TSANGAYAR MATI CHAPTER 3

Advertisements

_____

TSANGAYAR MATICHAPTER 3

“To ai saiki kauce daga samanmu tunda dai shegen bakin cikinki yajawo kinji abinda Tsohonki ke aikatawa a waje.” Mati ya fadi yana hararar Abule da tayi tsaye hannu bisa kugu tana jinjina maganar ‘Yar Magaji. 
“Oho dai, dadin ta Bazawari aka ce ba ‘Barawon Jakai ba.” Ta fada tana hararar Nene dake yatsine-yatsine. 
“Kyale kinji Nene uwargidan Mati, muje na raka ki daki ki kwanta, daga yau ko tsinke ban yarda kin dage a gidan nan ba, wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani a kasa.” Ya fada cike da lallami. 
lta dinma mikewa tayi cike da kwarkwasa har da rike rigar Mati. Gab da zata daga labulen kabar ta ne ta waigo ta kalli Abule fuskarta dauke da murmushin kadan kika gani. 
Dogon tsaki itama taja tana hararardakin bayan shigewarsu. “Wai Kura ce ta samu damar mike kafa, ayi dai mu gani, muna nan za kazo kana min ‘yar murya. Haryaushe ma akai daren?” Jin shiru ba su amsata ba sai tashin dariyarsu da takeji ne ya sata juyawa a fusace zuwa na ta dakin. 
Kwana biyu gidan shiru daga uhumm sai hu’umm wai uwargulma tayi cikin shege. Duk san Abule nata gane gaskiyar cikin Nene abun yaki yiwuwa. Sai ma barinta da takaicin arba da ledar Burodi da Tsire da take yi kullum safiya. Idan ma tayi dakon hana ido barci dan a kasa da ita Mati baya shigowa gidan sai dare ya raba, kafin ta gama barcinta ya kada 
nasa Jakan yayi gaba tsabar rashin gaskiya. 
Sauri take ta isa gida, dan ta fara gwada maganin saka laulayin da Gwaggonta ta bata ta dinga shansa duk dare, bayan ta sanar mata da abinda ke faruwa a gidansu. Ta tsinkayi 
muryar Delu na kwada mata kira. Kamar ba zata tsaya ba, sai dai taja tunga ganin Delun harda dan gudunta. ‘ 
“Uhm! Tunda na taho nake Addu’ar Allah yasa na ganki, dan kuwa ba za,ai wannan cin Amanar a gaba naba.” Gabadaya ta mai da hankalinta kanta “Me ya faru Delu? Na sanki baki maganar banza.” “Ke dai Allah ya raba mu da Miji mai dabi’ar hankaka. Mati na gani yanzun nan gun ‘Yarbaiwa mai Fara ya sai harta Naira Hansin wai Uwargida ke kwadayinta, baki ganta ba 
fal ledar…” “Fara fa kika ce? Farar da tunkan muyi aure yake min alkawarin cinta?” Ta tari numfashinta. “Idan karya nake miki wannan zance tsawar bana ta sauka gonar Malam Alkur’an.” . 
“A’a me najan masifa? Zaiyi fin haka ko dan ya nunan shi Namiji ne kwandon zawo, barni da shi, yau ko zai mutu ba zataci Farar nan ita kadai ba. Ke har ke sai kin dandana,
Na gode miki Delu, bari na karasa gidan. 
Da sallamarta gidan tayi jifa da kallabin kanta gefe, luma yatsunta tayi cikin gashinta 
ta fara wargaza shi, kan kace mene wannan ta tada hankalln gashinta yayi tsaitsaye tamkar gemun Mahaukaci daya shekara ana jifansa. Nene dake gefe ana kokarin sai ta kai, sai gani tayi Abule ta zube tana wani nannadewa, doka ihun da zata yi sai ga shigowar Mati yana mai da aljihunsa baya. Ganin Nenejiki na kyarma ya sashi yin wurin Abule yana salallami. 
“Karka karaso! Kana karasowa idan muka fyade ka saika dangana da Gyatumarka” Yaji murya na gargadinsa kamarta Kuyangar Kutare. 
Turus! Yayi kafafuwansa na rawa kafin kuma ya zube kasa yana kallon yarda Abule ke nadewa bakinta na dilalar yawu. 
“Kiyi hakuri Abule wallahi bansan kina da larura ba.” Ya fada kamarzai fashe da kuka. Taja majina. 
“Kai! Ka iya bakinka, wannan ba lalura bace, kaine ka kira mu da kanka da kake taba mana Godiya kana sata kuka.” 
Ta fada tana zare manyanjajayen idanuwanta. 
“Karya take min bantaba sata kuka ba, Nene ma shaida ce.” “Munafuki menene wannan a aljihunka na hagu?” “Fa..fa …fara ce.” “To waka siyo mawa?” 
“Abule mana, ita ce Amarya ta da bana iya motsi sai da ita.” 
“To bawa waccar ta kawo farar nan gabanmu, gargadin karshe kuma ka kuskura ka kara kawo ko Dusa ce baka hada da Godiyarmu ba sai mun musanya mata yaron cikin da take dauke dashi da Kadangare.” 
“Ban..ban..gane ba…” “Au! Dan fitsara ma baka San Godiyarmu nada cikin kaba?” 
“Na sani, kuyi hakuri. Ke Nene mika musu Farar mana.” 
Ya fada yana jefa mata kullin ledar dake ta kyallin mai . 
Abule ta kalla idonta kamar zai fado dan tsoro, gani take kamar bakinta ma ya koma gefe, dan haka nene tayi baya cikin hawaye.tace “Ba zan iya ba Mati.” 
“To kuwa zan fita na barki dasu, ki mika musu ko zasu tafi.” Ya fada da tsawa. A darare ta mika ledar gaban Abule dake nade, a guje ta juya zuwa dakin ta ta lafe bayan kaba tana hangen su. 
Katuwar Hamma Abule ta saki, kam kuma ta bingere gefe makale da ledar farar ta. Akwai alamun Borin ya sauka. 
Hmmm
Muna zuwa 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

TSANGAYAR MATI CHAPTER 8

Advertisements _____ TSANGAYAR MATI  CHAPTER 8 Kamar wasa cikin Fadime ya tabbata, Inna har Asibitin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *