[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 32 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 32Dakyar laila tai bacci, saboda bakin» ciki da kishi, hade da takaicin da ya rufe mata zuciya, in banda ma namiji da bai raina abin kunya ba, ace ‘yar aikinka yana kula ta, sai ta sanya tsaki sai kwafa Washegan’ da safe. 
Laila bata nuna komai ba,jira kawai take ramadan ya sanya kafa ya fice ita kuma ta fara aiwatarda kudirinta, dan tasan tabbas zai iya zama ramadan ya hanata. 
Sai data bari hansatu duk ta gama aikace -aikacenta sannan ta dumfari dakin ta turo hansatu,ta na tsaye tana gyara jakar kayanta taji saukar bulala a bayanta, sai ta gantsare ta fasa kara “wayyo.” 
Da sauri tajuyo kafin ta kara magana laila ta kuma shaula mata, nan fa hansatu ta gigice ta shiga kuka wiwi, “dan Allah Anty kiyi hakuri, me nai miki.?.“ 
Cikin tamke fuska tace “wato ke ga ‘yar iska ko ga maha,incinya mai bin mazan mutane ko, wato ke gaki mai wayo ko?kinzo a bagar kina iskanci da mijina ko? to wallahi yau sai na lahira sai ya fiki jin dadi ke idan akace ki kuma kula mijina ba zaki kara ba.” 
“Dan girmarn Allah anty ki hakuri, ni ban komai ba.” Dundu ta duma mata tace “naji komai kuma na ganki da idona,jiya da daddare.” “Wallahi Anty shine…” “Shine me?.” 
Nan haushinta ne ya kuma rufe laila ta kuma rufeta da duka tace “wallahi yau karshen shan jar miyarki ya kare a gidannan, sai ki tafi can kauye. Ganin yanda take dukanta kamarta samu jaka, ya sanya ta mike aguje ta fito falon tana kuka, sai sosa baya take, adaidai lokacin baba saude da ladifa suka firfito suna tambayarta ba’asi, da sauri laila ta koma dakin ta shiga watso kayan hansatu, tas ta watso su tace “ki kwashe ki tashi ki fita.” 
“Dan girman Allah ki hakuri,” hansatu ta fada da kuka tana adduar Allah ya kawo ramada. 
Lad’ifa tace “wai laila akanme za kina duka yarinya ne? me tai miki? Ai wanana zalunci 
haka.” Nan ta shiga rattabo mata komai, rike baki ladifa tai sannan ta runtse ido tabbas! dama tasan hakan zata iya faruwa. Kallon hansatu tai tace “yanzu hansatu halaccin da zaki mana kenan? ashe! dama ke baki da kunya hansatu, ai ana barin halak dan kunya kodan yanda muka daukeki. Gaskiya ba ki kyauta ba sam”Kiyi hakuri anty sharrin shedanne” 
.Wani irin wawura laila tai mata tace sharrin shedan ko? to yau zaki gane, rufeta da duka ta karayi hansatu ta cika gidan da ihu, ladifa ta kwaceta tace “ya isa haka haba.” 
Baba saude ta girgiza kai tace “baku da kaico, ai babu yanda ban fada miki ba. Amma ki daina dukan ‘yar mutane haka saboda tsautsayi.” 
Wallahi baba saude saina illata yarinyar nan, yanda za taji tsanar mijina aranta. Ta fada tare da watsama hansatu kayanta akai. Ta kuma wawurarta zata daka. Ladifa ta kareta tace 
haba mana, kefa laila baki da hakuri, ki barta haka ki duka mijinki, shine mai babban mai laifi kuma idan kin tuna babu yanda ban dake ba akan a canjota kika ki, har da gayan magana waike kika daukota, ai gashi nan ta dalilin gaddamarki kina son janyo mana matsala.” 
“Kinga ladifa ki kyaleni na huce haushina akan yarinyar nan.” 
Janhansatu tai ta watsa ta wajen sai kace kayan wanki, ta dau kayan ta wulla mata “karna kara ganinki a gidan nan munafuka, anji gidan dadi ana kwasarjar miya, sai ki koma kauye.” 
Kuka hansatu keyi na fitar rai domin dama ranar nan take tsoro, amma mijinsu baya ganewa, sai yayi ta shigo mata daki,jitai ta kara tsanar laila, nan ta kudire abubuwa da dama aranta, ta tashi ta hada kayanta, ta tafi da yake da kwai kudi ajakarta tayi tasha ta tafi garinsu. 
Laila kuwa zama tai a falon tana ci gaba da fada, baba saude tace “tunda dai kin koreta ai shi ke nan, ai daga yau kwa hankalta, in banda rashin wayo wannan ranbatsetsiyar yarinya ku dauko matsayin‘ yar aiki kamar baku da kunnuwa ko bakwajin yanda wasu mazan ke lalata da ‘yan aiki, wasu suyi ciki, wasu su auresu, ina laifin ma ku dauko ‘yar karama, amma ku kamar wawaye saboda tsabar kyiwa, musamman ke laila ai yanzu ga irinta nan. 
Lad’ifa kuwa tana kitchen tana aikinta domin ita abin bai wani dadara ta da kasa ba,don 
tafi bawa ramadan laifl, amma takan kaurara mamakinta akan yarinyar, yanda akai har ta 
sake dashi, lalllai duniya ba yarda, ai indai da lafiyarta da komai ba zata kuma bari a dau ‘yaraiki ba.Ko da kuwa karama ce. 
Hansatu kuwa a tasha ta buga wayar ramadan tana kuka ta sanar mai ta tafi garinsu, ya tambayeta dalili ta gaya mai, Yadan shiga damuwa amma yanayin aikin da yake ciki sai ya dauke mai hankali, wanda sai karfe shida daya koma yake tunanin dalili. 
Laila na tsaye tana kaikawo a falo dan tun da rana take dakon mijin nata. Sai kaikawo take ta kasa tsugune! 
Yana shigowa laila ta tare shi yana kallonta yasan fada ta keji, shiisa direct yayi samansa, sai ta bishi a baya,yana shiga dakin tana taka kafarta. 
Ko zama bai ba ta fara magana “yanzu ya dace ramadan ka nemi cin zarafina.” 
“Zarafinki name naci?.” Wallahi ramadan ban taba tunanin za kai mana haka ba, wai ‘yar aiki to ai gashi na koreta.” 
Da sauri ya kalleta irin kamar bai sani ba, sai tajuyarda kai tace “haka kawai aje wani abu ya faru ajanyo mana jangwam! to idan ma sonta kake wallahi ka cireta, dan bata isa nai zaman kishi da ita ba wallahi me akai akai ita, ‘yar aikina wadda nake bawa umarni imposible wallahi, ni laila nafi karfin kishiya, kishiyar ma wai ‘yar aiki.” 
“Hey you girl….! ramadan ya fada tare da daga mata hannu, wanne irin magana kike haka ne? baki da wayo ne? ke miji ya dawo ma ko dan ruwan sha balle ma kiyi kokarin tararsa da shi  kinzo kin tare ni da masifa da bala’i, duk abinda kika fada kina bani umarni ne ko kuwa gargadina kike iye?.” Ya fada yana mai zaro mata ido. 
Cikin takaici tace “amma kasan abinda kai bai dace ba ko? Ko kasan cewajiya na ganka kaida hansatu da daddare ka shiga dakinta.” 
Tsaki yayi yace “sai me? me ki kaga anyi? laila ki shiga hankalinki.” 
Sai ta fasa kuka “na rantse da Allah ba a isa aimin wulaknci agidan nan ba, ka rasa wa zaka na kulawa sai ‘yar aiki na. Amma ai na koreta sai kabi ta can muga aiki da cikawa, dan wallahi na kara ganin kafafuwan yarinyar nan a gidan nan sai na kusa karairayata,abin kunya kawai.” 
Ta fice tare da sakin kofa barn! Tsayawa kawai yayi yabi kofar da ido tabbas! yasan jiya itace ta gansu dan yaji karar bude k’ofa, tsaki yayi dan bai so hakan ta faru ba. Shi kanshi buyagi kawai yake ma lailar amma yasan bai kyauta ba. 
Toilet ya shiga yayo wanka ya fito, shashin ladifa yayi ya shiga falonta, tana tsaye da doguwar rigar material green da black tayi kwalliya abinta tana ta kamshinta, haka falonta make tashin k’ashin tiraren wuta, tana kallonsa taji duk yana wani bata haushi, saboda ko ita abinda yayi bai mata ba. Amma sai ta dake. Kar zafin yayi mai yawa danta jiyo shi shida laila suna babatu. 
Sannu da zuwa tace mai tana wani basarwa, zama yayi akan d’aya daga kujeru, yace please “baby abani ruwa.” 
Amsawa tai ba tare data juyo ba. Dawo wa tai da gorar ruwan da pineapple juice ta ajje mai. 
Sai ta zauna agefensa, “abinci fa?.” 
“No barshi, sai anjima saboda magrib ta kusa, tabe baki tai tace “yayi.” Ya tambayeta “ina fuad?.“ Tace masa “yana wajen baba saude dan yana son matar kullum yana wajenta.” Murmushi ya yi yace akarbo minshi na ganshi.” 
So take tai mai magana kan abinda ya faru, sai kuma ta kasa dan tanajin tsoron fadansa, amma kuma tana son tayi din, sai taja numfashi tace “zauji,” 
Ya kalleta tare da kafe idanuwansa akan fuskarta zuwa labbanta dake kyallin man baki “ina jinki.” “Ka yi hakuri da abinda zance, haka kawai indan ban fada ba bazan ji zuciyata tayi wasai ba, game da zancen hansatu ne, gaskiya bai dace ace ka biyewa ‘yar aiki ba har kana zuwa 
dakinta, a matsayinka na shugaba agidan nan.” Kallonta yayi yace “kema korafln zakiyi kenan?.” 
Sai ta girgiza kai ba zanso shaidan ya rinjayeka ba, ba zan so ka afka gonar daba taka ba, domin duk abinda ya sameka muna ciki, mune farkon masu jin ba dadi saboda ba zamu so
ace wataran azo wani yayiwa yaranka ba, duba har mun fara tara yara fa.” Hannu ya daga mata “kema kin dau maganar da laila ta fada ko?.” 
“Ai ko bata fad’a ba na sani, duba da irin kallon da kakewa hansatu, wadda tafi mu? kuma mai mana hidima. Duk da cewa dai itama mace ce ‘yar adam amma bai dace ba. Gaskiya ni banji dadi ba, kai gwanda ace ma aure zaka kara akan wannan abin da kai.”. 
Kwantar da kansa kan dokin kujera, yayi ya kalli sama “shi tunanin ma hansatun yake, yaya taje gida yaya take ciki. 
Tsaki yayi ya ce “problem.” Ya kalli ladifa yace “koma menene ku ku kuka kawo yarinyar nan, dan haka babu ruwana.“ “Au! haka ma zakace, ai shi ke nan Allah ya bada sa a.” 
Sai ta tashi ta mike, da sauri ya kamo hannunta ta kijuyowa, kuma rike hannun yayi sai ta juyo tace “nika sakarmun hannu dan Allah babyna zan dubo. ” 
“Oya zonan niba babynki bane kenan.” 
Juya mai ido tai dan tasan waske wa yake neman yi, da karfi yajanyota ta fadajikinsa suka fuskanci juna yace am”sorry my love life, kinsan ayanzu dai babu fushin wanda bana son gani bayan na mahaifiyata sai naki ko. To please adan rangwanta min kar zafin yayi mini yawa, babyna na san ke mai sona ce.” 
Tana kaunar mijinta, tana sonsa sosai, amma yakan gudanar da harkokinsa ba tare da yasan za ta shafeta ba, yakan yi komai ne cikin gadara, ta rigada ta sadaukar kawai haka nan mijin nata yake, dole dai hakurin nan shine za tayi shi, domin in tace zata bijire mai za taiwa Allah butulci kenan, saboda ada babu yanda za ai ramadan yayi mata laifi ya bata hakuri, idan ma zata kwan tana fushi ba zai damu ba, amma yanzu fa, sai dai ta godewa Allah.kome ma zai faru ta san duk zafin da za taji ba zai kai na laila ba. 
Numfashi taja tace “kana da yakinin hakan shiisa kake abinda kake so ko? amma ai kasan masoyiyar zuciya ba zata so ta ga wanda take wa dokin so yana aikata abubuwan da basu dace ba k0.” 
Daga mata kai yayi yana wani irin killer smile dan yarinyar kan burgeshi da irin baiwar hikimarta da iya tafi da shi. Jelar gashinta ya ci gaba da wasa da shi yace “inajinki..” 
Sai taci gaba “to a yayinda duk ya aikata wani abin zuciyarta ta kanji kamar ta fashe, yakamata ya tausaya mata yasan cewa fa bata bukatar irin abubuwan nan, ita mai mara mai baya ce aduk wani abu da zai yi indai halattacene agun Allah shi ya halatta, amma ba za ta taba mara mai baya ba aduk wani aikin haram da Allah ya haramta.” 
Hancinta yaja yace “sai iya tsara kalamai kamar ita ta kerasu.” 
Fari tai tace “Nidai kawai kaimun Alkawari.” 
“Naji ba zan kara ba ko to ai min murmushi.” Sai tayi mai dan murmushi ta tashi ta sauka kasa. 
Da kallo yabi matar tasa abar sonsa, sai kuma yaja numfashi ya shiga ayyana abubuwa da yawa aransa shi dai har ga Allah yana son hansatu, ga shi yanda yanzu yake jin wani irin zugin sonta, gashi kuma baby ta kashe shi dajinin jikinsa, sai yaji yana ma jin kunyar yakuma hada ido da lad’ifar. 
Tashi yayi jin an kira sallah. Sai yayi Alwala ya sauka k’asa yai kicibus da laila zaune akan 
kujera, sai ta dauke kai tana huci, dan ji take kamarta hadasu ta babbake shi da hansatu. 
Bai bita kanta ba ya fice. Ita kuma tai kwafa hannunta rike da najwa tana shayarda ita, wanda sai sakin tsaki take akai akai. 
Al’amarin hnasatu kuwa tana zuwa garinsu ta shige gidansu ta sakijaka hip akasa,ta rusa kuka inna dake daki ta fito da muflci a hannunta zaninta har yana kuncewa tace “lafiya 
meya faru ne hansatu.“ Fasa kuka ta kuma yi tace “sun koro ni gashi ko kudin aiki ba su ban ba.” “Ke meya faru suka koreki?.” 
“Wai dan anty laila ta ganni da maigidan yanai min magana shine yau da safe tai min duka tace na bar musu gida.” 
Ke barta, ina da yakini akan aikin boka wallahi dole zai biyoki zauna nan.“ 
Kuka sosai ta ke tana mamakin abubuwan daya sanya maza kesan yi mata haka gida uku kenan da tai aiki tana fuskantar irin wannan matsalar, gidan da tai aiki a kaduna ta bar aiki 
a gidan ne adalilin maigidan dake son sai yayi iskanci da ita, dan karara yake nuna mata yace zai bata kudi, dalilin haka ta bar gidan. 
Gida na biyu kuma a Abuja kanin mai gidan saurayi shi ke san lalata da ita, karshe ta fadawa matar gidan aka karyatata, suka koreta, sai yanzu gidan ramadatha bata san 
meye tattare da ita ba suke san lalata da ita. Amma wai duk da hakan mahaiflyarta bata daina turata aikatau ba. 
Numfashi taja tare da share.hawaye Sai da uwarta hada mata ruwan wanka na dumi ta gasa jikinta 
saboda tsabar dukan data sha. 
Wayar hansatu yake ta kira, amma taki shiga duk yabi ya damu kansa tunda suka sallamo daga masallaci ya kasa shiga, bai sani ba ko rashin network ne oho, dan ya san kauyukan nan dole a rasa wadataccen service. 
Bayan kwana 2 
Yau da ya kama weekeed ramadan ya yi shirin zuwa kauyen su hansatu, dan jiya ya sameta a waya tai mai kwatancen garin nasu. Bai sanya manyan kaya ba, sai yayi ahigar kananu. Saboda yanayin zafi karfe goma ya ce musu za shi wani wuri, laila duk hankalinta ya kasa kwanciya dan tun da abin ya faru idonta yake kansa, ko fita yayi sai taji ba dadi, karma yaga wata yace yana so, dan tana da yakinin tunda ya fara haka da wuya in bai kara aure ba,gajego ga shi jibi za tai arba’in. 
Har ya fice wajen sha daya laila na zaune ta rafka tagumi , baba saude ta fito ta mika mata najwa da akai mata wanka sai kamshi take, kallon yarinyar ne ya sanyaya zuciyarta, soyayyar da ta keji na babyn nata na shigarta, shi ya dan rage zugin da ta keji ta aranta. baba saude ta zauna agefe tace “abinda nake so ki bude kunne kiji shine;ki cire duk wasu damuwa da kishi tunda ai an koreta, kinga haihuwa kikai yakamata ki gyara kanki, duk da dai yanzun ma kina kan gyaran, amma daiki dage atoh. Ayanzu tunda kika haihu tofa sai kin kara da hakuri ta bangaren mijinki da yarki.. ‘ 
Ki share komai, gobe kije ki gyara jikinki,jibi ma haka, mujinki ya ganki fes! atoh kina dai ganin kishiyarki kamar ba ita ce ta haifl yaron nan ba, wani ma sai yace budurwa ce dagwas dagwas da ita, kullum cikin walwala bata sanya komai aranta , amma keji bi fa kwana biyu kawai akan dan sabani kin tada hankalinki, duk kin koma wata iri, toki hankalta, dan wallahi namiji da kike ganinsa ba a sanya shi balle a hana.” 
To kawai lailan tace dan ita kanta tana bukatar hakan. 
Ladifa kuwa hankalinta kwance take gudanar da komai nata, kuma take farantawa mijin nata a haka, dan tayi alkawarin ta daina sanya komai aranta. 
Sai daya tsaya yayi ma hansatu kayan kwalam! sannan ya karasa garin dakyar ya gane gidansu. Yara sun baibaye motar ana ta kallo, mata sai lekowa suke ta katanga suna kallo, 
wasu ta kofa saboda sunga ya tsaya agaban gidan ladi masifa. Tsaigumi sai cinsu yake. 
Shi dai ramadan kawai sai ya samu kansa da kasa fitowa saboda yanda duk yaga garin wani irin sai ya shiga godewa Allah kan irin niimar da yayi mai. 
Hansatu ce ta fito daga daki da sauri tace “inna yana waje yazo.” Washe baki tai tace “to maza je kiyi wanka.” Inna ina zuwa tace “dalla tsaya a haka zaki ne?.” 
“inna kin manta nayi wanka fa, tunda yace ya tawo. Ke dalla rufen baki ai yaci ace ki canja,” 
“To inna bari naje na gani, ta fita. 
Yana cikin motar da yake me bakin glass ce sai ya kalleta ta ciki yana danna waya. Kasa tai ta tsugunna ta gaida shi bude motar yayi, da sauri ta sunkwi da kai saboda yanda gabanta ya fadi alal hakika sai taji ta raina kanta tana ganin anya batai azarbabi ba! ko abirnin ma macen data samu wannan zankadeden, ai tasan ta taki sa‘a, balle ita, sai taji 
jikinta yayi sanyi.Sai ta tashi ta koma gidan kan za taje dawo 
Ta shiga ta yarda hijabin ta ce “inna gaskiya ni sai naji yama ban tsoro wallahi kamar nai azarbabi.” 
Kallon gaula inna tai mata tace “ban taba sani ke shagira bace sai yau.” 
Umma kin ganshi kuwa? ulhmm! bari dai naje na kara wankan nima nai fes! ai wallahi umma daga yanzu sau biyu zan dinga wanka kullum, ke kinga matansa kuwa? hmmm musamman uwargidan kamar yar india kyakkyawa ce.” 
“Ke dallah yimin shiru, shashasha, kin zauna kina koda kishiyarki. Yo ai nasan ko tafl ki kyau, wallahi sai dai ko ta fiki a fuska, amma ba dai jiki ba, saboda Allah ya kera ki, ni kije kiyi wanka kawai .” 
Da sauri taje tayi, ta dade tana durzar jiki, sannan ta fito tana fitowa ta shafa manta irieiren wanda ramadan ya sayo mata ta farfesa body spary da turare wanda duk shi ya sayo, ta sanya riga da siket din daya taba sayo mata, laila ta hanata sawa, ta dauko hijabinta da shima dai shine ya hado mata akayan, bama ta taba sanya wa ba, ta sanya ta fito fes! kai baka ce wai a kauyen take ba dan kalar birni ce. 
Washe baki inna tai tana yabawa ‘yar tata, da sauri ‘yar ta fice bata dade ba ta dawo ta cemai, wai kinji zamuje cikin gari ya sayo mana kayan abinci.Amma inna kar fa yan gulma su ladiyo su gannni.” 
Guda uwarta sanya tace “jeki dukdan uban da ya tanka ni da shi ne agarin nan, ba maici dake balle ya sha dake, nice nan dai nake fafatuka, atoh jeki.” 
‘yar ta fice a dadarare ta shiga gaban mota ta baya saboda kallon jama’a shiyasa ta shige ta daidai murfun kofar gidansu, wanda babu wanda ya kula kuma tana da bakin glass. 
Barin wajen sukai har suka hau kan titi dodar! sanyin Ac sai bugar hansatu yake tana ta lumshe ido, duk da cewa ba yaune farkon shigarta mota mai ac ba, sakamakon gidajen aikin da tai duk na masu kudi ne, sukan shiga mota in zata raka matar gida unguwa, amma sai taji wannan yafi mata dadi kodan tana son ne motar ne. 
Wani fili mai bishiyu da dan dama ba mutane ramadan yaja gefen wata bishiyar mangwaro ya tsaya, da alama wajen hirar wasu mutananne . Yana kashe motar ya kalleta yace “hafsa. 
Sai ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuska.” 
Yace “shine kika gudu ko?.” Tace “aaa ai anty ce ta koreni.” “Kin taba makaranta?.” Ya tambayeta 
“Na fara firamare har na kai aji biyar, sai aka cire ni na tafi aiki, acan gidan aikin dana fara 
ne aka sanyani a makaranta na karasa naje har aji d’aya na sakandire.” 
Kallonta yake sosai, musamman yanda tudun kirjinta suka fito sosai ta hijab din jikinta, shidai yana mamakin yarinyar nan gata bamai shekaru da yawa ba. 
Gabansa ne ya fadi, tuno laila musamman cikon nan da tai, sai ya samu kansa da cewa hansatu ta cire hijabin jikinta ya ganta sosai. 
sukuyarda kai tayi ta kasa cirewa. 
Cewa yayi bakya son muyi auren kenan, ina mata ke kunyar miji.” sai ta cire masha Allah ya ambata a zuciyarsa, musaman ganin yanda kirjin suka ciki kamar su fasa rigar,, rigar tai mata tsantsan ajiki ga kugunta ya futo sosai akayan, ga shafaffen ciikinta daya dada sanya rigar tai mata das!. 
Cewa ya yi ta bashi labari. Nan ta shiga bashi labari na kauye kala‘ kala yana dariya, sai ya juya ya dauko leda abayan kujera ya bata, yace ta dauko iceream ta sha nan ta dauko ta bude ta aje ledar agefen kafarta, ta bude ta fara sha, shi kuma yana danna waya, aloakacin kiran laila ne keta shugowa sai yaki dauka, dan yasan masifa ne zatai mai ita ko tana can ta kasa nutsuwa gani take kawai wani wurin yaje ya sanya wayar a silet yayi ya ajje gefe ya kalli hansatu sai sha take tana mirmushi. 
idonsa sai karakaina kawai yake ajikinta, runtse ido yayi ya juyar dakai dan tarin sha’awarta dake damunsa ce ta taso mai, karbar robar yayi ya ajje a gefen saman gaban motar wanda hansatu ba tai zato ba taji ya shiga yi mata wasu kalolin abubuwa,jikinta ne yayi lakwas ta kasa hana shi, shi kuwa duk ya canja, ya dade yana chakuda hansatu, sai can ya saketa da sauri ya daki sitiyarin dake gabansa. Yana maida numfashi itama kuma ta sunkwi dakai tana jan munfashi ta sanya hijabinta gabanta sai duka yake, ga jlkinta na rawa.
Tuno nasihar umma dana babynsa ladifa ne ya sanyashi dakatawar, nan da nan yaji ya fara istigfari, tabbas dama muddin mace da namiji suka kebance waje daya shaidan ne na ukunsu, wanda zai ta kada musu ganga, yanajan hankalinsu, tare da kawata musu kawunansu. 
Dan tsaki ya sanya yajuya motarsuka barwajen, yana ayyanawa aransa dolene yayi wani abu, neman auren hansatu zai nema agidansu ya huta kuma asatin nan. 
A wani shago da ake saida kayan abinci ya tsaya ya siya da yawa yaja ya tafi,har kofar gida ya kaita ta fita ta shige da sauri, ya bita da kallo yana murmushi, wani ya kirawo daya zo wucewa ya bashi damarshiga da kayan. 
Sai da ya shigar da shi tas! ya bashi kudin ladawa, sannan hansatu ta kara fitowa yace mata zai tafl zai dawo neman aurenta, ta kuma dage tai chargin waya ya bata kudi ya tafi. 
Hansatu asoro ta tsaya ta tsugunna ta saki kuka dan abubuwa biyu ne suka taso mata lokaci daya, bataso ya tafi ba, tana sonsa sosai,ji take zata iyayiwa matansa biyayya idan har idan zasu bari ya aureta. 
Sai kuma na biyun tuno surajo. Ko jiya da yazo yake mata zancen an fara fitar masa da bangarensa agidansu.” 
Kuka ta kuma sanyawa ta shiga addar Allah ya sanya karwannan dalilin ya hanasu aure ita da ramadan dan tasan tabbas akwai badakala. 

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]