har nakan tambayi kaina akan wa nafi so a cikinsu, ‘Afrah ko Amrah’ saidai kuma amsar dayace, duk daya suke a wurina. 
Bayan mun rubuta jarabawar JSS ne Allah ya bani sa’a kuwa na samu sakamako mai kyau, ina daya daga cikin wanda suka zamo na daya a cikin kaf class mates dinmu, Hakan yasa gwamnati ta dauki nauyin miyar damu Private School mu uku daga cikin 
‘daliban makarantar. 
Babana yaji dadi sosai saboda ya dade yana mafarkin ganin ya kaini private school nida Afrah da Amrah, 
Nima naji sosai hakan yasa na sake d’aure damarar yin karatu sosai har sai inda karflna ya kare. 
Shigata makarantar na hadu da yara kala kala, wasu ‘yan rainin wayone wasu kuma 
mutanen kirki ne, amma kuma ‘yan rainin wayonsu sunfi yawa. 
Ina zaune ni kadai kamar ko yaushe na fiddo chemistry note book dina ina kara duba wasu equations da akayi dazu. 
Wata yarinya ce tayi min sallamah tare da miko min hannu don mu gaisa, 
Cikin mamaki na amsa sallamar nima na mika mata nawa hannun muka gaisa, 
Abunda yasa ni mamaki kuwa dan ban taba tunanin akwai irinsu a wannan makarantar ba, tunda naje babu wadda tayi kokarin yimin magana saidai masu bina da kallon banza 
musamman ma yanda sukaga ina participating a cikin class. 
Bayan na gyara mata wuri ta zauna ne tace min “sannu”, 
Nima sannun na miyar mata dashi. 
Murmushi ta sakar min ta sake fadin “naga kaman You’re busy k0? Gashi kuma magana nazo muyi dake”. 
Ajiye littafin nayi nima na miyar mata murmushin nace “babu komai ai, ina maimaita karatun dazu ne kuma ma na gama, ina saurarenki, Allah dai yasa lafiya”. 
“Ahh lafiya lau karki damu, na kula dake tun shigowarki makarantar nan kinfi son rayuwarki ke kadai, baki damu da rayuwar kowa ba, baki da kawa k0 d’aya ko magana bata dameki ba, iyakacinki kawai ki bada amsa idan wani teacher yayi tambaya, kina da kokari sosai kuma kowane teacher yana alfahari dake, baki dade da shigowa makarantar nan ba amma har an Fita outing dake kusan sau biyar ko sau shida, kuma duk wata queeze ko debate dinda zakuje zakiyi winning, shine nake son idan babu damuwa me zai hana mu zama friends? Ba dan komai ba sai dan ki ringa koya min karatu, saboda nidai bana ganewa idan akayi karatu, amma kinga idan ke kika natsu kika koya min zan gane sosai, amma fa idan babu takura”. 
Murmushi kawai na miyar mata dashi, “Babu takura ko daya, sai dai matsala daya kawai”, 
Kallona tayi tace “matsala? Wace irin matsala?”, 
“Nidai kinga ba diyar kowa bace ba face “yar talakawa“, bamu da komai sai rufin asiri, yanzu haka school din nan da nake gwamnatice ta dauki nauyina, iyayena sun min nasiha sosai akan na guji yaran masu kudi saboda matsalace dasu, suna da wulakanta talaka sosai, 
Shi,isa kullum nake ni kad’ai sabda gudun wulakanci, gaskiya kiyi hakuri kinfi karfina”. 
Kallona tayi sosai hawaye ya fara kwaranya daga idonta, 
“Mesa zakice nafi karfinki? Kin manta cewa da talaka da mai kudi duk dayane a wurin Allah? Wanda yafi wani shine wanda yafi wani tsoron Allah, dan Allah ki daina wannan maganar, nidai bani da matsala ko daya kuma ki tambaya kiji, indai har kinji na kwanta 
miki a rai to kiyi kawance dani kar kiji komai” tana gama fadin haka ta goge hawayenta. 
Shiru nayi munjima babu wanda ya kuma fadin komai, Saida na nisa sannan nace “to ki bari zanyi shawara da mamana, duk abunda ta yanke zan sanar dake insha Allahu”, 
“To babu komai, ina fatan zata amince saboda nikam kin kwanta min a rai, ina son mutum mai irin halinki, gaki da kamun kai sosai duk mazan class din nan babu ruwanki dasu kin huta”, 
“Nagode sosai sai kin jini” na fada bayan na sake bude littafina, 
“Au! Shine ba zaki tambayeni sunana ba ko? To tunda baki damu daji ba ni ki fada min naki sunan”, 
Kunya naji sosai nayi mata murmushi, “Sunana Aisha Abubakar amma anfi kirana da Ummimah, kefa?”, 
“Sunana Salmah Abubakar, amma Gentle ake kirana dashi”, 
Nice name, surname dinmu daya dake kenan?” Na tambayeta, “Ehh kam hakane”. 
Da haka har lokacin dawowa break fast yayi, malami ya shigo akaci gaba da karatu daga inda aka tsaya. 
Karfe uku daidai aka tashi kamaryanda aka saba, 
‘Yarjakata na rataya a kafad’a, na nufi hanyartiti don in samu keke napep in hau. 
Gentle ce da sauri ta ringa kwala min kira, daga farko ban jita ba sai daga baya, hakan yasa na dakata na jirata har ta iso inda nake, “Tunda aka tashi nake rarraba idona ta inda zan hangoki, sai daga baya baseerar in biyoki tanan hanyarta fado min, 
Ina zakije ko tanan ake zuwa daukarki?” Bayan nayi mata dan murmushi nace “keke napep zan tara in tafl”. 
Da sauri tace min “a’a dan Allah karki tari napep din nan, kizo gashi can anzo d’aukata, 
dama neman da nake miki kenan inji idan ba daukarki za’ai ba sai mu tafi dake a ajeki a gidanku”. 
“A’a nidai ki barshi wallahi nagode”, 
Bazanji dadi a”Raina ba idan baki zo mun tafi dake ba. dan Allah kiyi hakuri mu tafl”. 
Dafa kafadarta nayi nace “Salmah kenan, iyayena zasu min fad’a idan sukaga kun bani lift, kiyi hakuri babu komai wallahi zan hau keke napep din dama kullum ita nake hawa”. 
Badan taso ba tace “to shikenan sai anjima, ki gaishe dasu mama” ta tafi, 
Kallo daya za’a mata asan bataji dadin rashin bintan ba, nima kuma kaina banji dadi ba, saidai kuma dole babu yanda zanyi sai dai hakan, babana zai iya yimin fada sosai kuma yace na fara bin yaran masu kudi ina son in canza hali wanda kuma sam ba haka bane, kuma na kula da Salmah ko a cikin yaran masu kudin ma ita batada mugun hali, tanada halin kirki kuma tanada son kyautatawa. 
Da wannan tunanin na isa bakin titi na tsayar da keke napep na hau. 

Hmm 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]