[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA COMPLETE - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA 


CHAPTER 38
Binta dakin yayi yaja, ya tsaya. yace “laila ina gaya miki ki fahimta, wallahi zan sabar 
miki bana son neman magana kinaji na.” Juyar da kai tai tana Zumbura baki “wallahi tallahi ba zan yarda ba, haka kawai akan wata mata ana cin zarafina, ai dama na san kafi sonta, shiisa kake hakan. Sai kuma ta sanya kuka 
ta zauna gefen gado. Tsaki yayi ya kalleta. 
Ba kuka zaki min ba laila, idan kina son zama lafiya ki zauna da kowa lafiya agidan nan, bana son neman fad’a . 
Yana fita ta kifa fuskarta kan gwiwarta ta tsiri kuka, anan ta kuma shan alwashi komai ta 
fanjamafanjam! Dan babu wanda za ta ragawa. 
Zama tai gefen gado ta dau kiran mamanta tace “wai ina kika shiga ne sai kira nake kinki 
dauka?.” “Wallahi mama ina falo ne .” “To ya gidan ne?.” 
Ta amsa da lafiya lau. Maman tace “wai ni yanaji shiru ne ehe? safna tun da kika turo kudi sau daya baki kuma ba. Ni gashi kin barni dajidalin uwa uwa, ko dazu sai da tazo ta zuba min kwandon masifa kan bashinta. Ga lawwali kojiya saida yayiwa muftahu waya wai kan cikon kudin show glass din da kika karba. 
Kinsan ni dai ba kudi gareni ba, in bakin wafto kin kawo ba, dariya za ai mana, mun fita 
kunyar mutane kuma kina son bari na dajangwam!” 
Safna tace “mama nima fa ba samun kudin nan nake ba, wanda ma na baki da dabara fa 
na same shi, “to ina kika kaisu kai umma?.” 
“Kinci gidanku, har sai kin tambayeni ina na kaishi? to amfanin yau da kullum nayi dasu. 
Kina dai ganin yanda mutan gidan nan suka zubo min ido? 
Da zaki ce bakya samu ai wallahi karya ne yanda mijinki ke da kudin nan ai yanzu ne zaki wafto, tunda kece ake yi dake.” 
“Umma kenan, wallahi yanzu tunda aka d’aura aure baya wani bada kudi fa.” “Ko kudin cefane baya baku?.” 
“Umma baya wani bada kud’in cefene kinsan irin gidan, sai dai komai ya saya ya ajje na amfani, wanda babu mu kuma ya fad’a a sayo, sai muna son abu ne zamu gaya mai ya sayo 
“Ke dallah! kamar ba mace ba, duk hanyoyin nan da zaki wafta aikin sani, koda kissa ai kya karba.“ 
“Hmm! mama kenan, ni fa kawai ki biya.” 
“Wallahi dakuwa na sabar miki, wallahi zan turo miki lawwali da uwa uwa suzo har gidan naki ki san yanda za ki da su.” 
Zaro ido ‘tai ta ce. “Aa mama,ki saurareni kawai, sukai sallama.” 
Yana zaune a farfajiyar gidan ta baya yana shan iska, yana danna laptop dlnsa, ga gorar 
ruwa a gefe da wayarsa. 
A hankali safna ke takawa harta karasa gareshi, ta zagaya ta baya ta dan saka hannuwanta cikin kunnuwansa ya dago da sauri, sai ta dan yi baya tana dariya,juyawa yayi ya ganta, sai yayi murmushi yace “yau dayar haka kika tashi kenan.” 
Murmushi tai ta dawo gefensa ta zauna tace “wallahi fa ashe! Haka wurin nan ke da iska 
shiisa kake sonsa.” 
 Ya kamata kema ki zauna awajen.” 
Laila da ke ta saman benan Lad’ifa suna hira, kamar ance ta leka sai ta leka ta ganaso su, 
kamarta fasa ihu sai ta juya ta kalli Ladifa dake gyara kayan fuad daza a kaimai.” “Bari na sauka maman fuad.” Ta fada tare da fita. Direct waje. 
Wanda alokacin safna na yiwa ramadan zancen ya bata kudi ya kalleta “ke mai zakiyi da kudi?.” Sai ta dan rankwafar da kai tace “wallahi bashi zan biya wata kawata.” Tsaida dannawa yayi ya ce “har bashi kike cine?.“ 
Ta daga mai kai tare da sanya gefen adon hannun rigarta a baki tana dan wasa dashi, tare 
da lullumshemai idanuwanta. Numfashi yaja yace “kamar nawa kike sone wai?.” Sai tayi fari tace “kamar dubu dari.” Ya dago ya kalleta ” baiyi yawa ba kuwa? wallahi banda kudi sosai! sai de dubu hamsin.” 
Adaidai lokacin laila ta isa wajen. kuma lokacin safna tace “kai godiya nake sugar na, kafi kowa ongo na.” Dariya ya sanya yace “har dake?.” Sai ta sanya dariya “har ni din.” Wato bayan sugar har onga na koma ko.” Dariya ta kuma yi Tace “E Mana my ice cream.” Murmushi ya kuma ya ya kalleta yace “lalle kina ji da jin dadi safna.” Laila data karaso ta tabe baki tace “Habiby ina son magana da kai.” Daga kai yayi ya kalleta yanda tai ne ya bashi dariya sai kace wani saurayi da budurwa.” 
“To ina jinki maman najwa. Kallon safna tai suka bankawa juna harara, tace “bamu wuri mana amarya.” Safna tace “akan me? Bani kika zo kika tarar ba.” Tsaki laila tai za tai magana ramadan ya katseta, fadi abinda zaki fada maman najwa.” 
“Hmm! Dama kudi nake so,” ta fada tana kallon safna. 
Wanda da sauri safnar ta kalleta. 
Ta yatsine fuska ta banka mata harara. Tofah! ya ambata aransa yace “me zaki da shi ne?.” “Wasu ‘yan hidundumu zan yi.” 
Ta fada tana kallonsa domin tasan shi ba ma,abocin bada kud’i bane, dan sai suyi wata bai basu ko kwandala ba amma duk wani kayan bukata zai sayo, itama ba don zatai amfani dashi bane kawai dan ta bakantawa safna ne jin da tai zai bawa safna ta sanya kishi ya 
motsa. Kallonta yayi yasan halin laila ciki da bai, yasan ba abinda za tai, kawai gasa ne. Suka Hade ido dashi, sai ta dan juya tana murmushi. ‘ Sai ya girgiza kai don yasan jazaba ne in yace mata babu, dan yasan taji zai bawa safna.“ “To karki damu zan baki.” 
Kashe murya tai tace “thank you habiby.“ Ta kalli safna ta kuma banka mata hararta ta mike tai nata waje.” 
Haka ramadan ya bawa kowacce dubu hamsin har ladifa da bata tambaya ba, amma hakkinta ne dan yin adalci. Tana zaune a falonta ya shiga ta gaidashi, ta dan kauda kai, yace “kinga alert na 50k ko?.” 
Ta daga kai mai kai E yace”to ki amfani da shi.” 
D’an kunya ce ta kamata ganin yanda ‘ake shareshi kwana biyu, cikin ido ta kalleshi tace nagode Allah ya kara budi. Yana jin dadin aduarta, wacce ba tun yau ta saba yi mai ba, duk cikin matansa, babu wacce kemai irinta, fita yayi ta bishi da kallo taci gaba da aikinta. 
“Eh mama ya bani.” “Haka nake sanki safna, ai yanzu sai da dan dababaraku ko kema kya samu ki nuna cewa E me kudi kike aure. amma dubu hamsin fa ta iya uwa-uwa ce atoh saura lawali.” 
“Umma ni fa gaskiya karya ga kamarna dame shi,” To ai shike nan ki sanya naji kunya agidan nan azo ai mini tijara. Jiya jiyan nan saida murja ta saima uwarta kekyan dinki, da karamin firij, karki ga yanda akai ta yi mana yanga, to ina 
so kema ki bude wuta ki nuna kema mai kudi kike aure.“ 
“Mama ai nima ‘Ina son naga na kyautata miki fa, ki saurareni insha Allah zan samu kudin 
biyan lawalin.””To da dai ya fi.“ 
Haka lokaci yaja ramadan nata kokarin ganin ya saita kan matansa amma, duk yanda yake zato abun ya faskara, domin laila da safna basa jetuwa kokadan! kullum cikin fada. 
Ta bangare daya har yanzu matan nasa sun kasa sakewa da shi. 
Yau da yake girkin laila ne bayan gama duk girkinta tayi bangarenta, yana dawowa yayi duk abubuwan daya dace yayi bangarenta ya shiga dakinta tana kwance sanye da kayan bacci ya kwanta abayanta, tana ganinsa sai ta mike ta dau Filo ta Fice  falo ta kwanta, 
tashi yayi zaune yana mamakinta, afusace ya mike yayi falon yace “laila tace “naaam.” 
“Wai me yasanya kike haka ne? nifa mijinki ne, idan laifi ma nai muku ai yaci ace kin sauko, amma kamar wacce na kashe wani nata, yau wata nawa da auren nawa,kusan an kusa shiga wata na biyu fa haba. Amma ke idan bukatarki ce kikan zo na baki amma ni kin kasa. Kwanaki ba kudi kika bukata ba na baki, amma ni kin kasa ko? Ga shi kinje kin zuge min matata wacce wallahi nasan ba dan kin zugeta ba bazatai haka ba.” 
“To meye amfanina, ba kana da amarya ba, ai ni na bata kwana na, duk ku hada tunda kafi
sonta, har da sanadin aurenta aka kasa gaya mana.” 
Saita sanya kuka, dan har yanzu abin na mata ciwo musamman abubuwan da yake mata 
akan safnar.” Kallonta kawai ya ke cike da mamaki. Sannan ni ban zuge matarka ba. Watakil itama ka kaita bango ne dan haka ni ka kyaleni.” 
Ta tashi ta shige daki ta rufo abinta.Wani irin bakin -ciki ne ya zuyarci zuciyarsa, sai ya 
tashi ya shige bangarensa ya kwanta. Yana tunanin Gobe zai nuna mata cewa tayi kuskure. Washegari
Ya zamanto girkin ladifa, suna zaune a falo wajen 10 safna, da ke kwanciya da wiri harta kwanta, sanin cewa ramadan baya shashenta, saisu uku kawai, ladlfa ta mike zata tafi. dan itama bacci ta keji, nan ta tashi tai musu sallama, mike wa yayi yabi bayanta, laila ta bishi da ido ta tabe baki, ta mike sai ta dan bisu a baya dan ta ga ina zai shiga, taga ya shiga shashensa sai ta basarta tashi ta mike ta yi shashenta. 
Tuno da meat pie din da ladlfa tai na yamma ya sanya ta mike dan ta karbo, dan ita kam bata jin bacci lokacin, ta fito zata hau matattakala ta ganshi ya fito daga shashensa ya shiga na ladifa ya rufo. 
Dafe kirji tai, duk da tasan cewa ba ranar girkinta bace, amma taji d’ar! sai ta tsaya taga zai fito, amma shiru har wajen goma da rabi sai ta koma shashinta da gudu tana dafe da kirji. 
Shi kuwa tun lokacin daya shiga ladifa na shirin kwanciya tana ganinshi ta dauke kai ya 
zauna gefen gado yace “baby.” Tace ” ya dai?.” 
Ta hau kan gadonta ta karkade ta gyara ta kwanta, tai addua ta shafa ta rufe ido, bayanta ya dawo ya kwanta ya sakalo hannuwansa, sai ta tashi zaune . Tace “meye haka ni dai gaskiya ka fita, ” 
Ta taso da sauri ta sauka kasa, tai falo “tofa!” ya fada. ‘itama irin hakan zatai min.’ 
Sai ya mike ya bita a baya yace “haba baby me yasanya ke dana sanki me hankali ace nazo kin ki kulani, ko kina ganin hakan da kike shine mafita? Allah fa na ganinki abinda kuke, lefi ne nayi kuma na nemi afuwarku, kinfi so Allah ya kamaki da lefln guduna. Kinsan dai hukuncin matar dake hakan.
Sai tajuya jikinta asanyaye ta koma daki. ya bita abaya, “please baby.” 
Bata kara cewa komai ba ta zauna ta shiga tunani aranta ‘wannan fa abinda take duk ba shine ba, kana je garin neman gira ta rasa ido. taje ta dau alhakinsa. Allah ya damketa,’ sai 
ta kalleshi yayi wani marai rai, sai ya bata tausayi ta sunkwi da kai. . 
Ganin hakan da tayi yasan ta amince. 
Kashe musu fitila yayi. Asuba ta gari ramadan ladlfa. 
Da safe laila ta mike idonta dukyayi Iuhu ~luhu. Da yake zai tafi aiki,!karfe bakwai suka fito shi da ladlfa rike da jakarta yana kallonta, yace “sweat baby jiyan nan nayi missing dinki fa 
sosai.” Murmuahi tai tace “Ai ba kai kadai ba harni.” 
Hannunta ya ruko yace “karki kara barina please baby.” Sai ta sunkwi da kai cikin annurin fuska, suka karasa sauka kasan. ba kowa afalon ya zauna kan dining . 
Alokacin safna ta fito ta kalleshi ta zauna gefen kujera ta harari ladifa dake titowa daga kitchen, safna ta gaisheshi. 
Ganin sai wani rawarjiki yake yana kallon ladifa taji wani banzan haushi ya kamata, wai namiji me ita har ya zauna yana wani rawarjiki kan wata, sai ta mike tace “sugar adawo lafiya.” ta fada ya daga mata kai tare da binta da kallo yana ayyana abubuwa da dama yanda yaji tada ladlfa. Murmushi yayi tabbas ladifa dabance ko ada yakan samu nutsuwa gamsuwa da ita. Kawai matsalarta abubuwan da bata dashi da yake da muradi ne, amma kuma abin mammaki ita safna yakan nishadi ne sosai in yana tare da ita, amma tabbas gamsuwa sai a gurin maman fuad. 
Ya kusa shanye tea, sai ga laila ta fito ta kalli ladifa ta buga mata harara ta juya sukai ido 
hudu da ramadan ya dauke kai. 
Tashi yayi ya fita tai mai adawo lafiya, yana fita Iaila tace “amma maman fuad ban taba sanin abinda ake fada akan kishiya gaskiya ne ba sai yau, wato duk wacce ta hade kai da kishiyarta sai ta munafurceta, ayau na yarda, shine mun shirya abu ni dake, amma dan tsabar kini bibi kika biye mai, kika amshe shi, wannan ai bata rawarki da tsalle ne, wato nama gane nice mahaukaciya ke kina can da miji ni ina nan ina haukana.” 
Ladifa tace “maman najwa ni ban munafirceki ba ,kuma ba zama mukai muka rubuta ba cewar babu wacce zata kula shi sai lokaci kaza, ni bansan sanda akai haka ba, ki sani ban munafurceki bafa, baki fini jin haushi ba kawai na duba ne meye ne aciki ba a kishiya ake aure, dole dama wani ya zo ya samu wani, ko shi da yayi lefin nan yazo ya nemi gafararmu, meye to? haba kamar mara galihu nikam ban munafurceki ba, na karbi abuna da naje 
Mala’iku na tsinen ba gwanda na amshe shi ba. Mijina ne fa. Kema kiyi hakuri kawai.” 
Safna da kejinsu ta buga shewa ta ce “kai Allah na dawo inji mai yawon duniya. Ayi dai mu 
gani in basilin zai toya kosai.” 
Harara laila ta buga mata ta kalli ladifa tace “haka kika ce kenan, ai shikenan dan bakara k0.” 
Girgiza kai kawai ladifa tai ta haye shashinta. Tare da lumshe ido tuno darenta da mijinta 
ko ba komai itama ai tayi missing kayanta. 
Laila k0 duk sai ta zauna tana huci lallai ma ita ladifa za taiwa zagon kasa.Hmm ta mike ta bar wajen. 
Wannan abinda ya faru shi ya dada hargitsa gidan, domin ramadan sam ya daukewa Iaila kai, duk yama daina zuwa shashenta, domin yaji haushin abinda tai mai yasanya aransa har sai ta kai kanta gareshi, dan ba damuwarsa bace tunda ga sauran matansa. 
Laila ta daina yiwa ladifa magana, k0 ganinta tai sai ta dauke kai, ita kuma ladifar tun tana kulata har tazo itama ta shareta. 
Wani abin mamaki sai safna ta tsiri shigewa ladifa, sai ta hau samanta tace maman kaza ko kina da kaza, ta dan zauna tai hira ta sauka ita kuma ladifa data gane sai take danja baya 
dan tana tsoron itama wataran tai mata irin na Iaila tace ta munafurceta. 
A hakan dai take ta shige mata ita kuma tana ja baya, musamman da aka dawo da fuad sai 
take daukansa tana ba shi alawa, akace maida mai da wawa sai ta fara dan sake mata. 
Laila kuma duk na kula sai ta kuma Cika, tace ai dama dan su yi mata sharri ne suke haka, sai dukta hade su su biyu ta kejin haushi. 
Lalla duk ta damu kanta ramadan na kula da yanayinta, sai dal yayl dariya ya basar, dan Shl ya dana mata bomb. 
Laila takai makura domin haushin yadda duk ya daina ma damuwa da ita take, hakan ya sanya ta kai kanta, wanda shima sai da yaja aji daga karshe suka shirya aka koma kamar da. 
Ayanzu da duk komai ya koma normal ramadan duk ranar girkin ladifa yafi zumudi, shi kansa baya sanin hakan yanayi, inda safna kejin matukar haushi dan fa har ta zarce laila akishi sai dai ita tafl laila iya boye shi ne, akwai iya bagararwa. Takan iya zama ta shake bakinciki na kishi idan ta gani kuma bakin nan haka zatai ta murmushi, tana nunawa kamar ita bata damu ba. Wanda da bambamci dana ladifa. tana iya shanyewa amma bata iya zama wajen da ta san inta ga wani abun sai dai ta barwajen kawai. 
Ayanzu kuma safnar har laila itama sai data shigeta, inda itama sai da aka kawo najwa taja ta ajiki duk haka takejan yaran ajiki, taita nunawa tana sonsu sosai! wanda azuciyarta ba 
Haka bane nata iya kissar makircin kenan. 
A haka dai duk ta kanainayesu suka duk saki jiki da ita, duk da cewar laila ba duka ta sakar 
mata ba. Sukan dan taba fada wataran. 
Yau suna zaune su uku najwa da fuad nata wasa akan kekunansu na yara. Safana ta mike ta shiga shashenta yaran suka bita aguje, dan sun saba da ita. Takan basu alawa, suna shiga najwa tace “awawa,” juyowa tai ta zare musu ido “ku futa jarababbun yara, dan kunga ina janku ajiki zaku dameni, ta kwade su har da rankwashi dan duk wani sonsu da take nunawa a gaban iyayensu ne bai kai ciki ba. Musamman ganin yanda ramadan ke nuna soyayyr sa akan yaran muraran!. Hakan yasa take jin tsanarsu ba wai kuma yau ta fara make suba, indai zasu bita shashenta sai ta makesu. 
Amma agaban ramadan kamarta cinyesu, hakan ya sanya ramadan ke dada jin dadi. Ganin yanda yaran suka doshi hanyar fita suna kuka ya sanya ta debo alawa biyu tace ” gashi banda fada ku karba.” 
Ladifa tace “sun dameki ko?.” 
Sai tai murmusi tace “haba dai nida yarana. wanne damu kuma zasu yi min bakomai ai.“ 
A bangaren ramadan halin safna na karbar kudi yayinda zai mu’amala da ita ya fata isarsa. 
Yauma da yake shshinta. Ya nuna bukatarsa ganin yanda yake dan doki ya sanya tai murmushi, ko ba komai zata samu kudin biyan bashin lawali, dan kojiya saida mamanta 
tai mata magana kan yace zai debo mata ‘yan sanda in bata kawo ba. Sai ta gyara zama tace “Inji dumus.
Ta juyar da kai. Tsaki yayi yace “kinga safna, wai zaman daduro muke dake ko meye ehe? Ke bakya da tunani ne? So wajen hudu kina min irin haka to agaskiya ba zan lamunta ba, 
wannan wacce iriyar dabia ce? ba ki da ilmin addini ne?.” Sai ta kalleshi da mammki tace“toni kuma yau bacci na keji tajuya baya tare da turo baki. 
“Ki sani matana dukkansu babu wacce ta taba cewa na biyata k0 da kwandala ne, amma ke sai na baki kamar wata wadda naje nai hayarta?
Sai ta juyo ta kallesh’ Ni jarabarka ta iseheni haba! In kana so dole sai ka bani wasu kudi, 
maganar ilmi kuma ina dashi na sani kawai ra’ayina ne.” 
To shi kenan, kici gaba indai nine wallahi ba zan kara biyan wani kudi ba domin sadaki na 
biya.Kuma ki rike abinki domin Allah ya hore min wasu matan” 
Bata kara magana har ya fice daga wannann lokacin suka fara samun sabani da ita. Ganin babu sarki sai Allah ya sanya ta hakura da mummunan tsarin nan nata. Wanda kuma ya kafa musu dokar duk mai girki sai dai ta bishi dakinsa ya daina bin kowacce.” 
‘Yar kanwar hajiyar ramadan ce ta haihu, safna da Iaila zasu je suna, saboda ramadan yace 
ba za abar gidan haka ba kowa ba.Sai ladifa ta zauna. 
Sunje gidan suna wajen karfe biyar da rabi, daman ramadan yace su dawo alokacin sai ga wata kawar Iaila da suka dade basu had’u ba, nan fa hira ta balle. Agaggauce suka mike tace “kai sadiya wallahi zanso musha hira dake na dade ban ganki ba.” Sadiya ta gyara tsayuwarta “kimin kwatancen gidanki sai nazo.” 
Safna dake gefe tadan tabe baki tace “ki zauna mana Iaila. ai ba wani abu bane da sauran 
lokaci , idan ma na koma abu fuad ya dawo na sanar mai kina taya aiki ne.” Da sauri Iaila ta kalleta tace “kai ammafa nagode sosai.Kije sai na tawo.” 
Sai ta kama hanya ta tafi sadiya tace kai “Iaila kishiyarkin nan me kirki, wacece za tai maka haka?.” Iaila tace “gata nan dai ba laifl.” Ita kuwa safna ta karasa gida hankali kwance bata dade da komawa ba ramadan ya koma, suna zaune ladifa na kitchen na girki, safna kuma na falo ya shiga, sannu da zuwa tai mai 
ladifa ta fito itama tai mai sannu da zuwa yace “ina Iaila take ne?.“ Safna ta dan tabe baki yace “ba tare kuka tafl ba?!‘ 
Sai tace “ai nawan, Lokacin daka ce mu tawo ita kuma ta nemi wurin zama, nai mata magana ta ce wai ba yanzu ba saboda taga kawayenta wai har da karna fada maka, kawai nai taho wata, saboda karka dawo kaga bamu dawo ba.” Fuskarsa ce ta canja. Wani haushi ya kume shi, sai ya girgiza kai . Zata dawo ne.” 
Ladlfa na rike da jakarsa suka haye sama, ita kam a yanayin da ta kalli safna tana ganin 
alamar rashin gaskiya a tattare da Ita. 
Suna shiga shahinsa ladlfa ta shiga taya shi cire kaya, tana yi suna magana tace “zaujina ka tsaya kai bincike pls karka dau babban mataki, naga ranka ya baci.” 
Numfashi yaja yace “raina ya baci baby amma zanbi shawararki.” Murmushi tai tace “Shiisa nake sonka jarumina gwazon maza daya tamkar da dubu.
Ji yayi kansa ya fasu, jin wannan kirarin da tai mai. “Har kika kaini ! sonki yayi ma zuciyata yawa. ” Dadi ne yasanya ta rungumeshi tace “ada ban taba tunaninn za kaci gaba da gayan wannan kalmar ba yanzu, na dauka nayi balaguro da ita tun bayan daura aurenmu. Musamman ganin yanda ka daukeni ni bada kulawa ba, duk sai na sare. ashe zan samu.” ‘ 
Matsarta yayi a jikinsa yace “adaina tuno baya, domin yanzu farin-cikinki nake so. Murmushi tai ta kwanta ajikinsa tace “ankusa kiran sallah bari na sauka.” 
Sai ta tashi ta fita, shi kuma ya yi shirin wanka. 
Sai bayan sallahr magriba laila ta dawo da sauri ta shige shashinta tai sallah lokacin duk 
sun sauko falo ta fito. Ramadan na kallonta tace “wallahi yau goslow a hanya.” 
“Bansan cewa laila kin raninai ba sai yau, nai magana kinki bi ko? ga lokacin da nace ku dawo, amma ke kika ki tawowa, saboda kawaye sunfi magana ta muhimmanci agareki k0? safna ta dawo ke kika zauna.” 
Kallon safna tai, safnar ta dauke kai. Sai tace “kayi hakuri ni dai nasan safna tace zata gaya maka.Kuma bance ba zan tawo ba dan banyi haka da ita ba.” Hannu ya daga mata “ba san sanjin bayaninki, kawai ki guji gaba.” 
Cike da mamaki ta kuma kallon safna da mamakin irin gadarzaran da taso kulla mata . 
Kwafa tayi.” Safna ba haka ta soba taso ai mata babban hukunci sai ta share kawai.. 
Aduk lokacin da ramadan ke dakin ladifa to duk matan sun gane yanayin yanda yake komai da hanzari. Hakan ke sanyawa safna najin wani irin kishi takan tuno yanda ramadan din idan awajenta yake yanda yake zuzutata, da irin baiwar da take dashi, bakinsa bai gushewa wajen ce mata tana sanya shi nishadi, aduk lokacin da zai’ fada sai ta ringa jin cewa kamar babu wata mace agareshi da yakejin dadinta kamarta. 
Amma kuma takan shiga mamamki da tunanin waye namji idan taga yana rawar k’afa 
dakin ladifa, ta kan kalli ladifa taga daman tafita. Wannan dan dalilin ne ya sanya tafi jln 
kishin ladifa aranta sosai duk da cewa sunfi samun sabani da laila. 
Ladifa na kwance ramadan agefenta duk da cewa bama wani abu suke ba. Wanda safna na can ta kasa tsugun! Wayarta ta dauka taga karfe sha -biyu na dare, sai ta latso kiran ramadan taji wayarsa ta shiga, ta katse bai dauka ba, ta kuma bugawa ya dauka,safna na jinsa sai ta tsiri kuka da sauri ya mike, alokacin ladifa ma ta mike yace “meye safna.” “Kaina kirjina duk ciwo suke wayyo! ka zo dan Allah.” Kashewa yayi ya mike “bari naje safna bata jin dadi.” Cike da tausayi ladifa tace “Allah ya ba ta lafiya “amin,” ya flce. 
Shashenta ya shiga tana ganinsa ta dada narkewa ya zauna, tashi yayi zai dauko mata magani, tace ya dauko mata zuma ciwon kirjin zai sauka, haka akai, ya kawo mata ta sha sai ta lafe ajikinsa, tana numfarfashi, sai nishi take na wahalar ciwon karya, sai wajen biyu yakoma dakinsa, sai lokacin tayi bacci tasan koya koma ladifa tai baccinta. Da safe a makare ya mike kansa har ciwo yake. Ga idonsa yayi ja. Haka ya tafi aiki. 
Haka ta tsiri irin wannan makircin idan tayi a bangaren laila ma,wanda su lokacin ma ba a nutse suke ba, taita kwarara kiran waya, yayi tsaki ya dauka, nan ma tace ciwon kai ya tsananta mata tana kuka wiwi, haka ya tashi yaje duk da cewa yaji haushin katse mai jin dad’in da yake, laila kuwa wani haushi ne ya isheta,ji take kamar ta mirkushe safna. 
Kafin ya dawo har laila tayi bacci.Wanda da safe idan yace su je asibiti sai tace yanzu batajin ciwon. 
Sai data yi a bangaren ladifa sau biyu haka laila ma sau biyu, abin ya dame su. ladifa ta rasa yaya zatai, dan ta kula makirici ne kawai irin na safna, ba wani ciwo dan da safe garau take mikewa shi kuma yaki ya fahimta, in akai magana yace dole ya kula da ita. Saboda karkashinsa take. 
Dan kwana biyu ta daga kafa, ta dade bata kumayi ba har aka dad’e, kwatsam! wata rana ladifa suna mu’amalar aure safna ta bugo wayar, sai tsuwa take wanda shi yaki dauka, sabida hankalinsa sam! baya wurin yana wata duniyar, ladifa ce ta ankare tai kwafa a hankali ta zura hannunta ta dau wayar ta kashe ta dif! ta ajje gefe wanda ramadan bai kai 
ga ganowa ba ma. 
Safna kuwa lokacin da taji an kashe kuma ta buga taji dif! sai ta hakura haushi ya kume ta, tanajin kamarta kurma ihu duk kishi ya dameta. 
Washegari ta canjawa ramadan fuska ya rasa gane kanta. Sai shima ya shareta Saboda matsalolinta sun fara damunsa, dan tafi laila matsala dan ita laila bata komai a nutse ne shi.isa, amma safna sumumu ka sau ce.Tafi iya tsiya. 
Sai da akai sati daya bata kara kuma aikata hakan ba. Ranar da taiwa laila kuwa domin itama ta gane makirci ne irin na safna, tasha alwashin da safe saita gane bata da wayo. 
Hayaniyar laila da safna ce ta tada ladifa, da yake ranar lahadi ce, ta duba agogo karfe goma sha-daya, ta juya ta kalli faud na bacci, tun bayan data bashi abinci karfe takwas na 
safe suka koma baccin. sai ta sauka tayi kasa. 
Laila ce ke ta bala’i tana cewa “wallahi tallahi na rantse da Allah muddin kika kara kira da daddare sai na nuna miki ke karamar mara kunya ce, in banda dabbanci mutun tare da iyalinsa kina kira da daddare, da yake cutartaki ita sai dare take tashi ko, na kula baki iyacin kwan makauniya ba” 
“Ke laila dakata, na kira din an gaya miki da lafiyata kalau zan kira ne. Yanda kike takamar 
mijin kine nima nawa ne.” 
“ln kinsan zaki kirasa saiki bari ba ramar girki naba atoh dan wataran zan nuna miki danyen hauka wallahi.” Najwa ce ta tashi daga baccin da take akan kujera, tana kuka ta sauka ta gefe ta rike safna ta dauka laila ce safna ta huge yarinyarta fadi ta buge da gefen kujera ji kake gum! ta fasa 
kara. Wanda adaidai lokacin ramadan ya shigo falon, karar da najwa ta sanya ne yaji fadiwar 
gaba. 
Da sauri laila tajuya ta dau najwa ta rungu meta ta shiga jijigata.Dan bata san ta tashi ba ma, ganin yanda yarinyar ke wani irin kuka ya hana laila maidawa safna martanin abinda taiwa najwar. Wani irin takaici da huci ne ya kume ramadan ya tako inda suke afusace ….. 

Hmm ana buga rikici a gidan ramadan koya zata kasance oho

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]