[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA COMPLETE - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA 


CHAPTER 39

Yana karasowa ya zuba mata  mari a gefen kuncinta na hagu. Wanda saida taga stars a idanuwanta. Dafe kunci tai ta shiga kallonsa da mamaki kobi ta kanta bai ba ya amshi najwa dake hannun laila tana kuka. “Sorry cutie.” Ya fada yana kallon gefen goshinta daya dan tashi, ya shiga mulmula mata. Abin tausayi yarinyar sai kuka take haka ya dada fusata ramadan.Sai ya mikawa laila ita, tana karbarta tayi daki da ita, domin bata da sauran kalubale da safna, domin ta sha mari daga hannun masoyin nata. 
“Yanzu ni ka mara akan nayi abinda ban sani ba. Dana sani ta yaya ‘yar babyn nan zan mata haka.” 
“Shut up,na mareki safna, tunda naga ke kin fara wuce gona da iri, dan rashin tausayi yarinyar kamar yar mage zaki wullata ta bugu da kujera kice kuma baki sani ba, yanzu data karye fa?.” 
Saita rufe mitsi-mitsin idanuwanta ta bude su akansa tace. “Lalle na shaida namiji sai shi. “Duk abinda za kice safna sai dai kice, zan miki last warning akan ganganci da yarana zan iya sabar miki akansu. Gudanjini nace dan haka karki kara gargarin kara irin haka wallahi dan zanyi mummunan saba miki.” 
Kallon mamaki ta kuma yi mai, sai ta sanya kukan borin kunya ta koma da baya da sauri ta shiga wajenta tana kukan borin kunya. 
Ladifa dake gefen dining ta ce “Allah ya kyauta ta shiga kitchen dan yin shara da wanke wanke. 
Jin yanda har lokacin najwa na kuka ya sanya ya taka shashen laila. Ya karbeta suka fito Yayi waje da ita dan tai shiru. 
Share hawayenta tai ta danno kiran mamanta. Tana d’auka ta fasa kuka. Uwarta bugu kirji tace “mugunji da mugun gani Allah ya kare, meye sanadin kukanki safna.” 
Nan ta gaya mata. Uwar tai tsaki. “Share hawayenki, daman namiji akan yaransa baya daga kafa, wani komai son da yake miki kika taba ‘yarsa ko dansa sai ya nuna miki bacin ransa. Ko nan gaba ki kula. Kuma ki bar kuka zan share miki hawaye.” 
Sai ta share tace “babu tamkarki duk duniya mamana.” Uwar tai murmushi Ta kashe. 
Tun daga wannan ranar ta daina kiran ramadan a waya da dare in yana wani dakin, hakan ya sanya suka samu salama. 

BAYAN WASU MAKWANNI 
Laila ta fara rashin lafiya inda sosai ko abinci bata iya sanyawa acikinta, da taci za ta amayo shi, hakan ya sanya suka je asibiti, gwajin farko aka tabbatar da shigar ciki ajikinta. Sunyi murna bakadan ba. 
Suka dawo gida, cikin yazo mata da laulayi ba kamar na cikin najwa ba, ta hakan ya sanya ma bata da lokacin sauraron safna har suyi fada dan ta kanta take.Sai wataran lad’ifa ke taimaka mata da girki. Dan wataran kasawa take. Duk da wannan fama da laulayin da take, indai safna na wurin haka, za tai ta iyayi ita fa tayi ciki. Da gangan saita bari ramadan na bangaren safna sai ta tafi tana dan yatsina ta ce 
abu kaza da kaza take so ya taimaka ya samo mata. Wanda safna ji take kamar ta maketa. 
Duk yanda safna takai da kwakwa da hanashi amma hakan zai tashi, dan wataran laila har kuka take sanyawa kan in bai sayo wani abu ba.Duk dan safna taji haushi. 
Yau da safe laila ta tashi sam! Ba tajin sha’awar komai sai kosan da ake sayarwa. Karfe shida da rabi taje dakin ramadan ta shiga kwankwasawa safna tai juyi ta kalli ramadan, sai ta tashi ta taje ta bude. Ta dishi dishin idonta ta ga lailace sai ta dada matse kofar ta tabe baki tace “meye?.” 
Laila tai mata wani shagi dadden kallo tace “mijina nake san gani. Yakamata ki barshi haka nan ya fito.” 
“Bai da lokacinki kin gane. ki bari idan ya tashi, ya sauko, saiku gamu, haba danjaraba karfe shida da rabi kin wani zo san ganin miji.” Iya wuya laila ta shaka. Za tai magana taji yayi magana.“ 
Alokacin ya taso yazo ya sakalo hannunsa ya rike kugun safna yadan dora kansa kan kafadarda yace “sugar me kike ne atsaye?.“ Sam! Bai lura da laila ba. Wani lumshe ido tai tace “ga wadda ke nemanka.” 
Da sauri ya daga kai ya kalli laila, sai ya saki safna ya bud’e kofar duka ya fito yace “laila ya dai?.” 
Laila kamarta fashe ta harareshi ta ce “kosai nake so na bakin titi, nasan an kusa farawa. Ka sayo min dan Allah kasan masu ciki sai a hankali.” 
Murmushi yayi yace “babu damuwa.” tajuya ta tafi. 
Safna ta tabe baki azuciyarta ta ce ‘yar renin sense, ba sai na bashi dama ba.” Komawa yayi dan ya sanya riga yaje ya sayo mata. Safna ta dauke hankalinsa tace “ka tsaya ka watsa ruwa,” wanda bashi ya fito ba harsai wajen tara. 
Yana fitowa yaga laila a zaune a falo tana huci, ta kalleshi ta ce “yanzu habiby shine ka manta da ni? idan na jigata fa.” Ta fad’a muryarta na rawa. 
Zama yayi gefenta ya ce “sorry dear yanzu zan sayo miki.” Ta ce “ba naci kawai,”ta tashi ta bar wajen. 
Sai yayi murmushi al’amarin mata akwai rikitarawa. 
Yau safna ke shirin zuwa gidansu wanda kafin ta tafi sai da ta dibi shinkafa wajen kwano biyar da su macaroni. Alokacin ramadan baya nan hakan ya bata damar kwasa yanda ranta keso. 
Suna tsayuwa a k’ofar gidansu, ta shiga gidan, ta fesa kwalliya tana tafiya taku daidai, tana shiga gidan ido yarrrr! akanta, sai ta sakar musu murmushi sannunku ‘yan uwa.” 
Kowa tsadaddiyar shigarta yake wa kallo da kwalliyarta, sai girgiza kai suke. Wasu na bakin-ciki wasu na yabawa. Wanda haka al’adar gidan take. Duk iyayen sun d’ora yaransu kan turba mara kyau wajen nuna kyashi da hassada ga ‘yan uwansu wanda ba dakinsu daya ba, tun suna kanana wanda har suka girma suna kan tsarin. Babansu ya rasa yanda zai yi domin matan sunfl karfinsa. Saboda bashi da kudi dalilin daya dada sawa ma matan basa jin maganarsa kenan
Mamace ta fito daga d’aki tana cewa “Ga yar albarka irin albarka, mafi farinjini acikin tsaranta.” 
Murmushi tai tace “sai mamana.” Ta shiga ciki matan gidan suka tabe baki “ayi dai mu gani.” 
Nasiru kaninta ne ya shigo da manya manyan ledoji, mama ta saki guda tace “irin albarka haka nake san gani.” 
Duk kayan da ta debo ne na abinci harda danyar kaza data dauko a fridge su maggi da leman pepsi katan daya 
Mama tace “Allah yayi albarka,” safna tace “ba yawa mama. Kinsan Iamarin sai da dabara. 
Na store nawa na debo. Dan ba zan zauna ni ina cin mai dadi ba mama ke kuma kekina cin ta fashi kada.” 
Nasir da ke tsaye agefe da kwai nutsiwa da hankali a tattare da shi yace “amma yaya fa babu kyau mace ta debi kayan miji in bai sani ba tai kyauta da shi harsai ta tambaye shi.” 
Dakuwa uwar tai mai tace “ka ci gidanku fita ka bamu waje. Iyayi sai kace ba dashi za a ci ba.” 
Ta kalli safna tace “alhamdlh yan bakin-ciki sai dai su mutu,” ta tashi ta samo bakakaken ladoji ta saka lemo daya da doguwar taliya biyu, biyu da macaroni daya. 
Ta kirawo wata kanwar safna ta ce ta mikawa kishiyoyinta ta ce musu abin arzikin da safna ta kawo ne, duk d’akin da ta mika a tabe suke karba, ana kus-kus nan da nan habaici ya fara motsawa. 
“Kafin dai wasu suyi, mu muka fara.” Har maman safna ta mike safna ta riketa tace “kai mama ai yanzu kinfi karfin haka, bakin-ciki ke cunsu.” 
Ta kuma dauko dubu goma ta bawa maman wanda ta farauto, “mama ga kud’in da kika bukata, dan Allah ki dan sarara sai kwana biyu sabida kada a ga lagona.” 
Dariya maman ta sanya “kina kokari ma ai.” Nan ta zauna ta dada kisawa ‘yartata abubuwa da masu kyau da marasa kyau, tare da bata wani kunshin magani ta ce “naje gidan malamjiya, wallahi yayi aiki sosai akan mijinki, wannan wani lakani ne bita makale mata, shansa za kiyi, na musamman ne wanda malam yayi aiki akai, wanda in kika sha sai mijinki yaji ke kadaice mace a gareshi.” Safna ta washe baki kai “mamana ashe! karbar kudin ba abanza kike ba, tanadi kike min,
“Yo idan ban gyara aurenki ba wa zai yi ? kina dai ganin yanda mutanen gidan nan ke mana kallon hadarin kaji musamman maman murja. Ke dai rike abinda na gaya miki kuma ki tabbatar kinyi amfani da duk abinda na baki atoh. Yawwa na manta ga wani ma ta dauko wani dan leda. 
” Wannan maganin hayaki za ki da shi, ki tabbatar megidan ya shaka, koda ma wani ya shak’a ba zai mai amfani ba,sai wanda akayi dan shi. Sai kin zamo mowa agurinshi, matan nasa kuwa sai dai ya kallesu kawai. Ke ko keb’ewa ba zai iya dasu ba. Sai dai kallo.” 
Ta kuma dauko wani leda babba wannan kuma maganin sanyin da kike nema ne, sai yau Allah ya sanya aka kawo, insha Allahu duk sanyi da kike fama da shi zai gushe, nan insha Allahu za kiji dadinsa.” 
“Kai mamana, na gode, ta fad‘a tare da rungume uwar sai wajen shidda ta tafI. 
Tun da safna taje gida ta shiga amfani da maganin sanyin nan, wajen sati d’aya tana shansa, sai gashi taji canji dan har sha’awarta ce ta ji ta karu sosai! Wanda da matsalar sanyin ce ta sanya yawan sha’awarta yayi baya.” 
A gefe ga kuma maganin da malam ya bata tai amfani da su dukkansu. Kamar almara komai ya fara canjawa domin ramadan ya wani makalewa safna, sai abinda ta ce kamar wani tsoronta ya dawo yanaji, gashi koda kwanan laila da ladifa ya zagayo baya nemansu a shimfida, kosu suka neme shi yakan zame yaji bai son yi, ko ya tsiri bacci.” 
Duk wani tarin sha’awarsa ya koma kacokam! kan safna. Wanda duk al‘amarin na tafiya ne da asirin da sukai na haka. 
Hakan ya sanya ta samu waje. Domin dama tana dan fama da sanyi maganin sanyin kuwa da ta sha ya karbeta domin kamar wata jaraba ya kara mata. Nan suka dinke da ramadan 
kullum abu daya, dare, asuba, dan har rana idan weekend ne beje aiki ba, tun yanajin nishad’in hakan, har abin yaso ya fara damun ramadan, ya fara kosawa. 
Wataran idan yana tunani ya kance “kenan daman duk jarabarsa safna ta dokeshi, dan inta sanya shi a daki yakan gane kurensa. Kullum babu daga kafa, su ladifa sai ido dan ramadan ya wani canja kullum cikin tamke fuska ga hade rai, musamman idan yayi tozali 
dasu ita da laila, sai dai kajiyo dariyarsa a wajen safna. 
Al‘amarin daya damu laila matuka, ga laulayi da take fama da shi, ga ba kulawar miji, duk ta rame, dan ma tun samun cikinta an kai najwa gun mamanta, hakan ya saukaka mata wani abubuwa. Sai dai kullum korafin ramadan ya canja mata, baya kaza ba ya kaza. Sai ya hau mata fada ta dame shi.Dame zai ji. 
Ladifa kuwa damo sarkin hakuri, idan ta tanka ya hau, sai ta yi kasa ta sanya ido ta fawwalawa Allah. A kullum safna na godewa mamanta mai hangen nesa, wajen taimaka mata na samun farinciki, dan yanzu juya ramadan take son ranta kamar waina, wallet dinsa kuwa har ta san kalar hannun safna, dan ko suna zaune za ta ce zan dau kudi, zan amfani da shi, ba zai ce kala ba sai dai yace “to dear.”
Duk da cewa akasan ransa ya fara gajiya da wasu lamuran na safnar amma babu yanda zai, na farko idan aka ce dare yayi ba hutu, indai ita ce da girki hakan za ai ta abu daya, da asuba ma ya maimaita wanda hakan ke sanyawa ba ya samun isassshen bacci gashi yana makara wajen aiki. Gashi akasan ransa yakanso ya kebe da matansa, amma yakanji ba ya so, dan indai yana dakinsu kasa komai yake. 
Tatsarsa safna keyi ta bangaren aljihunsa dajikinsa, tashi daya ya fada ya rame, sai dan wuya, dukjarabarsa ta shafeshi ashe lamfa tayi. Mamanta kuwa yanzu abun nema ya samu dan agidan nan kullum sabin kaya take sanyawa, wanda ‘yar ke dinko mata, sai ta sanya ta 
fito tsakar gida tana waka cikin habaici tana cewa “haihuwa mai rana, Shi’isa masu iya 
magana kan cewa k0 kana gudu haifi ka yar alhamdulllah. Sai dai matan suyi tsaki tsaki su juyar da kai. 
Yau ramadan ya dawo daga wajen aiki, ladifa ce kawai a falon ta kalleshi kallo daya tai mai 
tasan yana da damuwa ba yanda zai yine. Amma taji tausayinsa, muddin ta tuno cewar 
yanzu ga yanda yake musu duk sai taji haushi, dan yanzu takai ta kawo duk weekend yana 
shashin safna idan ya leka shashin laila ko ladifa to yana neman wani abun ne, ita dai 
yanzu sai tace rabonta da hada shimfida da shi ta manta, harta hakura ma, dukda cewa 
tana damuwa bisa hakan tanajin ba dadi sosai. Ta bangaren laila kuwa daman ita ciki yasa sam! abin ma baya gabanta, wanda cikin najwa ma haka yazo mata, sai dai tai korafin rashin kulawa da ita da bayayi. 
Da yake girkinta ne sai ta karbi kayan hannunsa ta ajje tai mai sannu da zuwa ya amsa a dakile. Hawaye ne suka kusan kawo mata ta dauke kai sai tayi sama dan kai hannunsa, shima ya hau yayi wanka ya sauko. 
Laila ceta fito dan lokacin cikinta zai kai wata hudu, ta zauna gefensa tace “habeey.” Ya kalleta da alamar gajiya atattare da shi tace “wai kwana biyu ba ka da lafiya ne?.” Yace “me kika gani?.” “Na ga duk ka rame.” 
“Yanayi ne kawai.” 
Sai ta ce “daman awo nake san zuwa kuma babu mai amota ko kai zaka mika ni.” Tsaki yayi “kina da matsala wallahi, ki rasa yaushe zaki sai yanzu.” 
“Aa gaya maka fa nai gobe da safe zani kar naje ka fita ban sani ba .” 
D’ari biyar ya mika mata yace “ki sha man ya tashi ya bar wajen.” 
Sai ta dafe kai tana jin wani iri aranta. Yanzu ta yaya d’ari niyar zata ishi mota, sai tayi tagumi. Sai taji dama ta bi shawarar ummanta kan ta fara sana’a ko aiki da duk haka ba ta faru ba. Sai ta sha da kudinta. Washegari a motar haya ta tafi asibitin ‘ 
Duk cikinsu babu wacce ta gano cewar da sanya hannun safna cikin tabarbarewar zaman laflyar gidan, saboda iya basaja, ita kanta takan nuna damuwa a wani abun na gidan duk danta bagarar. 
Wani abun mamaki kibarta take narkawa san ranta, dan ta dad’a yin kumatuwa sosai! Ta dad’a cika dam! saboda tana samun abubuwan da take so alokacin da take da muradi. 
Yau yana dakinsa duk da cewa gurkin ladifa ne, amma ba ta maje ba, dan ta san yayi bacci sai tai kwanciya a side dinta. Alokacin safna ta shiga dakin ta tashe shi, ya rintse ido ya bude taci uwar kwallaiya kamar ba dare ba. “Na ji ka shiru yau. ” 
Murmushi yayi ya lumshe ido dan yaga kyanta acikin shigar da ta yi, wallahi bacci nakeji kinsan bana samu sosai yanzu.” 
Murmushi tai tace lefina ne.” Tashi yayi ya shiga toilet sai ta dan kalli dakin ta bude wallet nasa ta zari kudi da yawa ta sunne a kugunta. Wanda sosai take mai dan hali wajen bincikar kayan da ya cire in ya bar kud’i, k0 in taje gyara dakinsa tai ta bincike. 
Yana fitowa ta mike ta ce “bari na tafi sabida ba girki na bane kar matarka ta nuna fushinta akaina. Ta fad’a cikin makirci.” Ta fice tanajuya jiki. Ya bita da ido. 
Ta fice, ba ta dade ba sai ga ladifa dan ta kasa runtsawa al’amuran mijinta ya tsaya aranta. Yana ganin ta sai ya dan canja ya zauna yace “ya dai ladifa?.” 
Jikinta na rawa ganin ya dawo mata ramadan nada. Tace “dan Allah baban fuad me nai maka kake guduna.” 
“Me kuwa kikai min sai ta ce yanzu wata nawa da wani abu ya shiga tsakaninmu” 
Kallonta yayi sosai shi kansa yasan gaskiya ta fada, acan kasan ransa yana jin tausayinsu ita da laila, amma yakan kasa aiwatar da komai ga matan nasa. 
Zama yayi a gefe ta dan rame ya ce “kwana biyun bana jin dad’i wallahi” 
Tunani ta shiga yi kodai basir yake fama da shi. Sai ta kalle shi ta ce “Toka nemi magani mana.” 
Murmushi yayi yace “ba zaki gane ba.” 
Sai kawai ta share ta kwanta, duk da cewa ta kai mak’ura wajen bukatar mijin nata, sai kawai tajuya tana kuka ahankali, haka shima yankwanta yanajin babu dadi aransa. 
“Wai ke safna bakya gajiya ne? wai ni ba dan adam ba ne? ni inji ne da zaki uzzura min? please ki kyale ni bacci zanyi. Kaina kamar ya tsage.” 
Sai taja baya ta hade rai ganin ta yi fushi ya rikice. Babu yanda ya iya ya shiga yi mata abinda take so, haka da asuba ma ya kuma yi, wanda bai samu wani bacci wadatacce ba. A makare ya je wajen aiki, gashi ba wani breakfast take mai inganci ba kullum tea da bread. Kuma ba shi da damarya ce zai je wajen wajen matansa yaci ta dinga bala,i kenan. ‘ Sai yana dakin ladifa ko laila ne kawai yake ci ya koshi. 
Duk wadannan matsalolin sun fara shafar aikinsa. Sai ga ramadan duk ya dada ramewa. Sai gashi har ya tsani girkinta ya zagayo saboda sam! Ya gaji, yana mamaki wataran daman 
duk jarabarsa akwai a mace wacce ta dokeshi sai gashi kuwa. 
Ramadan ne tsaye matan na zaune yana zazzaga balai, “wallahi ku shiga hankalinku na gaji da sace -sacen da ake min, meke faruwa ne wai?.” 
Sai safna ta sanya kuka “yanzu saboda Allah muna matanka kana zarginmu da sata, gaskiya bai dace ba.” 
Saboda tsabar takaici laila da ladifa ba suce komai ba, sai can ladifa tace “Yakamata kai bincike sosai. Saboda ba wannan ne kadai matsalar gidan ba.” 
“To wallahi zan dau mataki wallahi. Yana fita safna ta tashi ta bar wajen. “Laila ta bita da ido 
tace “wallahi na tsani matar can, wallahi muguwa ce, ina zargin ita ke satar ma, dan duk 
sai da tazo komai ya kwabe, kai ni inaga ita ta shiga tsakaninmu da mijinmu, dan wallahi sam! Ayananyin baban fuad dukya canja. Wani lokacin kiga kamar mai tunani.” 
Ladifa tace “babu kyau zargi fa, Allah dai ya kyauta kawai, addu’a itace maganin komai,” ta mike tai samanta tanajin kirjinta na zafl. Itama laila tai nata waje. 

BAYAN SATI BIYU 

Ramadan ne gaban likita na bincikarsa saboda kwana biyu sam! Bayajin dadi ga ciwon kai dake damunsa. 
Bayan gama rubuce rubucen likita ya dago yace “kana samun Isasshen bacci kuwa?.” Ramadan yace “gaskiya kwana biyun nan bana samu sosai.” 
Likita yace Rashin samun wadataccen bacci ma shine ya dada taimakawa wajen dada sawa kanajin bakajin dadin jikinka da ciwon kan, domin rashin hutu yayi maka yawa, ga rashin bacci dan bacci yana da matukar amfani ajikin d’an adam a lokacin dajikin ke bukatarsa, yakamata ka saukakawa kanka abubuwa.” 
Lumshe ido ramadan yayi ya ce “babu damuwa.” 
Nan likita ya rubuta mai magunguna ya tafi. Sai da yayi kwana biyu bai fita ba, bai samu yaje aiki ba saboda maganin da yake sha, yana taimaka mai wajen yin bacci. 
Ladifa na zaune asamanta, hajiyarta da yaya kareema sukai sallama, babu kowa a falon, sai kawai suka zarce sama suka shiga wajen ladifar, tana kwance idonta arufe, kallo daya za kai mata kasan ta rame ta dada haske. 
“Salamu alaikum.” 
Kamar amafarki taji muryarta, sai ta tashi da sauri tana ganin hajiya ce da yaya karima sai ta saka kuka ta shigejikin hajiya tace “sai yau.” 
Hajiya tai dariya “to meye na wani kuka baga ni ba.” Ta kalli yaya karima tace “ni nayi fushi ma.” Yaya karima tai dariya ta ce “hmm! da dai da yanzu ba daya ba da mutum zai na zuba shagwaba. Yanzu da fuad.” 
hajiya tace “kyalemin autana ita kadai ce autana koda kuwa za ta haifi yara goma. Nima kewarta ne ya dameni.” 
Murmushi tai tanajin dadin ganinsu. Suka zauna ta tashi jiki na rawa, ta fita ta rasa mai zatai. 
“Ina zuwa?.” Ta fita da sauri hajiya tace “auta kenan.” 
Kasa ta sauka ta shiga kitchen dinta ta hado lemu da ruwa ta koma saman tace “gashi ina zuwa.” 
Hajiya tace “zauna nan sai kace wasu baki.” Nan ta zauna hajiya ta kalleta “ya gidan?.” Ta sunkwi da kai “lafiya ya lau hajiyata.” 
kareema ta kalleta tace “ni auta ramar me kikai ne? kafin na tafi egypt naga da kibarki.” 
Sai tai dariya tace “banji dadi bane yayata.” 
Hajiya tace “yaya karema ta miko ledar da suka shigo da ita ta zaro wata jarka, irin yaluwar 
nan ta mai. 
Ta kalli ladifa “auta wannan ruwan addu’a ne da akai na izfi sittin da ruwan zam-zam, kina 
sha kina bawa fuad, kai har megidanki ma kuna sha tare tsari ne.Kina dai lafiya ko auta.” Ladifa ta sunkwi dakai tace ” “E! hajiya.” 
Hajiya ta kalli yaya kareema ta ce “wallahi kwana biyu da yarinyar nan da ita nake kwana nake tashi, har mafarkinta nake cikin yanayi mara kyau. Wannan dalilin ne yasama naiwa babanku magana kan irin mafarkan nan, shine fa yasa akai saukar alkurani da wannan rubutun, ku dukkanku aka yi wa, kema naki na gida.” 
Murmushi ya kareem tai tace “Allah ya kara girma mun gode hajiyarmu.” 
Dadi ne ya ishi ladifa tazo ta kwantar da kanta kan cinyar hajiya tace “Allah ya kara nisan kwana.Muna godia.” 
Nan ta dauka ta kai daki, ta dawo hajiya tace “kuma kita addu’a kullum kinji, mutum yakan 
zauna ne baisan yana tare da makiyansa ba. Kuma ai ta hakuri da rayuwa.” “ Tace “insha Allahu hajiya.” 
Adaidai lokacin laila ta shigo da cikinta da akalla zai kai wata shida lokacin ta sunkuya ta gaida su tace “ina daki bansan ku bane kuka zo,” suka amsa hajiya na mata addu’ar sauka Allah ya sauketa lafiya. Ta tashi ta fita. 
Sai ga safna nan ma ta shigo bakin nan a washe, cikin murmushi ta sunkuya tana gaidasu harda dan sunkuyar dakai na girmamawa ta ce “sannu da zuwa hajiya.“ 
Hajiya tace angode sosai! 
Tana fita hajiya tace “ke kam kinyi dace da kishiyoyi na gari, musamman wannan amaryar taku me kirki da kunya. Ladifa azuciyarta tace ‘hmm. Green snake kenan.‘ 
Haka suka zauna ladifa tai musu abinci suka ci. Hajiya na sallah kareema taja ladifa daki tace “zauna nan ladifa.”
Ta zauna tace “meke damunki auta?.” a yanda na ganku na san da matsala, sunkwi dakai ta yi tace babu komai.” 
“Auta ban sanki bane da zurfin ciki, na sanfa k0 wacce ke, idan wai baki gayan ba wa zaki gayawa, shi’isa najawo ki nan saboda kar hajiya taji, kinsan ta da sanya abu a rai musamman abu inya kasance naki, yanzu saiki ga hawanjininta ya tashi. Yau fa ita ta taso ni da sassafe wai nazo da ita gidanki.” D’an wani abu daga cikin damuwarta ta gaya mata. Ta fada tare dayin kuka kareema ta rungumeta tace “. Daman rayuwa ta gaji hakan, komai sai an had’a da hakuri,ji tai kamar tai hawaye, yarinya karama da ita dan ko babbar yayarsu zata iya haifar ladifar, amma duk cikinsu babu wadda take ma da kishiya sai ita har biyu, lamarin Allah kenan mai yanda yaso. 
Dago kanki ladifa wannan rubutun da hajiya ta kawo miki na tsari ne, idan ma wani sihiri ne ke dawainiya da mijinku duk zai kau.Ki dage ku tallafi mijinku, saboda duk abinda zai 
shiga sai ya shafeku, ba zargi ba amma watakil acikin kishiyoyinki sai dai addu’a kawai ki 
dage da addu’a.” “Yaya ina yi kullum,” “Ki dada dagewa Allah mai amsa addu’ar bayinsa ne , bawai alokacin da kai addu’ar lalle zata karbu ba. Allah yakanjinkirta dan ya tabbatar da imanin mutum. Ki dage kuma ki cigaba da nuna duk abubuwan da kike yi karki fasa kinji.” 
Na gode yayata Allah yabarmu tare,” tace “ameen.” Fita sukai falon, lokacin hajiya ta idarta ce “to taso mu tafi.” ladifa tace “kai hajiya tun yanzu.” 
A lokacin faud ya fito daga daki, dan bacci dama ya keyi, jikin ladifa ya shiga yana cewa “mami.” Ta dauke shi, ta tafi dauko mai abincinsa. Da zasu tafi ya saka kuka zai bisu,dan tunda aka 
kai najwa gidansu laila duk ya dawo shiru shiru agidan, gashi da nacin zuwa wurin safna, 
duk kuwa da yawan make shi da ta keyi, hakan ya sanya da ladifa ta fahimci yana kuka in yaje dakin sai take hana shi zuwa. Suke zama a samansu. 
Ganin ya dage aka hado mai kayansa suka tafi da shi. 


Hmm ramadan ya debo da zafi fa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]