[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 22 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 


CHAPTER 22
Darian Maisha kakejl tun awaje. Acikin dakinta take Ita kadai yau ba kowa agidan nasu dashike tin asubahi momy tashirya zuwa wajen aiki ayayinda tabar Maisha agida Ita kadei tana abunda taga dama. 
Waya take da abokinta Reza_Michiel tun tuni babu abinda take sai matsifar dariya tamkar 
mahaukaciya. 
“Reza wallahi Ina yinka sosal ba kadan ba, momsy ta ‘kori mutuniyar ai wallahi aikinku yayi Kyau sosai, Wai ni ina ‘ma kuka samo kayan yan Sanda kukazo mana gida tamkar mutanen arziki…? Shiru tai nadan wasu mintuna sannan ta’kara fashewa dawata sabuwar dariya “Ai kuwa Momcy ta gamsu da Shirin na’mu, shiyasama ta’kori Miemah daga gidan mu, ayanzu dei bamuda wata matsala, dani da Momcy na muke gida muna zamanmu cikin kwanciyar hankali. 
Tabe baki tai “aww wannan shegiyar, Mainah ta rigada tabar gidanmu tun tuni ayanzu Momcy ‘kanta tarigada ta mance da ita dama tun farko Daddy ne yake rawan jiki akanta momcy bata nuna mata kulawar uwa ba ko sau d’aya dan gwara Daddy shima yanzu baya nan kaga kenan I’m the boss”. Shiru tai tana sauraronsa sannan tace'” A’a a ranar damuka fara haduwa da CEO ai abige nake sedei ka sanni ai da Kisisina tuni na chanza masa kamanina na’sauya daga Maisha nakoma Ma’inah dashike ka’san muna kama sosai wallahi Bai gane ba, Amma dei abun Farin cikin shine tun ranarda yaganni I feel Yana Sona Kuma Insha Allah shine mijinda zan aura. 
Fuskarta ta nuna bacin rai sosai yayinda takecewa; Reza wace irin magana kake haka ka’san ni Kudi ce matsalata dazaran iyayena sunyi karayar arziki na gwammace na mutu akan inzauna dasu amasayina na y’arsu, Kai Allah ma yakiyaye sabida ko ran d’an Adam zan iya kashewa kawai sabida kudi
Ka’san dei Naira ba wasa bace mutumina. Kuma babbar maganan shine bazan iya rabuwa daku ba dazaran kuma Iyayena sunyi karayar arziki ai dokar kungiyar tamu ce dole murabu. …. 
Mommy ta dade da dawowa. tun tuni take labe a bakin kofan dakin Maisha take sauraron duk abubuwnda take fadi a waya, Aiko Saida tajira Maisha ‘taakammala surutanta tas! sannan taja kofa tashige dakin tamkar daga sama tafado. Wuf!!! Maisha ta mike tana zazzaro idanuwa yayinda ta gyara murya, tanacewa” Momcy yaushe kika dawo gida? Na tsammanin kince yau zaku dade sosai a wajen aiki. Tafada muryarta na karkaruwa domin ayadda taga fuskar mumsy’n nata ta tabbata babu shakka taji duk maganganun dasukayi 
awaya kuma del da alamu ranta yabaci sosai sabida har kwalla tagani a idanuwan ta. “ 
“lsha zauna” Momy tafada acikin sanyin murya. Babu musu Maisha tazauna agefenta kamar yedda tafad’a tai tagumi tamkar mutuniyar arziki. “Tarbiyar danabaki kenan? Momy ta’kara tambayarta cikin nitsuwa. Girgiza kai Maisha tai muryarta na karkaruwa tafara magana “Momcy amma toh ai’ Bata karasa kalmarba Mommy ta katseta “Rufemin Baki Maisha daman ashe Yan Sandan dasukazo nan gidanjiya hada baki kikayi dasu sabida kawai idan wannan yarinyar me ma sunanta… Miemah tadawo gida sai in’korota? lsha meyesa kike irin haka? Atunaninki San danake nunamiki tafi ta Ma’inah? Wallahi kinyi kuskure babba sabida duk daya kuke awajena, dashike ba’nasan tarbiyarki ta lalace sabida jinina ce ke, am your Mother, ni k0 kinfi kowa sanin babu abunda nafi so da ‘kauna a duniya inn Yayana wato dake da Ma’inah. Believe me chld Momcy zata iya sadaukar da 
rayuwarta kawai sabida ku, Amma sometimes I wonder, Kwata kwata halaiyar ki ta 
banbanta dana Yar uwarki she never disappoint me, Ma’inah ta banbanta dake Maisha I don’t know why she is really sweet tanasan kowa kuma batada wannan Kishin naki, she always makes us proud as her parents, Amma banda ke? meyesa kika zabi wannan rayuwar Maisha? Believe me or not l love you so much shiyasa ako yaushe idan kinyi laifl nakan danna zuciyata sabida bansan ai miki kallon wacce batada tarbiya, Maisha kin tura mahaifinki bango shima tun yana danna zuciyar nasa har kika Sanya masa hawan jini ayanzu Babu yedda zaiyi, Dani da Mahaifinki duk munsan kina shaye shaye Maisha idanfa baki dena wannan munanan ha’laiyar nakiba Zaki iya sanyamana hawanjini dikkaninmu mu mutu a tsanadiyar ki. ’ 
Anan ta’kafe hawaye sun hanata ‘karasa maganar datake haka tamike, Maisha tana ‘kiran sunanta amma ko ajikinta ficewa tai takoma d’akinta tacigaba da kuka dashike wannan maganganun sun dade aranta sosai ako yaushe tanasan tafada sedei alkawarinda tama ‘kanta tun ranarda tahaifi Maisha ce take hanata furta komai sabida tun ranarda likitoci suka tabbatarmata cewa yarta tana d’auke da Ciwon Blood Cancer irin wahalhalun da Yar tasha tun tana karama yasa Momy tadauki alkhawari cewa bazata taba batawa Maisha rai 
ba har karshen rayuwarta. 
Komawa d’aki Ma’isha tai, cikin matsifar bacin rai tabuga kofar tamkar balleta zatayi inda kai tseye ta kulleta da kwado Waldrop d’inta tabude daman anan take boye Wines dinta musamman sabida taringa Sha asirrance. Kwalbaye biyu ta zaro kai tseye tabud’e, alokaci d’aya ta dirkoshi dika Nan da nan tajita tana yawo a sama damuwar duk ta gushe, anan takwanta ko motsi ba’tayi dakyar tabude Baki tana magana ita daya “Ma’lnah laifinki ne, kece kikasani cikin wannan rayuwar ta shaye shaye, kece kika rabani da Mahaifina gashi Kuma kinasan kirabani da mahaifiyata to ta Allah ba Taki ba Wallahi sai naga bayanki sai na rabaki da dikkanin farin ciki na duniya wallahi Ma‘lnah sai na rabaki da kowa babu wanda zai rage arayuwarki, you will be alone always sad and lonely because that’s exactly what you deserve Ma’inah Sambo Maidugu. 
Ta Gangaren Mainah kuwa tana kitchen tareda Anisa suna girki. Jikinta tadan warware, Ayau daman sunyiwa kowa alkawari agidan cewa su zasuyi girkin dare, masu aiki duk sun huta sai murna suketayi, Babu dei irin nau‘ukan abincinda basu girkaba ko ina kanshi 
kakeji tamkar ranar Sallah. 
Zaid yana magana a waya yashigo bangaren nasu sai masifa yaketayi” How dare you? do I resemble your mate ya kuke wasa da hankalina jiyajiya mukayi magana da oganku yace 
an’kamata sannan tun bata koma China,n ba kucemin ta tsere muku , yan 
Sandan Nigeria bakuda anfani kwata kwata. 
Wayar tasa yajefota kasa tawarwarse ko ta ina yayinda yadaga hannu zai buga teburin dake gabansa kenan Mainah tarikeshi “CEO lafiya? Tafada cikin zazzakar muryarta, Kamar kullum guntun tsaki Zaid yaja “Damn it, Ma’inah just take care of yourself sannan kifadawa Mamy cewa Ammi ta’kara tserewa a wajen y’an Sanda yazama dole inje in nemota da kaina. Da wannan maganar yajuye aguje yabar falon tunkam Ma‘inah tafurta kalma guda “Zaid Kar 
kaje. Tuni yafita yabarota awajen tana tseye. 
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ hawaye ne suka fara zubowa a idanuwana tana mamakin rayuwar Zaid ko meyesa mahaiflyarsa take irin wa‘innan abubuwan oho, Ko meyesa ta tsanesu? Uwa uba kuma meyesa aka kamota tun afarko aka kaita gidan yari. 
‘Ka rar wayar tace takatsemata doguwar tunanin datakeyi, a firgice taduba fuskar “Mommy”. Jiki a sanyaye ta d’aga “Sallamu Aleikum Mommy an yini lafiya? Kai tseye ta amsa“ Alhamdulillahi Ma’inah inasan kizo gida yanzun nan kisameni. Tabe baki Mainah tai “Mommy Lafiya?”. Cikin sanyin murya ta amsa “Laflya kalau Mainah please come. Mainah bata amsa mataba takatse wayarta. Anan tashiga tunani “k0 meye dalilin nemanta da 
Momy takeyi abu d’aya ta tuna aranta “kodei Maisha ce kuma tai hatsari?. 
Tunani iri iri take a ranta haka ta’kira Mamy a waya ta tsanar mata komai harma da sa’kon 
da Zaid yace afad’amata cewa mahaifiyarsa ta tserewa a hannun yan Sanda duk tahada tafad’a 
mata alokaci daya. Daga nan takoma d’aki, anan tai wanka ta shirya sukayi sallama da Anisa sannan tatafi ’ 
Aiko gidan ya had’u ba shakka. Ta dad’e tanabin gidan da kallo tanakuma mamaki. 
Wannan ne gida na Uku wacce Miemah take aikin shigewa tun tuni neman aiki, duk dacewa sauran gidajen datashige duk ko’rota sukayi cikin wulakanci, tana sa ran ko zatayi sa’a 
anan sabida girman gidan zata bukaci masu aiki da dama. 
Alokacin garin tad’an fara duhu, Magriba ta kawoki kai, dasauri tai sallama Kai tseye 
tashige gidan,Aiko tanashiga karnuka aka sake mata kamar gidan mayu, haka tafito aguje tana sula ihu. karar mota taji abayanta ka’ min tabada hanya motartarigada ta iso wajenta 
nan da nan ta taka ta, ai kuwa bata kara minti guda ba tafice daga hayacinta…. 
Tana flta Mercedes Benz tashige da’kanta take tuki, tayi tunani iri iri aranta ka‘min ta’karaso gidansu. Alko tana isowa ta danna horn Garba Mai gadi yabude mata gate. Yana Iekowa cikin motan yaganta tsalle yafara bugawa cikin farin cuki yana mata Maraba, maraba Hajiya Ma Inah mutuniyar kirki”. Ta fito mota tana murmushi suka gaisa cikin fara a sannan ta karaso falonsu tana shiga tahango katuwar cake dama wasu decorations 
harda balloons an shirya ako ta ina, Ganin Favourite cream d’inta akayiwa cake in yasa tai 
murmushi ahankali ta matso har kusada ita aiko sunanta tagani asaman cake in “HAPPY BIRTHDAV MA’INAH”. 
Tseyawa tai shiru tanabin Kwalliyar da akama falon da kallo, anan ne Mummy tafito daga dakinta itama ta’sha makeup ga rigarta Shar! abar azo agani. Cigaba da tseyuwarta tai tanabin Momin nata da Kallo. 
“Happy birthday to you” Momy tafara Waka tana tapi. Karasowa wajenta Mainah tai kai tseye ta rungumeta “Thank you Mommy na gode ‘ Tafada tana murmushi. Rungumeta 
Momy tai sosai tafara zubar da hawaye tana tuna maganganun dasukayi da Maisha. Babu 
yedda Ma’mah batayi da lta akan tafad’a Mata abundake faruwaba ganin duk ta sauya ba amma Taki ahaka tarike damuwar nata suka yanka cake. Da hannunta tabaiwa Ma’inah aba’ki haka itama tamaido mata, sunyi nishad’i sosai kamin Ma’inah takoma ayau taji dadi 
sosai kuma sai yau ta gamsu cewa Mahaifiyarta tana Santa ba kadan ba. 
Alokacinda Ma’inah tafito, magriba ta’kawo kai, garin ta‘ dan fara duhu haka tafara tuki 
tanakuma bin birnin da kallo ta window’n motarta cikin farin ciki. 
Dashike babu makaranta yau Sunday, tin da safe Asad yaflta tareda Muna, babu Kuma inda bai kaitaba, sunje playground sunyi tawasa sosai shima biyemata yai suka sha gudu harda rawa tamkar yaro, sun shiga ruwa sunyita swimming hankalinsu a kwance, Munah taji dadi matuka shiyasa takeson Shushun nata and he is the best shushu ever ‘kirarin datake Masa akoda yaushe kenan (Shushu tana nufiin Uncle da yaren Chinese). 
Maghriba takawo kai alokacin suka kammala seyayyarsu suka koma mota inda Asad yaja Motar yafara tuki full speed sabida yasan idan suka makara Zaid zai saukar da dikkanln haushinsa akan shi shiyasa yake tuki dasauri sabida su iso da wuri. Munah ce tarufeshi da surutu tana masa waka “My Shushu is a good man iyaiyayo”. Shima haka yake bi “My Daughter is a good child iyaiyayo”. 
Suna isa babban titi, babbar mota tashlge gabansu Asad yana kokarin kaucewa sterin ta sakarmasa haka Motar tafara tangaliya yana kokarin kaucewa sausayi ta riskeshi inda yabige wata yarinya. Dasauri yazaro key yafitar sannan ne Motar ta tseya, Munah yafara 
dauka cikin sananin damuwa da tashin hankali, ganin babu abunda yatsameta Asad ya 
ijiyeta Kai tseye yai wajen yarinyar da yataka idanuwa yazaro kororo kororo “Ma’lnah? Meya kawota nan? Tambayarda yafara ma kansa kenan. Ihu Munah tasaka “Shushu Mina taaa mutuuu. 
Shafa ‘kanta yai “Munah kidena fadan haka maza shiga mota mutafi.Yafad’a cikin sananin tashin hankali. 
‘Daukota yai chak! Yakaita mota, Munah tanayimata fifita har tseida suka karaso Zabirs Mansion. masu aiki yakirawo kai tseye aka d’auki mara lafiyar aka kaita falon Aunty Rahila. Kai tseye Asad yakai Munah wajen masu kula da ita yadawo Cikin damuwa Anisa ce tafito ta tsamesu “Inna lIllahi wa Inna ileihi rajiun Ma’inah? Meya tsameta?’ Babu abunda Asad yafad’a ruwa yad’auko ya yayyafo mata dashike bataji ciwo sosai ba Nan da nan 
idanuwarta suka bude. Anisa ta’kira sauran mutanen gida duk suka fito cikin damuwa. 
Layin Zaid Asad yasaka awayarsa hannunsa na karkarwa yadanna. kai tseye yafara kiransa. 
‘Karfe Bakwai dedei Mainah ta‘karaso gida dasauri tai parking motarta twee aguje, Zaid tahango achan yana gudu shima da dukkan alamu kuma cikin tashin hankali yake, Da ‘karfu
Ma’inah ta ambaci sunansa kamaryedda ta’saba “CEO”. 
Da mamaki a fiskarsa yayinda ya waiwayo “Ma’inah? Ya tseya chak! Yana binta da kallo Sanda ta’karaso inda yake ya rungumeta muryarsa na karkarwa yace” Toh wacece tai hatsari Malsha kenan? Clkin rudani Ma’inah ta’kara tambayarsa “Hatsari kuma? Babu abunda yafad’a janyota yai suka shigo har dakinta, su Aunty Rahlla suna ganinta dukkaninsu suka mike da mamaki afiskokinsu. Malnah ta‘kasa gane abundake faruwa 
Saida tadaga ido sannan taga Miemah ce kwance akan gadonta ansa mata drip ahannu. 
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ abunda tafara furtawa kenan “Miemah ce”. Tafad’a cikin sanyin jiki. 
Wacece Miemah? Dukkan ninsu suka hada baki alokaci d’aya, Maisha ce kenan kike nufi? Aunty Rahila ta’kara tambayarta cikin rudani. Girgiza kanta tai hawaye suna zuba 
idanuwarta yayinda ta’kara cewa” Miemah ce wannan ba Maisha bace. Haryanzu dei 
mutanen gida cikin duhu suke tamkar anga barawo na sata cikin dare… 
IYA ABUNDA YA SAWWAKAA YAU KENAN ‘

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]