[Advertisements⬇️]

TSANGAYAR MATI COMPLETE - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANGAYAR MATI 

CHAPTER 6
Inna ta hau tafa hannuwa tana salati iyakar karfinta, kan kace me magulmatan makwaftansu sun hau leke cike da al’ajabi. 
“Yau naga abinda yafi karfina ni Uwar biyu! Kai! Kai! Wallahi ba zata sabu ba, Mati!” 
Ta juya ga Mati wanda zufa ke ta karyomasa, gabadaya ya susuce, daman ita Abule ya san karya ceta shukamasa musamman da yaji tana maidawa Delu irin tuggun data shirya na iska, ita kuwa Nene bai taba kawowa karya take hlba, a zatonsa idan Abule ta bata rawarta da tsalle to yana da mafaka a wajen Nene. Sai dai ashe dukkansu taron na ayya ne. 
“Eh dole ka rasa bakin magana mana! To wallahi ba zata sabu ba! Ko ka kara aure ko kuma ka saki kowace shegiya ta koma akurkin ubanta. Zabi ya rage naka, yanzu na keson amsata.” 
Inna ta karashe tana gyara zaman siket dinta na buje. Nene da Abule suka shiga tashin hankali, kada fa suyi biyu babu. 
“Kai nake sauraro ka tsayamin kerere kamar liman ya manta Fatiha.” 
Mati ya saci kallon Matansa, to daya rasa tafkekiyar gonar Inna da kuma gida ai ya gwammace ya kara auren ya samu haihuwa. 
Ya mai da idanunsa kan Innarsa. 
“Shikenan, ki nemo min mata.” 
Ai sai Inna ta rangada guda. 
“Ayyiriririii! Haba ko kaifa, yanzu na tabbatar da cewa kai jini na ne. Saika shirya don kuwa yanzu zaka yi aure.” “To amma…” 
“Amma me? Inna ta katseshi tana harararsa. 
“A’a wai dama gani nayi su biyun ma matsalar jakai na biyu bana iya rikesu da ita, shine 
nake tunanin kar ta ukun ta shigo kuma idan ina cin abinci sau biyar a rana na dawo sau uku.” 
“To batunu kiyama sarkin ci, ince dai gidan nan nawa ne?” 
“Naki ne har ni dinma.” Ya fada yana dukar da kai. 
“To tunda ni zan ma auren menene na tunani? Idan ta ciyarwa kake zan karama akuya da rago ka kiwata. Ina ce dai shike nan?” Ta waigo barin dasu Abule ke tsaye. 
“Ku kuma saiku shirya don kuwa falleliyar budurwa zan samar masa, ba irinku zawarcin titi ba.” 
Bakin ciki ya turnuke Nene da Abule. Musamman Nene data tabbatar bata kai nata yan matancin ba, amman dai ai ita ceta fari, kuma ma ta toshe yanda ba za a gane ba, don haka ta karkata baki. 
“Allah na tuba ko dubu zai auro ba kamar ni a zuciyarsa, nice dai Nenen Mati, kaf kauyennan an shaida soyayyarmu.” 
Inna ta bankamata harara kawai ta wuce daki. Shima Mati da saurinsa ya fita ya hau jakinsa ya fice. Abule ce ta saki shewa. 
“Aikin banza wai bille a duwawu, duk dai abinki bai sanya an fasa auroni ba, dadin abin ma ba abinda bansani ba. Ina ce dasa hannun aljanu da ‘yan bori a aurenki da shi k0?” Nene ta fusata, zata kai mata bugu tuni Abule ta nufi daki, ta mai da dubanta ga masu leke. 
“An yi asara munafukai da tsakar rana babu ko kunya!” 
Babu wacce ta tankamata acikinsu, ta gama haukanta ta fada dakinta. 
BAYAN WATA BIYU 
Ta faru ta kare, duk wani shiri da gyare-gyaren daya dace a yi na zuwan Amaryar Mati an kammala, amaryar ba wata bace illah Fadime diya ga aminiyar lnna, Ladidi. Daidai da lefe Inna ceta koma birni tare da Ladidi suka hado. Abu kamar wasa dai aka sanya biki sati biyu, duk irin borin Nene da Abule baisa an fasa ba, ganin babu Sarki sai Allah ya sanya suka hakura. 
An kawo Amarya lafiya lau da guda da komai, cikin ‘yan rakiyarta har da Shafa da Delu. 
Kwanan Amarya daya a gidan Inna ta tattara ta koma birni da zummar sai nan da sati biyu za ta kara lekowa. 
Nene na zaune ta tsefe kitsonta wanda ya kusa shekara yayin da Abule ke kwance saman tabarmar kaba tanajifanta da wake-waken habaici tana ramawa suka tsinci muryar Mati da Amaryarsa suna sheka uwar dariya, suka dubi juna da sauri kamar wadanda aka mintsila suka nufi kofar dakin nata har suna bangajejuna, karshe dai suka nutsu suna lekesu. 
Amarya Fadi ke kwance saman cinyar Mati, shi kuma yana yagar tsire yana sa mata a baki suna hirarsu cike da nishadi. Nene ta dafe kirjinta gami da hadiyar yawu. Ba tajira komai ba tayi wuf ta shige ganin haka Abule taja baya tana mai rike kugu. 
“Kan uban can! Wato Mati dama amanarmu ku keci? To wallahi ba za ta sabu ba! Sai dai ayi raba daidai!” 
Za ta dauke ledar naman Fadime ta cafke hannunta ta mike tsaye. 
Baki Nene ta saki ganin shigarta. 
“Riga da wando a gidan nan? Jakar Uba! Mati karuwar birni Innar ta auromaka ashe banda labari?” 
Harara Mati ya sakarmata bai ce komai ba don wani sa’in yana shakkarta. Fadi ta kauda fuska gami da murguda bakinta da yasha jan baki. 
“Ke Malama don Allah ki bar nan wallahi warinki na tayarmin da zuciya. Ga dukkan alamu dai ko wankan tsarki ba kya yi.” 
Ta saki hannunta. 
“Kuma wallahi kika kara taba ledar nan sai na miki ihun mahaukaciya. Ce miki akai Ni hadamammiya ce irinki? Ga naku kason can a gefe dan bazan yarda Miji na ya tashi da shanyayyen barin jiki ba ranar gobe kiyama ba,” 
Nene ta hau tafa hannu da shewa. 
“Hehehe! Yau nake ganin bariki a gidan nan, ashe kuwa yau wata za tabi tsohon najadu barzahu. Idan kin fasa kirana mahaukaciya baki cika diyar Ladidi mai siyar da kayan maye ba!” 
Fadin haka keda wuya, ta kai hannu zata dauki ledar, Fadime ta damki gashinta ta mai data baya, tayi taga-taga zata fadi kafar Mati dake kasa ya miketa taci karo da kafar sai gata Tim A kasa tayi zaman ‘yan bori. 
Fadi tajuya da Mini-minin idanuwanta ta dubi Mati “Sannu Maigida bata daijima ciwo ba ko?” Mati ya washe baki yace “Fadi Amarya ina gabanki ai bana jin ciwo.” Tayi masa farrr Da ido tace, “Mai gidana nasha ce maka Timah zaka dinga kirana yarda kawuna na birni ke fadi. Tabdijam! “Yau naga sabon salo wai tafiya bariki da Uwa” Cewar Abule daga bakin kofa. 
Amarya ta waigo ga Nene dake baje kasa tana cije baki, “Ke kuma kici gaba da shiga shirgi na, wallahi da ruwan sanyi zan dafaki dan ban iya damben tsakar gida ba, balle na haifarwa maigidana talauci, ku da kuka saba kuje can ku karata, ga tsiyarku nan.” Ta fada tana tura mata kasonsu na tsire. 

Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]