[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 


CHAPTER 21
 
Kowa ya maida Idanuwansa akan Saminu ayayinda yakammala bayanansa Aisha ce tafara magana Kai tseye tace’ ya mai girma mai sha‘ria a taimaka ai mana adalci wallahi kamar yadda Mijina ya fad’a hakan ne laifinda kotu take zarginmu da ita gaskiya ce mu muka kashe Lawan. Ta’karasa kalmar nata ne tana hawaye sosai… Miemah ce ta mike wuf! “Umma meyesa kuke amsa laifinda baku aikataba, Umma bazaku iya kisa ba Wallahi inada tabbacin cewa Umma ko kiyashi baki taba kashewaba ballentana ran dan Adam. Miemah tana kuka sosai yayinda tafito gaban kotu aguje ta rungume mahaifiyarta “Umma please kada kuyimin haka ina shan wahala agidansu Maisha ….. 
“Order in the court! Judge ya’kara buga na’uran dake gabansa sannan yace’ Barrister Mustapha your client is violeting laws kayimata magana ba’a surutai cikin kotu… “Agafartamana.” Barrister Mustapha yami’ke nan ta’ke yarike Miemah yamaidata wajen zamanta. Zubewa har kasa Aisha tai ahankali takefadan “Saminu bazan iyaba, duk dacewa ayanzu na tabbata Miemah ba Yarmu ta jini bace wallahi hakan bazata taba chanzawa azuciyata ba Ina santa, banson ganinta tana wahala har abada Miemah Yatace kamar yedda Maisha da Mainah suke Yayana I’m sorry Mijina ka gafartamin zan fadi gaskiya wallahi bazan jure ganin Miemah cikin wannan yanayinba. Mikewa tai nan take tana kokarin magana Saminu yasa karfarsa da karfi ya takata da hankali yace” Idan kin fadi gaskiya kotu zata iya bincike mai zurfi kan case d’in akarshe zata kamo Yarmu Ma’isha kuma gidan yari za‘a kaita amasayinki na uwa Zaki kai jininki ga hallaka… Bai ‘karasa 
furucinsaba Aisha tace toh ai laifinta ne, she is a criminal Saminu believe it or not Maisha ba kalata bace batada tarbiya wallahi na gwammace Maisha ta wahala akan Miemata she is innocent meyesa zamu daurata tana wahala akan laifin Maisha wallahi bazan lamunta ba. ‘ 
Haushi ne yakai har makokoron Saminu ya‘kasa fahimtar tunanin Aisha, awannan lokacin mantawa cikin kotu suke yai inda Yasha’ke wuyan Aisha tamkar zai kasheta yace’ Wallahi sai na hallakaki idan kika tonawa Maisha Asiri zan kasheki in kashe Miemah harma da Mainah …… 
Nan take securities suka taho,jansa akayi sunaja yana ja har sanda aka chanza masa wajen tsayuwa yanacewa” Aisha mark my word. Barrister Ahmad ne yamike sai wani murmushi yake Yana dariya” Ya mai girma mai sha’ria wa‘inda ake tuhuma da kansu sun amince da zarginda kotu takeyi akansu kamar yadda sha’ri,a ta fad’a idan wa’inda ake zargi 
sun amince da Lafinsu Kai tsaye za’a zartar musu da hukunci. 
Objection my Lord Barrister Mustapha ya mike duk dacewa jikinsa tayi sanyi bashida abun fada” Ya mai girma mai sha’ria bai kamata barrister Ahmad yaringa fadamaka abinda zakayiba amasayinka na shugaba. Judge ya dade yana rubutu a littafinsa sai yanzu yai magana” Objection Sustain, Korafi Bata karbu ba gaskiyanka barrister Ahmad sha’ria tace idan wa’inda ake zargi sun amso laifinda ake tuhumarsu babu bata lokaci kotu zata zartar masu da hukunci dazaran sun kara tabbatar da maganar ta’su. Saminu ka tabbata cewa da kai da Matarka kuka kashe Mai gadin gidan? “Ehh haka neh”. Saminu ya amsa Kai tseye babu alamun tsoro tattareda shi. 
Akan wani dalili? Meyesa kuka kashe shi? Judge ya’kara tambayarsa. Kai tsaye ya amsa” Sabida musamo kudi, dama munje wajen boka batun neman kudi yacemana idan munasan arziki mai zurfi yazama dole mukashe rayuka Goma, wato mutane tsoffi maza 
biyar da yan Mata biyar amma akan Lawan muka fara asirinmu ya tonu. 
Haka ne? Judge ya maida ldanunsa akan Aisha, itako mamaki ne ya isheta sosai tanabin Saminu da kallo cikin sananin kad’uwa daman haka ya iya tsara karya. Bugamata wata kallo Mai matukar tsoratarwa Saminu yai ayayinda takoma cikin hayacinta dasauri tace‘ Ehh haka neh ya Mai girma mai sha’ria. Tanafadan wannan tafara zubar da hawaye masu zafi yayinda tamaida idanuwarta akan Miemah wacce take zaune achan baya tana kuka. “Wallahi Ko dana amince zan tafi gidan yari bazan taba barin Yata ta wahala a gidan Mahaifinta ba, yazama dole Miemah tasan gaskiyan zance cewa ba mune asalin lyayenta ba, Sambo da Safeenah sune Iyayenta na ainihi. 
“Abisa wannan kwararrun hujjojin, kotu ta yankewa Saminu da matarsa hukuncin daurin 
rai da rai agidan yari. COURT!!!” 
Mikewa Miemah tai aguje tabar wajen yayinda Yan Sanda suka kamo Iyayenta suna fita dasu zuwa prison. Tana zaune kan Varrendern tana kuka tareda tuna irin wahalhalun datake sha a gidan kawu Sambo gashi ko ayanzu batada inda zataje bayan Nan. 
Dakyar Umma ta roki alfarma abarta tai magana da diyarta kamin sutafi amma tanazuwa wajen Miemah tai Banza da ita, Umma tana kokarin sanar mata batun asalin lyayenta amma Miemah ta ‘ki sauraron dukkannin maganganun datake, barin wajen tai aguje takoma wajen Barrister Mustapha. Zaunawa tai tasashi agaba sai kuka take ta’kasa cewa komai. Barrister shima rasa abun fad’a yai, tausayin Miemah yashige zuciyarsa amma babu yedda zaiyi yataimaka mata. “Miemah kiyi hakuri kaddara ce, kuma haka Allah ya tsara tun FILazal sedei karki damu zan zurfafa bincike akan case din, kuma Insha Allah ko ba dade ko ba jima sai na gano gaskiyan wanda ya aikata wannan laifi Kinga idan nayi hakan kuma iyayenki zasu fito Insha Allah ke dei kitayasu da Addu‘a. ‘ 
Sai yanzu Miemah tai magana” Maisha ce, Attorney kai bincike akanta sosai I’m very sure itace, Sabida Ummata ta fadamin tun afarko Maisha ce ta turo mutanenta gidanmu, kuma aranar ne kisan yafaru. Gyad’a kai Barrister yai yana murmushi” Ba komai Miemah, yanzu zan biyamiki kudin jirgi gobe da yardan Allah kawai sai kikoma Abuja gidan kawunki, Amma karki samu damuwa na’tabbatar miki zan ringa bincike anan kuma zan sanyawa Maisha Ido kamar yedda kika fad’a Insha Allah iyayenki zasu bar nan wajen very soon just trust me Miemah. 
Jiki a sanyaye ta gyada kai” Na gode Barrister Allah kuma ya bayyana gaskiya. “Amin thumma Amin” Ya amsa kai tseye. Ayayinda suka shige motarsa sukaje gida. 
A ranar barrister yabiya mata kudaden jirgi, da sassafe suka kaita Airport tareda matarsa, Saida suka jirajirgin nasu ta tashi Sannan suka koma gida. 
Kwana biyu Mainah tai a asibiti aka sallamosu suka koma gida tana jinya, tinda akayimata Surgery ba’ta magana ko menene aka fad’a shiru take sedei taringa binsu da kallo tana kuka babu yedda ba’ayi da ita ba, a kwana biyun an ‘kasa gane kanta gaba d’aya. Kalma guda ce take nanatawa, sunan Mahaifinta “Daddy” bayan wannan ba’ta cewa komai, shiru 
Zaid yayi iya bakin kokarinsa ya’kasa shawo kanta, haka su Aunty Rahila duk sun kokarta sun ka’sa, Uffan bata tankamusu. Akarshe Asad ne Zaid yakirawo sabida ya fahimci cewa Mainah tafi sabawa dashi sosai ko kila idan shine yai Mata magana zata amsa masa. Da yamma aka kirasa yazo gida inda Zaid yayi masa bayanin komai, Yayi mamakin hakan ba kadan ba, shi da yasan Ma’inah dasan Fara’a meyekuma yamaidata haka. “Wallahu A’lamu sai Allah” Zaid ya tabe baki “Babu yedda bamuyi da itaba amma tun shekaran jiya babu chanji sai kuka take, likitoci duk sun ko’karta amma still babu alamun chanji abun mamakin shine gwaje gwaje da dadama sukayi akanta kuma sun tabbar mana babu wata matsala it’s very Confusing dude we don‘t Know what to do anymore, Ko dei muturata asibiti a China a zurfafa gwaje gwaje ne?. 
Dasauri Asad ya katseshi” No Dude kada muyi hanzari, Ma’inah tafuskanci abubuwa da dama a rayuwarta So inaga wannan depression data shiga is normal sedei a ringa kokari dei ana kwantar Mata da hankali, ko Taya dei anuna mata ana tare, don’t let her feel alone Zaid always protect her, sabida na‘san kana Santa. Yafada Kai tseye. “Asad come on” Zaid ya katseshi, murmusawa Asad yai “Will you deny? Ba’ka sonta neh? 
Shiru Zaid yai nadan wasu mintuna sannan yafashe da dariya kamar ba shiba, kuma babu shakka yayi Kyau sosai, dariyar ta ‘karbeshi ba kad’an ba “Alright fine I admit Ina sonta. Murmushi ya’kara yi, inda dimples din fiskarsa suka ‘kara bayyana sosai yace; Asad wato kaifa dan sa ldo ne, I have been noticing you tun ranarda mukafara haduwa da Mainah ka fahimceni, I was like this guy is not serious yaushe mukayi magana dashi har nacemasa Ina San Ma’inah. 
Bai karasa maganarba, Asad shima yafashe da dariya, yayi dariya sosai ” Aww azatonka bazan gane bane? Ai na’ma fika sanin kanka Mutumina believe it or not. 
Suna wannan hiran har suka kai d’akin Ma’inah inda kai tseye yai knocking aka bud’e musu. 
Matan gidan duk suna ciki, daga Aunty Rahila, Aunty Nasibah harda Anisa. Suna shiga Aunty Rahila tamike cikin sananin damuwa tace” Zaid inaga ya’kamata mu maidata asibiti wallahi Babu chanji kamar dei yedda kabarota. 
Asad ne yai magana” Ba komai Aunty Rahila zata koma normal nan bada dadewa ba Insha Allahu, a ringa kulawa da ita sosai, This is normal yawancin mutanen da sukeda damuwa haka suke dawowa bayan surgery amma bazasufi sati guda ba idan ana kulawa dasu sosai nan da nan sai kika sun koma kamar yedda suke ada. “Toh Allah dei yasa hakan ne”. 
Jiki a sanyaye Aunty Nasibah tace’ Ya’kamata mubasu waje, ko Wala Allah zatayi musu magana tinda dei naga Asad Mutumin tane sosai. Babu musu duk suka tashi kamar yedda tafada sukabar dakin. 
Asad ya matso har kusa da ita, ayayinda Zaid ya tseya shiru Yana binsu da kallo. Tissue Asad yad’auka yasharemata hawaye cikin sassanyan murya “Miss Ma’inah meke daminki? 
meyesa klke kuka? Shiru tai tamkar bada Ita yakeyi ba taci gaba da kuka, “Come on Mainah talk to me please ko dei mukori wannan Monster. Yanuno Zaid yanacewa” Zakiyi magana idan yafita? 
Babu abunda tafada, Kallon Zaid din kawai tafayi yayinda yai shiru shima yana kallanta. “Mutumina Kasata dariya mana meye kawani tseye kaman statue. Asad yami’ke tseye “inaga ya’kamata musata dariya ko da murmushi ne it will less her temper. “Kamar ya?” Zaid ya tambaye shi cikin rudani “How”. Kai tseye yace” lrinsu rawa,jokes ko irin abubuwan nishadi haka. 
Rawa? Zaid ya katseshi “Asad you are not serious kawai dan munyi rawa sai tayi dariya? “Ai Zaid Matsala ta da kai kenan rashin bin shawara. 
Girgiza kansa yai sannan yahada da dan guntun tsaki cikin sanyin murya yace ” Inbanda rashin tunani irin na Asad ma mutum kawai sabida yanasan dariya, idan yaga ana rawa kawai sai yafashe da dariya ina ruwan mahaukaci ai sai awuce da mutumin psychiatry koba haka ba Ma’inah? Mutumin na’ki ne akwai shirme. Yajuye yana ganin Ma’inah, aiko 
kamar a mafarki sai tai murmushi tana kallansa itama. 
“Kema dei shirmen nasa yabaki mamaki Koh” Zaid ya’kara kure mata Ido shima yana murmushi. Mikewa Asad yai yanabinsu da kallon fuskarsa duk fara’a yace’ CEO yanzu zan barku, sabida zan koma office. “Alright take care” sukayi sallama da juna yai tafiyarsa. 
Mikewa Zaid yai shima zai fito kenan Mainah ta bude Baki a hankali ta ‘kira sunansa” CEO” da sauri yajuyo “Ma’inah” baima san yedda ya ambaci sunan nata ba, tsaban farin ciki haka yakoma wajenta aguje, kai tseye ya rungumeta yanacewa” I love you so much Mainah. 
“I love you more zaid” Mainah tafada tana hawaye na farin ciki da cikon buri. 
Miemah tana sauka daga jirgi tasamo Taxi har gida suka kaita ko kud’in Motar Suma basu ansaba sabida sun tausaya mata matuka, irin kukan datake sai kowa yai tunanin rasuwa akayi musu. Shigowa gidan tai jiki a sanyaye tana tuna karshen maganganun da Sukayi ita da Aunty Safeenah Kuma kamaryedda tafada hakan ne taje Maiduguri tadawo Babu mafita daman Aunty Safeenah tace’ Kamar yedda taje haka zata dawo musu gida babu chanji. 
“Ke Yar masiyata daga ina haka? Sai yanzu da Maisha tai magana Miemah taga harma ta ‘karaso falo ba’tareda ta saniba. “Kishigomin gida kai tseye haka Miemah k0 sallama babu. Mommy tamike tseye cikin masifa tace’ Toh wallahi wannan rashin tarbiyan naki bazan lamunta ba. 
Durkusawa Miemah tai har kasa tana Bata hakuri” Aunty kiyi hakuri wallahi iyayena ne aka kama yanzu hakama suna gidan yari. “Rufe mana Baki Yar gidan matsiyata” Maisha ta katseta “Meye alakarmu da Iyayen naki, to ai dama chan din tafi dacewa dasu. 
“Wato Miemah tsaban wulakanci ki rasa wanda Zaki ‘kalawa sharrin laifin Iyayenki sai Yata? Mikewa Momy tai kai tseye ta sinketa da Mari afuska” Jiya yan Sanda sukazo mana gida akan sunzo domin suyiwa Maisha tambayoyi cewa sukayi kece kika fadamusu Maisha ce ta kashe Lawan ba mahaifanki ba. Fashewa da kuka Miemah tai domin a iya saninta dei babu wanda tafadawa batun Maisha sai Attorney shi din ma ayau sukayi maganar dashi. To kuma wani dan Sanda ne yazo gida yana tuhumar Ma’isha? 
Ki kwaso tarkacenki kifitarmin daga gida maza. Momy ta daka mata tsawa” Domin kila gobe tuhumar dakikama Yattawa zata koma kaina. “Umma kiyi hakuri ko da wanke wanke ne nayimuku sabida ba’nida inda zanje bayan nan Kuma babu kudi a hannuna 
wayatama tun tuni na tsei da ita …… 
Babu bata lokaci Maisha tashige daki Nan da nan tadawo da akwatin kayanta ta wurgomata shi “Fita kibar mana gida Jaka, dabba. Share hawayenta tai kai tseye tadauko akwatin kayanta tafita kamaryedda suka umarceta. “Miemah ba yanzu kika dawoba ina Zakije ko hutawa bakiyiba? Garba Mai gadi ya tambayeta cikin mamaki. “Koroni sukayi” Miemah ta amsa masa tana hawaye. Shiru mai gadin yai nadan wasu mintuna sannan yace toh ya za’ayi kowa dei yasan Halin Matar gidannan ta banbanta dana Alhaji ko kad’an batasan d’an wani ita sai jininta takeso. “Toh yaza’ayi? Miemah ta amsa ayayinda taturo gate kai tseye tai waje. 

IYA ABUNDA YA SAWWAKA AYAU KENAN  
 x NEXT CHAPTER SPOILER X 

Wannan ne gida na Uku wacce Miemah take shigewa tun tuni neman aiki, duk dacewa sauran gidajen datashige duk ko’rota sukayi cikin wulakanci tana sa ran ko zatayi sa’a anan sabida girman gidan zata bukaci masu aiki da dama. 
Alokacin garin tadan fara duhu, Magriba ta kawoki kai, dasauri tai sallama Kai tseye tashige gidan, Aiko tanashiga karnuka aka sake mata kamar gidan mayu, haka tafito aguje tana ihu. ‘karar mota taji abayanta ka’ min tabada hanya motar tarigada ta iso wajenta nan da nan ta taka ta bata ‘kara minti guda ba tafice daga hayacinta…. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]