TAGWAYE CHAPTER 16

TAGWAYE 


CHAPTER 16
Daddy ya’kasa barci, dare guda yashafe yana tunani dakuma mamaki alokaci daya. Ya rasa ga’ne dalilinda yasa Saminu yai masa irin wannan karyar da babu fasali, Bai taba tunanin san kudinsa ta’kai hakaba duk dacewa dei yarigada yasan yana matukar ki’shin dukiyar dayatara amma bai taba tunanin zai yi anfani da irin wannan hanyan sabida abun 
hannunsa ba. Wannan tunanin Daddy yake har zuwa wayewar gari. § borno STATE : MAIDUGURI 
Sha biyun dare ko ina shiru kakeji babu motsin dan Adam bare aljanu cikin gidan. Saminu tare da Matarsa yake cikin daki suna barci mai kwanciyar hankali‘ Shegiyar ‘karar datake fitowa daga waje yasa duk suka taso a razane. A tsorace Aisha tarirrike mijinta yayinda take zaro idanuwa tana Kuma tambayarsa abindake faruwa shima kwata kwata yarasa meke faruwa cikin gidan ‘Inna lillahi wa lnna ileihi rajiun’ Addu’ar datazo bakinsa duk karancewa yake jikinsa na rawa. ‘Karar dasukaji kuwa matsowa take tamkar sautin balle kofa. Yai ajiyar zuciya yami’ke cikin sananin tashin hankali yahasko wutan dakin sannan yaja kofa yafice cikin duhu yaji an chapke wuyarsa ankuma rufe masa baki da wata aba nan yafara ihu cikin wuya babu wandakejinsa. Nan ne mutanen suka kunna wuta Saminu ya daga ldo ya kallesu, wasu katti ne sosai sunkai su goma fiskokinsu kuwa duk arufe suke tamkar Yan fashi. 
Zagayeshi sukayi da bindigogi, inda yake zaune a tsakiyarsu wannan lokacin idan ka yanke jikinsa dawuya kasamo jini sabida a tsorace yake!!!. ‘daya daga cikin sune yai magana cikin wata katon murya yace “Tasowa zakayi kakawo mana cikon kudin gidan Maisha daka saya ka bata million Uku saura million Bakwai sabida million Goma kukayi. Idan Kuma kaki yanzun nan zamu parpasa kanka da bindiga. 
A wannan lokacin ne Aisha tafice daga d’aki ta lekosu a tsorace ta rapka ihu tana kuka nan 
da nan jikinta yafara daukan zafi tana rawa ‘kar_Kar_Karr, Dakyar tabude Baki tafara magana “Dan Allah Kar kukasheshi kudubi girman Allah ku kyaleminshi. Bata karasa kalamanta ba daya daga cikin mutanen ya janyota, aka dauremata ba’ki itama suka jefota kusa da mijinta. ‘ 
Nan ta zauna tana mamakin abunda mutanen suke nema gunsu, tun tuni take kokarin magana amma babu hali dashike duk an daure bakunansu. Falon suka wargaza babu abinda suka gani sannan Kai tseye suka shige dakunan gidan suma duksun binciko babu abindasuka gani. Sannan ne suka dirko Babbar Falo inda suka tarar dasu anan wajenda suke ko motsi basuyiba bare suyi kokarin guduwa ko kiran yan Sanda. “Kai!!! Ina ka ijiye kudaden gidan Maisha? Daya daga cikinsu yadaka masa tsawa yayinda yai pointing dinsa da bindiga babu tsoro ya gyara bindigarsa deden sakewa yace; Zaka kawo kudaden k0 kuwa. 
Aisha kuwa se kuka take tana tsananin mamakin maganganun da mutanen sukeyi “Alhaji wasu kudaden Maisha ka dauko Dan Allah kabasu su tafi wallahi zasu kasheka. Tafada cikin nunfashi daya. 
‘Kasa magana Saminu yai jikinsa na rawa yanakuma hada gumi, tunanin dayake dei itace Ina zai samo Million bakwai shida ko sisi yanzu bashida ita, gidan ma da’ake magana ya tsayar da ita ya biya basussukanda kotu kebinsa. “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ sunan Allah yafara ambata tareda addu’oi yana kuka dakuma Salati duk alokaci daya. 
Suma yayi adedei lokacin duk dacewa bindigar a sama aka sake ba akansaba. Aisha kuwa nunfashinta ne ya tsinke Raz!!! Zuciyarta ta’kara tashi tana tambayan mutanen wasu kudade suke magana. Ai kuwa Labarin gidan Maisha duk suka kwaso alokacin suka tsanar da ita. Mamaki ce sosai ta bayyana a fuskarta “Shine kwata kwata batasan da maganar ba, Toh ma shin Maisha ce ta aikosu gidan kenan sabida a anso mata kudaden ta. 
Kai tseye daya daga cikin mutanen yai pointing bindigar a deden ‘kan Saminu dake kwance ba hankali yana kokarin sakewa Yayinda Aisha tai saurin dakatar dashi “Dakata kada kukashe shi zamu biyaku kudaden ba dei million Bakwai bace kunsamu. Tana wannan maganar tanufo daki inda tadauki takardun gidan dasuke ciki ta mallakamusu a maimakon kudi sabida gidan dasuke ciki Sambo ne ya sayo musu ita Million Shida, Sannan ta tahad’o musu da furnitures dama komai na cikin gidan, Cikon million Bakwai dinsu kenan. 
Suna ansowa, Ogansu ya ciko bokati da ruwa duk aka zube ajikin Saminu. A Firgice ya taso yana zazzaro idanuwa tamkar mara gaskiya. “Kudubi girman Allah ku kyaleni zan biyaku kudaden nan da wata guda kuyi mana afuwa ku kyalemu …… 
Babu wanda yake sauraron abubuwnda yake fadi, Akwatunan kayansu aka tattaro inda 
aka hada dasu duka aka jefosu awaje. Rasa abundake faruwa Saminu yai inda yake 
tambayar Matarsa dalilinda yasa aka korosu cikin gidansu. Aisha batayi wata wata ta, 
tsanar masa tun farkon abubuwanda sukafaru bayan sumarsa har izuwa yanzu. 
“Innalillahi wa Inna ileihi rajiun takardan gidanmu kika mallaka musu, how dare you’. 
Ya daka mata tsawa “Wallahi sai kin biyani Sha Sha sha, mutuniyar banza kawai. ‘ 
Janyota yai tamkar Ragon layya, Ya fisgo akwatunan nasu, Da ma dei yayi sa’a Keyn Motarsa tana hannunsa nan take ya jefa akwatunan abayan mota, ita koh agaba ya daure kafafunta. ‘Karfe daya na dare” abunda agogon motarsa tanuna kenan ayayinda yaja Motar yafara tuki babu alaman sassauci. 
Mahaifiyar zaid a gidan yari, Inna lillahk wa Inna ileihi rajiun ‘tunaninda Ma’inah ta kwana yi kenan. Zuwarta gidan Zaid alokacinda ya rungumeta ne taji yanacewa Ma’inah please save my family Mahaifiyata ta fito daga gidan Yari she will destroy our Family please help us. Yana fadan wannan kuwa ba’a barsa ya’kara wata maganaba nan da nan Asad yakira bodyguard dinsa suka tafi dashi daki domin yasamu hutu, Tareda Anisa wacce tafi”: kowa zagewa dakuma nuna damuwarta akansa, ko wacece ita? 
Akan sallaya take tun wayewar gari har izuwa yanzu tana tunani iri iri, awannan karon kwakwarta ta rude rasa mafita tai, so take ta zamanto tsanadiyar farin cikin Zaid takuma yaye duk wannan matsalolin dake faruwa a wannan Zuri’ar tasu Amma ta’kasa gane hanyarda zatabi tai hakan. 
Ma’inah please excuse me, Zanyi waya and it’s Private;. Anisa tashige dakin tamkar daga sama, wannan maganar datai ne tafitarda Ma’inah cikin duniyar tunanin datashige. Mamaki sosai ta bayyana a fuskarta ayayinda ta’kara tambayarta abunda tafada ko kunnuwarta ne sukaji ba dedei ba. Ba tsoro a idanuwarta ta’kara maimaita mata “Cewa nayi kibani waje zanyi magana awaya. Murmusawa Ma’inah tai tanacewa “Dakin kifa? Ko Parlour duk bakiga daman yin privacy achan ba sai Nan. Bata ‘karasa kalaman nataba Anisa tadakatar da ita “Excuse me please this is my Uncles house Kuma ko ina Zan iya yin privacy how dare you to interfere, me alakarki dasu, Rashin gurin zama ce takawoki nan ko dei kina tsammanin bamu sani bane, an gaji da dirkan koko da kosai an dawo nan cin kaji da ruwan roba. 
Zuba mata Ido Ma’inah tai har Sanda tagama jero maganganun nata sannan tasanya hijabinta tare dacewa “Allah yabaki hakuri. Babu abinda ta’kara fadi tasowa tai tana kokarin fitowa tabata waje Anisa tace’ Daman azauna man in ba’aji kunya ba, Mahaifi yaga maiko yace bari yadawo da Yarsa. “Me kikace? Nan da nan Ma’inah ta waiwayo “Anisa duk takamar dakike kada kisake kisa sunan mahaifina sabida wallahi cire kunyan zanyi in koyamiki hankali. 
lyeeee, zoki koyamin hankalin man, meyesa kika tsaya achan baya, ai kuwa wallahi da yau Zaid ya koroki cikin gidan nan kuma ya kori banza. Anisa tafada cikin nunfashi d’aya. 
Dawowa cikin dakin Ma’inah tai babu tsoro ko fargaba tazauna kan kujera tanacewa “Nama fasa babu inda za’ni sabida Naga salon naki akwai rainin hankali. ‘ 
Anisa bata ‘kara wata ‘kalma ba,fitowa tai ko minti guda bata bata ba suka dawo tareda mahaifiyarta Aunty Nasibah. Kana ganin Matan zakasan akwai kudi kuma Hajiya ce Kalar manyan Mata. Tare suka taho da Anisa da masifarta tashige tanacewa “Ma‘inah kekuma wato da salon rashin mutunci kikazo mana gidan kenan, tunda dei kinzabi zama anan gidan yazama dole kibi dokokinmu, Anisa dakike gani Yar gata ce abunda taga dama takeyi agida sabida haka yazama dole kibi dukkannin ka’idodin data gandayo miki sabida nan gidan tamkar gidan Mahaiflnta ne…. 
Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Ma’inah, Uffan bata tan’ka musuba haka tajuye babu abunda tafada yayinda tafara tafiya Anisa tace’ Momy you have to warn her bansan ta’kara mamaita irin wannan kuskuren datai, tama rainamin wayo she must apologize. Ta murguda baki ta’kara turo keya tana bin Ma’inah da Kallo. Bata juyoba cigaba da tafiyarta tai har Sanda Aunty Nasibah ta daka mata tsawa “Bakiji abunda take fadi bane come on juya kibata hakuri. 
“Wakuma za’a baiwa hakuri?” Aunty Rahila ce ta katse maganarta’su inda ta’karaso har cikin dakin tanacewa; Mai’natu me kuka zauna yi tun tuni ke da Anisa baku fito munyi breakfast ba? Tana hango Aunty Nasibah tai murmushi “Hajjaju kema nan kika boye kuka barni a falo ni kadei, Ma’inata ta rirnke ku tana muku hIran Bola koh. Tafada cikin zolaya. “Hajiya Rahila yar nan taki batada tarbiya kwata kwata gwara kija mata kunne Anisa tafl karfinta wallahi. Da wannan maganar ta janyo diyar ta suka bar wajen. 
Jikin Aunty Rahila ce tai sanyi sabida daman ta’san hakan zata iya faruwa, Aunty Nasibah tanada ta’ kama dakuma nuna Isa dashike tanaji ita ‘kanwar Mai gidan neh. 
“Mainah kar kiji komai kinji, haka suke. Aunty Rahila ta matso har kusa da ita tana share mata hawaye “ke Yata ce mainah kuma ba‘zan taba bin bayan wani yaci zarafinki ba, I love you so much my dear. Murmushin ‘karfin Hali Ma’inah tai sannan tarike hannayenta tanacewa “Na’gode Aunty Rahila. 
“Mainah ko Zaki iya kirana Mamy kamar yedda Zaid yake kirata? Gyada kai tai “Uhum me zai hana Mamy” Tafada kai tseye. Rungumeta Aunty Rahila tai tana tsananin farin ciki. Ta rasa gane dalilinda yasa san Ma’inah ta shige zuciyarta sosai tun ranarda tafara sanya ta cikin idanuwarta. 
Tasowa Ma’inah tai tana dada murmushi “Mamy na’gode. tseyawa tai shiru tana bin Mamin nata da kallo yayinda tatuno mahaifiyar ta wacce kwata kwata Bata taba nuna mata wata soyayya ko shakuwa irin wacce uwa da ya suke sharing ba, shiyasa ako yaushe san Ummanta Mahaifiyar miemah ke dada Karuwa a ranta sosai sabida itace tafara nunamata soyayya da Kulawa. 
Aunty Rahila kuwa duk wannan tunanin da Ma’inah takeyi shiruu ta zauna take binta da kallo tana murmushi. 
Me zamuyi cikin wannan dajin? Aisha tafara bibbige kofa tanacewa Saminu wannan wace irin tafiya ce wacce bata karewa tunda daddare muke wannan tafiyar se daji muketa pasowa ina zaka kaimu? Saminu bai tanka mataba har Sanda suka kai wata kodaddiyar gidan Bukka wacce babu komai cikinta sei tsunsaye da bishiyoyi. 
Yanzu kana nuFIn cikin wannan gidan zamu cigaba da zama? Aisha tadubi gidan sama da kasa tace‘ wallahi ba’zan iya zama anan ba, yazama dole mu koma Abuja domin mu tsanarwa Mahaifin Maisha duk abubuwnda suke faruwa sabida ya‘kamata sufara nunamata hankali, yarinyar ta baci ba tarbiya ko kadan tattare da ita ….. Se yanzu Saminu ya soma bakinsa cikin maganar “anan zamu cigaba da zama sabida ba’zan taba bari ki tona wa Maisha asiriba, Kuma na yafemiki batun gidan chan sabida Ma’isha aka mallakawa babu matsala sedei sharadi gudace nake da ita, ba’zan taba barinki kitona mata Asiri ba sabida haka anan kauyen Zaki cigaba da zama, zuwanki Abuja ta’kare, kuma alakarki da Sambo ko Matarsa ko yayansa duk sun kare anan. 
Baka Isa ba Wallahi, Maisha ta Aiko mutanenta gidanmu su anso mata kudadenta kosu kashemu, idan fa bamu basu komaiba kashemu zasuyi, Taya zakace nai shiru wallahi, Wallahi, Wallahi sena tsanarwa Mahaifinta idan Kuma ka hanani Ma’ka ta a kotu zanyi, sabida ba’nida laifi hakama yata Miemah itama batada laifi cikin wannan maganartaku, tsakanin ku kukayi abarku, Kuma gashi muna fuskantar irin wannan hukuncin taya yarmu zatayi rayuwa anan gidan? Kaduba fa kauye ce anan zatayi aiki kake nufi bayan kammala karatun datayi. 
Da wannan maganar Aisha tajuye batama ‘karaso cikin gidanba taja Jakarta tana tafiya. 
Tasowa Saminu yai yashige gabanta, cikin mamaki yace Ina zaki? Babu tsoro ta amsa masa cewa “Abuja zani idan Kuma ka hanani Kotu Zan wuce sabida Future Yata nake dubawa Miemah bazata zauna anan gidan ba, yazama dole mufadawa Maihaifin Maisha domin ya dauki mataki. 
Daka Mata tsawa Saminu yai “Nace kidawo, idan kinfadawa Mahaifinta wannan maganar zaisa ya tsaneta, yadena bata kudi kuma yai mata kulle cikin gida. Kuma dakike maganan bakyasan rayuwaryarki ta lalace, ita Maisha so kike rayuwarta ta lalace bayan kinada tabbacin cewa idan kin fadawa mahaifinta zai dena kula da ita… 
Se Yaya?, Aisha ta dakatar dashi; ba Yarsa bace inyaso yadena ce mata sannu bata shafemuba mu dei Farin cikin Yarmu muke bu’kata. Tasowa Saminu yai cikin sananin bacin rai yajanyota, tana ja Yanaja har Sanda yakaita wata daki ya rufe kofar da kwadau, ransa ne yamatukar baci yayinda yakecewa’ Anan zaki cigaba da zama har zuwa lokacinda kika chanza ra’ayi. Sabida babu yedda za’ayi kije Abuja kibatawa yarinya suna a idon Mahaiflnta, Wallahi kinyi kadan Aisha, kuma bazai taba yiwuwaba sabida kamaryedda Maisha take Yar Sambo haka nima take Ya awaje na. 
Muryar Aisha kakeji cikin daki tana bibbige kofa tana kuka tareda cewa” Saminu katuna ni matarka ce kuma inada hakki akanka, Allah Zaiyi fushi dakai idan ka cigaba da kulleni cikin daki tamkar dabba. 
“Aw dama kinsan da haka shiyasa kike kin bin umarnin mijinki” Saminu ya maida mata da martani “Allah yace ku Mata kubi mijinku sau da kafa idan kunasan Aljannah wannan duk bakisani ba toh wani wa’azi zakimin, anan Zaki cigaba dazama har zuwa lokacinda kika chanza ra’ayi, abinci ma dakaina zan girka inringa turomiki ta window sabida Ina Sanki ke matata ce bansan kikamu da Ciwon Ulcer. 
“Allah wadaran miji irinka wallahi” Na tsaneka. Aisha tafada cikin sananin hawaye. 
Kyaleta Saminu yai, tacigaba da magana ita kadei tamkar mahaukaciya, yayinda yad’auki sinsiya ya shashare dakinsa sannan yaja akwatunan nasu daya bayan daya yakai daki yajerosu. Yana kammalawa yakoma kan gado yami’ke Shiru yashiga tunani, “Aisha tayi gaskiya, harga Allah shi kansa baison Yarsu (Miemah) tadawo nan kauyen tacigaba da rayuwa bayan duk kudaden dasuka kashe akan karatunta ba daga nursery School har zuwa University yazama dole yanemo mafita kamar yedda yazama dole yasa Ido kan Matarsa kada tai kuskuren tonawa Maisha asiri, ahaka kuma zasu cigaba dazama cikin wannan kauyen har zuwa karshen rayuwarsu, shi dei yanzu yaga’ne cewa Allah Bai nufl zaiyi arziki ba shiyasa yasadaukar da dukkan abunda yaragemasa ga Maisha, tunda dei kasuwancin ma dayakeyi makiya sun hana, kuskure guda yai aka Ma’ka shi a kotu inda suka amshi dukkannin abubuwanda yatara. ‘ 
Ako yaushe idan yaduba abubuwanda suke faruwa da rayuwarsa, yakanji tamkar ya’fl kowa rashin sa’a a duniya Daman yawancin Tagwaye haka suke, ‘Daya zai fito successful komansa gaba gaba take zuwa daya kuma zai fito da rashin sa’a irinsa kenan. Da na’sani guda yakeyi arayuwarsa itace fitowa dasukayi yan biyu, Sambo shine babban matsalar rayuwarsa. 
Garin babu rana, dashi_dashi kake gani tamkar hadari sedei tunda safe yanayin bata chanzaba har izuwa yanzu, akwai hadari amma babu alaman ruwa, se wani iska mai tsananin sanyi dake busa tanasa garin sanyi. 
Daddy tun dasafe yafita aiki, Momy da Ma’isha suma duk sun fita babu kowa agidan Miemah ce kadei aka bari tana shiga da fita, shiru gidan babu dad’i. Bayan ta kammala aikace aikacenta, dakanta tai girkin abunda zata ci dashike Ma’isha tahana abata abinci idan an girka musu na gida, ahaka take hakuri tana girka abincinta daban. Har ga Allah ta gaji da zama a gidan nasu ba’tajin dad’in zama dasu ko kad’an, sabida Aunty Safeenah da Ma’isha duk ba son zamanta agidan suke ba shiyasa takeson Kawu yai sauri ya sallameta takoma gidansu domin ta san Umma na kewarta sosai. Gwara ma idon Mainah tana gidan, jiya Kawu yafad’a mata cewa Ma’inah takoma gidan Mai gidansa, alokacin taso ta tambayeshi a ina gidan yake amma kawai tai shiru. 
Wannan tunanin takeyi tun tuni, gidan shiru kakeji tamkar makabarta ko TV bata kunnaba bare Aunty Safeenah tadawo tasauke haushinta duk akanta, ahaka tazauna abunta tana daddana wayarta. Tamkar a mafarki taji muryan Ma’inah tun awaje tana “Teddy oyoyo,  oyoyol Dasauri Miemah tamike aiko tanajuyowa tahango Mainah tun awaje tana gudu, Cikin Farin ciki Miemah ta’karaso wajenta. Nan da nan suka rungumejuna suna farin ciki 
gaba daya. ‘ 
Mainah gwai gwai wa yafada miki Ina nan? Miemah tafad’a cikin zolaya. Se dariya Ma’inah keyi tana washe kakora, harma ta’kasa cewa komai. Daddy ne yai sallama yashigo falon ya tsamesu sannan Ma’inah tai wajensa tanacewa” Ga wanda yafadamin nan, har wajen aikin mu yaje yafad’amin cewa Miemie tana gida, sannan muka taho tare. Ganin Daddy yasa Miemah tai sanyi, babu abunda tafada shiru tai tana bin Y’ar Uwar nata da kallo Yayinda ita Mainah ko ajikinta se kaudi take, tana zumudi tamkar yarinya ‘karama. Daddy yana tseye achan baya, yana mammatse idanu, shi Daddy dei kamaryedda kuka sani son kuka gareshi yanzun ma ‘kasa rike hawayen nasa yai kai tseye suke zuba yayinda yake kuma murmushi duk alokaci daya. “Daddy Come on, Kadena kuka manaaaa. Mainah 
Kai tseye ya share hawayensa. Wannan shugwaba shi da Ma’inah keyi yasa yake dada kewarta ako da yaushe idan basa tare, she is one in a million koman Bacin ranka ta’san hanya mafi sauki wanda zatabi ta kwantar maka dahankali cikin mintuna ‘kalilan. 
Ma’inah, tun tana baya baya da Daddy har saida Daddy ya janyota a jikinsa and she finally feels comfortable around him. Sunyi nishadi sosai, sunyi wasa tare, ya kaisu wurare daban daban. 
Da la’asar suka koma gida inda ya sanar mata cewa da yardan Allah gobe zata koma Maiduguri, Sam Ma’inah bataji dadin hakanba, ita in ason samun tanema tafiso tadawo Abuja sucigaba da zama tare sedei hakanne bazata taba yiwuwaba. Sun sallami juna in a very emotional farewell. Jiki a sanyaye Daddy yahadata da Dreba aka maidata Zabirs Mansion. 
Tun tuni nunowa take ana jefowa a kwando. Kaya, Takalma,jaka komai dei tatseyo iya son ranta babu dei irin Kalar kayanda bata zasoba iri iri daga masu kyau har munana. Mommy ko se ‘kara karfafa Mata guiwa take tana dada kwasan ababe. 
Bayan Momy da Maisha sun kammala seyayyarsu cikin kwanciyar hankali ‘karfe shida da rabi ana ‘kiran sallah suka wuce makusanciyar restaurant anan sukayi Sallah, Ka’na aka had’o musu “Sea Food” Ma’isha’s Favourite dish. Cinyewa sukayi Tas!!! sannan Momy taja‘su a mota suka koma gida tun kam su iso Maisha tai barci cikin mota. 
What? Taya hakan yafaru. Daddy ya’kara murya yanacewa: Alhaji Muktar kanajina kuwa yazama dole inyi Urgent flight yanzun nan zanbiyo Private air nataho. Shiru yai nadan wasu mintuna sannan yace” No problem sir, wannan duk ajiyeshi a gefe I most protect my company domin ita kadei taragemin. Da wannan ya katse wayan inda yafara zufa nan take yashiga damuwa “No way wannan bazata taba faruwa ba. Babbar rigarsa yasaka yana sa kafa zai fito kenan wayarsa tafara ‘kara kuma yanadubawa yaga sunan dan uwansa “Saminu cikin wannan lokacin? Agogo yaduba yaga karfe “Tara na dare’ cikin sanyin murya yadaga wayar, Saminu bai tsaya yayi maganaba, Kuka yafarayi yanacewa “Sambo an koreni daga aiki kuma yau muka kammala shari’ar mu a kotu, Kayan dana mallaka duk sun karbe daga shagunana har zuwa kudadena wanda suke banki. Abu daya nake bukata daga gareka Sambo amanar Miemah Zan danka maka don Allah ka samo mata aiki a Abuja tacigaba da zama tareda iyalanka banida kudi Kuma ayanzu ba’nida hanyar kudi how will I provide all her need please Sambo kafada mata komai yadda zata gane she is brave na’san zata fahimceka. Idan kayimin wannan ka gama min komai kar’ka damu dani, I will take care of my self. Yanzu na bar gidan chan nakoma wata gida daban, sabida ko kaje bazaka samemuba. Na barka laflya. 
Wannan dogon turancin duk cikin nunfashi daya yayita yana kammalawa kuwa bai tsaya yaji abunda Dan uwan nasa zai fad’a ba, katse wayar yai alokacin. “Subhanallahi” abunda Daddy yafada kenan “Saminu Lafiyarsa kuwa mutum sekace yaro Yana girma amma kwata kwata baisan hakaba, Ni yanzu wallahi na gaji da dabi’un Saminu, Kai ba yaroba, bakasan yadda ake kasuwanci ba kashigeta gashi ka sace kudin lnternational company sun kaika kotu ta kwaso dukkan abubuwnda ka mallaka ya kakeso inyi? Ran Daddy dada baci tai bayan jin wannan Doguwar bayanan da dan uwansa yajero masa. Sedel karfin zuciya yai ya ijiye maganar a gefe yafara tattara kayansa yanasawa a jaka. Sallamar Momy ce ta tsorata shi ya amsa a firgice. “Honey lafiya kake tattara Kaya? Ina zakaje? Safeena takura masa ido cikin rudani. Rufe zip din jakar yai yaje wajenta kal tsaye ya rungumeta yanacewa” 
America Zan koma yau. “America? Safeena ta‘kara rungumarsa tana tambayarsa “Lafiya 
dei? “Ka’yan Confani na aka kama yazama dole intafl yanzun nan domin musan 
hanyar da zamubi asakarmana su. Kuka momy tashigayi “Amma ‘kasan ba‘najin dadin zaman gidan nan idan bakanan koh. Shiru  Daddy yazauna yanabinta da kallo “Zamu iya tafiya tare idan babu wata harka agabanki se muhada yara da Nanis. 
Munada wata muhimmiyar meeting gobe awajen aiki Kuma yazama dole na halarci taron” Momy ta amsa cikin sanyin jiki. Alright fine ba’zan dade achan sosaiba Zan dawo gida Karki damu sedei amanar Miemah zan danka ahannunki kidubi girman Allah ki kula’min da ita har zuwa lokacinda zan dawo, ‘Da nakowa ne Safeenah idan kina wulakanta dan wani wataran danki za’a wulakanta ….. Katseshi tai tana tambayarsa cewa Mieman dawowa tai ne ina gobe zata koma Maiduguri? 
Anan Daddy ya kwaso dukkannin maganganun da Sukayi da Saminu yafada mata, ranta ta’yi mugun baci sabida abunda tafi tsana a duniya shine rikon dan wani Kawai basarwa tai bata nuna masa afili ba. “Dan Allah kiyi kokari, ki sanar da ita dukkannin wannan abubuwnda Mahaifinta yafada sedei ki tabbata cikin Kwanciyar hankali zaki tsanar mata, kada kitasar mata da hankali Kuma kifadamata cewa idan Allah ya yarda zan yiwa Zaid magana awaya ya dauketa a confaninsa tafara aiki taredasu Ma‘inah na’san zataji dadi sosai. 
Tabe baki momy tai “bakomai zataji Insha Allahu …… 
A daren Daddy yaje wajen aikinsu Ma’inah sukayi sallama dajuna sabida zai koma America yacigaba da kasuwancin sa, Bai dade awajenba yadawo gida duk dacewa Ma’inah ta dan bata masa lokaci da koke koke domin zatayi kewarsa sosai. Amma dashike cikin daren zai tafl nan da nan ya sallameta. 
Maisha Tasha Kwalliya tareda mahaifiyarta sun fito pes!! Gwanin ban sha’awa suka fito falo inda akwatunan kayansa suke wajen. ‘Daya bayan daya masu aiki suka kai kayan mota sannan Daddy yafito daga baya. Yanafita yaje dakin Miemah yace itama ta taso sutafl airport tare kada abarta agida ita kadei. Babu musu ta sanya hijabinta suka fito tare. Momy da Yarta duk kallon Mara hankali sukemata, suna fita wajen motoci suka shige, dukkaninsu akujerun baya suka zauna yayinda dreba yake tuki a gaba. Momy tana manne da mijinta tana hawaye ganin zatayi kewarsa sosai idan ya tafi hakama Maisha Jugumm take zaune cikin Motar har tseida suka karaso Airport. 
Aikin kuka Momy takeyi har Sanda jirginsu ta fire sannan suka kama hanyan gida. Ma’isha tana nan tana Bata hakuri har suka ‘karaso gida inda duk suka fito babu dadi jiki a sanyaye. Karfe Goma Sha d’aya alokacin kowa yayi barci. Maisha ce tabude kofan falon Mummy tashiga itama tashige sannan taja kofa zata rufe kenan Miemah tasa hannu tanacewa “Me kike korinyi bakya gani ne? Babu abunda Maisha tafada Jan kofar tai tarufe Miemah na tseye awaje. 
Momy koh, kojuyawa batayiba haka tamike Kai tsaye tatafi dakinta. Ita Maisha bata 
joyoba ta kulle kofan tai dakinta. 
Anan bakin kofa Miemah ta kwanta tana hawaye ga sanyi gakuma babu komal akasan daga tiles se tiles, sanyin iska na busa ta ko ta ina. Ga hadari, saman na walkiya, kam kace Kobo ruwan sama aka fara mai tsananin iska da thunder 


Hmm

About Ismail

Check Also

TAGWAYE CHAPTER 35

TAGWAYE CHAPTER 35 Tukin awa guda ce takai Miemah gida, afusace taflto cikin gaggawa tanemi …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *