[Advertisements⬇️]

TAGWAYE COMPLETE - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYECHAPTER 24
Asad ya gangaro da motarsa Alhaji Zabir Mansions first gate, Nan yatarar da hayaniya anata rigima, Dasauri yafito, sai ko yaga Mommy da Maisha ce suke rigima tareda Yan Sandansu. “Laflya sergent meke faruwa anan?. 
Wannan mutumin daya’kira sergent ne ya nufo inda yake ransa a bace sosai yace’ barka da dawowa Sir, Ma’isha ce tazo tareda mahaifiyarta, muka hanata shigowa bisa umarninda aka bamu daga sama, Oga yace kada abarta tashigo, Shine fa yanzu mahaifiyarta ta’kira oga awaya tafada masa. Duk dacewa mun bata dama ita kadei tashige banda Yarta, Ta ‘kira oga tafada masa wai zamu kashesu karyan banza tin tuni sai rigima suketayi anan suna hayaniya. 
Shiru Asad ya tseya yana sauraransa har seida yagama magana, yajuye bangaren Mummy 
yana murmushi “Hajiya kiyi hakuri fa mutanen ne haka suke wallahi, kuma da gaske ne 
Zaid ya hanasu barin Maisha tashigo gidan, toh amma ai tunda dei tare kuka taho babu 
wata matsala zaku iya parking motocinku anan sannan kushige motata insaukeku acikin gida ….. Bai ‘karasa furucinsaba, Mommy ta katseshi‘ Saboda me zamu bar motocinmu 
anan wajen, Kai ma ashe dan rainin hankalin ne, wai so kake kanuna mana kafimu kusanci da gidan k0 toh wallahi karyarka tasha karya. Da wannan maganar ta janyo 
Maisha kai tseye tabude kofar mota suka shige gaba d’aya. Ganin Asad yana tseye awajen masu gadi basu musaba nan ta’ke suka danna remote aka bude musu kofa.
Shima Asad biyosu yai abaya da motarsa, shiyasa ma suka samu suka ‘karaso cikin gidan 
babu wanda yatseidasu. Suna isowa garrage sukayi parking. Mommy ta’yi mamakin ganin Ma’isha da akwatuna birjik tamkar barin gidan nasu tai, Matsowa tai har kusada ita 
tanacewa” Isha lafiya meyesa kika kwaso wannan akwatunan? ni atunanina fa zuwa kikayi domin kiziyarci Yar Uwarki ki sabida ku deideita tsakanin ku. 
“Momcy nifa dawowa nai, Ta amsa kai tseye. ‘Dawowa kuma Maisha angayamiki nan din gidan bariki ne Wanda kowa zai dawo idan yaga dama, toh maza ki maida akwatunan nan naki cikin mota mushigo mugaishesu sannan mukoma gida cikin Kwanciyar hankali. Zumburo baki tai “Nifa Momcy gaskiya bazan komaba haka kawai duba irin tsarin gidan nan fa dan Allah ki ‘kara dubawa ai duk wanda yasamu yana rayuwa awannan irin gidan shikam sedei yaroki samun lahira sabida duniya dei kam yasamu kina gani Masha Allah… 
Tabe baki momy tai tana binta da kallo har saida tai shiru’ Maisha nace ki maida wannan akwatunan naki cikin mota kada mutanen gida sufito su samemu anan. Tafad’a atsawace. “Toh Mumcy daman ai dalilin da yasa Daddy yadawo da Ma’inah nan shine kada muhad’u a gida d’aya Kinga kenan kawai sai ku koma gida tareda ita nidei gaskiya nan dei kam naga wajen zama. Da wannan maganar taja akwatunanata inda kai tseye tafara tambayan securities bangaren Zaid. 
Bakin ciki da bacin rai ce sosai tacika Momy ayanzu, Ta’san halin diyar tata kuma Babu yedda zatayi tachanza mata ra’ayi dazaran tayi deciding abu. Haka tabarota awajen tai cikin gida, falon Aunty Rahila ta’karaso kai tseye tana shiga sukayi Kacibis da Miemah ayayinda take gudu Anisa na biye da ita abaya tanason takarbi wayar Miemah taduba wani abu. Tseyawa sukayi dikkanin su alokaci daya. 
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun Miemah? Momy ta ‘kara bude idanuwarta sosai tareda Salati “lyeee Manyan mata su Miemah anga arziki koh, ina ke ina zama a irin wanan
kantamemiyar gidan, lallai ansamu waje harma anfara gina ‘jiki wato dei an Kwan biyu ba’aci Koko da tuwon dawa ba.ko
Hajiya Safeenah maraba,yaushe kika shigo gidan na’mu? Aunty Rahila tafito daga dakinta adeden lokacin, ‘Toh ya kika tseya achan baya kishigo ciki man. 
Mommy ta‘kasa kauda idaniyarta daga kan Miemah se mamaki taketa yi “lyee Hajjaji sannu fa daman ance matsiyata sunfi ganin darajar arziki kinga yedda kikayi 
Dakata Mana Safeenah lafiya kuwa? Aunty Rahila ta ‘karaso Inda suke Kai tseye tarike Miemah ayayinda hawaye suke zobowa a idanuwan Mieman sosai tana share mata hawaye tace’ Kinga Safeenah bamuson hayaniya anan gidan sabida ba gidan karnuka bane, meye ya kawoki? Fadi abunda yakawoki ki kara gaba, kodei kema maular kikazoyi agidan na’mu? 
Duk da gori ba halin Aunty Rahila bace batama’san lokacinda maganar ta subucewa ba’kinta ba, tsaban bacin Rai. 
Jikin mummy har tai sanyi sabida ta’san koda wasa ba’zata taba tunanin hada kansu da zuri’ar Zabir ta fanin dukiya ba, sabida d’ar sun daresu, wallahi dukiyar gidan Sambo batama’kai ko kwatan dukiyar da aka tarawa Munah ba, nata ita kadei.
Cikin salon kora kunya da hauka, inji hausawa Mommy tajanyo Miemah tanacewa inji dei babu zuri’ar uwa ko ta uba dake tsakanin ku, sai Allah ma yasan yedda akayi tadawo gidan naku tsaban son rayuwa irin nata. Nan mommy ta saukarwa Miemah mari a fuska “Meya kawoki nan so kike ki janyomin zagi agari koh, Mijina ya bani amanarki ki sannan kigudu kishiga Duniya ……. Aguje Miemah takoma ba’yan Aunty Rahila “Mamy ki taimakamin ba’nason komawa gidanta, don Allah Mamy ki taimakamin. Tafada cikin tsananin kuka. 
Anisa tana tseye achan baya tun tuni haushi kamarta shake Mommy tamutu kowa ya huta. 
Da ‘karfi Momy ta tsawatarwa Miemah “Maza tattaro kayanki mukoma gida, ina Baby na Mainah itama tazo ta tattara kayanta mutafl, sabida banson arabamin kan yara,Yara a haifesu Tagwaye sannan arabamin su Allah ya kiyaye. Ma’inah, Baby, Sweetheart, Ma’inah kifito mutafi. 
Wannan sautin ce ta tada Aunty Nasibah daga barci, cikin sananin bacin Rai tafito tana tsotsa Ido ” Waye wannan yaketa ihu sekace Mara hankali. 
Ni ce’ Mommy ta amsa mata kai tseye. Tabe baki Aunty Nasibah tai, tanabinta da kallo 
tamkar Kashi take gani ” To ke din fa, ke asuwa? Angaya Miki Nan kuma irin gidajenku ne da zakizo kina hayaniya any how. 
Hadiye miyau mommy tai, taji haushin maganar, sedei bata nuna hakanba juyowa tai tana Jan Miemah “Mara kunya biyoni mutafl Ina Mainan kuma dukkan ku yau wallahi se kun bar gidan nan. Cikin ta’kun kasaita Aunty Nasibah ta ‘karaso gunsu, Kai tseye ta janyo Miemah gamida cewa” Miemie koma daki kinji. Babu musu Miemah tai daki aguje takulle kofan da key. “, Ma’inah fa ina take? Tana tambayar Anisa. Dasauri ta amsa “Tana bangaren Yaya Zaid. 
Toh alhamdulillah. Aunty Rahila ta sauke nunfashi “se muga dei yedda zataje chan din kuma ta d’aukota, Sabida Yaran nan dukkansu biyu ba kece kika kawosuba, sabida haka Kuma babu inda Zakije dasu kamar yedda kikazo kika samesu anan wallahi haka zaki koma kibarsu. 
Toh Amma ai ni ce na’kawo ta duniyan ma gaba d’aya’ Momy ta amsa Cikin masifar bacin rai. 
“Wannan kuma mu bamu santaba ke kika sani. Da wannan maganar Aunty Nasibah ta janyo Aunty Rahila suka fara tafiya “Baby Ani, kishiga ciki kema kada a raBamiki jahilci. Kelkyelewa da dariya Anisa tai, wallahi shiyasa takeson halin Mahaifiyar nata “Toh momcy love yanzu kuwa. 
Mommy ta’yi niyar tafiya awannan lokacin amma data tunodawowar Maisha gidan, kawai sai ta daure tai magana” Wallai kunsan dei Zan iya kaiku ‘Kara kotu idan har bakubani yata da Miemah muka tafi tare ba. 
Achan nesa Aunty Nasibah taba’ta amsa Kai tseye” Allah na natuba muko wace irin kotu ce bamugani ba Wallahi sedei ta lahira. 
Cikin sanyin jiki momy tace’ toh idan har kunason inbar muku Yaran nan dukkansu biyu inada sharad’i guda. Aunty Nasibah tabud’e baki zatayi magana amma Aunty Rahila ta hanata dawowa tai tana tamabayar Momin wace sharad’i ce? Tafada koma menene zata iya dazaran za’a barmata Miemah da Ma’inah. 
Anan ne momy tadanji sanyi aranta ” Ba’nason Tagwaye na su rabu, kamaryedda suka zauna acikina su biyu haka nakeson su rayu tare, sabida haka sharadin d’aya ce tak! ldan Zaki amince Maisha tadawo nan gidan itama tacigaba da zama tareda Mainah. Bata ‘karasa kalmar nataba Aunty Nasibah tabuga tapi da yarta Anisa suka fashe da dariya” Daman ai dole a tattarosu duka azuba mana” Anisa tafada tana ‘kara kelkelewa da dariya. “Anga maiko ba” itama Uwar tafashe da dariya tai. 
Babu komao na amince, Aunty Rahila ta amsa Na amlnce Maisha tadawo nan gidan dazaran zakibarmin Miemah da Ma’inah har abada. 
Akwai wata sharadi Kuma: Mommy takatseta’ Zan rinka zuwa gidan nan akai akai ina duba Y’ayana because they still remain my daughter nice na haifi kayana. 
Anisa na’jin wannan ta’kara fashewa da wata sabuwar dariya tajuye domin suyi tapi da mahaifiyarta kenan taga Ashe ma tun tuni Aunty Nasibah kam tashige d’aki tabarosu, aguje tabiyota sabida takaimata wannan sabuwar labarin. 
Na amince, Aunty Rahila ta amsa mata, Nan ta’ke mommy ta mike tareda cewa Maishan tana nan zuwa please take care of her, amanarta nabaki ahannu don Allah kiriketa Amana da ita da Mainah, Na barku lafiya. Tana fita taduba k0 ta ina bataga alaman Maisha ba haka tashige Motarta tatafi tana mamakin inda Maisha tashige cikin gidan. 
Tanafita Aunty Rahila tamike kai tseye ta shiga d’akin Aunty Nasibah inda ta tarar dasu dukkansu, ita da Anisa sunata Shan fira da dariya harma da Mieman wacce batama’san lokacinda tafito d’akinta tazo tatsamesu anan din ba. “Aunty kwasau, to ai tinda kin kwaso Maisha’n kuma seki Kira Zaid ki tsanar masa. Aunty Nasibah tafad’a. 
Babu abinda Mamy tace, Zaunawa tai akujera kurun, inda tasa layin Zaid awayarta tafara ‘kira, a bugu biyu ya d’aga…. 
Suna shiga mota wayar Zaid tai kara ringing, “Assalamu Aleikum Mamy,yai sallama cikin sanyin murya kamar yedda yasa’ba. Subhanal|ahi, abunda ya’kara fad’i kenan. Toh shikenan muna nan zuwa. 
Mainah batayi maganaba har sanda tajira yagama wayar tukunna tace‘ lafiya? Twin Sister’n ki ta’ dawo nan gidan dazama. Dasauri takatseshi”Miemah kenan kake nufi Girgiza kansa yai “Ma’isha. 
Hadiye miyau Ma’inah tai “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun yaushe hakan tafaru? Kuma tayaya. Babu abunda Zaid yafad’a tabe baki yai “Haka dei Mamy tafad’a. 
Shiru Ma’inah tazauna sai zura idanuwa take dashike tafi kowa sanin halin Ma’isha Kuma idan har dawowartai da gaske daga yau farin cikinta ta gushe kenan da ita da Miemah, sabida ta’san Maisha ba’zata taba barinsu suji dad’i acikin gidan ba dazaran tana nan kuwa Zata iya yin tsanadiyar rabuwarta da Yayanta (Zaid) ….. 
Shiru tazauna cikin motan tana bin Zaid da kallo babu abinda suka furta dikkanin su ahaka har suka kai part d’in Mamy. 
Gata da akwatuna tamkar bala’i tana nan labe awata lungu tana lekan cikin gidan Zaid 
tamkar farilla ta dade tana nan sanda taga Zaid yafito tareda Mainah just like couples suka shigo mota. ldanuwarta na biye dasu har Sanda Motar tabacemata. Haushi tamkar taje tasha’ke Ma’inah kowa ya huta. Ma’isha kenan uwar tsiya, Kisisina harma da bala’i. a 
Dashike ta’san plan d’in da ta shirya aranta, sam bata damu da wannan ba, share Jan bakinta tai tas, Daman idan tanasan takoma kamar Ma’inah Jan bakinta take sharewa tas! 
Sannan tachanza tafiya takuma sake fiskarta tana murmushi, dashike haka Ma’inah take ako yaushe kaga fuskarta se’kaga tamkar murmushi takeyi. Nan da nan takoma Ma’inah exactly daman kamaninsu kam tamkar an sa’ga Kara ce. 
Maisha, Ma’inah da Miemah halittansu iri d’aya take sak! Babu abinda d’aya tafi d’aya dashi idan Maisha taga Miemah tamkar madubi take dubawa haka idan Miemah taga Mainah itama tamkar madubin take dubawa Babu abinda yarabasu sai ha’laiyarsu, amma dashike Miemah da Ma’inah ha’laiyar tasu kusan iri d’aya take yasa mutane basu iya banbantasu, Maisha kuwa wannan Jan ba’kinda take sakawa ako yaushe yasa mutane suke ganeta akallo d’aya amma dazaran tacire Jan ba’kin ta’koma Mainah ko Miemah. 
Ta’share Jan ba’kin tas! Daman Doguwar Riga tasaka da hula, hular tacire tasa ajaka 
Sannan tad’auki gele tad’aura yedda Mainah keyi, ayanzu kana mata kallo d’aya Mainah ce. Haka ta Janyo akwatunanta tashiga bangaren Zaid cikin ta’kun kasaita, “waiku baku iya gaisuwa bane. Tafad’a tana ganin masu gadin. Sunyi mamakin Jin hakan daga gareta, 
dashike wannan Sam ba halin Ma’inah bane, idan ma tazo ako da yaushe da’kanta take fara musu gaisuwa. 
Madam sannufa, maraba ina yini: Suga gaisheta cikin fara’a, daman sunasan halinta, sosai take birgesu. Sharesu Maisha tai, Kai tseye ta’karaso cikin gidan, ‘Kanta a sama, sosai tsarin gidan ta birgeta harma tafara day dreaming aranta ita da Zaid amasayin Amarya da Ango. 
Daman akwai mutumin da Sukayi magana, ta biyashi kud’i ya turo mata dukkan Hotunan da Ma’inah tai da Zaid tareda Munah cikin ruwa, Tana karasowa island, daman anan sukayi magana da mutum idan tashigo zasu had’u. 
Ta hangoshi chan yana tseye, da dukkan alamu ita yakejira, daman ta cemasa idan sunje wajen itace zata fara masa magana koda kuwa ya ganta kada yai kuskuren mata magana kila ko da Ma’inah zasu fara had’uwa kada plan d’insu ta warware. 
“Ka nuna masa hotunan? Maisha takashe murya tana tambayansa, “Malam nace ka nuna masa hotunan? Har yanzu dei wannan mutumin shiru yai yana binta da kallo “A’uzubillahi lafiya irin kallo haka, kudi fa nabiyaka yazama dole muyi aiki tare wallahi ko kanasa ko bakaso. Se yanzu wannan mutumin yadawo cikin hayacinsa, a firgice yace’ Kigafartamin Hajiya wallahi tunda nake rayuwa a duniya ban ta6a ganin kamaninni irin haka ba, anya ba Madam Maina’n bace kuwa? 
Da’fa keya Ma’isha tai cikin sananin bacin rai tace’wallahi danasan haka kake da’ma tun 
farko ban fara aiki da Kai ba, you are not serious at all. Nace ka nuna masa hotunan ne? 
A’a kinsan ba’ a barin kowa yashigo dakinda yake bisa lalurar rashin lafiyar dake damunsa, sai mutanen gida, idan Kuma y’an uwansa ko abokanan arzikinsa ne sukazo dubajikin nasa akwai Abdulfattah Mai kula dashi tawajensa akebin process d’in har aganshi, Kinsan ni ma’aikaci ne kawai anan gidan ba’zasu taba barina inshigo cikin d’akinda yake ba, sedei ke tunda yanzu kowa ya’san Mainah Budurwar Zaid ce za’a bari kishigo kawai kicemusu kinzo duba jikin Baba I’m definitely sure zaki shigo kai tseye. 
Murmusawa Maisha tai “aww daman haka nan gidan sukeda dokoki, toh ba matsala zanyi kamar yedda kafada kaga idan na samu na aureshi wallahi dolensa sai ya mance da maganar Ma’inah sabida Mijina mijina ne believe me cikin kwana daya tak! zan sace zuciyarsa, Maisha Sambo Maidugu kakeji yaro. 
Agaskiya Hajiya ko da cikin minti daya kikacemun zaki sace zuciyar namiji zan amince. Koh? Maisha ta d’age gira tana tambayansa. Wallahi kuwa, mutumin ya amsa yanabinta da kallo. Fashewa da dariya Maisha tai “Toh Malam Audu kallon ya isa haka. Sun fara tafiya yayinda mutumin yace’ Malam Audu Kuma? Sunan datafi dacewa dakai kenan ai. Haba ke kuwa iyayena sunsakamin suna mai d’adi kina chanzawa “Farhan nake ai. Tabe baki Maisha tai ta’kara duba fiskarsa da Kyau “Wallahi sunyi asara kuwa, suna mai dad’i haka Farhan to wallahi ni dei Malam Audu zan ‘kiraka. 
Suna isa Sha‘shin Mahaifin Zaid suka labe cikin lambu inda mutumin ya kwatan ta mata komai, yanuna mata hany’a sannan yakoma ba’kin aikinsa. Kai tseye Maisha taflto tana ta’ku d’aya d’aya. Ko ina anata Hajiya sannu, Itako hannu kurun take d’ago musu cikin girman Kai. Tana isowa ba’kin kofa tace’ Assalamu Aleikum barkanku dei sunana Mainah Sambo Maidugu kamar yedda kuka sani ni ce budurwar Zaid Kuma matar dazai aura nan badajimawa ba, kubudemin kofa zan shigo in indubajikin Baba. 
“Aee munsani Hajiya, ai Iabarin soyayyarki da Oga yana streaming akota ina anata breaking news, ga wani ma anan Opera news akace finally Landlord Zaid (Mafiya’s Grandson) finds his love Mainah Sambo Maidugu. Dasauri Ma’isha tasa hannu takarbi wayan tanadubawa wani irin bakin ciki taji aranta tamkar ta kashe ‘kanta ta huta “lna’ma ace ni ce, lna’ma ace wannan sunan zata chanza daga Mainah takoma Maisha”, Wai daman haka rayuwar yan Blyu take? ako yaushe daya yakanfi dayan sa’mun nasara, Imagine rayuwar mutum sekace gasa ako yaushe kana competiting da dayanka, A gaskiya da’nasani gudace nakeyi arayuwata wato kasancewarmu Tagwaye, wallahi duk wanda kuma yasan shi kadei yafito to fa sai yafara godewa Allah tun yanzu. 
Hajiya ai Hoton yayi ba laifl, wallahi kuwa dole kiyi kuka Allah na na tuba ai idan mutum yasamu Zaid amasayin miji yagama da duniya sedei yafara sallar dare kuma yana neman lahirarsa. Sanda taji maganar wannan mutumin ne ma tagane Ashe har kuka takeyi dasauri tashare hawayen ta, tamaida masa da wayarsa sannan aka bude Mata kofa Kai tseye tashigo. 
Tana shiga Abdulfattah suka fara had’uwa afalon mikewa yai cikin girmamawa ya gaisheta “Madam kinzo duba jikin Babanmu ne? Gyad’a kai Maisha tai jiki a sanyaye ba’tareda ta furta wata kalmar ba. Tana biye dashi abaya har Sanda suka iso wata d’aki yabud‘e kofar kai tseye tasa kafa tashigo. Likitoci ne kachokam suke cikin d’akin duk larabawa ne Kuma Babu bakin Fata. Tana shiga suka amsa sallamarta “Mrs Zaid” abunda suka fara fad’i kenan sunata maganganu da larabci. “Congratulations Mainah you have found the right man, Our son is great Masha Allah. 
Daganijikin Mahaifln nasa ya warware, sabida yau azaune yake babu ko da igiya gudace ajikinsa sai dei katifar da aka D’oura masa a wuyansa, shima dei da alamu ta d’an warware. “This is your In-law sir” Larabawan suka fara introducing Maish nan da nan gun Baban Zaid, “she is your son’s Choice Ma’inah Sambo Maidugu. 
Baba yana murmushi sosai yayinda ya gyad’a Kai yanacewa” Ehh jiya Zaid yakawota nan mun gaisa” cikin harshen larabci yai magana, Maisha bata gane abunda yafad’a ba sai kawai taga Larabawan duk sun fita sun bar musu d’akin. 
Surukata zauna mana: Baba yafada hakoransa duk awaje, agaskiya ban taba tunanin Dana zaiyi kwanciyar hankali har yazabo mata da wuri haka ba, I’m really so greatfull Alhamdulillah kuma ga kinan kamila da dikkanin alamu zaki kulan mana dashi. Maisha ta zauna kan kujera kamaryedda ya umarceta sedei batayi tunanin wannan fargaban zata addabeta ba, Amma tana shiga dakin sai kawai taji jikinta ya mutu tayi sanyi sosai, tana tunanin kadafa akamota idan Mainah tazo tareda Zaid ayanzu fa yazatayi? sabida idan an kamota da dikkan alamu gidan yari za’a kaita. 
Surukata kinyi shiru, Karki samu damuwa bawata matsala k0 yau Zaid yace a d’aura aurenku wallahi na amince sabida Ni kaina kin kwantamin a rai…. Bai ‘karasa furucinsaba ta katseshi” Kaga wannan hotunan, tamiko masa hotunan da Mainah tayi ‘areda Zaid acikin ruwa, Kai tseye tace‘ Ana kirata Ma’inah amma sunana na ainihi, wato babbar sunana na yan’ka Maisha ce sedei dan Allah banson Zaid yasan wannan sunan har sai ba’yan auren mu dani dashi. 
Tabe baki Baba yai yana binta da kallo yayinda ta’kara dacewa: Zaid yace yana kunyar yazo dakansa ya tinkareka batun aurenmu shine ya aikoni sabida yanzu na’san duk d’aya muke awajenka yace na tsanar maka cewa yau yakeso a d’aura aurenmu, yanada aiki sosai akansa bazaku samu haduwa ba ayau har sai bayan aure, Amma yace a tabbata an daura auren ayau Kuma a hanzarta kamin yadawo a tabbata anyi komai, kuma yace kada afadawa su Aunty Rahila sabida duk ya‘rigada ya sanardasu harma sunfara shirye shirye. 
Zaid din shi ya aikoki afad’amin wannan? Kwarai kuwa Baba shi ya aikoni. Maisha ta cije taimasa karya. Dafarko dattijon kamar bai gamsu da karyar nataba sedei daga baya Kuma tamkar tsafi Maisha tai Masa nan da nan yadauki wayarsa yafara gayyatan mutane yana farin ciki sosai. Itako tsit tazauna tana waina idanuwa tareda lisassafai iri iri aranta. 
Zaid ya baro Ma’inah a gidan Mamy yayinda wani abokin kasuwancinsu Bature (Clifford Esthen) yakirashi urgent business call, Tawaya yaturo masa adreshin meeting point din nasu. 
Zaid bai bata lokaci ba yafito, daman already drebansa yana mota yana jiransa Kai tseye yashige “Billionaires Suit Hotel zamuje”. Alright sir’ Dreba ya amsa Kai tseye sannan yaja motar yafara tuki. 
Wajen tanada nisa sosai awanni uku suka shafa a hanya ka’min su iso hotel d’in suna shiga dreban yai parking adedei entrance, dashike yau sauri yake babu security’n da yadauka. Shi kad’ei yashige ciki, Yana shiga aka fara gaidashi ana girmamashi wasu yan suka taho suna rokansa wai Dan Allah yad’an tseya suyi hoto. Kai sunma Rainawa kansu hankali, anfanin securities din kenan sabida irin haka ba‘zata faruba idan suna bayansa, wucewa yai abarsa yai wajen receptionist sukayi magana, Yan matan sunata gulmace gulmace wai gaskiya wannan receptionist taji dadi Landlord Zaid yai mata magana ayau today is her lucky day, da ma su ne.
Anan sukayi zasu had’u daman, sabida ba kowa ne yakeshigowa wajenba, VIP restaurant ce sai billionaires suke iya seyan abinci awajen koda coffee ce sunada tsadan tsiya, ita kofin coffee daya anan wajen 50 thousand kudinta, plate na abinci kuwa it depends amma least kud’in abinci awajen 150 thousand ne, Abu sauki awajen ruwa ce itama gora guda 10k ake tsaidawa. lrin shugaban ‘kasashenda suke ziyartar kasa Nigeria dakuma manya manyan ma’aikata irin billionaire in nan su suke iya zuwa cin abinci awajen, idan kud’in tayi musu yawa kuma anan zasu kama daki a VIP kwana d’aya rabin million 500 thousand 
Naira. Asalin babbar branch din hotel din a China take, anan Zaid yasa’ba zuwa akoda yaushe. Ya shige restuarant Kai tseye yazauna, inda yasa layin Client d’in nasa awaya yana kiransa. Abugu daya ya d’aga da harshen turanci sukayi magana, mutumin yace yananan zuwa sannan Zaid yakatse wayar. Baturen bai batamasa lokacinba yataho suka gaisa cikin fara’a daban girma. Nan ta’ke aka shiryamusu table da coffee dakuma fruits. “Back to business, Zaid yace dame kazo da ita, shima da harshen turanci yace’ Sorry sir mud’an jira kad’an Oga ta tana zuwa kaga kuma babu yedda za’ayi mufara magana abayanta. Fine, Zaid ya amsa masa sannan yafara danna wayarsa suna jiran Madam. 
“Y’an Mata kuyi sauri ku shirya dan Allah kada mu makara Kwalliya haka tun d’azun, Ni 
kudena wannan shafe shafen kufito mutm da kyau’nku Allah yayiku gakunan Masha Allah kowa yad’aga Ido yaganku sau d’aya dolensa ya’kara muku wata kallo. 
Aunty Nasibah tafad’a cikin sauri tad’auki Jakarta, “Hajiya Rahila kema kwalliyar kikeyine haryanzu baki fitoba. 
Ta’ke Ma’inah da Miemah suka sha kwalliya, sukayi shiga iri d’aya suka fito tareda Anisa wacce ita kanta bata gane waye Mainah waye Miemah sedei idan sunyi magana taga’nesu a murya. Suna fita Aunty Nasibah dake zaune tamike “Masha Allah biyu biyu suyan d’aya d’aya y’an biyu kyautar Allah gaskiya kunsha Kyau Yara, Baby Ani ke dei gaskiya mumuna ce cikinsu, kina ganin Yara kaman larabawa. Zumburo baki Anisa tai “Haba Momy haka zakice gaskiya ban yarda ba. Tafad’a cikin muryar shugwaba. 
Kai tseye Aunty Nasibah ta rungumeta “Allah Sarki Yaya Babba, Yayar Abi Zaid,  dan Gayena da Auta Hani, to ai gaskiya momy tafada, amma ai ko ba kyau akwai iya taku Baby Ani Fashionist. 
Aunty Nasibah sam halinta ba’a ganewa, wataran kuwa sosai zakajita tana yabon Kyaun Anisa harma tace Anisa zatafl y’an matan Abuja duka Kyau domin acewarta tunda tazo Abuja bataga wacce tafi Baby Ani ‘nta had’uwa ba, Toh gashi kuma yau abinda take fadi. 
Duk dacewa gaskiyarta ce Mainah da Miemah zasufi Anisa Kyau da had’uwa, Anisa ma kekkyawa ce sosai idanma ka ganta sau d’aya dole zaka ‘kara ganinta tabiyu. 
Y’ay’an Aunty Nasibah Biyar, Anisa ce babbar y‘arta sekuma Zabir takwaran Mahaifin Zaid wanda shiyasa ake kiransa AbiZaid, Zaid ne yakebin Zabir, takwaran Zaid shiko ana kiransa Ianabir, Sekuma Ziyad dinta wanda take kira d’an gaye, Autarta ce Hanifa ana kiranta AutaHani.
AbiZaid yana karatu ajami’arAmnity University Dubai level 2, lanabir kuwa yana SSZ Chuik_quin College a China daman shikam agidansu Zaid d’in yake zama alokacinda suke China. ‘Dan gayenta Ziyad da Auta Hani suna karatu a makarantar British Leaders a Kasar America, shi ‘Dan Gaye yana primary 5, Auta Hani kuwa tana Primary 3. Zaid ne yake d’aukan nauyin Makarantar su duka sai shi AbiZaid ne mahaifinsu dashike shima mai kud’in ne yana biyamasa kud’in Amnity University Dubai shima Zaid yace zai biya Baban kunyarsa yayi shiyasa yad’auki nauyinsa shikam dashike shima a Dubai yakeda zama suna zumunci sosai tareda Zuri’ar Zabir. 
Anisa ta kammala karatunta shine suka taho tare da Aunty Nasibah, da labari tazo musu cewa Turai Mafiya ta addabe Zuri’ar Zabir a China sun dawo Nigeria. 
Aunty Rahila tafito da d’an doguwar rigarta mai tsadan tsiya ta yafa mayaflnta da Jakarta a hannu. Tana fita taduba irin kwalliyarda su Miemah suka sha, tabe baki tai “Out thing d’in ne da irin kwalliya haka. “Mamy kinsan mu bamuson kwalliya sosai Anisa ce tai mana. Mainah tafad’a Kai tseye Mamy ta gyad’a kai Baby Ani Fashionist inji Mominta. Babu abunda tafad’a murmusawa kawai tai. Suka tseya sukayi hoto sannan sukafito. Lemozine d’in Mamy suka shige dukkansu, inda dreba yakejansu cikin kwanciyar hankali. 
Suna ma compound dake tsakar gida ka’min sukai last gate, suka tarar da taron maza ana tsei tseye tamkar d’aurin aure “Lafiya mesukeyi anan? Aunty Rahila tace dreba dan tseya mu tambayesu abindake faruwa anan domin idan munfita bazamu dawo gidan nanba sai dare ko kila wani abun ne yafaru. 
“Dalla Malam ja’mu muje” Aunty Nasibah ta tafad’a cikin mamaki tatabe baki tanabin jama’an da kallo, “Bazai wuce maula ce takawosuba masiyata talakawa ai haka suka ga’da. Dreba bai musa ba sabida sosai yasan halin Aunty Nasibah jansu yai kamar yedda tafad’a suka tafl, itama Mamy batace komai ba. 
“ZMZ Sulte zaka kaita, kuyi sauri kuma immedietly kuna kammalawa kudawo nan domin afara shirye shirye’ Gyad’a kai matardake gefen Maisha tai ‘Toh Hajiya babu wata masala Amarya kishigo. 
Aka bude mata mota kai tseye tashige, Tsit tazauna tanabin gidan da kallo har sanda suka kai ZMZ Suite “Masha Allah” Maisha tai hamdala aranta taji tafi kowa sa’a a duniya domin samun miji mai matsayi irin Zaid babbar nasara ce, Nan da nan taji aranta babu wani d’a namijin dazata iya zaman aure dashi aduniya ba’yan Zaid, sabida ya Tara duk abubuwnda take bu’kata ga Kyau ga kwarjini gakuma arziki, Yanzu babban burinta a duniya itace kawai taga Zaid yazama mallakinta ita kad’ei, yazama mijinta Kuma uban y’ayanta. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]