[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 25 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE




CHAPTER 25




Maisha Tasha wedding gown mai masifar kyau, wacce da’ka ganta, kallo daya za’kasan naira na aiki awajen. Ta‘sha kwalliya pes! Gwanin sha’awa, Aka kashe millioyin dukiya akayimata gyaran jiki, gasu kunshi, gyeran gashi abar azo agani. 
Farin cikin datake ayau ba’a misaltuwa, hakoranta awaje suke sharr! tunda safe taketa zumudi ta matsu a daura auren sabida hankalinta ya’kara kwanciya, atunaninta wannan plan na auren Zaid data dauka itace best plan a rayuwarta. Kai Harma ta sanarwa abokananta aka fara kiranta ana tayata murna. 
A zaune take cikin wata kantamemiyar daki a bangaren ZMZ Suites, tasa computer agaba tanabin video’n CCTV camera wanda ke nuno mata duk abubuwanda suke faruwa wajen daurin aure. Tsit ta zauna tana kallo, Maisha yau harda charbi a hannu tanaja tanakuma Addu’a aranta “Allah yasa agama d’aurin auren nan lafiya, sabida dazaran an daura, shi Zaid ba matsalarta bane sabida na mijine, minti guda zatajanyo zuciyarsa baki daya takama ‘kanta, Adduarta kawai a daura auren cikin kwanciyar hankali, kada ma yasani har sai ba’yan ankammala komai. 
Tana bin videon dai. Harma an shirya wajen sosai, kujeru akajejjero ko ta ina dasu dardumai, dadei sauransu, manyan mutane sunata pasowa cikin gidan da motocinsu, wasu ma harda escourt polisawa suna biye dasu abaya tsabar masayi. Maisha sai ‘kara walwala take, ayau jinta take asama, farin ciki tamkar zai kasheta, sabida tunda take rayuwa a duniya bata tabayin farin ciki irin hakaba. Ayau dei burinta ya cika ta’samo miji na gari wanda kuma ta tabbata zai dare mijinda Mainah zata kwaso sau dari. Daman ance haka Tagwaye suke, daya kanfi d’aya nasara da samu. Ayau dei Allah yarigada yanunawa Duniya cewa tafi Ma’inah Daraja da matsayi a idanun jama’a, tinda da kaddarar Uban giji yau zata chanza daga Maisha takoma Mrs Zaid ko Gimbiyar ZMZ. 
Cikin wannan tunanin na farin ciki ta kwanta kan gadon tsit! tana kallo dei abar sha’awa. har barci barawo ya tsaceta daganan video’n nata taringa tafiya ita kadei. 
Zaid Yana barin Sha’shin Mahaifinsa, bangaren Mamy yanufa, kai tseye yaja motarsa 
fuuuuu!!! tamkar barin garin zaiyi gaba daya, Yana shiga Hajiya Rahila Mansion yai parking adedei kofan parlour yafice aguje, y’an Sandan wajen duk sun tsorata Sabida basu taba 
ganin Zaid cikin wannan irin bacin Rai hakaba. Da ‘karfi yake kwalawa Mamy kira tun awaje harma ya’karaso cikin falo, Ya tabbata dei Mamy itama batasan da wannan daurin auren ba, duk wannan abubuwnda suke faruwa Kuma plan din Maisha ce babu tantama and she must pay. 
“Allah ‘karama yawan rai ango kasha kanshi, Hajiya Rahila sun fita tun tuni sadei idan zaka kirata ta waya, Ango ….. Bai karasa kalmar da yake kokarin furtawa ba, Zaid ya daga masa hannu Excuse me, I don’t have your time. Abunda yafada kenan yai tafiyarsa, mutumin tsayawa yai shiru yana mamaki, sabida tun ranarda Zaid yabayyana Mainah amasayin budurwarsa ba’a sa’ke ganin bacin ransa ba, to yaukuma da’ake daura aurensu meye ya bata masa rai haka? Tabe baki yai yana binsa da kallo harya fice masa. 
Zaid na fita yanufo motarsa, zuciyarsa na bala‘in konawa yaja Motar Kai tseye yafara tuki wanda sai Allah yasan inda yanufa, azuciyarsa yake nanata “Mainah I’m so sorry trust me l love you so much, and I will never compare my feelings for you to anyone else, not even 
your twins Sister infact Maisha she is the worsed person I’ve ever known. 
“Yara ku more rayuwarku, ku sha’kata iya San ranku Allah ne yabaku arziki yan Gata. Aunty Nasibah kenan, tana kwance kan wata tattausar kujera anamata massage, yayinda idanuwarta suke kan su Anisa wa’inda tun tuni suketa wa’sa cikin ruwa suna swimming. Ita Miemah bata iya ba, dashike tunda ta’taso bata taba shiga ruwa ba, Aneesa ce take fama tun tuni tana koyamata. Mainah koh bata dade sosai cikin ruwanba ta futo, dayake yau wani iri takeji aranta tamkar Zaid yana cikin damuwa gashiko basuyi wayaba k0 sau d’aya bare suga juna. 
Dressing room tanufa, jiki asanyaye tacire kayan wanka, Ka’na ta sany’a Abayarta wanda sukayi dedei da farar fatarjikin suka kuma karbeta sosai, Masha Allah. 
Ta dade tana tseye agaban mirror tanakuma duba wayarta, Allah, Allah take call d’in Zaid tashige awannan lokacin sabida ta matsu tasan halinda yake ciki, Zuciyarta na rayamata cewa koma a Ina yake Yana bukatarta kusa dashi. Inma ason samunta ne, tafiso sukoma gida tun yanzun Amma dayake sun taho tareda Aunty Nasibah yazama dole sujira a kammala mata 3hours massage tareda 2hours Manicure and pedicure. 
Haka takoma kan gado tai ta”gumi Jugumm!!! Da farko dei ta‘yi niyan kiran layinsa amma daga baya sai wani tunanin yacemata ko ‘kila aiki ce tai masa yawa. 
Ta cigaba dazama anan wajen har na tsahon awa guda, amma hankalinta duk ta’koma gida kawai so take taganta tareda Zaid k0 hankalinta ya dan kwanta wannan tunanin yasa ta’kira layin nasa Kai tseye sabida tasamu kwanciyar hankali. Ta kuma tarbi gagarumar sa’a abugu daya ya daga tamkar Daman jira yake ta’kirashi. “Habibi are you ok? Abunda tafara fadi kenan. Muryarsa na karkarwa yace’ Habibti trust me wallahi bazan taba cin amanarki ba, I love you so much my dear please forgive Habibit I’m so sorry. 
Duk tabi ta rude da wannan maganar nasa, ko meyesa yake bata hakuri? Habibi lafiya meye ya faru? Bata ‘karasa furucintaba ya katse wayar, Jikin Mainah ‘kara mutuwa tai Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’. 
Dakyar Sunusi ya tsayo Babbar Riga, dashike tunda yake rayuwa aduniya bai taba sa koda Jamfa ce’ba bare babbar Riga. 
Sunusi Shi ne dattijonda Maisha tai hiring yazo yamaye gurbin Mahaifinta, ma’ana yazamo waliyinta a wajen daurin auren. Ya danyi latti kadan kamin ya ‘karaso gidan. Sake Baki yai harda miyau, yanabin gidan da kallo tamkar wani tsohon bakauyen da yafito daga cikin jeji. Ahaka har ya iso wajen yanata kauyancinsa ko kunya babu, Inbanda kwashe kwashe irinta Maisha ma, sai Allah yasan inda ta kwasosa shi. 
Shi Mahaifin Zaid dei yau ya’ga ikon Allah gun wannan mutumin, tsoho da rashin kamun kai, 
Waliyai sun zauna, kowa yayi shiru za’a fara d’aura auren Zaid da Maisha kenan akaji jiniyar yan sanda. Motocin sojoji sai shigewa suke babu fa’shi tamkar bala’i harma da motocin yaki rundunar sojoji duk Zaid ya‘kira gidansa ayau, Sai gangarowa wajen suke basa karewa. 
Take jama’a suka mimmike kowa na zura idanuwa, Sunusi kam tun yanzu yafara da’nasanin zuwa wajen tsabar yaga bala’i, Sojojin suna fita suka fara tattara mutanen babu wanda suka tan’kawa cikinsu, tattarosu akeyi daya bayan daya anasa su cikin mota, dattijai sunata kuka da babban rigunansu ake kwasosu anasa su cikin mota, da matsayin su amma ayau wulakanci ta faru anan wajen daurin auren Tas! sojoji suka kwashesu babu wanda suka bari awajen sai Alhaji Zabir Mahaifin Zaid kenan. Ya tambayi mutanen ko waya aikosu, kai tseye suka fada Masa cewa Zaid ne yace aikosu, Nan da nan ran Baba Tai masifar baci. 
Maisha ta’sha barci sosai, farkawarta keda wuya tabud’e labule ta leko waje, ganin Babu kowa abangaren daurin Auren nata yasa tashafa hannu afiska tana hamdala, tamkar 
mahaukaciya tafara buga tsalle kan gado tana rapka ihu “Finally Zaid is mine, mine Forever Alhamdulillah, Gimbiyar Zaid Maisha Sambo Maidugu. 
Zazzakar muryar Zaid data doso kunnuwarta tun awaje yasa ta ‘kame kanta dasauri tai gaban madubi, inda ta ‘kara gyara kekkyawar fuskarta sosai tai kyau, tana kammalawa tazauna a tsakiyar gado tana jiran shigowarsa. 
Bude kofan yai tamkar balleta zaiyi, yafado cikin dakin kamar daga sama. Maisha na ganinsa tamike kamin ma tabude Baki tafadi wata kalma Zaid ya’shareta da Mari, Ta’kara damke hannunsa tana hawaye masu sananin zafi “Zaid please l love you kar’ka barni zan iya rasa rayuwa ta. 
Zaid bai tanka mata ba, har sanda Yan Sandan da suke biye dashi, suka ‘karaso cikin dakin tareda wasu mutane. Ba’tareda ya daga Ido yakalleta ba, nunata da dan yasa yai “kutafi 
da ita and make sure you punish her well. Maisha na kuka yayinda yan sandan suka damke 
ta suna fita Zaid yabiyosu “Karku mata komai kawai kubarta cikin cell”. Yes Sir, Yan Sandan suka sara masa baki daya sannan suka fita da ita. Da karfi takecewa; Zaid idan kaci
amanata Allah ya Isa, ldan Kuma ka auri Maina wallahi bazan taba yafemaka ba, Kuma 
kasani bazan barku Kucigaba dazama tareba,just mark my words Zaid zakayi danasanin rabuwa dani. 
Babu Wanda ya ‘tankamata cikinsu, mutanen dasuke wajen ne Zaid ya umarcesu dasu chanza komai na dakin baya san ya’karajin ko’da kanshin turaren Maisha ce, sabida daga yau ba’zai ‘kara ganinta ba har abada. 
Sai yanzu yadanji sanyi aransa yanabude kofa zai fito kenan sukayi Kacibis da Mainah yayinda tabude kofan zata shige, Tamkar a mafarki ya tabe baki cikin mamaki yace’ Ma’inah u? Ta gyada kai, Kai tseye ta rungumeshi tanacewa’ Zaid ina zasu kaita. Ya’kara rungumeta sosai yayinda yakecewa’ Waye? 
Maisha mana; ta amsa cikin sanyin murya. “Zaid dan Allah kada kasa atafi da ita
Har ‘kasa ta durkusa tanacewa’ idan antafl da ita momy zata shiga damuwa sosai, dan Allah Zaid ka ‘kira yan sandan sudawo da ita… 
Tunda tafara magana, shiruu Zaid yatsaya yana binta da kallo, Bata ‘karasa furucintaba ya katseta ” Excuse me Ma’inah I’m not in the mood to argue with now just leave. Yafada yana nuna mata hanyan kofa. Mikewa tai jiki asanyaye tabude kofa tanasa kafa, Zaid ya riketa “I’m sorry” yaturo dan karamin bakinsa tamkar yaro karami yace’ Please forgive me my dear? 

IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN 

®NEXT CHAPTER SPOILER ® 

Sai tafiya suketayi tun tuni, Ma’inah ta rasa gane inda Zaid zai kaita ayau,After a very long drive suka shige  Police station, ko me yakawosu nan oho. Suna fita ya rike hannayenta tamkar dan jagora take biye dashi abaya babu mutsu, Basu tsaya ko inaba sai cikin Cell inda kuma akasa Maisha, Alokacin Maisha tana kwance tamkar ba itaba amma da’kaga fuskarta zakasan akwai gagarumar matakinda zata dauka akan Zaid. 
Zaid ya rike hannayen Ma’inah kai tseye suka shige d’akin, Sanda yakaita hargaban Maisha 
sannan yadurkusa har ‘kasa, Ma‘inah ta’rasa gane abunda yake kokarin yi har sanda ya’zaro wata zoben (Diamond) yanacewa”Mainah Sambo Maidugu will you marry me???? 

Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]