[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A

CHAPTER 2
Washe gari da sassafe Sultana ta tashi Umar suka fara shirin zuwa aiki, Bayan sun gama shiri ta yima Hafsa da Haydar wanka sannan ta shirya Hafsa cikin Uniform din School dinsu, 
Sauran pepper soup din jiya tayi warming nashi sannan ta soya mata Irish da kwai ta saka a launch box d’inta. 
“Wow! Kinyi kyau baby na, barin snapping naki” Hafsa uwar iyayi kuwa aka wani yi style na daukar hoto, Saida Sultana ta dauketa hoto kala biyar sannan tace “to ya isa haka, barinyi Feeding haydar shima tunda dai kinga anan zan tafi in barshi”, “0k Momy ki diba a nawa ki bashi” Hafsa ta fada cike da soyayyar kaninta, “Ahh Hafsa ai na d’ibar masa nashi daban, gashi kin gani” Sultana ta fad’a tare da nunawa Hafsa sauran Irish da kwan data ragewa Haydar. 
Saida suka gama tas Umar ya fito cikin suite d’inshi black and white, 
Yayi matukar yin kyau kamar a saceshi a gudu, 
“Yadai Madam? Hope kun gama saboda inada aiki da yawa a Office yau, kuma kema din nasan ba zaki rasa ba”. 
“I think bani da aiki nikam, bandai san ko sai naje zan sameshi ba, mun gama dama kai mukejira”, “0k muje kawai” ya fada bayan ya soka wayarshi cikin aljihu. 
Bai gama sakawa ba yaji k’arar text message ya shigo masa, 
Zarowa yayi ba tare da tunanin komai ba ya fara karantawa, 
_”Nasan zakuyi tunanin kawai inason inyi wasa da hankalinku ne, to sam ba haka bane, kamar yanda na fada maku an cuceta kuma bata da halin karbar fansa saboda anfita kudi, mulki da komai  na rokeku dan Allah da soyayyarshi ga mafificin halitta ku taimketa,_ 
_Idan har kuna bisa ga ra’ayin taimakonta zaku iya maido min da reply ni kuma sai in baku address nata”_ 
“Again?” Umar ya fada a bayyane. 
“Menene ya faru honey?” Sultana ta tambayeshi bayan ta gama sakawa Hafsa socks and sandals nata. 
“Karba ki gani” ya mika mata wayar, 
“Ana so ayi wasa da hankalinmu ne kawai, zanje wurin MTN su duba min wannan layin, inhar na gano kowaye yake mana yawo da hankali wallahi sai ya raina kansa, ni bana son raini ko kad’an”. 
Bayan Sultana ta gama karantawa ta mika masa wayarsa, 
“Ni ina ganin honey kafin kayi haka ka tura da reply din, tunda haryanzu akace za’a turo mana da address kaga kamar akwai alamar gaskiya a ciki”. 
“Alamar gaskiya? Acikin wannan maganar? Bana tunani kam, koma waye idan da gaske yake ai sai yazo ya tinkaremu da maganartunda dai yasan gidanmu yazo ya kawo takarda jiya, dan haka wannan shirmene kawai kuma kibar maganar nan kamar yanda na fada 
miki jiya, kuma yau yau din nan insha Allahu zanje MTN Office suyi min bincike akan layin 
nan” yayi gaba bayan ya mayar da wayarsa a cikin alJihu, “Ku fito mu tafi lokaci na tafiya” yayi waje. “Safiyya!” Ta kwalawa kira Nany din Haydar 
“Na’am momy” ta fada tare da saukowa daga kan bene da sauri. 
“Gani momy” ta fada tana kallon Sultana, 
“Ki dauki Haydar ki goyashi nasan yanzu zayyi bacci tunda na mashi wanka ya karya kuma”. 
Daukarshi tayi kuwa ta goyashi, harda byebye yayima Momy’n shi, Hafsa ma ta daga mashi hannu sannan suka fita suka samu Umar harya fitarda mota waje yana jiransu. “Afuwan honey, kanata jiranmu”, “Hmm! Bakya laifi wifey, ku shigo mu tafl”. 
Saida suka fara dropping din Hafsa sannan suka nufi Federal High Court Katsina, 
Kai tsaye kowa ya nufi Office dinshi, Zaman Sultana keda wuya kuwa sako ya shigo mata, Exactly irin wanda akama Umar ne, Aikuwa batajira komai ba ta miyar da amsa, “A shirye muke da taimakonta indai har da gaskene wannan sakonnin da ake turo mana, kullum burinmu shine muga mun taimaki wanda aka zalunta ko kuma wanda ake kokarin zalunta, dan haka ina jiran address dinta yanzu”._ 
Tayi sending tare da ajiye wayar akan desk dinta. 
Bada jimawa ba kuwa sako ya kuma shigowa, dauka tayi ta karanta _”Tudun Wada layin farko gida na biyu yana kallon masallaci”._ “Good” ta fad’a a bayyane, “Insha Allahu zan taimaketa, zanyi shiru bazan fadawa Umar ba har sai na tabbatar da gaskiyar al’amarin sannan in sanar dashi, shima kuma nasan bakin kokarinshi zai 
taimaketa idan ya tabbatarda maganar”. Karfe hudu daidai suka tashi aiki, A cikin mota Umar yace “nikam na rasa menene tsakanina da Barrister Sa’eed, kwata_kwata baya kaunata, ko a hanya na hadu dashi na bashi hannu mu gaisa baya amsa, na rasa dalilin hakan”. 
“Hmm! Ka rasa dalili fa kace honey, ga dalili karara a bayyane, 
K0 ka manta shari’arka ta farko dashi kayi winning? Kuma tun daga nan na kula yake neman shari‘ar da zakuyi dashi amma ba’a sameta ba, a tunanina dalilin jin haushinka kenan da yake, 
Kumafa na samu labarin tunda yake a rayuwarshi kaine mutum na farko daya fara kadashi a shari‘ah, kuma har yanzu ba‘a samu wani ba”, 
“Ehh hakane kam, amma ni sai naga kamar duk wannan bai isa yasashi jin haushina ba, ki duba kiga tun lokacin da akayi shari’ar, kusan shekaru goma kenan fa kilama ya manta me zai sashi ya rike wannan abun? Kuma in banda abunshi ma yanda yake babban barrister wanda duk fad’in kasar nan an sanshi yayi suna me zaisa ya ringa jin haushina ni dan karamin barrister”. 
“Hmm! Kai kaga haka honey, ai kuwa yanzu idan baka take mashi baya ba to kiris ya rage ka take bayanshi, yanda yayi suna kaima din haka kayi, duk inda ka shiga Barrister Umar Mohd ake fadi, kaga kuwa ka godewa Allah”, 
“Kema kinyi magana Wifey, Allah dai ya kara bamu ikon cin halaliyarmu, Allah ya karemu daga cin kudin cin hanci da rashawa, burinmu a kullum muga mun taimaki mai bukatar taimako, bama fatan mu tauye gaskiya akan karya kawai saboda kudi ko wata kawa ta duniya”. 
Da wannan firar suka isa gida, da sauri kuwa Haladu ya wage masu gate suka shige da motarsu, cike da soyayya suka fito hannunsu makale dajuna, Jin karar motarsu yasa da gudu Hafsa ta fito tana fadin “oyoyo oyoyo” ta rungumesu su biyun, “Oyoyo Hafsa” Umar ya fada bayan ya saki Sultana ya dauki Hafsa. Shigarsu ciki suka samu Haydar da Safiyya sunata wasa abunsu cike daso da kauna, Ganinsu da Haydar yayi yasa ya daina wasan yazo yama iyayenshi oyoyo, “Momy yau Safiyya bataje ta daukoni School da wuri ba duk saida aka watse aka barni 
sannan tazo” Hafsa ta fada tare da tunzuro baki ita a dole mai fushi. “Hafsa me naji kin fada?” Sultana ta tambayeta, Saurin dafe bakinta tayi tare da fad’in “Aunty Safiyya bataje ta daukoni da wuri ba har aka watse aka barni ni kadai a School”. 
“Au! Kin gyara kenan? Kuma ma ban hanaki kawo min karar Safiyya ba? Na hanaki ko ban hanaki ba?” Ta hada hannayenta biyu ta zare mata ido, “Kin hanani momy” Hafsa ta fada hawaye na shirin Fito mata. . 
“To mesa zaki kawo min kararta? Sa’arkice ita? Waya fada miki ana kawo babba kara?”, “Babu” ta fada bayan hawaye sun fito mata, “Ki bata hakuri”, Juyawa tayi ga Safiyya bayan tayi kneel down ta hade hannayenta biyu tace “sorry Aunty Safiyya”, Cike da so da kauna Safiyya ta jawota ta dora kan cinyarta ta rungumeta, “Babu komai Hafsa nima ki yafe min kinji? Keke napep ce tamin wahalar samu saida nayi 
trekking har bakin roundabout sannan na samu”. “Kema duk lalfinki ne ai, dan me zaki tsaya kinama yarinya karama kamar Hafsa wai bayanin abunda yasa bakije daukarata da wuri ba? Saisa take rainaki wallahi” Sultana ta fada dan ta tsani taga karami ya raina babba. 
“Babu komai Momy, Hafsa nada biyayya sosai wallahi, yanzu ma nasan fushi tayi ne saboda babu dadi a watse abar yaro shi kad’ai a School”, 
“Kudai kuka sani, akwai abinci ne?”, “Ehh akwai Momy” Safiyya ta fada tare da nufar Kitchen. 
Dama ta riga da ta zuba a food flasks, d’aukowa kawai tayi takai’ dining, Daki Sultana ta shiga ta kira Umar akan yazo suci abinci, “Wanka nake sonyi ne saboda yau na gaji sosai, idan nayi wankan sai in samu d’an karfi_karfi a jikina”, “Ehh hakan yayi, nima kaga sai muyi tare dan bakai kadai keson samun karfin ba” tayi murmushi bayan ta gama maganar. “Wifey na ta kaina, ina sonki sosai” ya fada kwayar idonshi akan idonta cike da soyayya, “Hmm. Honey niba sonka nake ba kaunarka nake, saboda kasan shi so yana raguwa watan wata rana, amma kauna bata taba raguwa duk tsanani duk wahala”, “Hakane wfey, ki kudura a ranki ‘ina tare dake‘ komai rintsi komai wuya”, “Nima ‘ina tare dakai‘ honey na” ta fada bayan sun kama hanyar shiga toilet, Nidai guduwa nayi saboda abun yana shirin fin karfin idanuna, amma fa ina bakin toilet ina jiran fitowarsu saboda ina son yanayin soyayyar wannan ma’auratan dan ina son in 
koya nima. Sun jima a cikin toilet din kafin su fito, Hafsa zaryarta biyu tana nemansu amma bata gansu ba, Dan haka ta koma ta fadawa Safiyya cewa Abba da Momynta sun bata, 
Dariya kawai Safiyya tayi dan tasan dalilin rashin fitowar tasu. 
Da fitowarsu kuwa mai ta shafa mashi shima kuma ya shafa mata, kananan kaya ta fiddo 
mashi bluejeans sai white T-shirt ajikinta an rubuta “‘YOU ARE MINE’” da kalar royal blue, 
Itama kananan kayan ta fiddo, three qurter ne blue itama sai ‘yar polo shirt white da logo na polo royal blue bayanta itama an rubuta “‘YOU ARE MINE TOO”.” 
Sosai sukayi masifar kyau, nidai “perfect couple” kawai bakina ke furtawa. 
Makale da juna suka fita kamar ba sune suka aje kamar Hafsa ba. 
Kai tsaye dining suka nufa inda suka fara feeding junansu duk da idon Safiyya da Hafsa baisa sunji ko kadan din kunya sun daina ba, 
Koda yake ai a soyayya babu kunya, idan kuwa aka saka kunya to bazaku tabajin dadin rayuwarku ba, wannan haka yake. 


Mu tara

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]