[Advertisements⬇️]

TSANGAYAR MATI CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANGAYAR MATI
CHAPTER 1

Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan tana waka. 
“Ahayye iye nana…” 
Difta dakata gami da sakin baki adalilin abinda ta hango a tsakar gidannasu. Maigidansu Mati a kofar dakin kishiyarta Abulle zaune suna hira da dariya. Ganinta ya sanya Mati yin tsuru da idanu yayin da ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da dabara ta fiddo takardar naman data boye a bayanta ta warware ta dauki tsoka dayan da ya rage ta jefa a baki tana tauna gami da fadin. 
“Maigida kana burgeni, kana kawomin irin wanda na keso.” 
Mati ya watsamata kallon muguwar mace, shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar tsiren, ashe makirar abinda ta shiryamasa kenan. Ya numfasa gami da share zufa yana duban Nene batare da yace uffan ba. 
Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango ta fisge mayafin kanta ta hadiye miyan daya taru a bakinta tsabar na ranta ya biya ta ci damara ta hau tafa hannu. 
“Allah na godemaKa daka nunamin abinda ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta ta ake yi ana dawowa idan bana nan? To yau dubunku ta cika Mati, yau sai an bambance tsakanin aya da tsakuwa!” 
Jin haka ya sanya Mati mikewa ya hau fadan karfin hali da borin kunya. 
“Ke ya isa! Yimin shiru dakikiya kawai! Kin shigo gida ba sallama ba komai sai waken banza sannan baki tsaya kinji dalilin dawowata ba yanzu kishi zai kaiki ya baro ki!” 
Kafin Nene ta samu bakin magana, Abulle ta saki wata dariya irin ta wadanda duniya ta yiwa dadi. 
“Kai namiji, namiji akace buhun ƙaya. Sannunka munafuki, inace munfi awanni biyu tare? Duk dai abinda za’ayi sai dai a yi don bana tsoron kowace mai yanayin kul6a, miji ne mun yi aurenmu na soyayya muna zaune laflya yana kawomin kayan makulashe koda kuwa ba kwana na bane, sai a mutu!” 
Da jin haka Nene ta zabura tayi kanta tana faman surfa ruwan ashariya. 
“Yau sai na nakasa ki tsohuwar bazawara mai bin maza, saidai wannan tsohon gurgun ya kara haifar wata.” 
Ai sai su ka shiga kokawa, Nene ta daddage ta bata kyakkyawan cizo a mamanta wanda yake fata ce kawai. Wani ihu Abulle ta saki gami da fadin. 
“Kan uban can!” Ta cafki jan gashin kan Nene mai kama da gemun dan Bunsuru ta hauja da karfl, ta kuwa shiga ihu har zaninta na faduwa sai gata zindir babu ko dan bante. Mati ya tafi da gudu ya dauki zanin yana kokarin suturceta ganin magulmatan makwaftansu wato Gidan Delu da Gidan Shafa har sun soma leke ta Katanga. 
“Menene haka? Ke Abulle don iyayenki sakarta!” 
Wani turi da Abulle ta yiwa Nene sai kuwa ta jefata jikin Mati su kayi kyakkyawan zubewa a kasa abinka da siririn mutum. Da sauri Nene ta mike ta suturta jikinta ta na huci. “Shegiya mai kalar mayu zanyi maganinki a gidannan, zaki san kin shigo gidan Nene.” Wani banzan harara Abulle ta watsamata sa‘ilin da take gyara zaman rigarta. 
“Yanzu aka fara tashin hankula a gidannan muddin ba zaki fita a harkata ba. Mace bata ajiye komai ba sai taci ta yasar da katon kashi a masai! Gwara ni, tunda koba komai nayi Gari anga shaida!” 
Nene bata jira komai ba ta nufi wajen girkinsu ta rarumo tabarya ta taho a guje, ai Abulle na ganin haka ta fada dakinta, ga shi ta kasa daga labulen kaban kofar dakin hakanan kawai ta turo kyauren. 
Nene ta tsaya tana huci ganin Mati yasha gabanta. 
“Shegiya kai, ashe ke ‘yar iskar karya ce, yoki tsaya mana idan ban nakastaki ba anan.” “Haba Nene, ya isa hakanan, muje daga ciki kiji.” 
Cewar Mati hankali a tashe don shi har ya rasa ma yanda zaiyi ga makwafta ‘yan gulma na kallo. 
“Haba ke kuwa Nene, kiyi hakuri mana.” 
Fadin Delu kenan cike sa tsegumi. 
Wani banzan kallo Nene ta watsamata, sai lokacin ta lura da tarin magulmatan makwaftansu dake leke. 
“Kai! Allah Ya tsaremu da munafukai, mutane basu ajiye komai ba banda munafunci da gulma, dadin abin dai mijina bai taba jibgata ba kuma bai taba haikewa wata ba.“ 
Delu wacce tasan ita miji kejibga taja tsaki tace. 
“Oho dai! Duk acikin sone.” Daganan ta bar leken tare da yanmatan yaranta uku. Ita Shafa salin alin ta sauka ba tace uffan ba, to ina bakin magana tunda tasan da gaske mijinta kwarto ne na a kwatanta. 
Dakyar dai Mati ya kashe rigimar tare da alkawarin zai kawomata nata kunshin tsiren. Abinka da kwadayyiya, ba musu ta hakura. 
Abulle ta tabe baki. Mati bai ko kula ba yaci gaba da maganarsa. 
“Sanin kanki ne dai Inna bata damu da zuwa kauyen nan ba tunda Baban su Ladiyo ya dandana mata zaman birni, yanzu kuma musamman donni zata zo ayi zumunci. Don Allah Abulle, kece karama, kece kuma bata sani ba, ki taimaka ku zauna lafiya har ta tafl. Sannan inda hali inason ayi wani abu.” 
“Menene shi?” Ta fadi da sauri. 
Yayi shiru sai kuma ya numfasa ya sassauta murya. “Karyar ciki.” 
Gaba daya ta zaro idanu tana dubansa. Ta murza bajajjen hancinta. 
“Yi min gwari-gwari dai.” Ya hau bayani. 
“Inna ta sanarmin cewa muddin ta tarar kema baki da ciki to lallai za’a samu matsala don kuwa sai na sake ki nayi wani auren. Ni kuma kinsan dai ina sonki ina son zama dake, don..” 
“Tsaya tsaya Mati, shi kenan wannan abu mai sauki ne zan yi, sai dai menene ribar? Wace kyautar bajintar zaka samu bayan hakan don nasan halinka, baka aikin banza.” 
Yayi ‘yar dariya ya shafi sumarsa. 
“Kai kai Abu tawa ta kaina, kina da saurin fahimta kam. To bari kiji, akwai wata tafkekiyar gona ta Inna da kuma gida da take bayar da haya ana biyanta balas duk karshen wata, ba yanda banyi ba akan ta bani gonar taki,amma daga baya ta tabbatarmin da zata bani har da karin gidan nan ya zama mallakin jikanta.” 
Abulle ai sai ta hau tsallen murna da sakin guda. 
Mati ya hau rufemata baki a tsorace. “Ke ki rufa min asiri kada waccan taji.” Tunanowa da Nene da tayi ne yasa ta saurin sai ta kanta. 


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]